Yar tallah3

YAR  TALLA

         Chapter3

Mun tsaya a
*Inda inna laure ta leqo taga sai sharar barcinsu kawai sukeyi wani takaici ya kamata ta juya ta debo ruwa cikin kwanon sha ta daga labulen ta sheqa musu a firgice duk suka tashi sukai wuqi wuqi kamar ya,yan zakaru*

*Zamu tashi a*
Inna laure ta tabe baki cikin masifa tace nan har lokacin barcin safe gareku?
Sannunku yayan hutu to saiku tashi
Kai kaje ka jido mana ruwa ke kuma kije ki share mana gida ki tafi kai markadan waina
Ta saki labulan ta juya tai gaba
Babu wanda yace komai cikinsu rabiu yadau jarka ita kuma tadau robar markaden ta fice babu alwala bare wanke ido
Rabiu ya jido ruwa yafi jarka goma
Saida ya ciccika komai na gidan sannan ya fara gyaran gidan
Saude ta dawo daga markaden tana hada wuta iklima ta fito riqe da kofin shayi da qaton biredi a hannunta
Saude tai saurin tashi daga hura wutar
Da take ta kalli iklima tana miqa mata hannu sanmin zo indan gutsira kadan kinji?
Rabiu yai saurin kwAbarta ke da,ala kyale mata abinta
Saude ta bata fuska nidai don allah zanci
Yace toki bari idan na samu kudi zan siyo miki
Ta qara bata fuska nidai zanci
Kullum saikace zaka samu kudi kuma ba samu kakeba
Rabiu yadan kura mata ido kafin yace insha allahu yanxu zan samu kinji?
Kai kawai ta daga masa yana juyawa ta miqama yarinyar hannu iklima tace ban badawa
Ta juya ta shige dakin nasu tana fadin laure wai kinji wai in san mata biredin ni kuma nace ban badawa
Laure ta hankado daki tana fadin au biredin yar tawa kike sama ido
Wato ta kawo miki ki cinye ita kuma ta fadi ta mutu kenan  ko?
Ta shaqo wuyan rigarta tana fadin dan ubanki kin sabacin irin wannan ne ?
Ko sAlon kici kiyita zawo ne? yar banza kawai wuce ki bama mutane wuri ta hankadeta saidata fadi
Ta juya ta kalli rabiu kai kuma zakaci gaba da aikin gabankane ko kuwa zaka rama matane?
Bai tanka mataba ya duqar da kansa yaci gaba da sharar da yake
Ita kuma taja kujera ta zauna taci gaba da hada kullun wainarta
Malam ya kwalama rabiu kira. Ya ajiye tsintsiyar ya tafi
Ya watsa masa kallon banza kafin yace. Ungo ka bata munafuki wanda yai gadon mugun hali
Rabiu ya amsa jiki na rawa ya fice
Dan guntun biredi ne wanda bazai wuce gutsira biyu ba. Sai dan ruwan shayinda ba ko madara
Rabiu ya miqa mata ta karba cikin rawar jiki
Ta tura biredin duk a baki tana tauna da kyar sbd yaddah ya cika mata baki
Rabiu ya kalleta yace kisha a hankali kar kiyi amai bata kulashiba ta
kafa kai ta shanye ruwan shayin tas tana lashe kofin
Inna laure ta kafa mata dundu wanda yasata amayo duk abinda taci yayo waje cikin takaici tace shegiyar yarinya mai kama da mayyah maqerin kofin zaki tando duk wanda kikasha bai isheki ba? Munafuka tashi kibar wurin kona haureki
Ta saka kafa ta tunkudeta
Saude ta kwasa da gudu ta nufi dakinsu tana kuka mai sauti
Rabiu ya rakata da kallo inna laure ta daka masa tsawa zakaci gabane kokuwa binta zakayi
Dan iska mai kama da igiyar shanya
Rabiu ya durkusa. Ya soma kwashe aman, sautin kukan nata na dukansa a kirji
Laure ta gama tuyar wainar ta kukkulla a farar leda naira Biyar biyar ta zuba mata a cikin bokiti ta dauki ta goma ta miqawa rabiu sannan ta kwalawa saude kira 
Ta fito tana matsar hawaye laure taja tsaki au kukan kike har yanxu kenan? Baki bugu bane shiyasa tashi ki dauka gatanan ta murtala huduce kiyi maza ki dawo kinsan alala nanan tana jiranki
Saude ta durkusa ta dauki bokitin tana fadin ina tawa?
Inna laure tace eh lallai ai dadin sai yayi miki yawa kisha shayi kici waina ai dadin sai yayi miki yawa yar gidan uban waye ke a garinnan?
Batace komaiba ta lallaba ta wuce rabiu dake kusa da ita ya kamo hannunta ya damqa mata nashi wainar ta fice tana murna
Inna laure taja tsaki tace matsalarkace nidai ko suma zakadingayi sbd yunwa wlh tallahi saika gamamin duk ayyukana dondai na rigada na fita haqqinka
Zakara kawai mai neman suna ka bada kwaya kaci tsakuwa
Bai tanka mataba yaci gaba da aikin nasa
Yana gamawa inna laure ta tattaro kayan iklima masu himilin yawa ta watsomasa ta wurgo masa kullin  omo maza ka sabe mata kayannan
Rabiu ya durkusa yana tattare kayan bayansa na faman cijewa ya nufi bakin rijiya ya soma wankin
Malam bala ya fito daga dakin hannunsa riqe da wani dan takurerren buhu na zuwa kasuwa harya wuCe yadan dawo kadan yace kai rabiu idan ka gama wankin ka shiga daki ka tattaro nawa ya wurgo masa naira hamsin ga wannan nan kasai omo
Kuma banason wankin banza don wallahi na dawo naga basu fitaba komin dare saika sake wankesu kanajina ko?
Ya karba da hannu biyu gamida daga kai alamar eh
Saidaya kammala na iklimar gaba daya sannan yaje ya siyo omon talatin garin goma sugar goma
Yaxo ya jiqa saidaya kumbura sannan yasa suga ya fara sha
Baiyi cokali biyuba ya tsaya gamida kafama kofin garin idonsa ya cikoda hawaye
Wata rayuwa can ya tuno lokacin da mahaifiyarsu ke jiqa musu gari ta tasasu gaba shi da saude susha. Ita kuma ta zauna a gefe tana kallonsu
Ko cokali daya ba zatayiba duk kuwa da yunwar da zata tashi da ita ta wuni da ita
Tausayin mahaifiyar tasu ya dirsar masa ya tuno yar uwarsa saude yanxu haka yasan da  yunwar a cikinta
Yaja numfashi sannan yaci gaba dashan garin
Laure ta giftashi kamar zata wuce don taga me yakeyi ganin garin rogone yasa ta wuceshi kawai ba tare data tankashiba
Shima kuma bai tankataba yasha garinsa ya rage sannan ya tashi ya tattaro kayan mahaifin nasa yaci gaba da wankewa
Karfe daya na rana saude ta dawo daga tallar wainar tana aje bokitin laure ta miqa mata tiren alale idon yar ya ciko da hawaye wahala ya isheta
Ga wahalar yawo ga azababbiyar rana ga uwa uba yunwa ita kenan tallah ba dare ba rana
Har yaran unguwa sun nada mata suna da YAR TALLA ina kika fito tallah ina zaki tallah ina kika dawo tallah
Saude ta daura tiren saman kai wasu hawaye suka gangaro kuncinta laure ta tafa hannuwa na shiga uku
Muhammadu dan Abdullahi mezan gani ni laure ? Tallar ce bakyason zuwa to dawo ki ajiye ki zauna ki huta yar hutu zoki ajiyemin tunda baki zuwa
Saude ta wuce tana faman sharbar hawaye inna laure tace uhm hum yarinya kenan ai dama kin adana hawayenki don tallah yanxu kika fara alalata ta murtala hudu ce da goma ki dauki ta gomar kuma wallahi ragin sule idan kikayi a jikinki zan fanshe sannan ko kanxo bance ki dawomin dashiba

*Hmm su inna laure manya mu tara gobe daidai wannan lokacin donjin cigaban book din tareda niii*
                        *ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE