Yar tallah34

               *YAR.  TALLA*

                  *CHAPTER34*

kawai kin raina ni,’ kina ganin daidai kike dani 
don kawai na baki yancin yin duk abin da kike so, saiki rinka yi min gadara da isa? Don kawai kin ga ni din mai tsantsani ne, ban damu da harkar wasu mata ba, k0 k0 don kin fahimci ina sonki ne kuma kina da kyau shi yasa kike min abin da kika ga dama ni ban sani ba? Baki san daraja taba, balle darajar aurenaba shin ni dutse ne da zan kasa watsar dake na samu wata? Tunda matan ga su nan tamkar  ledar pure water wanda suka kai ki da ma wanda basu kai kiba”‘ ‘Asma ta dago da sauri tana kallonsa, ya “ daga gira. “Yeah, duk abin da ki ke takama da shi suma sauran matan suna da shi, sannan don kuma rashin kunya kike neman rusa min kwanciyar , : hankalin iyali don kawai kin ga ina kyale ki? To Wallahi I will  surprise u matukar ki ka Kara shiga, hurumin Saudat zan iya yi miki komai, Sannan da kike kiranta da matsiyaciya, kodaddiya, ai Saudat ta fiki komai a idanuna kuma don ina sonta na aure ta kamar yadda kema nake
sonki na aure ki, kuma duk wani shirmenki da haukanki ba zai sa na rabu da ita ba don ita ce rayuwa ta, wallahi tun ranar da  naga tausayina. a cikin idanunta na soma jin soyayyarta a zuciyata, kina tunanin’wannan soyayyar ta wasa ce?
Ki gafarce ni Asma, da gaske nake ina son Saudat, wallahi please Asma ki taya ni mu sota in har da gaske kina sona“ Wani irin ihun kuka Asma ta saka saboda yadda ta rinqa jin kalamansa na neman tarwatsa ‘ mata zuciya, ta daga masa hannu cikin karaji tana
fadar, “Stop it…  don’t repeat dis word to me  again please, ba sai ka bude baki ka fada ba zan gane ka daina sona ba, ba sai ka fada ba Ahmad zan fahinci ka gama dani ba, nayi condaim a wurinka amma don Allah ka kyale ni haka da wadannan zafafan kamalan naka masu qona min zuciya da sassan jiki”.
Dr. Ahmad ya koma kan gadon tare da rungumo ta yana fadar, “Please Asma, wallahi ban fada miki wadannan maganganun don ranki ya Baci ba, iya gaskiyata nake fada miki, kuma ki daina fadar na daina sonki, wallahi har yau har gobe sonki yana nan a zuciyata, kuma a shirye nake da na ninka shi idan har ki ka gyara halayyarki, ki tuna fa ke din mai ilimi ce amma ki rinka abubuwan da mai hankali ba zai yarda da su ba, haba Asma”.
Kukanda take tare da sauke ajiyar zuciya shi ya tabbatar masa kalamansa suna shigarta, ya dago da kanta ya Dora a kan kiirjinsa yana share
mata hawaye, tare da gyara mata gashin kanta cikin _ sassanyar muryarsa yaci gaba da fadar, “Am sorry
Asma, ki yarda dani wallahi har yanzu ina sonki idan har ki ka sauke gadara da girman kanki zaki same ni a duk yadda ki ke so.
A yanzu Asma ta daina kukan sai dai sauke numfashin da ta ke, Dr. Ahmad ya janye ta daga jikinsa ya barta a kan gadon ya nufi bandaki ya hada mata ruwan dumi da Belton robb sannan ya fito ya kinkime ta ya nufi bandakin da ita Sai da ya watsa mata ruwan ya wanke ta sol sannan ya fito da~ ita da kansa ya Ciro mata kayan baccinta ya bata ta saka, sannan ya kamo hannunta ya kwantar da ita a. kan gadonta ya ja lallausar bargonta ya. lullubeta ya kashe wutar dakin tare da furta mata sai da safe.
Ba ta da yadda za ta yi tana jinsa harya fice duk yadda ta so danne zuciyarta sai data fashe da. kuka, don ta sani a yanzu Ahmad ya yi mata nisa, ta riga ta yi sake har dan hakin da ta raina yazo ya tsone mata ido, duk yadda zuciyarta ta‘ kai ga. chashewa a kan al’amarin fa namiji a yanzu ba ‘abin da tafi bukata sama da shi k0 don ta lura yana neman subuce mata ne?
’ ’ Yau din nan ta kasance mata rana mai muni saboda kunnuwanta sun jiye mata mummunan albishir din rasa wanda tafi so fiye da kamai a rayuwarta, kuma yau ne rana ta farko data fahimci.
rashin kyautatawarta a zamantakewarta da mijinta  kuma a yau ne ta gane kuskurenta bayan ta
rasa shi, kuka ta ke sosai tare da nadama marar amfani. . .
Asma mace ce mai zafin kai da izgili da raina mutane, ba ta da son jama’a k0 kadan shi ya sa ma k0 abokai bata da su, sai dai tana da raguwar zuciya, ba ta da juriya ko kadan nan da nan damuwa ke wujijjiga ta saboda ba ta saba da ita ba, don haka a yanzu tunaninta guda, hanyoyin da za ta bi don ganin ta karkato da hankalin mijinta a kanta su koma irin zamansu na farkon aurensu.
Bangaren Saudat kuwa tunda ya fita ta tsinci kanta da wani irin matsanancin kishi da damuwa ta gagara runtsawa, sai faman juyi take tana duba agogo, amma har sha biyu saura bai shigo ba, zuciyarta ta ba ta yana wurin Asma, to me suke har yanzu da bai dawo ba? Wannan tunanin ne ya sa ta ‘ soma ‘yar kwalla, sai karfe daya saura kwata na dare ta ji ya turo Kofa, hakan yasa ta saurin jan bargo ta lulluBa tamkar mai bacci, tana jinsa ya hayo kan gadon ya ja ta jikinsa ya kwanta tare da lulluBe su da bargo ya soma shafar kanta yana kiran sunanta, amma ta Ki motsawa tana jinsa har ya gaji ya yi shiru, a haka bacci ya yi awon gaba dasu
‘ Da asuba ma suna kammala sallah Saudat ta
mike za ta fice taji muryarsa na fadar, “Ina kuma zakije?”
Saudat ta dan waiwayo kadan kafin tace’ ‘Bangarena” . .
Ya dan harare ta,“ “Okay nan din da yake gutsirarki ake k0? To dawo ba inda za ki”. ~ Kamar kada ta dawo din hakata daureta ‘ koma kan gadon tana kokarin hawa ta kwanta ta ji ya tisgota ta fada kirjinsa, har tana buge fuska. Ya dago kanta yana fadar, “Wai fushin me ki ke da ni? Saudat laifin me nayi tun jiya ‘da na fita na dawo na lura kinata kumbura shiyasama nayita magana ki ka share ni, ki ka nuna bacci kike, oya fada ‘ min menene? ‘
Saudat ta kasa tankawa saboda irin riqon da yayi mata, dakuma rashin takamaimain amsarda zata bashi don tasan babu abin da ke damunta, wandaya wuce kishi, dakunya kumatadubeshi ta ‘fada masa hakan, saidai damamakinta tajiyana fadar, “Kishi ne ko Saudat? To sha kuruminki Ahmad naku ne kubiyu, kuma soyayyarki daban ce acikin zuciyarsa. Ki sani ni Ahmad ban buqatar kowa tunda na same ki, ban bukatar abinci in dai.
inajin muryarki, bani da bukatar ruwa matukar ~
akwai miyau abakinki banbukatar iska indai ‘akwai numfashi acikin kirjinki bananeman komai tundana sameki,karki kara damuwa balle har shaidan ya cusa miki wasu al’amura kisa. a
zuciyarki kedin matata ce wadda nake
Asma matata ce wadda nake so, dukkaninku an halicce kune da hakarkarina kuma kowaccenku tana bukatar farin cikinta daga gare ni, idan na wulakanta dayarku saboda ‘daya ki sani Allah ba
zai bar niba please Saudat ina so in yi adalci a
tsakaninku”. Saudat ta lumshe idanunta tare da kwantar da kanta a kan kirjinsa tabbas abin da ta gani cikin idanunsa ya tabbatar mata da haqiqanin gaskiyar da yake fada, ya kara matse ta a jikinsa ta ji tamkar za ta rabu gida biyu ta bude baki da hanzarinta, .tana fadar, “Wayyo Yallabai, za ka karya ni”.  maimakon ya sassauta mata rikon sai ‘ma ”ya qara matse ta a qirjinsa ta yadda .Saudat ke jin bugun zuciyarsa da sauri da sauri cikin wata irin , rikitacciyar murya ya soma fadar, “Yi haquri don Allah Saudat, wallahi ji nake tamkar in maida ke cikin jikina don Allah Saudat duk abin da ki ka zama a rayuwa kada ki Juya wa zuciyata baya”. Wani irin abu ya rinqa sukar Saudat ‘a Zuciya, tausayinsa ya kashe mata dukkanin gaBobin jiki, duk da ta fahimci ya saki layi amma hakan bai hanata rungumar mijin nata ba, wanda ta kejin *tamkar a yau ne ta soma sonshi. a Cikin sati guda Saudat ta yi matukar shaquwa” da Dr. ta saki jikinta da shi ya koyar da ita  darussa masu yawa, takuma bude kwakwalwarta
ta dauka ba ta zubar da su a kwandon Shara ba, duk abin da ta lura’ya fiso atareda ita shi ta ke masa, har ma ta kara da kalar’ nata salon don qarin ~ armashi. ‘
Yau ta tashi da son shiga kicin duk da kuwa yau din ne miji zai bar hannunta ya koma gurin Asma, tunda kwanakinta sun Kare, so ta ke ta yi girki da kanta, duk da ba wasu abubuwan kirki ne ta iya ba a bangaren girki, to amma gani ta ke gwamma nata girkin sau dubu da wanda kuku ya yi musu daren jiya, wanda ya sa ta amai babu ‘ gaira babu dalili, shi kansa Dr. bai iya cinsa ba da ya kira kukun don jin abin da ya girka musu, sai cewa ya yi tuwon alabo ne da miyar manja,sai drinks din kayan itatuwa da madarar ‘ruwa, da danyan kwai, girkin sai kana Kasashen qetare.
Abin da ya qara tayar wa Saudat da zuciya kenan  take ta sa ya shigo kicin din ya nuna mata yadda ake amfani da kayan na’ urorin kicin din nata har Dr na musu dariya.
Don haka yau tunda sanyin safiya ta gama shirinta cikin wata doguwar rigar shadda ash colour wadda aka yi wa aiki tun daga sama har qasa bata daura kallabin rigar ba sai dai ta daura dan qaramin mayafl a kanta wanda ya tsaya iya kafadarta, ta zura takalminta flat shoe ash colour sannan ta fice; ta nufa kicin din ta bar Dr nata sharar baccinsa.
Sai dai ba girin-girin ba tayi mai, ga shi dai babu abin da babu ta bangaren kayan .abinci tun daga na gida Najeriya har zuwa na kasashen qetare sai dai bata san yadda za ta sarrafa suba.
Can dubara ta fado mata ta yanke shawarar ta girka musu alala da kunun gyada don a nan din ta san ita gwana ce don kuwa sune sana’ar Inna Laure, don ‘haka ta nufi store ta debo wakenta ta zuba a turmin ta sa ruwa ta surfa sannan ta nufi wurin famfo ta wanke shi ta fitar da dusar ta bude freezer ta debo kayan miya wadanda suka daskarar da Kankara ta gyara su ta zuba a cikin wakenta, ta ‘ sa a blander ta markade suka yi laushi sosai sannan ta juye a roba mai fadi ta kawo spices ‘kala-kala ta zuba ta yanka alayyahu da albasa masu yawa, ta zuba ta sa manja da mangyada ta motsa sosai sannan ta daddaura a fararen ledoji ta zuba ruwa. a tukunYa ta zuba alelenta a ciki ,ta dora a kan gascooker sannan ta koma ta debo kullun gyadarta ta dama kunun gyada sannan ta koma tana gyara kicin din nata.
Dr, wanda ya farka ya laluba ya ga ba ta nan .
ya mike ya nufi bandaki ya watso ruwa ya fito ya ’shirya cikin qananan kaya bulue din jeans sai milk din T shirt ya gyara sumar kansa, sannan ya zura silifas dinsa na fatardamisa ya fice kai tsaye kicin din ya nufa, yaja ya tsaya ya tokare bayansa da
qofar kicin din tare” da zuba hannuwansa cikin
aljihu yana kallonta. ” Saudat ta juyo tana kallonsa lokacin da ta
gama jera abincin a kan tebur din bakinta dauke da murmusln ta ce “Bismillah mana, yau za ka ci irin girkina, don Allah ka shigo”
Ya tabe baki yana kallonta tare da make kafada alamar ba zai shigo din ba.
Saudat ta nufe shi ta riqo hannayensa tana
fadar, “Don Allah ka shigo ka gani ka taBa cin alala?” Bai tanka ba hakan kuma bai hana ta jansa ba har bakin‘ dinning table ta ja masa kujera ya ‘ zauna sannan ta bude kula ta ciro masa alala kwara biyu ta sa masa a faranti, ta tura masa tare da cokali mai yatsu ta zuba masa kunun gyada wanda ya ji madara ta mika masa tare da cokalin shan tea, ta , langwaBar da kai tana fadar, ‘Don Allah kaci kaji na iya?” Murmushi ya yi kafin ya cokana cokalin ya . soma ci bai tanka ba sai da ya cinye duka biyun tana zaune tana kallonsa zuciyarta cike da jin dadi, > ita ma ta zuba nata ta soma ci.
Yana cinyewa ta dube shi na Karo maka, ya
waro ido, “Haba Madam tausaya min bani dai kunun insha”.
Ta miKa masa ya sa cokali ya soma sha a
nan fa ta ga santi ya dube ta, “Amma wannan ‘ kunun da madara ake yinsa k0?”
Saudat ta girgiza masa kai alamar a’a, ya jinjina kai, “Amma Allah wannan ana iya bude kamfani a rinka yin na roba a rinqa siyarwa, ba qaramin ciniki za a yi ba don ‘ni ban taBa shan irinsa ba fa”. ‘
Saudat ta tuntsure da daniya, ta ciro mayafin kanta ta nufe shi tana fadar, “Kai yallaBai bari in yi maka waigi kada ka fadi”.
Ya tuntsire da dariya tare ‘da riKo ta yana Kokarin kwace kallabin suna dariya, nan fa kokawa ta kaure basu suka baro kicin din ba sai sha biyu saura, ya tsaya a falo tare da fadar, “Jeki dauko key din motarki mu je in miki rijistireshon din makaranta daga nan mu je islamiya in sai miki form sai mu wuce Hikima Driving School a nan za su koya miki
tuKi tare da shaidar iyayin tuqi idan ba mu yi yammaci ba sai mu wuce mu gaida Momy”.
Dadi ya cika’Saudat ta makale shi tana murna, sannan ta yi falonta da gudu ta dauko key din ta fito, yana nan tsaye inda ta barshi ta dafo kafadarsa kamar irin abokinnan  nata, duk da kasancewar ya fita tsawo amma‘ ita ma din doguwa ce, haka suka fice tana ta zuba masa shagwabanta, shi kuwa sai Kara narke mata  yake ita kuma tana
Kara sangarcewa, shi da kansa ya ja su a motar: kasancewar mai bakin gilas ce Sai da suka fara zuwa wani studio  aka yi mata passport sannan suka wuce
social. development ya yi mata rajista da komai da
komai, suka wuce islamiyya nan ma ya siya form, a
take ya yi mata komai, suka wuce Hikima ba su suka kammala da komai ba sai shidda saura na maraice, sannan Dr. ya nufi gidansu da ita.
Sun yi sa’a kuwa Faridat ta zo don haka ‘Saudat ta samu tattali da kulawar da ta dace daga Momy din har Farida zuwa Daddy kowa sai riritata yake, ana wasa da dariya a nan nema taji’ Dr. zai yi tafiya jibi zuwa qasar Singpore ya yi sati biyu ya dawo majalissar Abuja, ya kwana guda sannan ‘ya wuce America ya yi sati guda ya biyo ta Mexico city
ya yi sati guda sannan ya wuto gida.
Zuciyar Saudat ta yi mata ba dadi don a yanzu ta riga ta saba da mijinta ba ta qaunar abin da zai sa ya yi nisa da ita tun a lokacin ta soma jin ta fara missing dinsa basu baro gidan ba sai bayan sallar isha.
Suna. dawowa kuwa ya wuce sashinsa, kai tsaye Saudat bandaki ta nufa ta watsa ruwa ta fito ta saka kayan baccinta riga da wando baqaqe masu . Laushi ta daure gashin kanta da ribbon kwara guda
sannan ta zira takalnan baccinta masu laushi ta fito falo ta fada kan kujera ta ja ipad dinta ta soma
latse latse don a yanzu ta soma Kwarewa, duk a warin’ta shigowar mijinta ta ke saurare
Shi kuwa tunda ya isa sashinsa ya watso ruwa ya saka Rigar baccinsa mai budadden gaba, ya fito falonsa ya zaunakan kujerar falon yaja Karamin tebur na gilashi ya! dora computer dinsa ya soma tura sakonni, a haka Asma ta shigo falon ta same shi ya dago ya dube ta ta cikin siririn farin gilashin dake idanunsa, sanye ta ke da kayan bacci skinny dress kalar suminti sun mata matukar kyau tamkar saukar Kasar Saudiya don da ma can Asma kyakkyawa ce ajin farko
Ta zauna saman kujerar dake gefensa cikin jan aji ta soma fadar, “Sannu da aiki dear”.
Ya amsa da, “Yauwa, kina lafiya?”
Ta dan tabe baki kafin ta ce, “Lafiya na shigo dazu ka fita” , Da kai kawai ya amsa mata ya ci gaba da abin
da yake tsawon wasu ‘yan mintina falon ya dauki
shiru, Asma ta mike ta koma kan kujerar da yake zaune, ta kutsa ita ma ta zauna ta raba jikinta a kan bayansa ta kwanta tana fadar, “So nake na kwanta da wuri saboda yau muna da wani meeting na gaggawa, qarfe biyu na dare”.
‘ Bai tanka mata ba sai dai sakonnin da ta aika masa a gab0bin jikinsa sun yi matukar tasiri wurin saukar masa da kasala
, A dole ya rufe computer din ya mikar da ita ya shureta ya nufi dakin baccinsa ya kwantar da ita, ya
mike da niyyar yace yayi wa Saudat sai da safe, Asma ta qankame shi tare da saka masa kuka tana fadar, “Haba Ahmad, don Allah horon ya isa haka, karka koma kana daukar alhakina, kana kallo fa da ajina da qimata da ‘martaba ta na-karya su na z0 inda ka ke, amma kaKi ka yafe min kuskurena haba Ahmad ka yafe min haka nan, don Allah wallahi ba
zan iya jure wannan horon ba”
Duk yadda ya kai ga mazantaka a wannan karon lamarin yafi karfinsa ganin kasawarsa ya sa ta Kara qaimi wurin cakume shi tare da Kara kunna shi da salon kissarta. ‘
Saudat kuwa da ta gaji da danne-dannenta ta ji bacci ya some kwasarta ta duba agogo, Karfe sha daya da ‘yan mintina ta lalubo wayarta ta soma; danna masa kira tayi ringin harta tsinkebai dauka ba,tasake danna masa wani kiran harsaidatakusa tsinkewa sannan ta ji ya dauka cikin wata dakusasshiyar murya yake fadar, “Saudat bakiyi bacci ba har yanzu? Ki kwanta kinji dare ya…”
Din-din taji an datse kiran.
, Ta bi wayar dake hannunta da kallo tsawon lokaci zuciyarta na barazanar tarwatsewa a haka ta kwashe tsawon wasu mintuna kafin ta haurar da [pad
din da wayar ta. nufi dakin baccinta ta fada kan gado, kishi babu dadi, sai dai haKuri ya zama dole tunda
Allah ‘ya. halicce mu Shi Ya halitta auren mace sama da daya. ‘ .
K0 da Saudat ta farka da safe bata fito k0 bakin qofar falonta ba, tana kudundune cikin bargo bata sauko ba, haka Ahmad ya turo kofar falon ya shigo.
Da sallamarsa yana sanye da wata tsadaddiyar‘
shadda gezna fara mai laushin gaske ta sha aikin
hannu, kansa na sanye da hula zanna baka  kalar aikin shaddar sai siririn farin gilashi a idanunsa, ya daura bakar agogonsa Rolex ta fata wadda ta kwanta ‘ lallausar farar fatar hannunsa wadda bakin gashi ya yi wa kawanya. ‘
Ya yi matuqar kyau musamman yadda fuskarsa ke cike da annuri ya zauna bakin gadon da take kwance tare da yaye bargon da ta lulluba ganin kayan barcine a jikinta ya sa shi saurin duban ago gon dake girke saman bed side drower, qarfe sha biyu da rabi ya waigo yana kallonta lokacin da take gayar da shi, bai amsa ba sai dai ya jefe ta da tambaya, “Lafiyarki Saudat, baki da lafiya ne?” .
Ta girgiza masa kai ba tare da ta bari sun hada ido ba, tace, “Lafiya ta Iau.
‘ Ya girgiza kai, “Yarinta na damunki Saudat, yanzu don kina jin haushina shine ba zaki tashi kiyi wanka ki gyara jikinki ba?”
Ya dan ja wani siririn tsaki, “To tashi tunda. gani nazo kije kiyi wanka kigyara jikinki
Saudat ta dauke kai cike da kunya. tace “Ni fa ba. yanzu zan yi ba” .
Yace “Tokuma wannanne kobaki isaba”. Ya sa hannu ya janyo ta tana turjewa, ya
kyaleta yana fadar, “Kwanta keki ka sani qazama ke zakita tsami bawaniba donni kuwa yanzu
Katsina na nufa inyi wasu Momy sallama don so nake inyi isha agarinnan kuma zankai kararki
wurin Momy infada mata baki wanka bare Kwalliya… ”
Tun kafin ya rufe baki ta zabura ta tashi za ta
dafo shi ya yi saurin mikewa yana fadar, “A’a qazama kar ki sake ki taBa ni ki bata min kwalliya, na yi wankana”
‘ Saudat ta bi shi tana kokarin ya tsaya ta ba shi sako wurin Momy, amma bai kula taba, ya fice yana faman tsokanarta.
” A dole ta dawo tunda kayan bacci ne a jikinta ga shi ta k0 ina harabar gidan maza ne, tana dawowa dinning table ta ‘nufa ta karya sannan ta mike ta koma bedroom dinta ta’nufi bandaki ta watso ruwa ta fito ta sakawata ‘yar sassaukar doguwar riga, sannan ta yi sallar azahar tana gamawa ta fito ta sauko falon qasa ta kira Mansura kukunta, wadda ke shirya abincin ‘safe dana rana, sai Emanuel shi ke dafa na dare. ‘Mansura yarinya ce wadda ba za ta wuce shekaru’ ashirin da biyu ba, musulma ce amma ba bahaushiya ba, tana dai jin Hausa sosai, ‘yar asalin
, qasar Ghana ce, Saudat ta yaba da girkinta don tafi Emanual iyawa, don haka ta kira ta don ta fara koya

jama,a waishin ina yaya rabiu ne?zai dawo ko bazai dawoba? wani saqo ya bama inna mai danwake ta bama saude?meya faru dashi bayan malam bala ya sake masa korar kare daga gidansa a karo na biyu?
amsar tambayarku na cikin YAR TALLA CHAPTER35 wanda zan kawo muku gobe idan mai sama ya nufemu da kaiwa kuma yasa ina numfashi
naku
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE