ZAFIN RABO CHAPTER 12 BY SAKIEYY
ZAFIN RABO CHAPTER 12 BY SAKIEYY
Tun bayan had’uwar ta da jabir a airport rayuwar gidan ta canza, ma’ana kamal ya fita harkar ta gaba d’aya, bata ganin shi, bata jinshi, ita abun mugun dad’i yake mata, in har ya fita toh har ta kwanta bacci baya dawowa in kuma ta tashi baza ta tab’a samun shi a gidan ba, yanzu sati biyu kenan bata saka shi a idanunta ba, ko abinci da tana mishi ta ajiye mishin akan dinning amma da taga wahalar da kanta take ko tayi mishi baya ci, yarda ta ajiye haka take zuwa ta d’auka ta daina.
+
Rashin ganin kamal ne da yarda baya takura mata ya saka ta cikin tsan tsan farin ciki kwanikin nan, bata da damuwar sa yanzu, rayuwar ta kawai take yi, tayi salla, ta karanta qur’ani in san kallonta ya motsa tayi, amma kuma wani sashe na zuciyar ta bai hana ta tunanin anya kamal ba wani mugun abu yake shirya mata ba, barin ma yarda taga ranshi yayi bala’in b’acci randa suka kai su kausar airport.
Bata tab’a ganin irin b’accin ranshi ba kamar na ranar, yayi mugun bata tsoro, duk bakinta ta kasa gaya mishi wata maganar dan ganinta tana gaya mishi mara dad’i zai buga kanta da bango, yayi mata jina jinan da sai tayi satit tika a asibiti, kuma sannan halin kamal wannan ba k’aramin aikin shi bane dan a azalimai ma ya fita daban, shi ya saka ta kama bakinta tayi shiru dukda a lokacin tana san gaya mishi shine yayi sanadiyar had’uwar ta da jabir tun farkon auran su.
Tana zaune a kan sallaya, qur’ani a hannuta tana ta raira k’ira a mai dad’in sauraro, karatun ta take cikin nustuwa da jin dad’i, k’arar doorbell d’in taji ne ya d’an tsai da ita daga karatun ta, shiru tayi dan tana so ta k’ara ji dan tunda tazo gidan ba wanda ya tab’a danna mata doorbell in ba lokacin dasu kausar suka zo, kamal in zai shigo key d’inshi yake amfani dashi, bata da wani da zaizo ganinta, k’ara jin k’arar tayi, sakeena ajiye qur’anin tayin akan sallayar bayan ta rufe tare da mik’ewa da fita, tana isa parlor tayi wurin k’ofa, a hankali ta murd’a muk’ullin ta bud’e.
Kamal ta gani a tsaye a jingine da k’ofa, kanshi a k’asa, bayan suit jacket d’inshi dake hannunshi, tie d’inshi a kunce, tsayawa tayi tana kallon shi dan bata san dalilin danna mata doorbell ba da yayi, a hankali ya d’ago da kanshi tare da sauke idanunshi da suka yi ja suka k’ank’anci a kanta, sakeena gabanta ne ya fad’i dan yarda taga gaba d’ayn shi ya canza, ya koma pale instead of fari, lips d’inshi sun koma purple, ga wata irin rama da yayi, bata san lokacin da ta tambayi kanta ba anya lafiya.
Ya d’anyi mintuna yana kallanata amma kina gani kinsan baya cikin hayyacin sa, da kyar ya iya matsawa daga jinginan da yayi, a haka ya fara dafawa zai shiga cikin gidan, sakeena kuwa ta bishi da kallo ta kasa koda mosti, yana fara taku d’aya yayi kamar zai fad’i, sakeena bata san lokacin da tayi kanshi ba tare da ruk’o shi, gaba d’ayan shi ya fad’a kanta, saboda baza ta iya da nauyin shi ba dukan su suka zube a k’asa a wurin.
Wani irin zafi taji ya kama jikinta dukda hijab d’in da ta sanya, ruk’e hannun kamal d’in da tayi dan ta gera shi daga kanta ya bata tabbacin zafin daga wurin shi ne, juya shi tayi ya zaman kanshi nakan hannunta, idanunshi a lumshe, hannunta ta saka akan gojin shi taji shi kamar garwashin wuta alamun zazzabi ke damun shi.
Sakeena tsayawa tayi ta bishi da kallo, sati biyun da bata ganshi ba shine ya koma haka, hannun ta ta saka ta fara d’an taba fuskar shi wai koda zai farka, dan ita baza ta iya dashi ba,
“Kamal, kamal, kamal”
A hankali ta fad’i sunan shi amma shiru, sai ma ganin da tayi ya d’ora hannushi akan cikin shi da d’amk’e cikin da duk k’arfin shi, tare da k’ara lumshe idanunshi da suke a kulle, alamun he is in pain, a hankali ya d’an far murgususu a jikinta, ganin yarda numfashin shi ya fara yin sama ya saka sakeena rud’ewa,
“Kamal, Kamal, me ya same ka?”
Da k’arfi take mishi tambayar, bayan tab’a shin da dake a fuska wai dan ya bud’e idanunshi, da taga hawaye har sun fara zuba a fuskar shi bayan ya damke hannunshi akan cikin shi, ga wani irin numfashi da yake fitarwa ya bama sakeena tabbacin wannan ba wasa bane da gaske bashi da lafiya, mallam isyaku ta kwada ma kira, sai gashi ya fito a guje, da yake da kamal ya fad’o mata a jiki, suna hanyar k’ofa ko cikin parlor d’in basu shiga ba, malam isyaku na isowa, ta fara ce mishi
STORY CONTINUES BELOW
“Yi sauri ka kama shi mukai shi asibiti, kamar cikin shi ne ke mishi ciwo”
Subhanallah, abunda mallam isyaku ya fad’i kenan, tare ciccib’o kamal daga jikin sakeena, ita kuwa tana ganin a d’auke shi daga kanta tayi sauri d’aukar muk’ullin motar da ya yar a wurin da bud’e ma mallam isyaku motar ya saka kamal a baya, sakeena da sauri ta shiga ciki ta d’auko takalmi, sannan ta fito bayan ta kulle k’ofar parlor.
Tana fitowa taga already mallam isyaku ya bud’e mata gate, da sauri ta shiga cikin motar, tana shiga motar ta juya bayanta, a zatanta zataga yana murgususun sai ganin tayi baya ma mosti, yana kwance idanunshi a kulle, ga ya fita daga hayyacin shi gaba ki d’aya a d’an k’aramin lokaci, k’ara rud’ewa tayi da sauri ta kunna motar ta fita daga gidan a guje, dukda ta tsani kamal, zatafi kowa san ace ya mutu baza ta tab’a iya barin shi a cikin hallin nan ba, haka tai ta fusgar motar har suka isa makeken asibitin nan umc, a guje ta fita taje ta kira nurses aka zo aka tafi dashi cikin asibitin.
Tana zaune a kan sofa, da take a cikin d’akin ta aka kwantar da kamal, idanunta kaf akanshi, har k’arfe tara tayi na dare amma har lokacin bai farfad’o ba dukda allurar bacci akayi mishi, kallon shi take dan ta kasa gane yarda za’ace namiji kamar shi na da wannan muguwar ulcer, doctor ya ce ulcer d’inshi ce ta tashi, ga stress da rashin baccin da baya samu.
Haka tana zaune da wayar shi a hannunta, tana ta tunanin ko ta kira gidan su ta fad’a ko kuma ta kyale, tana zaune tana shawara da kanta a haka har ta fara gani ya fara mosti, da sauri ta mik’e ta isa wurin shi, a hankali ya bud’e manyan idanun shi, sai da ya gama waige waige yayi realizing yana asibiti, sanna ya k’ara lumshe idanunshi tare da d’ora dantsan hannun shi wanda baya dauke da drip akan fuskar shi.
Sakeena kuwa ta zuba mishi kallo a hankai ta furta,
“Ka tashi?”
Tana ganin ya k’ara bud’e idanunshi ya sauke akan ta, mamaki ne ya bayyana a fuskar shi kamar sai a lokacin ya lura tana d’akin, bayan wani kallo da yake mata ko k’ifta idanunshi baya yi, ganin baya da shirin amsa ta ya saka sakeena tunani ko dai akwai wata matsalar ne,
“Bari na kira nurse”
Haka ta ce ma kamal wanda har lokacin kallon ta yake da yake dauke da abubuwan da ta kasa gane wa, ta juya zata fita kenan, kamar daga sama taji an fisgi hannunta gaba d’ayan ta ta fad’a kan k’irjin shi, tana jinta akan shi tayi sauri zata mik’e amma ya saka hannayen shi gaba d’aya ya k’ara shigar da ita jikinshi bayan wata irin ajiyar zuciya da yayi, kamar ya sami abunda ya dad’e yana nema,
“Mu tsaya a haka na minti d’aya kacal”
A hankali, a sanyaye yayi maganar, tare ta k’ara rungumeta, yarda ya k’ankame ta ko mosti ta kasa yi, wani irin k’arfi ya sakar mata sai kace ba mara lafiya ba, sai kace baiyi kamar zai mutu ba awa takwas da suka wuce, so take ta kwace amma ina ba hali, d’akin yayi tsit ba abunda kake ji sai k’arar ac, da bugawar zuciya, sakeena tasan dai ba daga ita bane daga wurin kamal ne, a ganinta duk rashin lafiyar ce ta saka shi behaving this way.
K’arar gyaran murya da aka yi ne ya saka sakeena saka duk wani k’arfinta da kwacewa daga jikin shi, tana mik’ewa daga kanshi tayi saurin juya wa wurin da akai gyaran muryar, doctor ta gani a tsaye da wasu nurses guda biyu a kusa dashi duk murmushi dauke akan fuskar su, wata irin azababbiyar kunya ce ta kamata da ta saka ta sauri matsawa gefe, a lokacin doctor d’in ya k’araso gun kamal, wanda ko da wasa, ko na sakwan d’aya bai d’auke way’annan mayun manyan idanunshi ba daga kan matar shi tun bayan ya farfad’o.
Nurses d’in ne suka fara shirin cire mishi drip da saka mishi wani yayin da doctor d’in ya fara gwaje gwajen da zaiyi, sakeena kuwa na gefe, idanunta a k’asa amma gaba d’aya hankalinta na kan su,
“Komi ya fara dawo dai dai, you just need alot of rest and food” doctor d’in ya fad’a cikin professional voice amma tana d’auke da wasa, ya kuma k’ara da,
“Kwanan ka nawa rabon ka da abinci?”
Sakeena najin tambayar tayi saurin d’ago da kanta da kai idanunta kan kamal wanda shima ita d’in yake kallo,
“Kwana bakwai, matata ta daina bani abinci”
Yana maganar yana kallonta, da wannan manyan idanun nasa da baya k’ifta su, sakin bakinta tayi dan bata yi zatan zai fad’i a haka ba, nan doctor ya fara masifa, dayi mata fad’a, na so take ta kashe shi, taya zata barshi har tsawon kwanaki haka ba abinci, sakeena kuwa tayi salalo a wurin da ta kalli kamal sai ta kalli doctor d’in, mamki ya cika mata ciki yarda ya d’ora mata laifi bayan shi ya hana kanshi cin abinci, doctor d’in na gama fad’an yace taje ta samu mishi wani abun da zai ci yanzu yanzu nan, dan yana buk’atar shan magani, yana maganar ya fita.
Yana fita ta juya wurin kamal ta sauke mishi wata muguwar harara, shi kuwa gogan naku ya kafe ta da wannan mugun kallon nashi, lips d’inshi d’auke da murmushin mugunta, k’ara k’ullar da ita yayi, wato abunda zai yi mata kenan bayan ita da kawo shi asibiti, ta bud’e baki zata sauke mishi buhun masifa taga ya d’aga hannunshi da yake d’auke da drip, kamar ya na nuna mata,
“Im a patient, ki ajiye duk masifar ki sai na warke, doctor said i need rest” ya d’anyi shiru na y’an sakwani, sanni ya k’ara da “and food”
Wani abu taji ya tsaya mata a mak’woshin ta tsabar takai ci, lallai wannan d’an rainin wayo ne, dama ta kyale shi a wurin ya mutu kowa ya huta, sai da ta gama harar shi tsab da sauke mishi duk wani mugun kallo sannan tayi hanyar fita, sai da tabbata da buga k’ofar da mugun k’arfi, tana jin dariyar shi a d’akin kan ta fita.Tana tafiya tana sauri, tare da zagin kamal a k’asan ranta, har ta ga wata nurse na tahowa, sakeena ta sauri ta k’arsa wurin ta, sannanta tambaye ta wane restaurant ne a kusa bayan sun gaisa, dan ita ba y’ar kano bace, bata san ko ina ba, da kyar ma ta iya kawo kamal asibitin nan, haka nurse d’in ta mata kwatanci, itama mik’a godiyar ta tayi sannan tayi hanyar fita daga asibitin.
+
Tura k’ofar d’akin shi tayi had’e da sallama, ta ganshi a zaune akan abun sallah, a nistse yake a wurin gaba d’aya nustuwar shi tana kan addu’o in da yake, yaso ya bama sakeena mamaki dan yauce rana ta farko ta tab’a ganin shi yana ibada, ajiye ledojin hannunta tayi akan wani table a gefe, sannan ta sami wuri ta zauna akan kujera tare da zubawa k’eyar kamal kallo.
Daman mugayen maza irin su kamal, way’anda basu san darajar mace ba sun san Allah, ai ita ta d’auka iskancin sa ya saka a gaba, ita tasan da yawon maza ba san addini suke ba, ganin shi a haka ya d’an daure mata kai, haka ta zauna tana sak’e sak’enta har ya idar da abunda yake.
Yana shafa addu’ar shi ya juyo ya sauke mata wannan murmushin nashi me mugun k’ra mishi kyau wanda duka dimples d’inshi sai da suka fito, d’auke idanunta tayi daga kanshi, kamar ba ita ke binshi da kallo ba sannan ta mik’e, ta koma wajan table d’in ta fara bud’e ledar.
“Tunda kace bana baka abinci, ga abinci naje na siyo maka”
Tana maganar tana bud’e takeaway pack d’in, ta dauko takeway d’in da yake d’auke da sauce d’in shredded chicken kenan ta bud’e shi shima, daga sama taji ance,
“Abincin ki nake san ci”
Tsabar bata zata zai zo dab da ita ba ya mata magana kamar rad’a a kunnen ta, ga numfashin shi da ya baibaye wuyan ta, bata san lokacin sa ta juyo ta saki gaba d’aya sauce d’in mai turirin zafi ba a jikin shi.
Sakeena na gani abinda tayi, tai saurin kai hannunta bakinta ta kulle, tare da zaro manyan idanunta waje, tunda ga kan cikin shi har k’asan shi ya b’aci da sauce, da sauri ta maida idanunta kan kamal wanda yake cizan leb’e tsbaar azaba, da sauri ta juya ta lalumo tissue, ta koma kanshi.
Shirt d’inshi ta d’aga, ta fara goge kan cikin shi, farar fatar wurin tayi jaa saboda zafin abunda ya zubar mishi, gaba d’ayanta a rud’e take, bakinta ba abunda yake ambata sai kalmar haku’ri, a haka da dage tana goge mishi jiki, har ta k’arso kasan shi wurin zip d’in wandon shi, fara goge wurin tayi tana dirza, can kuma da ta gane mi take tayi saurin tsayawa, a hankali ta d’ago da idanunta, suka had’a ido.
Hannunshi na nannad’e akan k’irjinshi, fuskar shi d’auke da murmushin nana nashi, ga ya kafa ta da mayun manyan idanun nan nashi da sunyi ja ja wur, kwyar idanunshi d’auke da wani abun da bata san ko mene ba, d’aga mata gira yayi, sannan a hankali yace,
“Go on, cigaba da abunda kike”
Wani irin abu taji ya taho mata, da sauri ta juya bayanta, wata kunya ce ta kama ta, Allah ya had’a ta da d’an rainin wayo, me ma ya saka ta fara goge mishi jiki bayan ba laifin ta bane shi ne yazo bayan ta yayi mata magana duk ya tsorata ta.
K’ara jin numfashin shi tayi akan wuyanta, a hankali ya fara magana da wannan deep voice d’in tashi, bayan ya ruk’o hannayen ta tare da had’a bayanta da k’irjin shi, a kan kunnanta yace,
“Yanzu ya zakiyi da kayan jikina? bani da wasu kayan”
Wani abu tsi taji ya harba tsakiya kanta, a dar’i tayi saurin matsawa, tare da juyawa da sauke mishi idanunta wanda yanzu suna d’auke da b’accin rai, yana tsaye a wurin, he looks calm and collected, sai ka rantse da Allah bashi yayi mata abunda yayi mata ba yanzun nan,
Haka suka tsaya suna kallon juna, sakeena da idanunta basa d’auke da komi sai baccin rai da haushin shi, kamal kuwa idanunshi d’auke da abubuwan da ta kasa reading, duk yarda take san sanin me yake tunani a lokacin ta kasa, sai da ya gama k’are mata kallo sannan yayi murmushin shi na gefan baki, ya koma hanyar gadon shi, sakeena hangame baki tayi tana kallan shi, sau nawa tayi warning d’inshi na ya daina shigar mata personal space d’inta,
STORY CONTINUES BELOW
“Zaki iya using kitchen d’insu ki dafa me zaki dafa, na sanar dasu”
Ta dad’e bakinta a sake sannan da kyar ta tattaro duk nustuwar ta, a dake ta cigaba da kallon shi, yana kan gadon, ya rufe jikin shi the cover, amma idanunshi a kanta, fuskar shi har lokacin na dauke da murmushi,
“Yanzu k’arfe goma ta wuce taya har zan dafa maka abinci har kaci, bayan kasan doctor yace yana so ka fara shan maganin ka yanzun nan”
Tana maganar had’e da ihu da masifa, alamun mugun haushin shi take ji,
“Na gaya miki bazan ci abincin kowa ba sai naki, in kuwa kinga baza ki iya girkin ba, then ki dawo ki gama abunda kika fara, im sure wannan ma kad’ai zai k’oshar dani”
Yana gama maganar bata san ya akai ba, kawai sai ganin idanunta tayi sunyi wurin da ta zuba mishi sauce d’innan,
“Eyes up”
Abunda kamal yace mata, da harrda sa mata wata muguwar kunyar da ta sakata fita daga d’akin a guje, ko kallon shi bata k’ara yi ba.
Tana tura k’ofar ta fara maida nunfashi, kamal nasan ya haukata ta, kullum in suna tare sai ya dunk’a saka tana ji kamar y’ar shekar 15 bayan shekarar ta 25, rainin hankalin shi yana so ya fara fin k’arfinta, haka ta tsaye ta cigaba da sana’ar da ta saba wata zagin shi har wata nurse ta tunkaro to, tace suje ta kaita kitcehn d’in.
Makeken kitchen ne wanda ya sha kaya, sai kace kitchen d’in gida, sakeena bata yi mamaki ba dan daga ganin asibitin kasan ba k’aramin asibiti bane, abinda ya bata mamaki bai wuce yarda kamal ya saka aka barta tayi girki ba a cikin shi, nurse d’in ce ta fara nuna mata inda abunuwa suke da kayan abinci, tana gama bayanin ta ta fita.
Farfesun kifi ta dafa mishi da couscous , dan shine kad’ai abun saurin da zata iya dafawa, tana gamawa ta zuba a tray da fitowa, tana zuwa daidai k’ofar shi, ta had’e rai tare da ajiyar zuciya sannan ta tura ta shiga.
Yana jingine a jikin gadon shi, wayar shi a hannunshi, ya canza kayan jikinshi, yana sanye a wata bak’ar shirt, sumar kanshi ma a jik’e take kamar bai dad’e da fitowa daga wanka ba, hannunshi dauke da drip d’in da aka maida mishi.
Tunda ta shigo idanunshi ke kanta, har ta ajiye tray d’in hannunta akan table, sannan taje ta jawo overbed table ta saka mishi ta k’ara dawowa ta d’auki tray d’in ta d’aura akai, duk idunun shi kaf akanta, suna bin duk wani takun ta, sakeena najin su amma tayi banza dashi, sai aukin cewa baya gajiya da kallo take a zuci.
Tana gama gyara mishi abincin ta matsa gefe, tana jiran ya fara complaining wani abu dan tasan halin shi, sai kuma ya bata mamaki, ajiye wayar shi yayi a gefe sannan ya d’auki spoon, farfesun ya fara kaiwa bakin shi, yana loma d’aya, ya zaro idanun, sannan ya k’ara saka wata lomar, dariya yaso ya bata yarda taga yana ta zuba loma, kwana bakwai mutum baici abinci ba ai dole, tsayawa tayi tana kallan shi,
“Kardai shima yana san farfesun kifi kamar kamil??
A zuci ta zata tayi maganar, amma ganin yarda kamal ya tsaya cak da cin abincin da yake, ya tabbata mata ba a zuci tayi maganar ba, spoon d’in farfesun da zai kai bakin shi ya ajiye, kan kice mene fuskar shi ta hade’e kamar wanda bai tab’a yin dariya ba a d’an k’aramin lokaci, farar fuskar shi ta fara komawa jaa, lumshe idanunshi yayi na tsawon sakwanni sanna can ya bud’e, a hankali yace
“D’auke su daga gabana”
Ji tayi jikinta ya fara rawa, barin ma yarda taga yayi maganar ba wasa ko kad’an, ta lura kamal ya tsani ta ambaci kamil, ita ma wallahi sub’utar baki tayi,
“Ka k’osh….”
Kan ta k’aras maganar ya kifar da table d’in, gaba d’ayan abincin ciki sai da suka kife, glass bowls din da ta saka mishi abincin duka sukayi raga raga, sakeena hannunta ta kai kunnanta ta toshe saboda k’arar.
Yanzu tsoro ya bayyana a fuskarta, barin ma yarda taga mutumin gabanta gaba d’ayan shi ya canza, fuskar shi bata d’auke da komi sai tsan tsan baccin rai sai kace bashi ne yanzu ya gama murmushi ba, ya sauya kamar wani mai aljanu, tsoro ne ya k’ara kamata yarda taga idanunshi sun koma jajawur,
“Bance kika k’ara ambatar sunan kamil ba sai na zubar miki da hak’ora”
Jijiyoyi ne suka fara bayyana akan wuyan shi, alamun ranshi yayi mugun b’aci, farar fuskar shi gaba d’ayan ta tayi jaa, jikinta ne ya fara rawa, a hankali ta bud’e baki zatyi magana yayi saurin dakatar da ita,
“GET OUT”
wata razananiyar tsawa ya daka mata da saka ta k’ara rud’ewa, jikinta ya k’ara rawa, tsabar tsoro ta kasa motsi,
“BAKYA JI NE?? NACE MIKI KI FITA”
Tsawar da yayi mata yanzu na tafi ta d’azu amma har lokacin tana tsaye bata mosti, tsoro ya gama cika mata ciki, amma ganin ba laifin da tayi, bashi da right din da zaizo ya dunk’a mata tsawa, kuma ita ke kula da lafiyar shi, he should be grateful, a dake ta kalli cikin kwayar idanun shi bayan da kwada duk wani tsoro,
“NO!! IM NOT GOING ANYWHERE”
Itama tsawar da daka mishi, sannan ta had’e hanayen ta akan k’irjinta, ta gaji ta halayen shi, ta canzawar da yake kamar hawainiya, ba zai yuwa kullum ya dunk’a daka mata tsawa ba yana mata abubuwa kamar wata y’arshi, dole ta fara ja mishi burki, in ma he is bipolar to dole ne ya sauko dan ita ba irin sauran mata bane, she is educated ta kuma san right din kanta.
“you are rude, and this is not the way to treat someone ta tayi awannin tana zaman jinyar ka, in ka san you dont need me here you could’ve said it in a polite way ba sai kayi mun tsawa ba”
Jajayen idanunshi akanta, kina gani kinsan bala’in mamakin ta yake gani, ranashi har lokacin a mugun b’ace yake amma ya kasa bud’e baki yayi magana, ita tasan tana da mugun baki, bata barin ta kwana, kayi mata dole tayi maka kaima. Sai da taga bashi da saurin abaunda zai ce ta juya ta bar mishi d’akin tare da buga k’ofar.