ZAFIN RABO CHAPTER 2 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 2 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Jogging ya fito yi a harabar gidan, kunnan shi d’auke da AirPods yana jin karatun qur’ani, ya d’an jima yanayi saboda gidan akwai girma sosai, sai da ya gama tsab sannan ya wuce side d’inshi, yana shiga parlor d’inshi ya fara cire shirt d’inshi ya zarce bedroom d’inshi, direct bathroom d’inshi yayi, sai da ya gama wankan shi tsab sannan ya fito d’aure da towel a jikin shi, wurin dressing mirror d’inshi yayi ya fara yin abunda ya zaman mishi al’adarsa, sannan ya wuce closet d’inshi, shiga yayi cikin sweatpants bak’i da bak’ar shirt dan yau kawai zaman gida zaiyi ba wani wuri zaije ba, wurin mekeken standing mirror d’inshi yayi sannan ya fara taje kanshi, sai da ya gama shiryawa tsab tara da feshe jikin shi da turaruka masu dad’in k’amshi sannan ya d’auki wayar shi ya fito daga bedroom d’in, ko da ya iso parlor d’inshi, bai d’aga ido ya kalli k’aton hotan nan ba balle har ya kai idonshi wurin bedroom d’in da yake kallan nashi, dan yau baya da shirin yin tunanin shi, yana fitowa side d’in mami ya wuce.

——-

Yana shiga ya ganta a dining area tana ta faman shirya abinci, murmushi ya saki tare da k’arsawa wurinta, yayi kissing cheeks d’inta had’e da fad’in good morning, sai a lokacin ta lura ya shigo, tana kallanshi itama sakar mishi nata murmushin tayi,

“Kazo a dai dai yanzu nake shirin sawa a kiraka daman”

Kamal murmushin nashi me k’aramishi mugun kyau ya k’ara sakar mata tare da jawo kujera da zama, bai dad’e da zama sai ga wata y’ar farar yarinya kyakyyawa sosai wace bata wuce shekara sha tara ba ta sauko daga sama, tana ganin shi farin ciki ya kamata ta k’araso wurin shi a guje,

“Oyoyo Ya Kamal”

Shima d’ago yayi da manyan idanunshi ya ganta a gaban shi tana ta murna, shima farin cikin yake dan raban da ya ganta tun last year da suka zo ganin shi ita da Mami da Abba, zama a kujerar kusa dashi tayi, ta fara mishi hira da labarai,

“Mami ta turani gidan Ya Kamila wai celebration d’in dawowar ka na tsufaffi ne mu zamu ganka har mu gaji”

Kausar na maganar tana zumb’uro baki, Mami ko kallonta batayi ba tama shige kitchen, in mitar autar tata ne har ta gaji da ji, shi kuwa Kamal sai murmushi yake dan yayi kewar fitinar ta da rashin jinta,

“Tun asuba na fara shirin dawowa Ya Kamila na ta cewa na tsaya mu taho tare nace a’a tunda kowa na da mota kowa yayi hanyar sa kawai”

Kamal dariya ya saki,

“Kice kinyi missing d’ina da yawa shi ya saka har kika kusan yima yayar ki rashin kunya”

Kausar saurin kallon shi tayi ta zaro manyan idanunta waje tare da d’ora hannunta akan bakin shi,

“Shiru kada mami taji yanzu tayi sakwara dani a cikin gidan nan baka ga a hankali nayi maganar ba”

K’ara tuntsirewa da dariya yayi, in har kana tare da Kausar baka da wata damuwa dan kullum tana cikin saka ka dariya ne, hira suka ci gaba dayi har Mami ta dawo dinning d’in hannunta ruk’e da mug me d’auke da black coffee, ajiywa tayi a gabanshi sannan ta fara serving d’inshi breakfast, fried potatoes ne da egg da kuma shredded beef sauce, haka suka fara cin abinci suna hira jefi jefi, Mami na gaya mishi yaushe Abba zai dawo daga Paris, kausar ce ta d’ago kai ta kalle su, sannan ta fara magana,

“Dan Allah in kunga potatoes wa yake tuna muku?”

Duka suka juyo suna kallonta, ita kuwa bama ta bari sun bata amsa ba ta ci gaba da surutun ta,

“Ya KAMIL ko?, dankali shine favorite abincin shi, bani da wayo sosai a lokacin amma zan iya tunawa yana san duk abincin da akwai dankali”

Tsit wurin yayi, baka jin mosti komi sai k’arar ac, a lokacin da kausar ta gama magana a lokacin tayi danasanin abunda ta fad’a, hannunta na kan bakinta ta toshe, bayan wata mugun harara da kallo da mami keyi mata, shi kuwa Kamal tana gama magana ya sunkuyar da kanshi k’asa, ya k’urawa abincin kallo, ya damk’e hannunshi da yake kan cinyar shi, gaba d’aya fara’ar da fuskar shi ke d’auke dashi yanzu babu, ya had’e fuskar shi tamau kamar bai tab’a dariya ba, lumshe manyan idanunshi yayi, shi ya saka baya san dawowa gida saboda ko da yaushe ana cikin tuna mishi abunda yafi komi san ya manta a duniya, wani irin haushin kanshi yaji da har ya yarda ya dawo k’asar nan, zumbur yayi ya mik’e daga kan kujerar shi, dan yanzu abincin ya fita daga ranshi, Mami da kausar dake faman kallo shi duk fuskokin su d’auke da damuwa, a hankali ya furta ya k’o shi zai koma side d’inshi, yana gama maganar ya d’auki wayar shi yai hanyar fita, yana ji Mami nama kausar fad’an ta cika shegen surutu kan ya bar parlor d’in.

——-

Yana shiga parlor d’inshi ya k’ara cin karo da wannan makeken hotan nan, wani haushi ya k’ara kamashi, da alamun yau dai ba zai samu nustuwar da yake so ba, intercom ya d’auka ya kira securities dake waje ya umarce su da d’aya yazo, yana kashewa ya koma waje ya tsaya jiran sa, bai dad’e a tsaye ba sai ga wani ya k’araso, ce mishi yayi ya shiga ciki ya d’auki wannan hotan ya saka a d’akin kusa da nashi, danshi ko hanyar d’akin baya san yi balle har ya shiga ciki, ba’ayi minti biyar ba sai gashi ya fito, Kamal na ganin haka ya koma ciki, yana shiga parlor d’in yaga bangon wayam, bai ji dad’in abun ba amma ya tabbata in har ya bar hotan ba zai tab’a yin rayuwar shi yadda yake so ba.

Yana shiga bedroom d’inshi ya fad’a kan gado, had’e da lumshe idanun shi, yanzu jin mood d’inshi yake yayi k’asa, danasanin zuwa breakfast wurin Mami yayi, daga gobe zai fara cin abincin shi shi k’adai saboda baya san tashin hankali, wayar shi ya d’auko ya latsa kan instagram, baya san social media bama shi da ko wane social media account in har ba instagram ba, shima kawai dan ya dunk’a stalking d’inta ne, cin k’aro yayi ta latest post d’in da tayi minti biyu da suka wuce, post d’in abinci ne, kallan saman yayi yaga location d’in, cilantro Abuja, ba wani nisa da gidan su, abun ne yayi mishi dad’i, tunda ya dawo Nigeria me ya saka bazai yi having fun ba.

Sauri yayi ya mik’e ya k’ara fad’awa cikin closet d’inshi dan ya canza kayan jikin shi, black jeans ya d’auko tare da wata maroon shirt, bayan ya gama shirin shi tsab ya k’ara feshe kanshi da turare, ya d’auki muk’ullin motar shi me k’irar Mercedes AMG-GT yayi waje, in ka ganshi ya had’u iya had’uwa, ko yadda yake tuk’in a nitse.

Yana isa cilantro wurin a parking lot ya hangi motar ta, duk da shekarar shi takwas baya k’asar ba abunda bai sani ba akanta, in har ta taka k’afa ta bar gidan su ya sani, rayuwarta kamar film ce a wurin shi, sai da saisaici wurin motar ta sannan yayi parking a bayanta, ta yarda baza ta iya fita ba sai in har ya matsar da motar shi.

Fitowa yayi yai hanyar shiga wurin, tunda ya fito kowa sai ya kalle shi da matan da mazan, kwata kwata baiyi kama da d’an nigeria ba, bayan farar fatar shi ga laulausan gashin kanshi, ga wani kwarjini da yayi mishi yawa bayan kyawun fuskar shi, yana shiga ya samu wuri ya zauna, tunda ya shigo ya hange ta zaune da wasu mata su biyu, hira suke yi sosai harda dariya, Kamal jin zuciyar shi yayi tayi sama, kawai ganintan da yayi ya k’ara saka zuciyarta tafasa da zugi, bai tab’a zata mutum zai iya irin tsanar da yayi mata ba, wannan dariyar da take yi ta k’ara k’ullar dashi, ta tarwatsa mishi farin cikin shi amma ita tanan tana rayuwarta cikin nishad’i da jin dad’i, ji yayi tsanarta na k’ara bin duka jinin jikinshi, lumshe idanunshi yayi a dadai wannan lokacin waiter ya kowo mishi menu, already yaci abinci a gida amma a haka yayi ordering burger da kuma chapman.

K’ara kafa mata ido yayi, yadda take shigar ta dai haka tayi yau ma, kimono ce a jikinta bak’a bayan jan mayafin da yake kanta, fuskarta ba kwaliya in ba hoda da kwali ba, gani yayi sun mik’e gaba d’ayan su alamun sun gama me suke, suka fita daga wurin, suna fita ya d’auko wayar shi ya shiga danna wa, can sai ga abincin shi ya iso, ko kallon abincin baiyi ba ya cigaba da yin harkar gaban shi, sai da yayi minti talatin a haka sannan, ya duba Rolex d’in hannunshi ya ga 11:45, mik’ewa yayi yaje ya biya kud’inshi sannan ya fito, yana fitowa ya hange su a tsaye ko daga nesa yasan ransu a mugun b’ace yake, abun yayi mishi dad’i dan ya barsu a rana na tsawan mintoci, itama tana tsaye a wurin motarta tana ta duba agogon hannunta, yana isowa inda yayi parkin motar shi, yaga matan biyu da suke hira sunyi saurin kallon shi alamun suna shirin sauke mishi buhun masifa, yana had’a ido dasu dukan su suka kulle bakin su, had’e da sunkuyar da kansu, ba wanda ya iya furta ko, a, ya tabbata kwarjinin shi ne, ga fuskar shi da take a d’aure sosai ba alamun wasa ko k’adan a cikinta, yana gani suka koma inda take da sauri suna mata magana, sai a lokacin ta d’ago ta kalli inda yake, yi yayi kamar bata wurin ya ciro muk’ullin motar shi daga aljihun wandon shi ya bud’e zai shiga kenan yaji an fusgo hannunshi, abun ya bama Kamal mugun mamaki, cikin idanunshi take kalla idanunta na d’auke da kwalla, fuskar d’auke da tsan tsan abun mamki, yana jin hannunta da yake kan nashi na rawa, a hankali ta bud’e bakinta ta furta sunan da baya san ji.Tun jiya da daddare tayi da su Faiza da Faheema y’ay’an yayar mamata zasuyi breakfast date, a UK suke zama, sati biyu da suka wuce suka zo Nigeria amma a zaria suka sauka wajan y’an uwan mamanta, sunzo abuja saboda tanan zasu koma gida, dukda da dadare suka shigo garin shi ya saka suka ce suna so su ganta washegarin ranar dukda flight d’insu na yamma ne.

Suna zaune a cilantro suna hirar yaushe gamo, tayi bala’in kewar su, ta so ace daddy zai barta wurin su ta zauna amma tasan bazai tab’a yiwuwa ba, faheema sai labarin Maman su (Anty Hadiza) take bata da na uk, kana ganin Sakeena a wurin kasan tana jin dad’in labarin sosai saboda yarda take murmushi, faiza ce ta kalle ta,

“Wai dan Allah daddy bazai barki ko hutu kizo mana ba”

Sakeena tsayawa tayi tana kallonta, Faiza akwai san magana, tasan halin shi sarai tasan yarda yake, tunda da rasa iyayenta shine ke ruk’eta a matsayin shi na k’anin babanta, abunda ya saka sam sam yanzu basa shiri da Anty hadiza kenan saboda bayan rasuwar su taso an barta a wurinta amma sam yak’i tunda ga lokacin sukai fad’a kaca kaca da dangin mamanta, ko su faheema da fa’iza sun zo Nigeria basa zuwa wurin su, itama duk lokcin da taje UK baya barinta taje nasu gidan sai dai da kyar.

“Kema zancen kike so kinsan abu ne me wuya” faheema ta fad’i tara da k’ara cewa,

” ba yadda ba ayi ba ya barta tayi university d’inta a wurin mama yak’i sai ma turata turkey da yayi”

Murmushi tayi, dan bata da abunda zata ce, tana ji ba wanda ya kaita jin ciwon abun, taya za’ace a rabata ka da dangin uwar da ta haife ka, ba abunda ya kai shi ciwo, dukda dangin mamanta basu da yawa amma tana san kasan cewa tare dasu, jin hannun Faiza tayi a cikin nata, d’ago idanunta tayi daga kallan kan table d’in da suke, ta zuba mata ido,

“Kin tabbata bakya cutuwa a gidan nan?, kullum muka tambaye ki haka kike ce mana ba komi, ki fad’a mana gaskiya kada ki b’oye mana komi”

Murmushi ta sakan mata, tare da kama hannunta itama,

“Ke dan Allah da akwai wani abun da zaki gannina haka”

Ta fad’i tare da kai idanunta kan jikin ta, Faiza da faheema shiru sukai suka bita da kallo kamar suna d’an wani nazari, can sukayi wata ajiyar zuciya a tare,

“Ya Faiza ko akwai wani abu kinsan baza ta tab’a fad’a ba”

Faheema ta fad’a tare da maida nustuwar ta kan Sakeena, ta k’ara bud’e bakinta,

“Yanzu baki da wani problem da Shaheeda?”

Yadda suke nuna kulawar su gareta abun na yi mata dad’i dukda shekarun su d’aya da Faiza sai dai Faiza ta girmeta da wata uku, sun kuma bama faheema shekara biyu, kai idanunta tayi ta fara kallan su d’aya bayan d’aya,

“Yaushe nake ganin shaheeda ma da har zan samu problem da ita?, matar da tayi aure tana zama a lagos bata zuwa sai sau d’aya a shekara”

Shiru suka k’ara yi, bayan wannan idanun nasu da suka k’ara kafa mata suna san ganowa ko akwai k’arya a zancen ta, sai da suka tabbata ba k’arya take musu ba sannan suka share suka saka hirar wani zancen har suka gama abunda suke suka tashi suka fita daga wurin.

——-

Ba mitar da Faiza da faheema ba suyi ba da suka ga mota a bayan su tayi parking, Sakeena ce daman zata maida su hotel suje su gama shiri daman da Uber suka zo, sun so suje ciki suyi complaining ta hana su, wai sun d’an jira tukun, gashi yanzu har sunyi kusan minti talatin a waje, faheema ce taga wani na zuwa wurin motar tayi saurin tab’a Faiza, haka suka k’ara maida idanun su kanshi, so suke suyi mishi masifa amma bakin su yak’i bud’ewa tsabar kwarjinin shi, saurin sauke kansu sukayi bayan yarda ko wacce a ranta take ayyana kyawun shi, haka suka koma sumi sumi wurin y’ar uwar ta su wacce bama tasan me akeyi ba.

Sakeena ji tayi an tab’a ta, d’auke idanunta tayi daga kallan agogon da suke ta maida su wurin su, tana ji suna mata bayanin me motar yazo, d’aga idanunta da tayi taji gabanta yayi wata irin mummunar fad’uwa, zuciyata ta fara wana irin bugawa kama zata fitowa guje daga k’irjin ta, tare da zaro manyan idanunta waje, mafarki take ko gamo tayi, jikinta ne ya fara mahaukacin rawa, ji tayi wani abu tsi ya wuce ta tsakiyar kanta, gwiwoyinta sun sage, idanunta sun cika taf da k’walla bata san lokacin da ta saki kayan hannunta ba tayi wurin shi da sauri, bama tajin maganar da y’an uwan nata ke mata,

Har zai shiga cikin mota tayi saurin k’arasawa inda yake, ta saka duk k’arfinta ta fusgo hannun shi, ita kanta bata san tana da irin k’arfin nan ba sai yau, ko da ya juyo suka had’a ido ji tayi idanunta sun k’ara cika da hawaye, jikinta ya k’ara wani sanyi bayan rawar da yake, hak’ik’a shine, amma kuwa ta yaya, ta yaya wannan zai zama KAMIL d’inta bayan….., sauri tayi ta maida tunanin ta gefe bama ta so ta tuna, a hankali ta bud’e bakinta ta fad’i sunan ta tayi shekara da shekaru bata ambace shi ba,

“KAMIL”

in har KAMIL ne ya zatayi, daman irin wannan na faruwa a duniya, dad’i zai kashe ta yau, bata kai ayar tunaninta taji shima ya fusge hannun shi, kallon da yake mata kallon tuhuma ne, bayan fuskar shi da take a d’aure sosai, girar shi ta had’e ba almar wasa ko d’igo d’aya a tare dashi,

“Me haka???, hankalin ki d’aya kuwa”

Yadda yayi maganar shima babu wasa a ciki, maganar da zata saka jik’ewa sharkaf da gumi, a lokacin hawaye sun fara guda a fuskar Sakeena, jikinta ne ya k’ara yin sanyi da taji muryar ba iri d’aya bace ko magagin mutuwa take in har taji muryar shi to sai ta gane, kuma tasan KAMIL bashi da irin wannan kwarjinin, bashi da wannan had’e fuskar, kullum yana cikin fara’a da murmushi, muryar KAMIL kamar ruwan sanyi take, me ma ya saka har ta zata shine bayan ta san abu ne da bazai tab’a faruwa ba, lumshe idanunta tayi da ta tuna ance ko wane mutum yana da mutane guda bakwai a duniya masu kama da shi, bata bud’e idanunta ba har sai da ta samu nutsuwa, hannunta ta saka ta goge hawayen ta, sannan a hankali ta fara bashi hak’uri, shi kuwa har lokacin bai bar mata kallon hararar da yake mata ba, bata tsaya taji me zai ce ba tayi hanyar motar ta ta bud’e ta shiga, su faheema kuwa da tun faruwan abun suma su suke kallo sukayi saurin bud’e motar suka shiga, suna shiga suka fara tambayarta Sakeena lafiya da har lokacin jikinta bai har rawa ba, basu dad’e da shiga ba me motar bayan su ya fusge ta a guje ya bar wurinZuciyar shi wata irin tafasa take yi, gaba d’aya ranshi a b’ace, wani irin sharara mugun gudu yake a titi kamar wanda zai tashi sama, ga yayi ma steering wheel d’in motar tashi mugun kamu sai kace wuyan Sakeenar ya kama, tsanar ta da yake ta sake nin nin kuwa, wani irin danasanin fita wurin ta yake dan yanzu ta saka mishi mugun k’unar rai,

+

“Dan bata da kunya bata da mutunci har ta isa sunan shi ya fito daga bakin ta?,”

Kamal ya fad’i a zuci bayan k’ara taka motar shi da yayi, yanzu zuciyar shi ta k’ara azal zala, wani irin takai ci da haushi yake ji, a haka har yazo gidan su Imran, horn ya dunk’a zubawa ba tsayawa securities d’in gidan a guje suka fito bud’e mishi gate, ana wangale gate d’in ya saka hancin motar shi ya shiga, ya so yayi zaman gida yau d’innan amma a ganin shi in har ya zauna tunani zasu kashe shi barin ma yanzu da ya ganta, samun wuri yayi yai parking motar tare da lumshe idanunshi, dama be biye wa zuciyar shi ba yaje inda take, bai tab’a ganinta ba sai yau, dana sanin saka ta a idanunshi yake, da kyar ya iya tattaro nustuwar shi ya fito daga cikin motar.

A hankali ya fara takawa har ya isa side d’in Imran, bai gaya mishi zai zo ba Allah dai ya saka yana nan, bai k’arasa tunanin shi ba sai gashi ya hango shi ta window parlor d’inshi a zaune yana kallo, wata hamdala yayi, tun kan ya k’arasa yagan Imran  ya bud’e mishi k’ofa, wato shima ya hango shi kenan, Kamal na isa inda yake ya mik’a mishi hannun suka fara gaisawa har suka isa cikin parlor d’in, samun wuri sukayi suka zauna,

Tunda Kamal ya zauna yayi shiru, kana ganinshi kasan tunani yake me zurfi, Imran shi kuwa ya bishi da kallo, yasan zuwan nan nashi ba lafiya bane, kuma yaga yadda gaba d’aya fuskar shi ta had’e ya canza kamar yana fushi da wani, haka ya k’ura ma Kamal da ke faman kallon carpet ido, can da ya gaji ya fara tambayar shi,

“Lafiya kuwa? Naga tunda ka shigo kayi shiru kana ta kallon carpet”

Yana yin maganar Kamal yayi saurin d’agowa ya kalle shi, sai a lokacin ya dawo daga duniyar tunanin shi, shiru yayi bai bama imran amsa ba, ji yayi yana san tambayar shi wani muhimmin abu, amma kuma baya son  a tuno mishi abun da baya so ya tuna, kai zuciyar shi nesa yayi, sannan ya d’an matso daga jikin kujerar ya maida hankalin shi gaba d’aya kan imran ya fara fad’in,

“Da ni da…”

Shiru ya k’ara yi ya dakatar da zancen shi, kallon hannunshi yake da suke sark’e a cikin juna, yin maganar wuya take bashi, yin wata ajiyar zuciya yayi sannan ya maida idanunshi kan imran,

“Da ni da KAMIL da wa kafi kusa?”

Yarda yayi maganar a sanyaye kamar kwai ya fashe mishi a ciki, ko ambatan sunanshi da yayi zuciyar shi wani irin zafi take mishi, kwata kwata baya san ya tuna dashi a rayuwar shi saboda yana saka zuciyar shi mugun rad’ad’i, ta b’angaran imran kuwa abun mamaki ya bashi, yau Kamal ne ya ambaci KAMIL, gaskiya duk abunda ke damun shi ba d’an k’aramin abu bane, shima kallan abokin nashi yayi ya fara bashi amsa,

“Duka ku biyun mana, ba wanda zance nafi kusa dashi dan dukan ku nasan ku cikin ku da wajan ku har siri kan ku na sani”

Gyad’a kanshi Kamal yayi, kenan tambayar da zai mishi zai sami amsar shi cikin sauk’i,

“Tunda kace kasan siri kan mu, kasan budurwar shi Sakeena?”

Imran d’aga kanshi yayi sannan ya fara jawabin shi,

“Na santa, ba sun had’u bane da yaje masters d’inshi turkey? Ita kuma tana Shekarar farko, tunda ya ganta ya fara santa, kamar love at first sight ne, gaba d’aya zaman shi a can binta ya dunk’a yi dan ta k’arbi soyayyar shi amma bata fara kula shi ba sai dab da zai dawo Nigeria, a lokacin suka fara soyyaya me k’arfi, in har zaka tuna yak’i dawowa ma ko bayan ya gama masters d’inshi, sai da Abba yayi mishi jan idanu”

Imran na gama zancen shi ya k’ara maida nustuwar shi kan abokin nashi, wanda yayi tsit a wurin, kallon Imran yake amma ya k’ara canza wa, kana ganin shi kasan akwai tsantsar damuwa a tare dashi, tunda Imran yake a rayuwar shi bai tab’a ganin y’an biyu wanda sukayi mutuk’ar shak’uwa, bayan san junan su da san farin cikin juna kamar KAMAL da KAMIL ba,

“Nasan kaima kasan zancen nan saboda duk duniya ba wanda KAMIL ya yarda dashi kamar ka, me ya saka ka tambaye ni?”

Kamal mai da kallon shi yayi jikin bangon d’akin ya k’ura mai ido, abunda ya saka ya tambaye shi ba komi bane kawai so yake yaji ko labarin da suka sani iri d’aya ne, k’ara maida hankalin shi kan abokin shi yayi wanda shima d’in shi yake kallo,

“Ka tab’a ganin ta ido da ido?”

Imran girgiza kanshi yayi, “a’a, ban tab’a ganinta ba, amma dai nasan ba’a wurin iyayenta take ba dan sun rasu, kawunta ne ke ruk’eta SUNSUSI ZUBAIR, wannan dan kwangilar, nasan kasan shi dan a k’asar nan ba wanda bai sanshi ba,

Dakatar da kanshi yayi daga bayanin da yake ma abokin shi, yasan Kamal ya sani saboda ya tabbata Kamil ya fad’a mishi kumi dan basa boy’ewa juna abu, shima yima abokin tashi tambayar ne”

“Kai baka tab’a ganinta bane?”

D’aga mishi kai Kamal yayi, sanyi ya bud’e bakin shi a hankali ya fara magana,

“Ban tab’a ganinta ba, lokacin da yake turkey ina da wannan chorionic ulcer d’in, Mami da Abba basa bari na nayi nesa dasu, kawai dai yana bani labarin ta duk lokacin da mukai waya”

Imran dai baisan me ya saka Kamal yake ambatar budurwa Kamil ba dan wannan tsohon zance ne, so yake ya tambaye shi me ya saka yake mishi tambayoyin nan amma yana jin tsoro, a cikin y’an biyu Kamil yafi sauk’in kai da san mutane da shiga cikin su, shi kuwa Kamal opposite d’inshi ne, duk abun hayaniya da jama’a baya san su, gashi da wani irin taurin kai da miskilanci, halin su yasha bam bam ga dai su identical twins, shi ya saka mutane da yawa ba su san Kamal ba, sunfi sanin Kamil saboda shi me jama’a ne, in har ba gaya maka akai ba baza ka tab’a sanin Kamil y’an biyu bane, saboda ko makarantar da sukayi daban ne, Kamil boarding shi kuwa Kamal day, harta university d’insu wuri daban daban sukayi, Kamil yayi degree d’inshi a Dubai, masters d’inshi a turkey shi kuwa Kamal gaba d’aya karartun shi a Nigeria yayi,

K’ara kallon abokin shi yayi da yake faman kallon carpet, ko mene a ciki ranshi haka oho, gani yayi yai zumbur ya mik’e,

“Ni bari na wuce, ka gaishe mun da Ammi kace zan dawo takanas kawai dan ita”

Dariya abokin nashi ya saki, tare da tashi daga zaman da yake yayi wurin abokin nashi, d’ora hannun shi yayi akan kafad’ar Kamal,

“In har Ammi ce kunfi kusa, amma zan sanar mata da sakwan ka”

Kamal murmushi yayi, haka sukayi ta zancen su har suka isa inda motar Kamal yake, nan sukayi sallama ya shiga shima Imran yace ya gaishe mishi da Mami, ana bud’e mishi gate ya fita daga cikin gidan a guje, zuciyar shi tayi fari yanzu dan ya gano yarda zai b’ullo wa alamarin, yayi akwarin sai ya mai da rayuwarta abun tausayi bayan ya ruguza mata farin cikin ta.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE