ZAFIN RABO CHAPTER 11 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 11 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ko da ya shigo parlor d’in baiga kowa ba, ba sakeena, ba kausar ba kamila, baisan me ya saka abun yayi mishi dad’i ba dan yau baya san had’uwa da matar shi, bedroom dinshi yayi, yana shiga ya fara cire kayan shi tare da fad’awa bathroom sai da yayi wankan shi sosai sannan ya fito, k’ugun shi d’aure da towel, yana fitowa yaji hayaniyar su a waje, gabanshi ne yayi wani irin fad’uwa, barin ma jin muryar sakeena da yayi, a hankali kamal yayi wurin closet d’inshi ya samu jallabiya ya zura bayan ya gama gera jikin shi da feshi shi da turare masu mugun k’amshi, sai da ya d’aure fuskar nan tashi tamau sannan ya fita daga d’akin.

+

Dukkan su na zaune tv a kunne, murmushin da ya gani a fuskar ta ne ya saka shi tsaywa cak, binta ya fara yi da kallo yana mamakin kamar ba ita bace jiya hawaye suka cika fuskar ta, yafi mintina yana kallanta, suma na parlor d’in basu san yana wurin ba, sai can kamar daga sama kamila ta juya ta ganshi,

“Lah ya kamal yaushe ka dawo?”

Maganar da tayi ce ta saka sakeena da kausar saurin kai idanunsu kanshi, suna had’a ido da ita tayi wani mugun had’e rai kamar bata tab’a dariya ba, sannan tayi saurin kwada idanunta, ya d’an yi sakwanni yana kallanta, sannan kuma ya maida hankalin shi kan kamila,

“Ban dad’e da shigowa ba”

Yana maganar yayi wurin su tare da d’an rankwashin kausar a kai yana jin ta fara mita, banza yayi da ita yayi wurin sakeena da take kan two seater idanunta nakan yatsun hannunta, tsugunnawa yayi a gaban ta a hankali, ya k’ura mata ido, sannan can ya kamo hannunta, yasan ta mishi kashaidin da ya daina tab’a ta ba da izinin ta ba, amma jikin shi ya gaya mishi baza ta tab’a tona mishi asiri ba duk abinda zaiyi mata, har lokacin bata d’ago ta kalle shi ba,

“Are you still angry?” A hankali yayi mata tambayar,

Yana gani ta lumshe idanunta alamun tana k’ok’arin kada ta saka duk k’arfinta ta ture shi daga kusa da ita, can ta bud’e su, mik’ewa tayi bayan ta fusge hannanuta daga kan nashi, sannan tayi kitchen ta barshi a wurin, shima lumshe idanunshi yayi, bai san me yake sashi kula ta ba bayan yasan dukkan su sun tsani junan su,

“Wani abun kayi mata ko?”

Jin muryar kausar d’in da yayi ne ya dawowar dashi daga duniyar da yake, mik’ewa yayi shima daga tsgunnawa da yayi, yayi wurin k’anwar tashi, tare da had’a lips d’inta da murd’awa,

“Wa aka cema ya rage shegen surutu?”

Kamila dariya ta saki da taga kausar sai faman so take da kwace daga hannun kamal, ta ruk’e hannayen shi tana fusga, shi kuwa sai k’ara ja mata baki yake, har idanun kausar ya fara cika da kwalla, ganin haka kamal ya sake ta,

“Haba ya kamal dan Allah”

murmushi yayi, sannan ya juya ya koma hanyar kitchen bai ce mata komi ba, yana shiga yaga sakeena na kaiwa da kawowa, tana zuba wasu abinci a cikin flask, jingina yayi a jikin bango ya cigaba da kallon ta da wannan mayun manyan idanun nashi, yasan tasan ya shigo amma ko da wasa bata kai idanunta kanshi ba,

“Ni kike had’a ma abinci?”

K’ara banza tayi dashi kamar bata jin hausa ta cigaba da abunda take, tana gama had’a abinda zata had’a ta d’auko su a k’aton tray, zata wuce shi kenan ta fita daga kitchen d’in yayi saurin tsayawa a gabanta tare da kwace tray d’in daga hannunta da ajiye wa akan cabinet, yana gani tayi wata harara dukda idanunta na k’asa sannan, ta juya ta zaga ta bayan shi zata wuce, ta sauri ya kamo hannunta, zata kwace kenan ya k’ara ruk’e ta,

“Nan da y’an awanun kausar da kamila zasu bar gidan na baza ki iya jurewa ba??”

Sai lokacin da kalle shi, fuskarta a had’e,

“Zan iya jurewa amma za’a sami matsala in har ka cigaba da tab’a ni”

Tana gama maganar ta fusge hannanta tare da daka mishi wata harara sannan ta koma ta d’auki tray d’in,

“In ka gama abinda kake zaka iya samun abincin ka akan dinning”

Tana fad’a ta fice daga kitchen d’in, lumshe idanunshi yayi tare da ajiyar zuciya, wai meke damun shi? me ya saka ya damu da ta nuna basa samun matsala a auran su?, me ya saka yake ta mata shishigi da shiga sha’anin ta?, ya lura tunda su kausar suka zo yake nuna halin da ba nashi ba, me yake damun shi?, ya dad’e yana tsaye a wurin da ta barshi yana ta tunani sai da ga baya ya fita daga kitchen d’in.

Bayan ya dawo daga masallaci, chewing gum a bakin shi dan cikin shi ya cika dam saboda tuwon da miyar ogbono da ya narka, ba gardama yasan sakeena ta iya girki, kullum yana cikin cinye duk abincin da ta saka mishi a gaban shi, kamila ya gani a zaune ta shirya tsab cikin atamfa ta d’ora k’aton mayafi akanta,

“Har kun shirya”

Yana maganar ya kalli agogon dake manne a jikin bango, yaga k’arfe 7:30,

“Ni da kausar mun shirya, muna tsoron in bamuyi sauri ba zamuyi missing flight”

D’aga kai yayi tare da cewa bari yaje ya shirya shima.

Sai da ya gama shirin shi tsab cikin wani farin yadi kanshi d’auke da wata bak’ar hula, k’amshi sai tashi yake daga jikinshi sannan ya fito, muk’ukkin motar shi a hannunshi, yana fitowa parlor yana duba agogan shi yaga k’arfe 7:50, d’auke idanun shi yayi daga kan agogon rolex d’inshi ya maida kansu,

Kausar da wani glass cup a hannunta tana shan ruwa, kamila da sakeena na zaune na hira, burki ya jaa ya tsaya, wai daman da ita zasu je, tana sanye cikin bak’ar abayar da tayi mata mugun kyau, fuskar ta ba wata kwaliya in ba hoda ba da kwalli, haka ya k’ura mata ido bai ma san yana yi ba,

“Yauwa tunda ya fito ku tashi mu tafi”

Kausar na maganar duka suka bar hirar, suka maida hankalin su kanshi, kamila ce ta mik’e tare da d’aukar handbag d’inta, sakeena kuwa sai da ta mishi wani mugun kallo sannan ta mik’e itama ta d’auki tata handbag d’in, ita ta fara ficewa daga gidan sannan sauran suka bi bayan ta, suka bar kamal a tsaye wanda ya kasa d’auke idanunshi daga kan matar shi Suna tsaye suna sallama dasu kausar wacce ta ruk’e sakeena gam, tak’i sakin ta tun bayan fitowar su daga gidan gaisuwa, tana ta cewa zatayi missing d’inta, ita kuwa sakeena ba abunda take sai murmushi, tayi kamar bata jin manyan idanun kamal akanta, mugun haushi yake bata dan ta lura yau tunda ya dawo daga office yake mata wani irin wawan kallo da ta kasa gane me yake nufi, sai da suka gana sallamar su sannan sukayi hanyar cikin airport, kamal ma binsu yayi dan yaga shigar su.

Tana jingine a jikin mota tana ta jiran dawowar kamal, a lokacin ba abunda bai zo mata kanta ba, na wannan ne chance d’inta, na da ta gudu, amma kuma bata ta ko sisi a jikinta ga kamal ya karya mata atms d’inta, tana tsaye tana ta sak’e sak’e, yarda zata samo wa kanta mafita kamar daga sama taji an kira sunanta, ta sauri ta d’ago dan tayi mugun tsorata, amma wa zata gani, JABIR ne a tsaye yana sakar mata murmushi, bata san lokacin da ta zaro manyan idanunta waje ba dan tayi bala’in mamakin ganin shi,

“found you”

Abunda ya ce mata kenan, wani irin dad’i ne ya kama sakeena da wani mugun farin ciki, tsabar murnar da jabir yake bai san lokacin daya jawota ya rungume ta ba,

“Jabir”

A hankali ta furta sunan shi, sakin ta yayi sannan ya maida hannunshi kan kafad’unta ya ruk’e su gam ga sai zuba mata kallo da murmushi yake,

” i looked for you everywhere, ba wanda ban tambaya ba amma basu san unguwar da kike ba, wanda suka sani kuma sunk’i gaya mun”

Ajiyar zuciyar farin ciki tayi, ta cigaba da kallan shi dan gani take kamar a mafarki, shi kuma sai zuba mata tambayoyi yake,

“Wait”

A hankali ta katse shi, “yanzu ina motar ka?” Bata san me take tunani ba a lokaci, dan kawai gani take wananan ce kad’ai damar ta, ta fita taga hannun kamal.

K’eya ya fara sosa wa, “ban taho da mota ba, yanzu ma abuja zan koma”

Lumshe idanunta tayi, dan taga samu taga rashi, tana bud’e su sai cin karo tayi da na kamal, tunda ga nesa yake mata wani irin kallo, gaban sakeena ne yayi mumman fad’uwa, shekenan kashinta ya bushe, yarda take hangen shi fuskar shi d’aure tamau cike da b’acin rai, sauri tayi ta maida hankalin kan jabir,

“Yi sauri ka tafi yanzu zai k’arso, i dont want you in trouble”

Tana maganar tana hangen shi, a hankali yake takowa amma kamar bijimin zaki wani irin huci yake, jabir zaiyi mata wata maganar tayi sauri bud’e front seat zata shiga, shima kamo jakarta yayi ya saka mata wani abu,

“Ga waya ta nan da kud’i nasan zasuyi miki amfani”

Yana fad’a yayi sauri yabi ta baya ya b’ace daga wurin, sakeena kuwa ita danna lock tayi ta shiga yin addu’a, bata dad’e a cikin motar ba kamal ya k’araso, tsayawa yayi a daidai saitin k’ofar ta, ya fara kallon ta, wani irin mahaukacin bugawa k’irjinta ya fara, tsoro ya kamata, ta shiga uku, tasan halin kamal tasan me zai iya, tasan wana kalar mugu ne, ga yanzu ya kamata b’aro b’ari tana magana da wani, yafi minti goma a tsaye a wurin yana k’are mata kallo, dukda glass d’in motar na sama bai hana jikinta yin rawa ba, tana jiran ya bud’e kmotar ya fito da ita ya ci mata mutunci a gaban mutane sai kawai gani tayi yayi hanyar driver’s seat, bud’e motar yayi ya shiga.

Zuciyar ta ta kasa daina bugawa, ga kamal sai sharar mahaukacin gudu yake akan titi, ko da wasa bata kai idanunta kanshi ba dan tasa mai zata gane ma kanta, tunda ya shiga motar bai ci mata komi ya k’ara saka sakeena tsurewa, ko da suka isa gida wani mahaukacin horn ya fara ta ba sausautawa, dannan horn d’in kawai yake, ya saka mallam isyaku fitowa a har gitse, figar motar yayi da guda da aka bud’e mishi gate d’in da sakeena bata saka seatbelt ba da sai ta fad’i daga kan seat d’inta.

Yana parking motar ya fito, ko key d’in bai cire ba balle ya kulle k’ofar shi, sakeena na cikin motar hankalint ya k’ara tashi da kasa ko mosti balle fitowa, ta dad’e a zaune, sannan a hankali ta kashe motar tare da cire key d’in, tana fitowa daga motar ta fara takawa kamar wacce kwai ya fashewa a jiki, ko da tazo k’ofar parlor zata bud’e sai da tayi addu’a tare da tattaro nustuwar ta sannan ta tura ta shiga.

Da bayan shi ta fara yin sallama, yana tsaye a wurin stand d’in dake dinning area, hannunshi ruke da glass cup ya gama shan ruwa, a hankali ta fara takawa yarda bazai ji takunta ba, bayan ta salallab’a ta ajiye mishi muk’ullin motar shi akan center table, har zata bud’e d’akinta ta shiga taji yace,

“Wanene shi?”

A hankali yayi maganar, sakeena tsayawa tayi cak sannana itama a hankali ta juya ta maida idanunta kanshi, har lokacin bai juya ya kalle ta ba, k’ara tattaro nutsuwar ta tayi ta kauda tsoro,

“Wanene wa?”

Ta amsa shi ta wata tambayar, tasan sarai raina mishi hankali take, sai a lokacin ya juyo tare da sauke jajayen manyan idanunshi akan ta, nanad’e hannunshi yayi a fad’eden k’irjinshi bayan ya jingina da stand d’in,

“Kada ki raina min wayo nasan kinsan me nake nufi”

Wani irin gumi ne ya k’eto mata, barin ma yarda taga idanunshi basa d’auke da koda d’igi d’aya na wasa, k’ara dakewa tayi tace mishi,

“A’a, bansan me kake nufi ba”

Tana gani ya lumshe manyan idanunshi tare da saka d’anyatsan shi a gojin shi kamar yana so ya kawar da ciwon kai, ya d’an jima a haka can komi ya bud’e idanunshi, sun k’ara kad’awa sun koma jajawur, a hankali ya fara takowa kusa da ita, sakeena na ganin haka hantar cikinta ta k’ara k’ad’awa, itma a hankali ta fara jan baya, amma still kamal ya fita sauri, sai da ya iso kusa da ita, idanunshi kaf akanta, sannan a hankali ya fusge handbag d’inta, zaro manyan idanunta tayi waje, karde yaga lokacin da jabir ya saka mata wayar shi a jakarta, zata sa hannu ta kwace ya ruge ta, d’aga jakar yayi ya zazzage komi na ciki akan kujera, duk abinda yake idanunshi basu bar kanta ba, sai da komi ya fad’o sannan ya d’auki wayar, tunkan ya fara magana sakeena ta ruga shi farawa, dan ta gama tsorata,

“friend d’ina ne, amma ba abinda ya had’a mu”

Ka ganta duk ta rud’e, ta zata ta daina jin tsoron kamal, amma ganin yarda yake a lokacin gaba d’aya ya canza ya koma mutum daban, kamar mutumin dai bai tab’a sanin mene ne murmushi ba gaba d’aya rayuwar shi, fuskar shi a d’aure sosai, kallanta ya cigaba da yi bai ce mata komi ba, sai can a hankali ya furta,

“Friend d’inki ne shi ya saka kika barshi har ya rungume ki??”

Ta shiga uku, wato ya dad’e a tsaye a wurin kenan yaga komi, jikinta ne ya fara rawa, tsoro ya k’ara cika mata ciki, jin k’arar da tayi ne ya dawo da ita daga duniyar da take, wayar jabir ta gani a k’asa tayi raga raga, kamal ya rotsa ta, a take hankalin ta ya k’ara tsashi da sauri ta tsugunna zata tattaro ragowar waya, amma kamal yayi saurin kamo hannunta, ya saka ta maida idanunta kanshi, ba idanunshi ba harta fuskar shi ta dawo jajawur, b’accin rai d’auke a cikin k’awayar idannunshi, matse hannayenta yayi da mugun k’arfi har sai da ta saki k’ara, sannan a hankali ya furta mata,

“In har kika k’ara tsayawa kika kula wani a gaba na ranar zan nuna miki ni wana irin kalar azallimin namiji ne”

Yana gama maganar ya sake ta tare da yin hanyar bedroom d’inshi, sakeena najin k’arar k’ofa ta zube a wurin ta fara maida numfashi.²⁸

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE