Yar tallah27

              *YAR.     TALLA*

                 *CHAPTER27*

        *ASHA  KARATU LAFIYA*

Tace Na gama na dibi tawa data dana na dibar masa nasa na zuba na mahaifinsa na kai masa, sauran kuma na barshi a tukunya. Nayi gaba abuna, amma abin takaici da ya dawo nace masa ga abincinsa, sai ‘cemin yayi ya Koshi yaci abinci a waje. Haushi kamar ya kashr ni, amma babu yadda na iya haka na hakura nayi
kwanciya tana barshi zaune yana wasu ‘yan bincike-bincike na gaira babu dalili.
Washegari ma bai tsaya karyawa ba ina kicin ina hada mana abin karyawa yasa qafa ya fice abinsa ya ajiye min kudin cefanen rana. Ai ban san lokacin dana fadi qasa ba ina kuka wiwi wiwi na shiga uku yau na lalace. Babu mai rarrashina don babu ma Wanda yasan ina yi, na karanci kukana na share hawayen na mike na nufi katifa na raBa inda
Rabi’u yake kwance yana sharar baccinsa na ‘ kwanta, na rufe idanuwana dukda ba bacci nake ba, haka na dauki tsawon lokaci ba tare  dana bude ido ba balle in kalli abin karyawar ‘dana hadaBa
Rabi’u ya farka daga baccinsa ya dauki abincinsa yana ci, ina jinsa ban kula ta kansa ba sai kusan sha biyu saura sannan na mike
Ina rarrashin kaina na dauki kudin cefanen na aiki Rabi’u ya siyo min kayan miya da sauran kayan girki na zo na zauna na dora sanwar jalof din shinkafa da wake da alayyahu
da kifi. Zuciyata tayi ta tashi saboda qarnin kifin
Dan sau biyu ina rugawa bakin maguji ina kwaraya amai, amma haka na daure na kulle hancina da kallabina nayi girkin na gama, wani irin ciwon kai mai zafi da juwa suka sauko min, na nufi dakina na kwanta k0 motsin kirki na kasa, ga Rabi’u sai kwaramniya yake min’ a dakin yana wasansa.‘
Bala bai tashi shigowa gidan ba sai ana’ . sallar magariba, nayi kuka har naji ba dadi, amma yana shigowa haka na daure na dauki abincinsa na je na kai masa.
K0 lura yayi da rashin walwalata da alamun na sha kuka oho sai kawai naga ya bude kwanon , abincin yasa cokali ya debo ya kai bakinsa,  , idona na kansa naga ya Bata’ fuska tare da furzar da abincin bakinsa a tsakar dakina ransa a bace ya hau masifa
“Ke wannan wane irin iskanci ne? bakin. buhun gishirin kubce miki yayi kika kwarara shi a ciki k0 ko me?” ,
Da mamaki a fuska ta na maimaita, “Gishiri kuma?” Don nina sani a girkina ma babu ‘gishiri k0 kadan saboda‘ magin dana zuba yana da yawa, Bala ya zaburo min.
Sai kizo ki kwashe abinki”.
Na mike jikina a sanyaye na durqusa gabansa na sa ‘cokali na debi abincin na kai bakina, ai sai dai naji tamkar zan mutu lokacin
dana hadiye, saboda azababben gishirin dake ciki, zuciyata ta karanta min makarkashiyar da . ‘ aka yi min.
Na daure na dago da kai muryata a sanyaye nace
“Kayi hakuri don Allah, wallahi hannuna ne ya kubce, amma bari yanzu in dora maka wani abun mai sauKi”.‘
. Ya daka min tsawa.
“Ke tashi nan ki bani wuri,nizaki kawo wa feleke saboda bakin ciki, amma daga yau kin gama girki a gidan nan don na lura da wasu halayen banza da kike bullowa dasu kwanan nan kuma lllllll wahala wallahi
, don‘Laure dai ‘yar uwata ce, kuma ke baki isa ki shiga tsakanina da ‘yar uwata ba, wallahi”. ‘ Ya mike yana karo da kayan abincin ya fice yabarni nan a tsugunne. ” ‘ Kwallar data cika min idanuwa ta soma
zurarowa, wato ba zai iya rabuwa da yar ’ uwarsa ba saboda ni, amma ni na rabu da nawa ; ‘yan uwan da iyayen saboda shi? Wayyo Allah gani gare Ka.
Na kife a gurin ina wani irin kuka, sai yau na fara yin nadamar  da‘  bazaimin amfani, ba nayi kaico a rayuwata da son da ya rufe min ido.
‘ Yau nayi kuka kamar zan mutu, bani da mai rarrashina, har Rabi’u wanda ke bacci ‘ ya farka ya taso ya rungume ni, shima ya saka nasa kukan, a dole nayi shiru naja shi a jikina
ina rarrashinsa. ~ ‘ Saudat al’amuran suka ida cakudewa na. rasa wanda zan kai wa kukana, ina ji ina gani Bala zai dawo gidan ya shige dakin Laure su. sha hirarsu sai nayi bacci sannan ya shigo ya raBa ya kwanta bani da bakin magana kuma
, Ga shi Laure ta daina girki da wuri sai yamma, don ta san Bala baya dawowa da wuri duk na
bi na tsumbure na rame na lalace na fige abinki ga mai ciki.
Bala’in Bala ya ishe ni, ga yunwa naje na same shi ina kuka, nace ya fada min laifin da nayi masa; Ai k0 ‘ranar kamar ya hadiye ni ’ danya ban dahu ba, don kadan ta hana ya kawo min duka, haka na tashi ina kuka.
Na ‘ kasa haquri na tafi wurin mahaifinsa ina kuka na fada masa duk abin da ake min a gidan, ransayayi masifar Baci, don a lokacin shi ya dawo zaure ya bar mana gidan.
Ai k0 a take ya tisa ni gaba muka shiga cikin gidan, yace in wuce dakina ya nufi
dakin Laure yace maza ta tattara kayanta ta ‘tafi gida,aishi baisa adaukota donta tarwatsa zaman lafiyar ma’aurata ba. Ina jin Laure na ba shi hakuri, amma yace ina! Sai ta tafi, yana tsaye ta hado ‘yan komatsanta a cikin buhu ya bata kudin mashin tayi gaba a lokacin kar kiso ki tona‘ zuciyata kiga farin ciki, don ni a ganina annoba ta tafi. To ashe an kashe maciji
ne amma fa ba a sarekanba. Don Bala na dawowa ya leka dakinta ya
ga bata nan, ya leqo wurina.
* “Ke Ina. Laure ta take?”
Gabana ya fadi yadda naga fuskarsa ba annuri amma na dake nace.
“Kaje ka tambayi Baba” _
‘ Fuuu’ Ya Wuce ba tare da ya sake kula niba, ni dai nabi keyarsa da kallo, a zuciyata ina addu’ar Allah ya daidaita tsakanina da ‘mijina, kominti gomada fita baiyiba saiga ‘shi ya dawo kamar an hankado shi, ya tsaya a kaina yana zazzaga min masifa
“To marar mutunci, munafuka wadda bata qaunar zumuncin Allah, wato ‘yar uwar .tawa yanzu saida kikasa aka koreta daga gidannan? Tokinyi daidai amma inasoki sani wallahi baki isa ki raba ni da‘ yan uwana ba, don ke kina ganin kin rabu da naki” yan uwanbaki isaba, babu macen data isa taraba ‘ nida ‘yan uwana wallahi baki isaba”. ‘
Ya juya fuuu ya sake ficewa daga gidan gabadaya.
Saudat duniyar tayi min zafi, rayuwar ta quntata a gare ni, na yi kuka har kaina ya
dauki ciwo, amma babu mai rar-rashing ga ciki
a jikina. Abin duniya yayi min yawa Bala baya shigowa gida sai na kwanta kuma kafin in
tashi zai kakkaBe rigarsa ya bar gidan, ya ajiye min naira ashirin kudin cefanen miya ga shi a gidan babu abin da ya rage sai masara, haka zani wanketa inbada aniko mana inyituwon kwana biyu, sai dai in canza miya. Amma shi k0 a  jikinsa don baci yake ba, sai dai muci nida dana, don mahaifinsa ma yanzu fura kawai yaké iya sha, baya cin duk wani abu mai nauyi saboda ciwonsa don haka shi ma bai san abin da ake ciki ba.
. Wataranar juma’ a ina zaune a dakina bayan ‘“ na gama sallar isha’i ina karatun alkur‘ani mai girma, na ji shigowar Bala, abin ya bani mamaki lokacin da naga ya shigo dakin ya zauna bakin katifa.
Na tsaya da karatun da nake na shafa addu’ata sannan na waiwayo na gaishe shi ya ‘amsa fuskar ba yabo ba fallasa na mike a sanyaye da niyyar in kawo masa ruwan randa mai sanyi da abinci
ya tsaida ni ta hanyar fadar
* “Tsaya meza kiyi kuma?” Na dan waiwayo na kalle shi murya ta a
sanyaye nace. “Abinci zan kawo maka”.
Ya girgiza kai. “A a a qoshe nake, zauna ki huta abinki”. Wani irin abu ya nusar min zuciya. idona ya ciko da hawaye na koma na zauna tare da janye kwallar da ta ziraro a kuncina,
Bala yace. “Magana nake son yi da ke Mariya idan
kina da lokaci”
Ba tare da na dago na kalle shi ba, na ce
“Ina sauraranka”
Ya muskuta ya gyara zama kafin ya fara dogon bayaninsa
‘Mariya, kin dai san iya so na soki a duniya, kuma har yanzu ba wai daina sonki na yiba, don haka inaso kiwa abinda Zanfada kyakkyawan kallo da kuma kyakkyawar * fahimta kikuma bani hadin kai idan harkina son zamanmu lafiya, don yanzu maganar nan . da ake mun gama magana da Laure, zan auro ta za a daura mana aure nan da sati mai zuwa, har sadaki na ,bata don haka na yanke shawarar zuwa in fada muku keda‘ Baba da
fatan ba za a samu matsala daga wajenki ba
, ‘A lokacin ji nayi kamar yana caccaka min wuka a zuciya, idona ya canza kala, wani irin tukukin bakinciki ya sarkemin na mike a harzuke jikina har bari yake kamar wata‘ yar dambe na fara magana kuka ya Kwace min,
amma ban fasa ba “Lallai Bala kun cika maciya amana,
yanzu don cin amana duk ka rasa wadda zaka aura a duniya sai Laure? Wallahi ka cuce ni ka yaudare ni, ka raba ni da dangina da ‘yan uwana kuma Allah sai ya saka min
Ban ida rufe baki ba naji saukar wani gigitaccen mari a kuncina wanda yasa har sai da na duke, ya nuna ni da dan yatsansa.
‘ “Kenan harkin isaki zageni banza,  Kenan harkin‘isa hanani yin abin da nayi niyya? To baki isa ba, aure k0ki so k0 kada ki so yinsa za a. yi kin ji na fada miki”. Ya juya a zafafe ya bar dakin, ya barni tsugunne rungume da kunci’ na. ma rasa a ‘ duniyar’ da nake ranar maganar kuka ma babu
ita, don idanuwana sun kekashe ga shi ‘ba
damar in tafi gidanmu don na san Umma bama saurarena za tayi ba
Abin Allah sai ga shi yana zuwa wurin Baba ya hau shi da fada har yana kumfar baki yace ba da yawunsa ba, bai amince da wannan auren ba. Bala ya yi juyin duniyar nan Baba yaqi yaddah, a dole ya haqura don ba yaddai zai yi.
Sai dai zamana da Bala babu abin da ya canza don sai ma ya dauki gaba dani, yadda ki ka san ni .na hana auren k0 gaishe shi na yi ba ya amsawa, duk na bi na gigice na rame ga ciki ya fara girma amma rayuwa sai a hankali, ni da Rabi’u muna fuskantar quncin rayuwa.
A haka har cikina yazo ya tsufa na haife
Ki a wannan karon Ummana tazo ita da Yaya  Sani, hakan ya tabbatar min da sun fara saukowa dani. Ummana ta bani kyautar kaya niqi-niki, shi kuma Yaya Sani ya yi min kyautat kudi dubu biyar a nan ne na samu labarin ya samu Aiki a cikin birni a babban banki first bank har ya yi auransa a can na yi masa murna sosai. Sun dade sannan suka tafi, amma na lura sun dan fahinci halin da nake a ciki, domin Bala bai siya wa jaririya k0 hankici ba Babu kaya a jikinta cikin zanina na qudundune ta, data ce ina kayanta ‘nace Bala ya; tafi ya ’siyo yanzun nan. Ta hau fada haihuwa tun jiya amma ace ba a tanadi kayanda za a sawa yaro ba, babu k0 sabon dan goyo saboda sakarci? Ta Ciro riga guda cikin kayan da ta kawo min mai tsada ta saka wa jaririyar
Ranar suna kuwa Saudat na sha kuka har na godewa Allah, don Bala bai yanka rago ba abincin suna ma masara kawai ya bari tiya biyar ya kama gabansa, . har yamma babu labarinsa. Naci kuka har na godewa Allah
don nasan abin gori ne a gari a ce ba a yanka wa yarinya rago ba. Haka na ciri dubu uku da dari biyar cikin kudin da Yaya Sani ya bani na bada aka siyo min madaidaicin dan taure aka yanka, sai a‘ lokacin mahaifin Bala yasan ba a yi yanka ba, ya yi fada har ya gode wa Allah ya Ciro kudi daga cikin aljihunsa ya bada aka siyo tikekiyar tunkiya aka hada aka yanka da yamman nan likis gab da magruba.
Bala bai dawo gida ba sai qarfe sha dayan dare mahaifinsa yayi masa tatas har ’ yace zai iya tsine masa a kaina. Shi dai hakuri _kawai ya bada ya shigo gidan ya qare min tanadi da wulaqanci.
. Da safe kuwa sai cewa ya yi abin yanka biyu yayi min yawa ni dawa ban san yadda aka yi ba, ashe ya sabe tunkiyar ya fice da shi ya kai wa Laure. Ya barni da dan tauren
Ke Saudat naga bakin cikin rayuwa don a lokacin ji na yi tamkar in hadiyi zuciya in mutu k0 daidai da rana daya Bala bai taBa .. cewa a kawo ki ya ganki ba, inda na samu sauki ma mahaifinsa don ya nuna maki so  kamar ya hadiye ki, duk da kina’ Jaririya amma » dake yake zama a kofar gida sai idan kin yi ?fitsari ko kuka yace akawoki abaki kisha bra minti goma kuma zai sake aikowa a kawo ki * ga yayanki Rabi’u wanda zance tamkar shi aka * haifa mawa don da Baba ya aiko a“dauke ki zai biku idan za adawo dake tare dashi haka idan za a sake fita, wannan ne ya dan rage min
‘ radadin da ke damuna. Ga shi Umma na min aike yanzu akai‘ akai tana aiko Zuwaira kanwata wadda a lokacin ta fara zama budurwa, shekararta goma tana aiko min ita da‘ yan abubuwan bukata k0
_ ‘yan kudi don a lokacin Umma tana samun
“kudi sosai wurin Yaya Sani ya tsare musu .komai “ .
Kwatsam mahafin Bala Allah yamai  rasuwa mutuwar‘data daga min hankali a lokacin kina da wata ‘biyu, naji mutuwar Baba fiye da~ yadda naji ta mahaifina aka zo aka yi sadakar
uku kowa ya watse.
Ranar da aka yi arba’in Saudat, ~a washegari aka daura wa Bala aure da Laure, a . ranar‘kuma aka yi mata jere ta tare. Bani da labari sai dai na ga jama’a na ta shigowa ana jejjera kaya ban tambaya ba har suka gama suka tafi da daddare na ji gudar ‘yan kawo amarya a lokacin zuciyata ta tabbatar. min da abin da nake zargi na shige dakina na yi kuka ~ har na ji babu dadi, na share hawayena naci gaba da hidimomina a cikin gidan Ummana da ta samu labari aiken kudi ta yi min masu yawa tace inja jari in rinka sana’a saboda zama hakan ba zai min ba. Kinji uwa mai dadi. ‘
Yaya Sani kuma ya zo garin da kansa yasa aka yi min sabbin kayan daki masu kyau da tsada, wanda ko na amaryar ba zasu kama kafar nawa ba don da ma kin san ba a yi min kayan dakiba, dan uwa mai dadi
Nan fa kishi ya Balle Laure da habaice’ habaice har tana fadar, wai Yaya Sani sun”
Samu labarin tsafi yake a birni, kin jifa! Baka da dama da arziqi ya sameka yanzu ance yankan kaikake, nidai bankula ta ba hidima ta da yarana kawai nake
Ga shi har a lokacin Bala bai damu da ni ba balle ‘ya’yana sai ma ta kai ta kawo bani da girki a cikin gidan, kullum ita ke sanwa, . kuma ita ke kwana da miji, suka bi suka hade min kai abincin da zan ci ma aka daina ba ni, da nayi wa Bala magana ya hau ni da fada wai bai riKe ni ba, idan ba zan iyaba ga hanya nan shi ba zai iya ba, ai yana da labarin idan anba .ni abinci zubarwa nake wai ni mai dan uwa, mai kudi, to in zauna dan uwan yaci dani. Haka ya qaraci Kaskancinsa yayi tafiyarsa. .
Na shiga rudani ga ‘yan kudin dake hannuna duk na cinyesu a ranar haka muka
wuni, washegari ne da naga yunwa na neman kashe mu a dole na mike na sabi ‘yata na goya
na kamo Rabi’u na kullo dakina na leka ~
_nafada wa Laure zan je gida don Allah idan ‘Bala’ya dawo ta fada masa, na bata makullin dakin. ,
Ta amsa a daKile muka tafi, ina tafe juwa tamkar zata kayar dani
Saboda yunwa, ga Rabi’u na ta kukan zaici abinci duk da kuwa da girmansa don’. yana dan shekara takwas a lokacin
Kai tsaye gidan Umma muka nufa a yanayinta ya tabbatar min da ta ji dadin zuwan namu,na kuma yardar wa kaina ta yafe min ‘ laifina a yanzu sai dai da alama tana min
kallon tausayi.
‘ ‘ A gidan mun ci mun sha, kamar cikinmu zai Bule. Muka yi sa’ a Umma ta gyara kaji guda shidda na zauna na soya mata su ta dibar mana kusan rabi da kwalayen lemuka masu “yawa da ledar kayan marmari, haka muka dawo gida niqi-niqi da naira dubu ta abin ‘hawa.
Muka dawo gida wajajen magriba ban ‘samu kowa a tsakar gidan ba,‘ ‘ na leqa dakin Laure na karBi makullina na bude muka shiga na ajiye niKi-niqin ledojin naje na dauro alwala na dawo nayi sallah sannan na zauna na baje kayan Ina cicciro wadanda zasu lalace. Da wuri
Na ji an hankad’o labule na tsaya ina
kallonsa, ya shigo dakin yana faman muzurai, na gayar da shi amma bai amsa ba, don haka ni
1 page is missing
Ya runtse idonsa yana maimaita innalillahi Wa’inna ‘ilaihi raji’un, ya bude ,su _sun kada sun yi jajawur muryarsa na rawa ya ‘ soma fadar, “Da ma an dade ana gaya min halinki amma ban taba yarda ba, sai yau da naga zahiri ba zan ce miki komai ba Mariya ki je ke da Allah, ba zan ce miki komai ba”.
Ya juya ya fice tamkar zai fadi a Kasa tunda na sadda kaina qasa ban iya dagowa ba, zuciyata ce keta faman kai kawo tamkar za ta fasa kirjina ta fito fili, babu abin da nake maimaitawa sai innalillahi daga qarshe kuma sai na kife kaina a qasa nasa wani irin kuka mai ban tausayi.
Rabi’u dake .zaune kusa dani ya sa hannu
‘ “Mama ki tashi ki yi shiru
. ’ Da dai yaga ban da niyyar yin shirun shi ma sai ya kifa kansa a kaina yasa nasa kukan. , Tsawon lokaci muna a haka babu mai tada wani sai da’na gaji don kaina na ji kaina ya fara bugawa alamar ciwon kai ne zai
sauko min, na lallaba na mike na kinkimi dana na dora kan gado, ni ma na kwanta a gefen
Keko kina ta sharar baccinki muka rinka. sauke ajiyar ‘ Zuciya a tare har bacci Barawo ya sure Rabi’u amma ni idona babu alamar bacci a cikinsa yadda naga rana haka na ga dare. ’ Washe gari haka na tashi jiki ba kuzari’ zuciyata tayi min masifar nauyi koba a auna ni ba ina da tabbacin jinina ya hau saboda yadda kaina ke wani irin masifar ciwo ga juwa ga nauyin kirji duk dai alamun mai hawan jini. Ga lamarin ba sauqi don sai‘nace ma gara jiya da yau don bala’in na yau yafi na jiya tashin hankalin yanzu ya linka na yau dan na fuskanci wulakanci da cin mutunci da muzanta ‘ a lokacin nan don har sai dana gwammace dama ba a halicce ni a duniya ba. : ~ Ga ciWo ya zoya tiso ni gaba kamar zan mutu daga ni sai dana Rabi’u muke jinyar, shi “keyi min komai daidai da shiga kewaye sai na dafa shi, ya kai ni har bakin qofa, amma‘ Bala bai taba yi min sannu ba balle yace mu je ya  kai ni asibitiba, da ciwo ya ishe ni a lokacin ne na rinqa bawa Rabi u nasiha a kan ya kula
da rayuwarki k0 bayan raina donni na riga na. gama. hango mutuwata kararafa na tsumbure
gabadaya babu ruwa a jikina balle wadataccen. jini, ciwo ya ishe ni a jiki Saudat na hango mutuwa karara a dole na aika wa Ummata tazo da kanta ta sa aka kai ni asibiti aka kwantar dani ‘wai ina dauke da ciwon zuciya mai tsanani, kuma bani da jini da ruwan a jiki a kalla ma ina buqatar Jini leda shidda da Karin ruwa
leda takwas ba musu aka kara min.
. Kwanana goma a asibiti aka sallamo ni amma Bala ,sau daya‘ya zo ya ganni shi ma a tsaitsaye don ko’ zama bai yi ba nairarsa bai ~, bayar ba, haka yazo ya yi tafiyarsa abinsa.
‘ Ummana taji haushi sosai har ta yanke shawarar ba zan koma gidansa ba ta wuce dani gida. Kwanana daya kuma ta tattara ni ta maida ni ‘gidana tare da siye-siyen madarar yara mai yawan gaske da su saralak, biskit, kifin gwangwani da sauransu, tace in yaye ki haka nan zan fi samun Karfin jikina. A lokacin kina da shekara daya da watabiyar aka yaye ki, a lokacin ne kuma Laure ta haihu, ta haifi
yarta mace aka sa mata suna iKilima
Ranar suna an sha bidiri rago biyu aka ‘ yanka, an sha kidan kwarya ranar kamar za a
tada‘ gidan ni dai ina géfe na zama “yar kallo. don k0 karabiti ban kai ba
. Bayan sati daya da yin suna ina kwance a dakina da daddare misalin qarfe hudu na
asuba na rinka jiyo maganar Laure da ‘Bala a tsakar gida tana fadar “ ‘ “Wallahi maigida da idona na ganshi ya ‘
shiga dakinta, k0 kewayen ban shiga ba na fito”. ‘
Bala yace, “Shiru ba ni toch light din in haskashi da kaina”. _ Gabana naji yayi wata mummunar  faduwa. don na fahinci bako muka yi a gidan (Barawo) ban ida tsurewa ba sai da naji ana laluben qofata  ai ko na firgita na tashi na koma can quryar gadona ina faman rawar jiki, gabana ya sake yankewa ya fadi’ lokacin da naga an haske ni da fitila na takure a cikin tsananin firgici .‘ ‘ Me zan gani? Wani shirgegen qato ne kwance a kan gadon nawa ta gefenki yana ta sharar bacci Bala na haske shi ya zabura ya
ya rarumi rigarsa yana fadar “Mariya sai anjima”
‘Ya fita a guje ya hankade Bala da ke shirin riqe shi har ya fadi.
Ya mike ya kuma bi shi, Saudat ba zan iya misalta miki irin tashin hankalin dana shiga ba a lokacin, musamman da Laure ta sa ihu tana kiran makota su .zo an kama kwartuwa ranar naga tashin hankali da idona. .
Kan ki ce me gidan ya cika da jama’a ana ta kallona, wasu na zagina suna Allah ya tsine wasu na jifa ta da takalma a Kofar gida kuma matasa sun taru‘suna jiran na fito a jefe ni k0 su cinna Wa gidan wuta, Saudat ranar na shiga halin ha’u’la’i har gari ya waye tangaram mutane basu bar gidanmu ba‘ sai ma Kara taruwa ake
’ Ana haka wani mummunan labari yazo min wai matasan unguwar sun je sun kunna wa gidanmu wuta, wayyo Allah na ai na kusa , shidewa a wurin, ni kuka ‘yaya na yayyaBe da ni‘su ma suna yi.
‘ A haka mai unguwa ya shigo gidan namu shi da bataliyar ‘yan sanda tare da Yaya Sani da kuma Bala a bayansu nan fa jama’a
suka! hau « gudu mai unguwa ya durqusa gabana yana fadar. ‘
“Mariya ina son muyi magana ‘dake tsakaninki da Allah zaki fada mana saboda kin ga dai yadda komai ya tarwatse so muke mu yiwa rayuwarki adalci don yanzu haka “matasa sun kunna wa gidanku wuta, ga mahaifiyarki har qanwarki babu wanda aka fidda da rai, kin ji aikin jahiliyya, don haka kiji tsoron Allah ki sani idan kin fadi qarya k0 gaskiya duniyar ta riga ta zo karshe a wurinki, muna so ki mana rantsuwa a kan randa kika fara neman, maza, kuma ki rantse ‘ya’yan nan na Bala ne~
Dacin zuciya da tashin hankali su suka tsayar da kukan da nake labarin -mutuwar Ummana yafi komai tarwatsa min zuciya, na riqa girgiza kai kamar wata marar ,hankali don gaskiya a lokacin banda bamhanci da mahaukaciya. ’
Mai unguwa yace, “Ba kada kai muka sa ki ba, rantsuwa ce zan fada ki maimaita idan . har kin san kina bisa gaskiyarki”.
Na yi shiru ina kallonsu daya bayan daya, kamar ‘yar mage Rabi’u na tsugune a gefe rungume dake, yana kallonmu yaci kuka har ya gaji.‘
Mai unguwa yace, “Ki je ki dauro alwala”.
_ .Ba musu na je na dauro alwalar na dawo, ya miqo min alkur’ani izifi sittin na karba na  tashi tsaye’ na daura a kaina, na mike nayi yadda yace, ya karanto min rantsuwa ya ce in maimaita, na rinka maimaitawa ina rantsuwaa kan ban taba sanin wani namiji bayan Bala ba, kuma ‘ya’yana nasa ne, idan na taBa Allah ya  tarwatsa ni, Ya halaka ni, Ya wargaza rayuwa ta, Ya yi rugu-rugu dani, Ya sa kar na gama lafiya, Ya hana ni ganin annabin rahama, kuma Yasa in tashi tare da fir auna, ina yi suna kabbara har na maimaita sau uku.
Mai unguwa ya juya ya dubi Bala.
“To kai ma kana da ja? Idan har kana daja to kai ma zaka rantse“ kamar yadda tayi a ‘ kan‘ yayannan ba naka bane, idan har ka rantse to za a bar mata yaran nata saita nemi ubansu”. . Bala ya sunkuyar da kai zuciyarsa na’ Kuna yadda yake jin ya tsane ni haka yakejin ya tsani ”yaran, amma k0 da wai bai Jin zai ”
.iya rantsuwar saboda girman hadarinta,don haka muryarsa a sanyaye yace
“A’a ranka ya dade , a gaskiya ni “ ba zan rantse ba, na dai san ‘yaya ba nawa bane, ban da haufi amma tunda al’amarin yaxo ,da haka na karbe su, amma ita kam ban iya ci gaba da zama da ita, don haka na sake ta saki uku”. . ‘ . ‘ Yaya Sani ya bude baki da kyar da muryarsa wadda ta dusashe yace. “Tashi muje Mariya” Na yunkura na mike na kamo hannun yarana, Yaya Sani yace , “Wadannan nan zaki barsu ai ba dasu ki ka zoba” A take na durkushe a gurin na fasa wani uban gunjin kuka na rungumesu wayyo yarana. ‘ Yaya Sani ya fincikoni  a fusace ina ihu ina komai haka ya bamBare ni daga jikin .yarana yana jana wani yaro ya fado gidan a. gigice ya fadi gaban Bala yana fadar YallaBai kasuwa ta kama da wuta tun jiya ‘ da daddare ta keci, har yanzu bata mutu ba, shagonka ya qone kurmus, ba a fidda ko haki ba”. Bala ya dora hannuwa bisa kai yana neman ,tai‘makon Ubangiji. Yaya Sani k0 kallonsa bai yiba ballantana -ya jajanta masa ya jani muka bar gidan ina ihu
A, haka muka bar gidan wanda ban qara taka shi ba har yau, dama tuni motar ambulance ta kwashe su Ummana a nan birni aka rufe su ranar nayi kuka’ kamar zan mutu.
Haka naci gaba da zama gidan Yaya Sani wanda ke zaune a Kwangiwa road shi da matarsa Fadila a sannanne naci gaba da karatuna har na tafi nayi doctoring degree dine. a A. B. U Zaria, ina cikin karatun ne na hadu da Abban Nabil a Saudiya naje aikin hajji, yana da mata guda da ‘ya ’yansa biyar muka daidaita, na aure shi. Ina gidansa na kammala karatuna shi ya samar min aiki a Medical Céntcr Hospital dake nan Katsina, da yake nan ya ajiye “ni shi kuma yana aiki a babban bankin Abuja, uwargidansa ma tana can. Yana zuwa duk Week  iyayensa ma ‘yan asalin nan ne Kankia, yanzu haka ina da yara kwara biyu, Nabil da Nabila sai ‘yar aikina Mairo, sai direba sai kuma maigadi mu kadai ne a gidan nan”.
Saudat ta lumshe idanuwanta wadanda ta kejin sun cicciko da hawaye, lallai mahaifinta ya  aikata babban kuskure wanda ita kanta ba tajin zata iya yafe masa, ya. gallaza musu bacin ‘gallazawar da yayi wa mahaifiyarsu, lallai dole
mahaifiyarta ta manta dasu don ta ma daina ganin laifinta

Hmm to jama,a munji lbr malam bala da uwargidansa maria mu tara gobe don  komawa tsundum cikin asalin lbr mezai faru ??????
Naku har kullun
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE