Yar tallah26

                *YAR.   TALLA*

                *CHAPTER26*

Da wautata na sanar da shi gudu zanyi don anKi aurar min da Bala, kin ji wauta fa wai ni duk a sona na son ya barni in shiga mota in tafine, naji karan motar na fadar, “Kano saura daya! Kano saura daya! !”
Kawu ya shiga. lallashina tare dayi min alqawarin shi zai tsaya min a yi min auren, haka ya rarrashe ni ya zaunar dani cikin
kasuwar ya gama saida kulinsa, a lokacin har rana ta fito sannan yazo muka hau mashin « muka dawo gida. , A lokacin da muka iso gida karfe sha , daya na safe ta wuce muna shiga gida muka same su hankali tashe an zagaye garin ana nemana hankali a tashe; Muna shiga Kawu ya basu labarin komai Baba ya shiga godiya, shi kuwa Yaya Sani da haushi ya kumeshe shi bacin yawon da yaci na nemana,
‘ saka kafa yayi ya fice yanajin zuciyarsa tamkar zata fashe saboda tsabar takaici  Babama yasa kai yayi tafiyarshi da kawu‘ Ummaru suna jajanta lamarin, Ummata kuwa wadda takaici ya kashe zuba min idanuwa tayi tsawon lokaci tana kallona kafin ta hau fadar, ‘ “Uhum, qalu innalillahi  yanzu mariya abinda kika zabarwakanki kenan? Ke yanzu harkinsan kitattara kaya kibi namiji Mariya yanzu har Bala ya iya hure miki kunne ke nan k0? Dame muka rageki agidannan meki ka nema kika rasa?” Na zumburo baki kafin inyi maganar data
tunzura Umma.
“Yo  da abinda aka hana ni in banda Bala?”
Umma ta watso min harara kafin tace, “Balan banza da wofi, Bala har sa an aurenki ne in bacin kina hauka, yaron da k0 sakandire baiyiba, firamaren ma bai kammala ba”. ‘ Na dauke kai ina fadar *‘Ai dai ya iya karatu da rubutu”. ,
Haushi ya kashe Umma ta wawuro  takalmin qafarta tajefoni da shi tana fadar.
. ‘Tashi ki bani wuri ‘yar iska mara kunya zanga ta tsaurin ido wallahi duk, duniyar nan babu uban daya isa ya aura miki shi in dai ina raye, sai fa idan guduwa zakiyi, to wannan fa! Amma wallahi baki aurensa”. Haushi ya kama ni jin ikirarin da Umma keyi, cikin takaici ina tunanin yadda za a iya hana ni auren Bala lallai kau ba a isa ba, kinji fa
.. wauta da sakarci.
Ashe abin da bamu sani ba Baba yana can kai tsaye gidan su Bala ya nufa ya yi sa’a ya iske mahaifinsa zaune saman tabarma a qofar gida suka gaisa, Baba yace “Da ma jiya naz0 baka nan, to dama ba wata magana bace ‘ maganar danka ne Bala, nasan baka san abin da dake faruwa ba. ,
Bukatata a nan ni dai daya ce, don Allah ka aika a kira makwaftanka guda biyu suzo‘ yanzu ina son mu daura auren Mariya ‘yata da danka Bala ammafa kayi haquri nazomaka da magana haka gagab, akwai abin da na
hango mana ne wanda dani da kai duka ba zamu ji dadinsa ba, don na san ba kasan danka na zuwa wurin yata ba, kamar yadda nima ban > san tana fitowa ‘wurinsa’ ba, amma yanzu tunda
na gani da idona to mafi alkhairin abin shine a ‘ ” halasta musu juna tun kafin su aikata abinda bai kamata ba Malam Mai tumaki mamakine ‘zuba a fuskarshi  idanunsa cike da mamaki kafin yace ‘Wallahl tallahi ban san abin dake faruwa, amma don Allah kayi haquri, ka natsu muzo muyi abin nan a tsanake Bala dai danka ne, kuma Mariya ma yata ce Baba yace, “A’a Malam kar muyi haka da kai, ka taimaka min don Allah don Annabi ka kira makwaftanka su zama shaidu in sauke nauyin dake kaina Malam Maitumaki yace, “A‘a ai gaggawa aikin shaidan né, kuma aure dole saida’ sadaki”.Baba yace “Ga Wannan naira dubu biyar ce na biya masa ‘ Malam Mai tumaki  Ya bude baki zaiyi magana Baba ya tsaida shi da hannu yana fadar, “Don Allah kar ‘kace komai ka yi fatan alkhairi kawai”: yace To “Allah ya saka da alkhairi Baba yace:“Amin”
Daga nan aka aika kiran makwabtansu :
‘ biyu suka hadu da Baba da Kawu Ummaru da mahaifin Bala aka daura mana aure a kan ‘sadaki naira dubu biyar sannan kowa ya watsé. ’
Baba ya dawo gida a lokacin ina daki na tasa buhun kayana a gaba na rafsa -uban tagumi, naji an Kwallo min kira, na kwaso da sauri na fito jin murya Baba. ..
Ina zuwa na ganshi tsaye a tsakar gida, tun kafin in Karaso yace, koma ki dauko hijabinki ki fito mu tafi
Na danyi jim ina kalonsa ya dan daga murya, “Nace kizo muje k0?”
Na juya da sauri na koma daki na dauko ‘gyalena na fito, Umma ta dube shi tana fadar, “Inazakada ita Malam ?”
Ba tare da ya dube ta ba yace, . “Gidanta”’ Umma tace, “Ban fahince kaba Malam”.
Ya waigo yana kallonta kafin ya ce “Gidan aurenta zan kai ta an daura aurenta ‘ ~ ‘ yanzu ita da Bala, gama sadakinta
‘* Ya mika min kudin
~ Dukda tsaurin idona da tashen balagar tauntsayen dake kaina saidanaji gabana ya fadi namika hannu dakyar nakarbi kudinda ya mikomin na saurara abinkamar almara, Umma tahau Sallalalami harda kwallanta tana
fadar
Yau na shiga uku ni Binta, yanzu Malam bintakan maganarkayi kadaura mata auren?” ‘ Baba ya watso mata wani kallo kafin yace,”sokike ingirketa agidan ina kallonta taje ta jajibo mana abin kunya a gari k0 me?” , Umma ta qara rushewa da kuka, ‘Wayyo Allahna shi kenan ta faru ta Kare, kin samu abinda kikeso,amma wallahi tallahiki sani bada yawunaba wannan aurenkuma wallahi karki sake ko a hanya ki nuna kin taba haduwa da mai kamannina, babu ni babu ke har abada”.
‘ Baba yace,”‘Kaji zancen banza, ke da zakiyi mata addu’a kuma saiki hauyimata mugun alkaba’i? ai ke da ita sai dai fatan
alkhairi yanzu tunda kin samu kin rabu da ita lafiya
, . Umma wadda takaici da bakin ciki ke cin zuciyarta ta duqa ta suri Zuwaira tayi gaba tana fadar “Ai kuma sai dai kayi da wani ba
dai Binta ba”
Ta yi gaba tana sharar kwallarta. .
Baba yace, “Ke taso muje kinji”.
Ni kuwa na mike cike da farin. ciki da dokin yau na samu abin da nake so. Muna ‘ ,zuwa qofar gida muka hadu da Yaya Sani ya rako a guje yaja ya tsaya kamar zai fada Wa Baba yana ta faman haki Baba ya dube shi. ‘
“Kai kuma lafiyarka?”
Yana faman shessheka ya hau fadar, “Wai da gaske Baba an daurawa Mariya aure
,da Bala?” Baba yace “Eh an daura mata, wani abu ne?” * Idon dana kura wa Yaya Sani yasa na tabbatar da duk‘wata lakka ta jikinsa ta tsaya idonsa ya ciko da kwalla, muryarsa a“ ‘ sanyaye yace, “Amma Baba bai kamata a. Bawa Bala auren Mariya ba, don bai biyo ta ‘ hanyar da ta dace ba wurin neman aurenta .
Baba. Mariya yarinya ce mai kwakwalwa da . haZaKa irinta gwamnati ke nema don daukar
dawainiyar karatunsu don taimakawa yan uwansu mata, musamman a bangaren asibiti Baba Bala bai dace da Mariya ba don bai san muhinmancin karatun boko ba, asalima ba shi da abin gaba daya Baba ya nisa kafin yace, “Nafika sanin haka Sani, amma kada ka manta wacce kake
’ son kayi yaqi don inganta rayuwar tata bata san kana yiba, bata da wannan‘ burin, ra’ayinta daya aure, shin me zaisa mu tauye. mata hakkin ta? Kana tunanin idan naKi aurar da ita Allah ba zai kama niba? Wallahi Kinyi mata auren nan Sani sai ya zame min abin ‘ bibiya a gobe qiyama, shin kaga laifina donna sauke amanarAllaha a kaina ?‘ ”
Yaya Sani ya girgiza kai wanda hakan yayi daidai da zubar tarin hawayen da suka Cika kwarmin idanuwansa, ya juya ya shige gida ba tare da yace min Kala ba, sai a lokacin zuciyata ta dan karye kadan nabi Baba muka ““tafi zagarai-zagarai daganisai shi, har zuwagidan
““su Bala Kinji fa Wani irin  kai amarya a nan bahu yan rakiya duk da a addinance hakan yana da
kyau.
Muna zuwa gidan su Bala Baba yayi sallama da Babansa, ya mika masa ni. Mahaifinsa yace ai Bala yana ciki bari a kirawo shi yanzu ya dawo daga kasuwa. Ya shiga sai ga shi ya dawo shi da Balan, ya zube
gaban Baba yana faman godiya.
Baba yace, “Ya isa haka Bala, ai bani zaka gode mawa ba, ka gode wa Allah kawai, don’Shi Ya‘ baka Mariya, don haka gata nan amana a wurinka, ka sani idan ka zalunce ta k0 ka ha’ince ta don kana ganin kamar sadaka ce a wurinka sai Allah ya kama ka, ni dai nauyi ne da Allah ya dora min, kuma ba mutane ba kawai hatta mala’iku sun shaida na sauke don haka na barku lafiya”.
Bala ya hau godiya shi da mahaifinsa, Baba ya juya yayi tafiyarsa ya barmu, mahaifin Bala ya juyo kanmu yayi mana nasiha sosai, sannan yace yaje ya gyara mana dakinsa mu zauna.
‘ Haka ya juya ya nufi cikin gidan, nabi Shi a baya ina kallon gidan don ban taBa shigowa ba saboda babu mace a cikin gidan,
mahaifiyar Bala tun yana dan shekara sha’ ~biyar ta‘ rasu,s shi kuma mahaifinsa bai Kara aure
‘ba saboda ya. tsufa sosau, girma ya kama shi,‘ ‘ ‘ don lokacin da aka haifi Bala. ma har ya cire rai . da haihuwar a duniya sai gashi Allah ya azurta shi‘ da Bala, daga shi kuma bai sake ba ‘ Allah ya yiwa mahaifiyar tasa rasuwa.
‘ Gidan ginin kasa ne, amma bai sha jiki sosai ba, yana dauke da dakuna uku, daya na mahaifin Bala, daya na Balan, daya kuma na ajiye~ajiyensu, sai qaton tsakar gida shareren gaske wanda aka raba biyu ana kiwo a cikinsa, sai qaton iccen bedi a tsakiyar gidan mai malalan kasa don babu sumunti.
‘ Bala ya tura kyauren dakinsa ya juyo yana min alama dana shiga, kamar karna shiga har sai daya sake yimin magana sannan na daure na sa qafa na shiga cikin dakin, ba wani mai girma bane sosai, yana dauke da katifar maza wadda aka lullube da bargo sai dan karamin tebur wanda aka dora wata ‘yar qaramar talabijin da bidiyo a sama.
Shi kenan abin dake dakin, sai ‘yar hanga ta katako wadda aka sargafe kaya sannan
‘kafet din daya mamaye dakin, wanda yaci  uwar qura. Kin san abinki da samari  bazaki taba tabbatar da tsabtar saurayiba saikinga dakinsa Hmmm lol
gayu a. ganku a .titi kar a ganku a masaukinki
Saudat in takaice miki haka na zauna dakin nan na gyara shi tas-tas kamar ba shiba, washegari Bala ya fita kasuwa yayi mana siye-siye, tun daga kayan abinci har zuwa na sawa irin wanda zamu bukata. Da kayan shafa wanka, turaren wuta, sabbin labulaye, karamar radiyo, Saudat haka Bala ya dawo da kaya niqi-niki don a lokacin yana samun kudi sosai saboda tun daga Dandagoro har zuwa cikin unguwarmu babu wanda ke saida kayan koli sai shi, don haka yake samun kudi sosai.
Sannu a hankali lokaci ya shiga tafiya
Saudat ina ganin , soyayya, qauna da kulawa fiye da yadda baki zato, hatta mahaifinsa idan ya tafi kasuwa ya dawo da kunShin nama na. Yake dawowa
A haka harna samu ciki, irin mai masifar laulayin nan kamar bana kai ba, amma daga gidanmu babu wanda ya leko yaga ya nake, da Bala yaje ma Yaya Sani wulakanci yayi masa, don haka ya dawo gida cike da takaici, ya fada wa mahaifinsa shine shi kuma  ya bashi shawara da yaje ya dauko diyar
Qanwar mahaifiyarsa  Laure wadda aurenta ya mutu take zaune gida: ”
‘ Bala ya amince saboda  jin jikin da ‘ nake, bana iya yiwa kaina komai  ‘haka ya tafi ya dauko min Laure, aka gyara mata dayan dakin ta zauna.
Laure ita ke kula dani, duk wata dawainiya tawa ita kemin, tana gefe tana kallonmu nida mijina duk abin da nake so shi yakemin inamai ’ tabbatar miki babu abin da’ zai hana a kawo‘ shi.
’  Idan kuwa nace ina son abu jikinsa har rawa yake yaje ya samo min k0 a ina abun yake daya shigo ya rinka tambayar Laure ya nake, ya jikina da sauqi dai k0? Naci abinci k0 banci ‘ ba? Idantaceban cibaba hakazai zauna yatusani agabayana rarrashi kamar zaiyi kuka har ya sai ya samu naci, haka mahaifinsa idan ya tafi kasuwa zai siyo min wannan kawo min wannan, ke naga gata da soyayya.
A haka Saudat cikina ya cika wata biyar na huta da laulayi a lokacin ne kuma naje gida ni
da. Bala, amma Umma k0 kallonmu ba tayi ba ita da Yaya Sani suka watsar damu a makar
gida sai ZuwAira ce wadda ta fara tafiya ta tattako ta maqalqale ni na rungume ta ina jin SOyayyarta a zuciyata donni a wautata” wai gani nake ita kadai ce ke sona, bata guje niba, haka na qaraci zamana na tashi muka dawo “ gida bamu ma tsaya Baba ya zoba . ‘
Wulakancin da aka yi mana yayi wa Bala ciwo, haka yayi ta maimaitawa ni dai Ina jinsa ban tanka ba, don idan da zai tona tawa .zuciyar na san daya tabbatar tafi tasa hawa da jin zafi, ni a ganina k0 don kyau da sauyawar da nayi yasa Umma ta saurare mu don ta’ tabbatar Bala yana sona sutturar kanta danaje gidan tsadarta ta hau dubu goma a lokacin kuwa dubu goma ba nan ba ce, kayan ‘ dubu goma sai dai dan wane da wane, amma hakan bai sa Umma ta duba qokarinsa ba ni kaina ta san ai na canza don nayi dumurdumur dani, haske naya Kara. fitowa na zama kamar wata. baturiya saboda kyau, ba yadda muka iya dole na share na manta, sai dai Bala ‘ bai .mance ba don duk lokacin da nace masa zan’ je gida sai yace ban ‘zuwa ba yadda zan yi . a haka nazo na haihu, babu wanda yazo ta Bangarena
gidanmu, sai dai Babana daya zo har gida yaga ‘ jariri yayi masa addu‘a, ya bani ‘dubu biyu da niki niqin kaya sannan ya tafi, daga shikuwa k0 kare bai ce komai ba. ‘
Sai dai Laure ceke dawainiya dani ita ke dora min sanwar ruwan zafi safe da yamma ’ta kwashe ta kai min kewaye ta yiwa jariri wanka, ta yi girkin abinci a gaskiya a lokacin ta yi dawainiya kodayake ta saba da wahala tunda a can gidansu wankau take na kudi da surfani.
A kwana a tashi har na yaye Rabi’ u, ban Kara zuwa gida ba, a ganina tunda sun Kini nima na manta da ~su kinji wauta fa, ‘ haka rayuwa taci gaba da tafiya tamkar bani da ‘ iyaye a garin, saboda Bala ya bar min Laure itake min komai na hidimar gidana iyakata ni dai inwanka nida dana mutafi wurin maigida., Ashe abindaban saniba Laure tana nan tana jin haushinmu kamar ya kashe ta nik0 sakaran ban taBa sani ba, don banyi zaton zata iya jin haushinmu ba, saboda yadda nake ‘ ‘ kyautata mata nida maigidana.
. Lokaci na  tafiya ban sake haihuwa ba a tsawon shekara bakwai a lokacin ne kuma
mahaifina ya rasu, to a nan ne na danyi hankali na dauki dana muka tafi gidanmu na zauna a can har sai da aka yi sadakar uku duk yadda Ummana ke shasshare ni sai data tanka min duk da ba wata maganar arziki bace muka yiba anagama sadaka na tattara na koma gidana, to a nan fa labari ya sauya don ban sani ba ashe na bar baya da qura, haka kawai naga Laure na min wani kallo-kallo, gashi shi kuma uban gayyar ya hau shasshare ni da nayi masa magana sai ya hau ni da fada dana yi laifi da ban yi ba duk daya wai anyi wa tuwo Barin miya. Inji hausawa
Abin duniya duk ya dame ni ya ishe ni, gashi ba ni da wanda zan fada wa matsala ta, a haka dai nayi ta hakuri ga shi a lokacin ban
san na samu cikinki ba, sai da laulayi ya matsa min, amma Bala ko a jikinsa ya watsar da mu baya kula mu nida dana balle abin dake cikina.
Rayuwa duk ta dagule min, na zauna na zama wata kalar tausayi, kin san halin da mace ke shiga idan miji ya juya mata baya abin ba dadi, sai dai in qule daki inyi jugum.
Ban“ taBa mantawa da ran Wata laraba ba ina zaune a daki shiru  ‘ Laure bata ,kawo mana abinci ba ga shi k0 abun karyawar ‘ da tayi mana da safe, ban samu cinsa ba nan na’bar wa Rabi’u yayi ta wasada shi ’har wurin uku na rana babu abinci babu dalilinsa‘ A dole na takarqare na mike na fice na shiga kicin din, sai dai abin dana gani sai daya so tarwatsa min zuciyana na tsaya turus ina kallon Laure wadda ta zabga uban goho ta takarkare tana ta faman barbada magani a kwanon miyar Bala, ban tanka mata ba har sai ‘ data gama barbade-barbadenta tas! Ta kawo cokali ta jujjuya miyar ta maida ta rufe, ta mike tana boye maganin a habar zaninta. Muka yi ido hudu, a take jikinta ya hau rawa ‘ tana faman karkarwa can kuma taja tsaki ta rabA ta wuce ta barni tsaye da. mamaki a zuciyata. ; Can na girgiza kai na dauki kwanon miyar na fito na zubar ’da ita, dama miyar danyar kubewa ce na dawo na zauna da’ kaina na takarkare na sake dora wata miyar’ ta
busasshiyar kubewar nayi na gama na debi * nawa na ajiye masa nasa da kyar na samu na ;
tuttura abincin amma zuciyata tamkar zata tarwatse.
Bayan la’asar Bala ya dawo. daga kasuwa tun kafin in fito kuma ta riga ni fitowa ta tare shi ta shimfida masa tabarma jikinta na rawa ta tafi ta kawo masa abincinsa da ruwan randa mai sanyi cikin kwanon sha.
A lokacin ni kuma na fito na tsaya daga bakin qofa ina kallon ikon Allah, Bala yaja kwanon miya ke nan ya bude suka yi ido hudu da miyar busassiyar kubewa yayi sa‘urin dago kai yana kallon Laure.
“Wannan miyar kuma fa? Bani na bada danyar’ kuBewa ba  nace a kawo miki ba, k0 ba a kawo bane?”
Laure ta karya kai cike da kisisima kafin tace, “To ai ‘yan bani na iya yau :su suka ‘ dauki miyar suka zubar suka shirya tasu ta musamman”.
Bala yayi saurin dago kai yana kallona.
, “Ban gane kin zubar da miya ba, kan wane dalili?”
Jikina yayi matukar yin sanyi ganinyadda ya zaburo min na daure na durqusa ‘ gabansa muryata a sanyaye :nace kayi haquri
Mai gida barewa  yayi ban sani ba
Shi yasa na sake maka wata, amma ina neman
wata alfarma a taimaka a maido girkin gidan nan wurina”. .
.  Bala ya zaburo, “Ke gafara can rufe min baki, ki dai ce wani mugun halin kika tsiro dashi, kuma wallahi ba zan dauka ba, ba ma zan laminta ba, tsabar almubazaranci kawai ki dauki abinci ki zubar saboda bake ke nemowa ba k0?”
Zuciyata ta kara ganin yadda Bala ya hau ya keta zuga min masifa haka, idona ya kawo kwalla na mike cikin kuka ina fadar, “Allah ya baka hakuri
Na juya na shige dakina na barsu. Ban san abin da suka kitSa ba, da zai fita ya . hankado labulen dakin ya leqo ya wurgo min dari daya, “Ga shi nan sai kiyi cefane a dafa taliya da daddawa, dama nasan dan sauran na saman kike mawa, toga shi nan sai ki dauka kiyita zubin adashe”. ‘
Ya juya yayi gaba abinsa’ya barta
‘ tana tattauna maganganunsa a bakinta tace haka na mike na ta Karkare duk da bana jin qarfin jikina na dora sanwar taliyar, na

*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*
*See y’all tomorrow by this time*

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE