ZAFIN RABO CHAPTER 1 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 1 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Da sunan Allah mai rahama mai jin k’ai.

+

Kaiwa da kawowa ake a cikin makeken gidan minister d’innan da yake a unguwar maitama a garin Abuja, gidan cike yake da y’an uwa da abokan arziki, fuskar kowa ka gani a cikin gidan tana d’auke da farin ciki da anushuwa, dan yau ne za’ayi babban bak’o,

A makeken parlor din gidan duka bakin suka zazzauna da yake dukkan su mata ne, ga kowa yayi kyau yayi shigarsa ta alfarma, barin ma matar gidan Hajia Rahima, wacce yau zuciyar ta k’al take d’auke da tsan tsan nishad’i kamar amma ta alkwari da gidan Aljanna.

1

“Yau ne dawowar babban d’an mu, wanda shekara da shekaru bai tako k’asar Nigeria ba, ni kaina da nake uwar d’akinsa bansa shi a cikin idanuna ba har na tsawan shekaru takwas, dan haka dole ne yau mu ci, mu sha kuma mu rawsaya, mu ragaje, muyi shoki dan kawai mu nuna farin cikin mu, ko ya kuka ce y’an uwa?”

Hajia laraba wacce take babbar aminyar matar gidan tayi jawabin tare da k’arashe maganarta da tambaya, ai kuwa gaba d’aya matan wurin suma shewa suka saka dan ba abunda zai hana su nuna farin cikin su yau,

Hajia rahima mik’ewa tayi ta zaman da take lokacin da wayar ta ta d’auki yin ruri alamun kira, fita tayi daga wurin hayaniyar, yayin da ta latsa wayar ta saka ta a kunne tare dayin sallama,

“Mami gani na iso airport ance nan da minti talatin jirgin su zai sauka, dan haka ku shirya ganin mu nan da awa d’aya da rabi”

Aka sanar da ita daga d’aya b’angaran, wani farin ciki taji ya k’ara kamata, hak’ika sanda take ma tilon d’an nata namiji ba k’aramin so bane, yau rabun ranta zai dawo kusa da ita, zatayi bacci harda munshari, godiya ta shiga yima na d’ayan b’angaren had’e da kashe wayar bayan sunyi sallama, koma wa parlor din tayi da sauri dan sanarwa abokan ta d’an nasu ya kusa shigowa.

—–

Sanya yake cikin dark blue jeans, da white shirt ya d’ora dark blue jeans jacket a samanta, bayan shades d’in daya d’ora a fuskar sa, yayi mutuk’ar yin kyau, kayan sun k’ara fitowa da farar fatar shi, duk inda ya taka sai an bishi da kallo saboda ya had’u, had’uwa ta k’arshe, tafiyar shi yake a niste kuma tafiyar kasaita, hannun shi d’aya rik’e da waya da take manne a kunnan shi, d’ayan hannunshi najan akwatin shi.

Waige waige yake yana jiran ganin inda babban abokin nashi zai b’ullo, bai kai k’arshen tunanin shi ba yaji an tab’a shi ta baya sauri yayi ya juya ya ganshi tsaye yana washe mishi hak’ora, shima d’in murmushin ya saki, murmushin da yake k’ara mishi mugun kyau, abokin nashi ne ya jawo shi jikin shi yana fad’in,

“Welcome back bro”

Murmushi ya k’ara saki, dukda ya tsani nigeria, ya tsani zama a cikin ta, yayi bala’in kewar y’an uwan shi da abokan shi, Imran ne ya sake shi daga rik’e shin da yayi, nan suka fara wasa da dariya har suka isa inda yayi parking motar shi, suna shiga ya kunna ya fara tuk’i, ci gaba sukayi da rahar da suke a cikin motar imran na bashi labarai kala kala, shi kuma ba abunda yake sai dariya, sun d’an dad’e suna hira, sai can kuma abokin nashi ya fara cewa,

“hope you’re prepared dan na gaya maka mami ta tara mutane a gida suna can suna celebrating dawowar ka”

KAMAL girgiza kanshi yayi, baiyi mamaki ba, daman tafi kowa san ya dawo, kullum sukayi waya tana cikin yin mita, ya guje ta ya guji y’an uwanshi, ba irin threatening d’inshi da bata yi ba dan ya dawo har daga baya ta gaji ta hak’ura,

Imran ne ya k’ara cewa,

“Wai kasan ta yaya nayi convincing d’inta ta zauna a gida kuwa, da kana fitowa zaka ga jerin motoci a gabanka, bayan marok’an da ta d’auko suna wak’e ka, sai dai kawai ta tara maka jama’a”

Dariya suka saki duka su biyun, KAMAL baya amsa shi sai jefi jefi, daman shi magana bata dame shi ba, haka Imran ya dunk’a jan shi da hira har suka iso k’ofar makeken gate d’in gidan,

Suna shiga harabar gidan ya nemi farin cikin shi ya rasa, gaban shi yayi wani irin mummunar fad’uwa, zuciyar shi ta fara mahaukacin bugawa a cikin k’irjin shi, hannuwan shi guda biyu suka jik’e sharkaf da gumi, gaskiya yana ji yana da matsala, iyayen da suka tsugunna suka haife shi na cikin gidan amma duk duniya shi ne abu na biyu daya tsana, ba abunda yake san nisanta sama dashi, ji yake dama zai iya juyawa ya gudu ya koma inda ya fito, ya tsani garin nan, ya tsani zama a cikin shi, ya ma tsani zama a k’asar gaba ki d’aya.

Imran da yaga har yayi parking ya fito amma shi bashi da shirin fitowa ne yayi sauri ya maida kanshi cikin motar tare da sa hannunshi ya tab’a shi, KAMAL firgit yayi ya dawo daga duniyar da yake, ya juya inda abokin nashi yake tare da zuba mishi wannan manyan idanun nashi,

“Ya dai?, ko jira kaki iyayen naka su fito har waje tarba’r ka ne”

Sauri yayi ya cire seatbelt d’inshi, kan Mami da gayyarta su fito dan shi yasan kad’an daga cikin aikin ta ne, abokin shi ba abunda yake in banda dariya, haka suka fara takawa har suka isa side d’inta, tun kan suyi sallama aka banko k’ofa aka fara yin gwud’a, wata irin azababbiyar kunya ce ta kama KAMAL, shi fa duk abunda zai sashi ya zama center of attention ba san shi yake ba, baya san hayaniya dan bashi da wuyar yin ciwon kai,

Maman shi ce ta kamo hannushi tayi cikin parlor d’in dashi, kan kice me gaba d’aya y’an tsufafun nan sun rufe shi suna mishi ya gajiyar hanya, shi dai sai dai ya sunkuyar dakai ya amsa haka dai har ya samu suka mar matsa daga kanshi, nan aka k’ara zama aka saka shi a gaba da tambayoyi, bai samu ya samu kanshi ba sai da aka kusan azahar, shima ce musu yayi zaije ya d’an watsa ruwa sannan yayi sallah, yasan da ba haka yayi musu ba da baza su k’alle shi ba.

Yana zuwa k’ofar side d’inshi ya tsaya cak tare da zuba wa k’ofar kallo, ba abunda yake jin tsoro illa shiga cikin wurin dan yasan mai zai tarar, shekara takwas yanzu, wani zaiyi zatan ya manta, ya hak’ura saboda harta uwar da ta haife shi rayuwar ta take yi kamar bai tab’a zuwa duniya ba, amma banda shi, har yanzu yana jin zafin abun a zuciyar shi, har yanzu yana ganin abun kamar jiya ya faru, lumshe idanun shi yayi dan ya samu ya tattro nustuwar shi, can ya bud’e tare ta tura k’ofar ya shiga ciki,

K’ara tsayawa yayi da ya shiga makeken parlor d’inshi, parlor d’in ya canza gaba ki d’aya an saka sabun furnitures an kashe mishi kud’i, ya tabbata ya shiga cikin bedroom d’inshi abu d’aya zai gani, d’aga kanshi da yayi yaga k’aton hoto manne a jikin bangon parlor d’in, zuciyar shi ce ta k’ara wani mahaukacin bugawa, bai san lokacin da kwalla ta zuba daga cikin manyan idanun nashi ba,

Kamar za’a kiraka ka fito

Yayi maganar a zuci, ya dad’e a tsaye yana kallon hotan da kyar ya samu ya iya tattaro nustuwar shi, sannan yayi mishi addu’a a ranshi, ya goge hawayen da suka zuba a fuskar shi, tare da yin hanyar bedroom d’inshi dan ya samu yayi wanka da sallah ko zuciyar shi zata d’an sami nustuwa.K’arar horn d’in da taji tunda ga wajan gidan ne yayi firgit da ita, da sauri ta ajiye book din da take karantawa ta duro daga kan gadon tayi cikin bathroom d’inta a guje, cire kayan jikinta ta fara yi sannan ta shiga yin wanka, bata dad’e da fara wankan ba ta ji an turo k’ofar d’akin ta an shigo da mita, dariya ta dunk’a yi amma mara sauti yadda ta cikin d’akin baza taji ta ba, sai da ta gama wankan ta tsab sannan ta fito, jikinta d’aure da towel, tana shiga d’akin tayi sallama da ita tana daka mata harrara harda rik’e kugu, dariya ta saki yanzu dan ta bala’in bata dariya, bata kula ta ba tayi wurin dressing mirror d’in har lokacin k’awartata harara take mata, kallon ta tayi ta cikin mirrior ta sakar mata murmsuhi,

+

“Kina yin dai dai abun da kike?, tun nawa na kira ki ma nace ki shirya” k’awartata ta fad’a mata,

Ita kuwa ci gaba tayi da abunda take bata kula ta ba, sai da ta gama shafa mayuk’anta tsab ta mik’e tayi wajan drawer d’inta, ta fito da kayan da zata saka, wata doguwar riga ce ta atamfa, tasha stones,

“Aw Ina miki magana ma baza ki kula ni ba, kinsan Allah zan daina biyo miki irin way’annan abun dan kullum kina cikin saka mutum yin letti” k’awartata ta ci gaba da yi mata mita,

Juyowa tayi ta kalle ta, sai a lokacin ta fara shirin yin magana,

“To me zance, ko nayi magana baza ki daina mita ba na riga da nasan halin ki”

Ta fad’i mata tare da fara shirin saka kaya, tana jira taji k’awartata tayi magana taji shiru, itama k’ara share ta tayi ta ci gaba da shiryawar ta, bayan ta saka rigar ta koma gaban dressing mirror d’in ta fara shafe shafe a fuska, ba wata kwaliyar zafi tayi, d’ankwalin kayan ta d’auko ta d’awra akanta, sannan ta feshe jikinta da turare masu laushin k’amahin wanda sai ka matzo kusa da ita zaka ji,

Tayi kyau sosai, kayan sun mata kyau, tana da jiki amma ba sosai ba ga dirin ta masha Allah, shi ya saka bata cika sa kayan ta zasu matse ta ba, kullum tana cikin saka free kaya, kayan da za su saka ta zama comfortable, bayan ta k’ara duba kanta tsab a mirror ta juya wurin k’awartata,

“Shall we” tace mata

Hamida, mik’ewa tayi itama, suka yi hanyar fita daga d’akin bayan ta d’auki mayafi da haka, tambayar ta tayi ko mommy na nan dan ta l’eka ta gaishe ta, cewa tayi a’a ta fita, haka suka k’arasa motar suka shiga, Hamida ce ta kalle ta bayan sun gama saka seatbelt ta kunna motar tare da yin horn dan a bud’e mata gate,

“Kinsan Aliyu zai je reunion d’in?” ta tambaye ta,

Wani irin kallo tayi ma k’awar tata, a lokacin Hamida ta saka hancin motarta tabar haraba gidan,

“Dan Allah dan annabi me yasa kike gaya mun?, me ruwa na dashi”

Girgiza kanta tayi, shegen taurin kai ne da ita, gaba d’aya ta daina kula ko wane namiji tun bayan shi, ta rufe zuciyar ta ruf da kwad’o da muk’ulli ta hana kowa shiga, tak’i bawa kowa chance, haka take son k’arasa rayuwar ta ne, ta tambayi kanta a zahiri ma tambayr tayi mata,

“Wai ke haka kike sun gama rayuwar ki ba namiji ba aure, duk friends d’in mu sunyi aure nima nayi aure, so kike ki zauna ke kad’ai”

D’aga mata kafad’unta tayi,

“Ance dole sai kayi aure ne?, Ina san yadda rayuwa ta take, ba wani tension daga ni sai ni”

Hamida shiru tayi a wurin, sunyi maganar nan ba sau d’aya ba ba sau biyu ba, kuma kullum the same answer take bayar wa, tana ji baza ta tab’a canza ra’ayinta ba, tana mutuk’ar yiwa babbar k’awartata kwad’ayin gidan miji dan tana son ta mallaki gidan kanta da kanta, ta mallaki yay’anta ta kuma raya sunnar manzo, amma sam sam duk way’annan basa gabanta, k’ara sacen kallan ta tayi ta gefan idanunta taga hankalinta nakan titi,

“Har yanzu baki manta dashi ba? Har yanzu baki hak’ura kin fitar dashi daga ranki ba”

K’ara sacen kallonta tayi, taga ta lumshe idanunta, can ta bud’e su, shiru shiru bata ce komi ba, tayi zatan haka daga wurin ta,

“Shekara takwas yanzu SAKEENA, ai ko wani irin abu kike ji a zuciyar ki yaci ace yanzu kin manta, kinyi moving on”

Nan ma shiru, bata bata amsa ba, sun d’an dad’e a haka sai can ta juyo da sauri ta nuna ya da d’an yatsa,

“Don’t spoil my mood, Allah kika k’ara yin maganar shi zan bud’e k’ofar nan na dirga”

Yadda tayi maganar she’s very serious, Hamida dariya da saki hade da yin alamun zipping bakin ta, tana bala’in son aminyar ta, tana son farin cikin ta, ta san ta ciki da bai, tana ji ma duk duniya ba wanda ya santa kamar ta, shi ya saka take d’an d’aga mata k’afa wani lokacin, ba wanda ya k’ara cewa komi har suka isa harabar restuarant d’innan me suna Tulip Bistro da yake a wuse 2,

Class mates d’insu duk na waje na jiran kowa ya gama isowa tukunnna, suna parking, suka fito, matan suka fara iho suna rugume juna, yadda dai mata suke in sunga k’awaye, ga dama an dade ba’a had’u ba da wasu,

SAKEENA Kallon Hamida tayi,

“And you were complaining munyi letti, gashi da yawa basu gama zuwa ba”

Share ta k’awartata tayi, ta ci gaba da gaisawa da abokan nasu, SAKEENA kawai girgiza kanta tayi, basu dad’e a tsaye ba wasu suka k’ara zuwa a lokacin kawai sukayi deciding su shiga ciki su jira suaran, daman sunyi renting gaba d’aya wurin.

Bayan anci an sha, suna zaune suna hira wasu na d’aukar pictures, ita dai sai jefi jefi take magana dan bata cika san surutu ba, ga a tukure take saboda ta lura idanun wani tunda suka shiga yana kanta, fuskarta a d’aure take sosai dan kadama ya sami damar yi mata magana, Hamida ce ta tab’a ta tare da yi mata rad’a na Aliyu ya kasa sauke idanunshi daga kallanta, daka ma k’awarta harara tayi, duk had’e fuskar ta da take yi a banza, dan kawai ganin mutum tayi a gabanta yana sosa k’eya, k’ara shan kunu tayi ta had’e girar sama da ta k’asa,

“Dan Allah d’an minti d’aya”

Wani irin haushin shi taji a lokacin, eh tasan sunyi soyayya da suna secondary school amma a ganinta a lokacin soyyayyar yarinta sukayi, kowa ya manta yanzu yana harkar gaban shi, dan kawai ita kad’ai ce bata da aure a cikin su bai bashi damar da zai zu ya fara yi mata maganar banza ba, baza ta tab’a gane maza a rayuwar ta ba, ita ta manta dashi wallahi dan sun dad’e rabon su da juna, da taga dukda tayi shiru tayi banza dashi bai bar kanta ba, ta d’aga kai ta kalle shi cikin kwayar idanunshi,

“Ajiya ka bani da kake son gani na?,”

Kowa na wurin saida ya bar abunda yake yi saboda yadda tayi maganar ya juya yana kallan su, wurin yayi tsit, har shi na tsayen shima yayi shiru ya kasa bud’e baki yayi magana, k’ara kafa mishi idanu tayi tana jiran amsar shi, da taga bashi da niyar yin magana, da k’ara da cewa,

“In baka da amsa zaka iya matsawa daga kaina, dan zaka samun ciwon kai”

Tare da yin alama da hannunta na ya matsa, sauran y’an wurin sakin baki sukayi suna kallonta, tasan wane shi kuwa, yaro da kud’i wanda matan abuja ke rububi, AK kenan Aliyu Kabeer, yaro me wasa da naira, tsabar yadda abun ya bashi mamaki dariya ya saki, sannan ya bita da wani mugun kallo ya fice daga wurin, tana gani mazan wurin suka bishi suna bashi hakuri, yana ta zuba iho a wajan wurin yana cewa,

“Ni zatayi embarrassing??, ni zata wulaqanta a gaban mutane, wallahi zan nuna mata ni wane”

Banza tayi dashi, ta d’auki lemonade d’inta ta tayi sipping, ita a ganin ta ba wulaqanta shin da tayi, kawai ta gaya mishi abunda ke cikin ranta, Hamida kuwa hankalinta a tashe tana ganin ya hau motar shi ya jaa ya bar wurin ta kama hannunta sukayi waje suma bayan tayi wa sauran abokan nasu sallama.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE