ZABI NA CHAPTER 16 KARSHE BY FADEELARH
ZABI NA CHAPTER 16 KARSHE BY FADEELARH
Www.bankinhausanovels.com.ng
FLASHBACK!!!
A lokacin da su Ameera suka ji labarin hatsarin Layla an sanar da su cewar tana raye amma unconscious don haka su je asibitin St Gerrard.
Ba tare da bata lokaci ba Zayd da Ameera suka nufi asibitin.. A asibitin ne ake sanar da su cewar wadanda suke tare a motar duk sun mutu.. Wato Haleema da Tukur!
Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..
Haleema ta rasu ba tare da ta gyara hali ba, ta rasu tana kan hanyarta na aikata mummunan aiki.. Ya Allah kar ka sa mu zamo masu aikata munanan ayyuka a duniyan nan Ameen.6
A yadda labari ya zo daga eye witness an ce tyre ce ta fashe shine motar tayi losing control ta fada daji..
Ko da suka samu ganin Layla ta farfado kuma bata wani ji ciwo ba domin kuwa kanta ne da ya dan bugu sai targade da tayi a hannu da kuma scratches here and there on her body… and she had already been treated accordingly.
Babu abinda take rusawa banda kuka jin cewar qawarta Haleema ta rasu.. Yanzu shikenan Haleema ta tafi a cikin wannan hali.. yanzu me zata ce ma ubangijin ta idan ta tsaya a gaban shi???
Ameera ce ta dinga lallashinta yayinda Zayd ya gama formalities na transfering dinta to Garkuwa hospital tunda dai wannan asibitin is far from cikin gari..
Ko da suka kamo hanya Layla ta roqe su akan su kai ta gida domin kuwa all she wanted a wannan lokacin was to seek forgiveness from everyone (musamman Abba) because bata so ta mutu ba tare da ta nemi yafiyar su ba.
Ko da suka isa gidan kuwa Abba bai saurare ta ba.. asali ma korar ta yayi daga sashen shi yayinda yace ta nemi wani uban ba shi ba… hankalin ta kuwa ya tashi matuqa da jin kalaman Abba.. tayi kuka babu sassauci. Ameera da Umma sune suka dinga lallashinta Yayinda Zayd ya dinga ba Abba baki amma sam ya qi sauraron shi.. Babu shakka Abba yayi fushi sossai!!
Ni kuwa nace ‘who wouldn’t?’
Sai a lokacin Mama take jin abinda yake faruwa.. Cike da borin kunya ta nufi sashen Umma wurin Layla amma a gaban kowa Layla ta fara fadin abubuwan da Mama ta sa ta dinga aikatawa wanda har shaidan ya ingizata ta fada mummunan aiki-ZINA. Daga nan ta kore ta akan bata so ta qara ganin ta.. sannan she made it clear to her cewar she should consider her dead!!
Su Umma basuyi mamakin jin abubuwan da Layla ta fada ba domin kuwa sun sani cewar Mama can do anything for money.
Anan dai Layla ta nemi yafiyar Umma da Ameera akan abubuwan da tayi musu.. a ciki kuwa harda ture Ameera da tayi wanda yayi sanadiyyar kwanciyarta a asibiti kafin aurenta da Zayd.
Daga Umma har Ameera sun yafe mata domin kuwa a halin da ake ciki a wannan lokacin she is in a much bigger problem than that.. Sun lallashe ta akan ta kwantar da hankalinta har Abba ya sauko.
Layla dai a nan sashen Umma tayi zaman ta.. Umma ta kula da ita sossai, bata nuna qyama a gareta ba ko kadan.. sabanin yadda mahaifiyarta ta nuna mata.
Ko da Ameera ta fadi ma Zayd abinda Layla tayi mata he wasn’t surprised domin kuwa ya sani.. lokacin da suke asibiti suna magana da ya zo wucewa he heard them talking about it and that was when he decided to just marry her dukda she was unconscious don ya ga tsiyar su! Ameera tayi mamaki matuqa na yadda Zayd bai taba fadi mata ba.. he really is a peaceful guy!!
STORY CONTINUES BELOW
Wasa-wasa dai sai da aka yi sati biyu ana lallashin Abba akan zancen Layla.. Kullum Zayd da Ameera suna gidan suna lallashin shi.. da qyar ya saurare su and he called for a general meeting in order to make his final decision akan Layla.
Aikuwa dama lokacin su Ibrahim sun dawo hutun mid semester and so the family was complete.
On the faithful day gaba dayan su suka halarta a falon Abba yayinda suka saurari labarin abinda ya faru tun daga farko har qarshe daga bakin Layla.
Mama dai tunda Layla ta fara bayani hankalinta yake a tashe yayinda take ta zubar da hawaye na munfinci. Su Ibrahim sunyi mamaki matuqa.. sun sani cewar halin Mama bayada kyau amma basu taba tunanin munin halin nata ya kai haka ba.. Sun yi tir da halin uwarsu yayinda suka ji tsananta a ran su…
Abba ya nuna fushin shi matuqa zuwa ga Layla.. yayi mata fada sossai sannan daga baya ya yafe mata abubuwan da ta aikata tunda dai babu yadda zai yi (aikin gama ya gama) and in the end yayi mata nasiha tare da bata shawara akan ta koma ma Allah, ta duqufa wurin neman gafarar shi har zuwa lokacin da zata koma gareshi.
Mama kuwa ko da ta bude baki zatayi defending kanta, Abba ya dakatar da ita ba tare da yi mata fada na abinda tayi ba ko kuma yayi mata nasiha.. Abinda kadai ya furta shine “Allah ya isa tsakani na da ke kuma ki je na sake ki saki uku”2
Daga nan kuwa ya umurce ta akan ta tashi ta bar mishi gida kuma kar ta kuskura ta qara waiwayo shi balle yaran shi… bai jira komai ba ya miqe tare da kallon dukkanin su a falon yace “duk wanda ya waiwayi wannan matar a cikin ku ban yafe ba” daga nan kuwa ya juya ya bar falon.12
A wannan karon kuwa jikin Umma, Zayd da Ameera yayi sanyi domin kuwa intention dinsu was to actually help her but Abba ya daure hannuwan su. Gaba dayan su sun san lallai ran Abba ya baci amma basuyi tunanin zai dauki mataki mai tsaurin haka a kanta ba musamman idan aka yi la’akari da tsawon shekaru da suka yi tare.
Gashi yace kar wanda ya WAIWAYE ta.. babu shakka she has crossed all limits!
Haka Mama ta dinga birgima tana kuka tana roqon yaran nata akan su yafe mata ko zata ji sanyi amma ko kallonta basuyi ba.. She has ruined Layla’s life, she has ruined her marriage.. bata cancanta ta zama Uwa ba.. A yadda su Ibrahim suka taso ta sanya musu tsanar ‘yan uwan su-Ameera da Aliyu, da sun biye mata suma da ta jefa su wani hali.
Miqewa ma suka yi suka bar falon harda Layla.
Ko da ta koma kan su Umma haquri kawai suka bata tunda babu abinda zasu iya yi mata. the truth is ta ci amanar aurenta da yaranta kuma abinda ya samu Layla is irreversible.. she has to face all that will come on her own!
Mama dai qin barin gidan tayi da farko.. har sai bayan kwana biyu da Abba ya ji labarin bata bar gidan ba ya sa Securities suka fitar da kayanta waje sannan aka ingiza ta da qarfi da yaji… tana kuka tana birgima haka ta tattara ta bar gidan.
Gaba daya yaranta babu wanda ya nuna tausayawa a gareta domin kuwa abinda tayi ko alama its unforgivable! Gwara su haqura da ita su rungumi Umma da Abbansu su cigaba da samu tarbiya ta qwarai..
Da wannan ne tarbiyar su Ibrahim ta koma hannun Umma.. ta dauke su tamkar yadda ta dauki yaranta Aliyu da Ameera.. haka suma suka dauke ta tamkar ita ta haife su.
A bangaren Layla kuwa ta duqufa addu’o’i tare da roqon Allah gafara yayinda ta cigaba da samun kulawa ta musamman daga wurin Umma.. Dukda hakan kuwa kullum tana cikin nadama da qunci.. cikin qanqanin lokaci ta bi ta rame ta lalace… Haka zata rufe kanta a daki tayi ta rusa kuka daga baya kuma tayi shiru don kanta.. that’s life!!
Qawayen ta Yusra da Maryam sun ji labarin abinda ya faru.. (dayake dai labarin duniya baya boyuwa) Basu yi mamaki ba don kuwa dama an riga an fara jita-jitar cewa cutar Aids ta kashe Habib wanda suka riga suka fara zargin itama Layla bazata rasa ba tunda dai sunyi mu’amala da shi.. Ga labarin rasuwar qawar su da ya bi gari… abun dai duk babu dadin ji! Sun je har gida sun jajanta mata abinda ya faru tare da bata shawarwari masu amfani as usual..
STORY CONTINUES BELOW
Bayan kwana biyar da tafiyar Mama ne Zayd ya zo ma Abba da labarin ya kammala formalities na tafiyar Layla qasar Vietnam don ta samu treatment (a special request from Ameera)
Da farko Abba hanawa yayi don kuwa babu wanda bai san cewar cutar Aids batada magani ba.. he understood cewar Zayd da Ameera wanted to help but in this case ai kashe kudin shi kawai zaiyi a banza tunda dai waraka bazata samu ba but Zayd ya fahimtar da shi cewar Vietnam sun qware sossai wurin treatment na cutar dukda ba warkewa ake yi ba amma they help people to stay healthy and even live longer by the grace of God through counseling.
Abba had no choice but to agree (kun dai san halin Zayd idan ya kafe akan abu musamman wannan din da gimbiyar shi ce ta kasa ta tsare)
Abba da Umma sunyi ma Layla nasiha sossai tare da yi mata fatan alkhairi.. Da wannan ne tayi sallama da su ta tafi qasar Vietnam don samun treatment..
Zayd yayi registering din Layla a babban asibitin qasar mai suna Franco-Vietnamese hospital wanda ya kashe millions of naira in order to get the best doctor to treat her.. and subsequently zai cigaba da biyan all of the expenses na treatment da counseling dinta tunda dai abu ne wanda has to continue…
Again Zayd ya sama mata wani luxurious and well furnished apartment a qasar tare da ajiye mata permanent nurse da wata mai aiki wadanda zasu cigaba da zama da ita suna kula da ita. Haka ya cika mata bank account dinta da kudade…
Ba tare da bata lokaci ba kuwa ta fara treatment dinta and it was going smoothly.. an gano cewar HIV dinta bai yi developing to AIDS ba don haka nan da nan aka dora ta akan antiretroviral therapy (ART)
A kullum tana waya da mutanen gidan wanda a koda yaushe idan suka yi waya da Ameera sai tace mata tayi ma Zayd godiya for everything…
Rayuwa kenan!
Ameera da su Ibrahim suna visiting dinta idan suka yi Hutu.. Haka itama tana zuwa Nigeria bayan lokaci don ta gaida Mahaifinta da Umma. A duk lokacin da ta zo Nigeria kuwa musamman take zuwa gidan Ameera wurin Zayd ta qara yi mishi godiya na dawainiyar da yake yi da ita…
The truth is Layla was supposed to live the life of a princess domin kuwa duk wani abun jin dadi Zayd yayi providing mata a qasar Vietnam but deep down within her she couldn’t stop thinking about cutar da take jikinta.. this always bring her back to kalaman da Abba yayi mata a ranar da ta basu labarin abubuwan da suka faru.. Kalaman da har ta mutu bazata manta su ba:
“Layla baki kyauta ma rayuwar ki ba.. baki kyauta mun ba sannan baki kyauta ma Umma da ‘yan uwanki ba. Kin shafa ma family din mu baqin fenti wanda bazai taba gogewa ba.. kin shafa ma kanki baqin fenti wanda har ki koma ga mahaliccin ki bazaki taba jin dadin rayuwa ba.. Na sani cewar mahaifiyar ki bata da dabi’u masu kyau amma ban taba sanin cewar abun nata ya kai haka ba… mu qaddara ta baki shawarwari marassa kyau wadanda da kanki kika fadi cewar kin san ba masu kyau bane.. akan wane dalili yasa baki gaya mun ba?? kin san yadda nakan tara ku tun kuna yara don in ji matsalolin ku a rayuwa sannan in nemi hanyar magance muku su.. meyasa ko da wasa baki taba kawo wannan zancen ba?? yanzu da kika zabi hanyar banza kika je kika sayar da jikin ki saboda kudi yau me kika amfana da shi??? ina kudin?? ina mutuncinki??? duka babu sai muguwar cuta da kika kwaso. ita mahaifiyar taki shin ba zaune take a gidan mijinta ba?? me zai sa sai ke ce zaki aikata Zina don ki kawo mata kudi? ita me ya hana ta fita ta aikata Zina ta samo kudin? kin ga kenan ta cuce ki sannan kin cuci kanki.. Yanzu fisabilillah Layla ina zaki samu mijin aure?? ya zaki cigaba da rayuwa knowing you are HIV positive??? kin sani cewar hatta ‘yan uwan ki maza a duk lokacin da suka samu matan aure dole sai wannan zancen naki ya fito??? shin baki san amfanin bincike da ake yi ba kenan idan za’ayi aure?? Layla, na yafe miki duniya da lahira saboda ni mahaifin ki ne. Ina mai tabbatar miki cewar rayuwan nan zata yi miki wahala.. zaki fuskanci matsaloli da tsangwama iri-iri daga wurin mutane.. Dole ne kiyi haquri, ki cigaba da roqon Allah gafara sannan kiyi tawakkali. ki dage da aikata ayyuka na qwarai and then you will find peace…Allah ya shirya mana zuri’a”
STORY CONTINUES BELOW
Tabbas ta samu matsaloli domin kuwa ko a asibitin an san bangaren masu cutar don haka zaka ga mutane suna qoqarin janyewa daga wannan bangaren.. A dalilin wannan cutar she cant even live in her country, she cant be with her family, she cant continue schooling saboda gani take yi kamar kowa ya sani sannan qyamarta ake yi, babu mijin aure.. wacce rayuwa kenan???
Tsawon shekaru uku rayuwa ta kasance ma Layla a haka.. babu cigaba!
Meanwhile mates dinta a makaranta sunyi graduating.. Ameera ta gama da first class.. ita kadai ta gama da first class a ajin nasu yayinda Zarah, Yusrah da Maryam suka gama da second class-upper which is very good.
Wata daya kacal da graduation dinsu kuwa aka yi bikin Maryam da saurayinta Khalil.. Layla bata samu daman zuwa bikin ba a dalilin wani counseling session da sukayi.. ta kira a waya ta ba Maryam haquri wanda she understood.
Yanzu haka presently itama Yusrah an sa ranar bikinta saura wata biyu.. Zata auri wani cousin dinta wanda ya dade yana bala’in sonta amma tana ta ja mishi rai… daga baya dai ya lallaba ta suka daidaita har an sa rana..
A bangaren dangin Abba kuwa gaba dayan su Zayd yayi furnishing dinsu.. dukkanin su both close and far relatives yayi transforming dinsu.. Aikin Hajji kuwa babu wanda bai je ba saidai yaro wanda shekarun su basu kai ba.. they are all living a good life Masha Allah!!2
***************
MAMA???
A lokacin da Mama ta bar gidan Abba dai gidajen qawayenta tayi ta bi don samun wurin fakewa kafin ta san abin yi amma abin mamaki dukkan su suka juya mata baya.. kowacce da irin excuses din da ta dinga bayarwa. Asali dai tsoro suke ji kar ta jibga musu cutar idan ta kwasa daga wurin ‘yarta tunda dai dama ta bi su ta gaya musu before now.
Da tayi sa’a ne ma Hajiya Zuwaira ta bata kyautar naira dubu Goma.
Da ta rasa wurin zuwa kuwa sai ta nufi tasha don zuwa Kano.
Asali dai iyayen Mama sun dade da rasuwa.. Gidan gadon nasu Yayan ta Badaru shine yake zaune a ciki tare da matar shi da yara bakwai.. Gidan ma yayi musu kadan sannan shi din ba qarfi gareshi ba balle ya gyara.. Asali ma Abba ne yake dan taimaka mishi wanda duk wata yakan tura mishi kudi. Mama kuwa ta watsar da shi gaba daya saboda baya da shi.. hatta dan hutu yakan so ya tura cikin yaran nashi su je suyi mata a Kaduna amma sam bata amincewa.. Gaba daya ma babu ruwan ta da shi, ko waya idan ya kira bata dauka duk dai saboda talaka ne… toh gashi kuma ta shuka tsiya a gidan miji ya koreta zata dawo mishi babu ko kunya… Rayuwa kenan!
Aikuwa dai ko da ta isa Kano ta sauka a gidan gadon nasu hankalinta yayi matuqar tashi domin kuwa yanayin gidan sai ahankali.. Ko da ta ba Yayan nata labarin abinda ya faru bai yi mamaki ba tunda har ta wulaqanta shi a matsayin shi na dan uwan ta wanda suka fito daga ciki daya… Ko da ya jajanta mata abinda ya faru ya sanar da ita halin da yake ciki wanda idan ta ga zata iya zama tare da su… fine, idan kuma bazata iya ba toh gwara ta san inda dare yayi mata.
Aikuwa Mama ta shiga tashin hankali… Na daya dai an gwada mata cewar a cikin dakin ‘yara mata zata dinga kwana tunda babu extra room, abinci kuwa idan ya samu sau biyu ne a rana.. Ya fadi mata gaskiya akan cewar Kudaden da Abba yake tura mishi hadawa yake yi da wanda yake dan samu a sana’ar shi ta gini ya biya ma yaran shi Maza kudin makaranta don kuwa bazai amince su girma su zama kamar shi ba-babu boko balle su samu aikin yi don kuwa rayuwa tayi wahala gashi ‘yan uwa basu dafa ma junan su!
Ni kuwa nace ya jefe ta da magana🤣
Mama dai had no option but to stay don haka kuwa ta tura kayanta cikin dakin yara mata. Yaran kuwa dayake sun san labarin irin wulaqancin da take yi ma mahaifin nasu lokacin da take da kudi sai suka qudiri niyyan karta mata rashin mutunci.
STORY CONTINUES BELOW
Bazasu tashi hira ba a dakin sai sun ga Mama ta samu bacci ya fizge ta… babu shiri hayaniyar su take tashin ta. Haka aka raba aiki a gidan.. a cewar su tunda uban su yana kawo abinci tana ci dole ta sa hannu a aikin gida.. babu shiri kuwa aka ba Mama portion na aiki, wanke-wanke ta dauka saboda dai bazata juri duqawa yin shara ba!
Matar yayan nata tana kallo yaran suna karta mata rashin mutunci amma sam bata magana.. dama dai haushin Mama take ji saboda irin wulaqancin da tayi musu a baya. Shima haka Badaru kawai ya barta ta zauna tare da su ne for humanity sake amma sam baya wani shiga lamarin ta.
Bayan shekara daya ne Badaru ya samu daman shiga wani kamfani na gini wanda har kamfanin suka samu project daga wurin gwamnatin Gombe state.. Makarantu ne da gidaje na gwamnati za’a gina masu yawan gaske.. aikuwa nan da nan ya tattara ya tafi. Tsakanin shi da Kano saidai aike na kudi domin kuwa baya samun lokacin ziyartar iyalin nashi.
Bayan shekara daya suna ta aikin wannan project din ne kwatsam watarana Badaru ya zo Kano da babban albishir.. An biya su kudaden aikin su masu yawa har ya siya gida dan madaidaici a garin Gombe don haka ne ya dawo ya kwashi iyalin shi su koma can tunda rayuwa tana da sauqi a can kuma da alama Kamfanin da yake yi ma aiki a branch dinsu na can din zasu ajiye shi.. Murna a wurin iyalin shi ba’a cewa komai!
Mama tana ta faman washe baki tayi zaton da ita za’a je amma sai ta ga sun hada kayan su tsab sannan suka yi mata sallama.. Badaru ya bata kudi har naira dubu hamsin yace ta ja jari ta cigaba da ciyar da kanta, Gida kuma ya bar mata halak-malak. Tana kallon su suka tattara suka tafi suka barta da ita da tsiyar ta.
Mama kuwa ta zama ita kadai qwal… babu motsin kowa! sai ta gwammace gwara lokacin da su Badaru suke gidan.. dukda bata jin dadin zama da su tabbas gwara tana jin motsin mutane.. Sossai ta qara regretting abubuwan da ta aikata… Ta sanya ‘yarta a hanyar banza, ta guji ‘yarta lokacin da ta kamu da cuta, ta wulaqanta abokiyar zamanta da yaranta, gashi halinta na banza yayi sanadiyyar barinta gidan miji, dan uwan ta guda ta wulaqanta shi yanzu ya samu arziki daidai gwargwado ya tafi ya barta, ga yaranta sun guje ta a dalilin munanan halayen ta… Lallai tana cikin wani hali!2
Ganin idan ta tsaya wasa kudin da Badaru ya bata zasu qare ne ya sanya babu shiri ta shiga kasuwa ta siyo murhu, kasko, ta auno wake, gero da sugar da duk wani abinda zata buqata na sana’ar siyar da qosai da kamu ta dawo gida ta duqufa… A kullum da safe sai ta fito wajen gida ta hada murhu tayi ta tuyan qosai! Tun mutane basu ganeta ba har dai suka gane ta.. babu laifi tana ciniki don kuwa tana samun na abinci da sutura.
A haka ta cigaba da rayuwa with the hope that one day, yaranta zasu waiwaye ta su yafe mata!!3
Wannan kenan!!!
****************
ANWAR???
Asalin shi dan Nigeria ne from Bauchi state, Mahaifin shi ya kasance hamshaqin mai kudi, Yana cikin top dogs na NNPC a garin Abuja… Anwar shine the only son a wurin Mahaifin shi… Yanzu haka yana zaune a qasar Vietnam ne a dalilin treatment da counseling na HIV da yake yi… ma’ana shima yana dauke da cutar wanda shima nashi kamar na Layla, bai yi developing into Aids ba.5
Anwar ya kamu da wannan cutar ba ta hanyar banza ba.. infact matar shi ta sunna ita ta sanya mishi.6
Asali dai Mahaifiyar shi ta rasu tun yana qarami don haka a hannun kishiyar maman shi (Mummy) ya girma.. Mummy dai bata qaunar Anwar ko alama saboda ta kasa haihuwa kuma ta sani cewar Anwar shi ne magajin tarin dukiyar mahaifin shi.. ita kuma tana baqin ciki da wannan!
Abin mamaki shine babu wanda ya san cewar ta tsani Anwar domin kuwa nuna mishi so take yi a fili amma a badini kuwa neman halaka shi takeyi… wannan ne ya sanya daga shi har mahaifin shi suka yi trusting dinta blindly!
STORY CONTINUES BELOW
Tayi qoqarin kashe Anwar tun yana qarami amma Allah bai yi ba.. Bayan ya kammala karatun shi na engineering a qasar Germany ya dawo gida ne aka fara maganar auren shi… a wannan lokacin kuwa bayada budurwa don haka as soon as Mummy ta nuna zata samo mishi mata sai kawai ya bata green light.
Nan da nan ta hada shi da wata yarinya Mansura. Babu dangantaka a tsakanin su amma kuma ko da tayi introducing dinsu sai ta gwada relative dinta ce. Asali dai wannan yarinyar tantiriya ce sannan karuwa ta bala’i wadda take dauke da cutar HIV. Musamman Mummy ta daukota sannan ta biya ta akan ta auri Anwar ta sanya mishi cutar tunda dai cuta ce da ba’a warkewa dole zata kashe shi.2
Aikuwa haka aka yi… Mummy dai sai da tayi yadda tayi na yadda ba’a dauko maganar gwajin jini a asibiti ba.. dama dai tunda ta gwada relative dinta ce sai komai ya zama na gida.
A dalilin auren Mansura ne Anwar ya kamu da wannan cutar.. A lokacin da aka gano it was too late don haka the only thing Anwar and his Dad could do was send both women parking. Dukda sun rabu da matan nasu rayuwarsu bazata taba komawa daidai ba, Mahaifin Anwar yayi takacin wannan al’amari, duk tarin dukiyarshi bazai taba iya magance ma dan shi cutar da ta ke jikin shi ba..
After so much research akan best HIV counseling country ne suka gano Vietnam wanda nan da nan mahaifin Anwar yayi relocating din shi zuwa can yayi registering dinshi a asibitin Franco-Vietnamese hospital sannan ya samo mishi aiki through his influence and contacts a babban manufacturing company na Samsung da yake qasar.. A dalilin Anwar is a very intelligent engineer, tuni qwalwar shi ta kai shi sama wanda sossai ake ji da shi a kamfanin! They are aware of his situation na cutar da take jikin shi but basu damu ba, basu nuna mishi qyama ba ko kadan and sun bashi the respect that he deserves.
It’s just eight months kenan da ya fara zuwa wanda tun daga ranar da ya ga Layla ya kamu da sonta. It wasnt difficult for him to find out all about her and dukda labarin nata da ya ji he didnt care… a cewar shi the past is in the past and ya tabbatar tayi nadamar abubuwan da ta aikata a bayan. kuma tunda duk suna dauke da ciwon it’s not even a problem.
Duk iya qoqarin shi na ya samo soyayya a wurin Layla ya kasa.. Gaba daya ta qi ta bashi fuska.
A haka har ya hadu da Ameera da su Ibrahim a wani zuwa da suka yi… A maganganun da suka yi Ameera ta fahimci cewar Anwar yana bala’in son Layla. Ko da tayi confronting Layla akan maganar shi ta gwada mata cewar she is not interested in marrying anyone don gaba daya maza sun fita mata a rai.
Ameera tayi qoqarin convincing Layla akan ta amince da Anwar considering the fact that they can even live a normal life tunda analysis ya nuna musu cewar akwai 99.6% probability na cewar idan suka kiyaye dokokin ART zasu iya haifan a healthy baby free of HIV amma ta qi.. Abu kamar wasa shi ya nace sai ita yayinda ta kafe akan bata yi da shi.3
Sati uku da suka wuce ne Ameera take ba Zayd labarin situation din Anwar da Layla da kuma yadda shi Anwar din yake yawan kiran ta a waya yana roqonta akan ta lallashi Layla ta amince da shi.. Zayd actually understood Layla’s point of view toh amma it doesnt mean haka zata zauna babu aure har ta mutu… ko babu komai aure ai raya sunnan manzon Allah (SAW) ne kuma idan tayi shi zata qara samun natsuwa don haka ya karbi lambar wayar Anwar tare da fadi ma Ameera ta bar komai a hannun shi…
toh me zai yi?????
End of flashback!!!!
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
One Week later!!
AMEERA Z. A. FADOUL SUITE
20TH FLOOR, BURJ KHALIFA- DUBAI
Zaune suke a babban lounge na Suite din yayinda suke ta hira.
Abba, Umma, Abbu, Ammi, Zayd, Ameera, Layla.
STORY CONTINUES BELOW
A yau da safe Zaheera da family dinta suka tafi qasar London a dalilin wani seminar da shi Mijin nata Sadiq zaiyi attending a can.. Maheera da Meher tare da twins din Ameera went with them.
Su Ibrahim kuwa sun fita shopping a Dubai Mall. Sauran dangin su Abbu kuwa tun kwana uku da suka wuce ne suka koma Saudiyya. Dangin Ammi da Abba ma shekaran jiya da safe suka yi boarding Jet din Zayd suka wuce Nigeria.3
Zara, Mustapha, babyn su da Nanny dinshi kuwa jiya suka tafi qasar France wanda sati daya kawai zasuyi su dawo Dubai. Shima dai Mustapha wani official aiki ne zai kai shi, da farko ma ba tare da su Zara zai je ba amma kuma daga baya sai suka canza plans suka tafi tare.
Su kansu su Abba banda don Zayd da yayi delaying tafiyar nasu da tun da safen yau sun tafi a cikin jet din Abbu. Yanzu haka da yamma zasu wuce.
Suna cikin hira ne wayar Zayd tayi ringing yayinda ya duba…. yana murmushi yayi answering.
“Yes, kana waje???” ya dan yi shiru sannan yace “okay toh, gani nan” daga nan ya kashe waya tare da miqewa yace “Finally wanda nake so ku hadu da shi ya iso”
Ammi ce tace “aikuwa dai na qagara in ga ko waye wannan da har aka yi mana delaying tafiya saboda shi”
Gaba dayan su suka fashe da dariya.
Ko da na bi bayan shi da ya bude qofa wani kyakyawan saurayi na gani. Shi ba baqi ba sannan ba fari ba, dogo ne sannan ba mai jiki ba. A fannin kyau kuwa zai yi making 5/10 na list din da Zayd ya zo na daya.
Not bad abi???🤣
Gani nayi sunyi musabaha yayinda suke yi ma juna murmushi.
“Good to finally meet you in person Anwar”
Anwar yace “same brother..”
“are you ready???”
Sakin ajiyar zuciya yayi sannan yace “more than ever my friend”
“Alright then, please come in”
Layla wadda take riqe da wayarta tana qoqarin qarasa booking flight dinta to Vietnam against Gobe ne ta jiyo muryar shi kamar daga sama.
Da sauri ta dago kai ta ga Anwar tsugunne a qasa yana gaida su Abba.
Ranta ne yayi mugun baci yayinda na ga ta miqe tsaye zata bar falon.
“Layla sit back down” Zayd ya fada in a commanding tone.
Da sauri ta koma ta zauna yayinda take ta danna ma Anwar harara. Ita kuwa Ameera dariya ce take nema ta subuce mata amma ta matse.
Abbu ne yace “bawan Allah ga wuri ka zauna mana..”
Anwar yayi godiya ya zauna.
Zayd wanda yake tsaye a kusa da Anwar din ne yace “uhm.. wannan shine wanda yayi delaying tafiyar ku da safen nan. Sunan shi Anwar Shehu Misau…”
“Wait kana nufin yaron gidan Engr. Shehu Misau ne???” Abbu yayi tambaya
“Yes sir.. Ni ne” Anwar ya amsa shi.
“Masha Allah.. na san mahaifin ka sossai ai.. he is a very good friend of mine plus he is a nice man” Abbu ya fada yayinda ya kalli Zayd yace “Muna ta son mu hada ku ashe kun san juna”
“Not until recently Abbu.. asali dai ya zo ne akan maganar Layla…” Zayd ya fada tare da dafa kafadar Anwar sannan yace “Go ahead bro…”
Daga nan kuwa Anwar ya basu taqaitaccen labarin shi sannan ya yi musu bayanin yadda yayi wata da watanni yana neman soyayyar Layla amma ta qi ta bashi.. Layla dai tunda ya fara magana kan ta yake a duqe, A yadda ta ji yana zuba bayani babu shakka Anwar yana masifar sonta, ita kanta sai da ta ji kunya na yadda ta qi tsayawa ma ta saurare shi da har ta bari zancen ya kawo kunnuwan su Abba..
STORY CONTINUES BELOW
Bayan ya gama bayanin shi kuwa duk suka cika da tausayin shi yayinda suka jajanta mishi akan wannan mummunan qaddarar tashi..
Abba wanda ya cika da takaicin Layla ne ya kalle ta sannan yace “idan baki son shi wa kike so??? kina nufin haka zaki zauna babu aure saboda cuta da kike da ita??? shin baki san aure raya sunan manzon Allah (SAW) bane? baki san auren shine kwanciyar hankalin ki ba?? toh bari ki ji in gaya miki… idan dai ni na haife ki…”
Tun kafin ya qarasa maganar shi tace “Abba na amince da shi… kayi haquri don Allah” ta qarasa fada yayinda take share hawayen fuskarta.
A duniyan nan tayi ma kanta alqawari there is nothing da Abba zai so tayi wanda bazata yi ba.. da ace tun farko ta kiyaye dokokin shi ta yi aiki da nasihun da yake yi musu tun suna yara sannan ta tashi a cikin tarbiya mai kyau wadda ya basu she would have been married to ZABIN TA but a yanzu haka bata da Zabi.. whatever comes to her, she has to accept in good faith.
Anwar dai zaro idanuwa yayi cike da mamaki.. bai taba sa ran komai zai zo mishi cikin sauqi ba. Kenan plan din Zayd worked for him!
“Masha Allah Layla.. kin kyauta ma kanki. Allah yasa hakan shi ya fi zama alkhairi” Umma ta fada.2
Gaba dayan su suka amsa da Ameen
Abba ne yace “Anwar duk lokacin da ka shirya zaka iya turo manyan ka sai ayi maganar aure.. mu kuma zamuyi bincike a bangaren mu kamar yadda addini ya buqata. Fatan mu Allah ya qara muku lafiya, yayi muku albarka”
“Nagode sossai Abba, ni kam a shirye nake don haka zan kira Daddy a waya in shaida mishi insha Allah”
Abbu ya kalli Abba yace “ai ina mai tabbatar maka Anwar ya fito daga gidan arziki.. his father is a very respectable man in the society don haka banda don wannan qaddarar da ta afka mishi I am sure baza’a samu matsala ba a bangaren shi”
“toh Masha Allah, ai haka ake so.. Allah yayi albarka”
Gaba daya suka amsa da Ameen.
Daga nan dai suka cigaba da random hirar su like the one big family that they are.. Anwar ya ji dadin yadda aka karrama shi, they treated both him and Layla kamar babu wata cutar da take tare da su, tabbas Family love and care is a very important pillar na rayuwar dan Adam.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
2 Months Later!!
ANWAR SHEHU MISAU RESIDENCE
HO CHI MINH CITY -VIETNAM
Wuraren qarfe tara da rabi na safe tana kwance a kan gadon dakinta cikin Duvet tana bacci.
Anwar ne ya bude qofar dakin ya shigo riqe da tray na abinci.. da alama dai breakfast ya hada musu.
Kwana biyu kenan da aka kammala bikin Anwar da Layla wanda aka yi a qasar Nigeria. Bikin dai was just a small one domin kuwa family ne sai close relatives da friends.. Babu wani sha’ani da aka yi domin kuwa ana gama daura auren su akan sadaki naira dubu dari biyu ne aka yi yinin biki a nan gidan Abba and daga nan ne amarya da ango suka yi tahowar su Vietnam wanda dai dama nan zasu zauna saboda treatment dinsu..
Ameera ta so Layla tayi haquri haka nan ta yafe ma Mamanta ta gayyace ta bikin amma sam Layla made it clear that she wants nothing to do with her.. Over the years Ameera tayi qoqarin re-uniting su Layla da Maman su amma sam sun qi.. Initially tayi zaton zai fi sauqi ta shawo kan su Ibrahim amma inaaa, da ta fara yi musu maganar sai su tashi su barta ita daya.
Yes, Nobody really knows where she is amma ta sani cewar neman ta ba abu bane mai wuya.. the most important thing is for them to forgive her.. tayi alqawarin watarana sai ta shawo kansu sun yafe mata, dukda ba dawowa gidan Abba zata yi ba atleast she will feel better!
STORY CONTINUES BELOW
Bayan Anwar ya ajiye tray din a kan bed side drawer ne na ga ya haye kan gadon ya qura mata idanuwa…
Abinda ya faru tsakanin su jiya ne yake dawo mishi.. rikici sossai suka yi da Layla sannan ta amince suka yi saduwar aure.. dukda ba wani dadewa suka yi ba he was very much grateful for the little goody he got.. Ya sani cewar he has to remain patient har a hankali ta saki jiki da shi.. he understands that abubuwan da suka faru a baya ne suke haunting dinta amma yayi ma kanshi alqawarin cewar he will make her forget her past completely!
Gani nayi ya shafa fuskarta ahankali sannan yayi mata kiss a baki..
Ahankali ta bude idanuwanta tana murmushi tace “hey..”
Murmushi yayi sannan yace “I love you, I promise you everything in this life, I promise to live and die for you.. you are my queen and I shall be your slave for the rest of my life”
Fashewa tayi da dariya tace “hey shut up.. I dont want you to be my slave.. I want you to be my love and my best friend.. just that”
Matsawa tayi ta kwanta a jikin shi tace “Hey, I am sorry for yesterday… na sani cewar ban baka abinda kake so just as you deserve ba amma I promise to work on myself…”
“Ssssshhhhhh, there’s no problem my love, I understand. the most important thing is we have eachother and we shall remain strong to continue fighting our illness together insha Allah” ya shafa cikinta ya cigaba da fadin “Allah ma ya sa na yi ajiya a nan.. I swear I just can’t wait to have a child”
Layla ta zaro idanuwa tace “so soon?? ni kam wallahi tsoro nake kar mu haifo baby mai dauke da HIV, I cant bear to see a child going through what we are going through right now”
Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “Insha Allah idan muka kiyaye dokokin likita we shall give birth to a HIV-free child.. Remember with a smooth ART, there is 99.6% chance na cewar zamu iya haifan yaro marassa cutar?? please let’s be optimistic and hopeful”
“Insha Allah.. I love you”
“I love you too my Love” ya fada tare da qara matse ta a jikinshi.
Tamat bihamdulillah!!!