ZAFIN RABO CHAPTER 3 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 3 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sakeena na ajiye faiza da faheema a hotel d’insu tayi hanyar gida bayan sunyi sallama sosai, tana isa tayi parking ta fito, ta fara takawa zata shiga cikin gidan tayi kicibis da daddy, yana zaune a compound d’in da newspaper a hannunshi alamun karantawa yake, ji tayi gabanta ya fad’i dan bata gaya mishi zata fita ba mommy ta gaya ma, ta sauri tayi ta k’arasa inda yake ta tsgunna har k’asa ta fara mishi barka da rana, jin muryar tan da yayi ne ya dakatar dashi daga karatun jaridar da yake, gyara reading glasses dinshi yayi sannan ya mai da idanunshi kan Sakeena wace ta sunkuyar da kanta tana kallon k’asa, tambaya ya shiga yi mata daga ina take, gabanta ne ya k’ara mummunar fad’uwa ta tabbata in har yasan daga wurin su faiza take sai ranta yayi mugun b’aci, tunda kanta na k’asa bazai gane bata da gaskiya ba ta shirya mishi k’arya cewa wani aiki taje ta k’arasa a office director d’in yace lallai da gama kan gobe wato ran littinin, ta ko ci sa’a ya yarda, maida duban shi yayi kan jarida tare da mata nuni ta tashi ta shiga ciki, Sakeena hamdallah tayi sannan ta mik’e tayi cikin gidan.+

D’akin mommy ta fara yi wato matar kawun ta dan ta sanar mata ta dawo, tana bud’ewa ta ganshi wayam alamun bata nan, yin hanyar kitchen ta shiga ta baya wurin masu aiki, taga blessing me aikin su a kwance, tambayar ta tayi inda mommy take, me aikin sanar da ita tayi bata dad’e da fita, Sakeena girgiza kanta tayi, mommy kwata kwata bata gajiya da yawo, kullum tana cikin fita, ficewa tayi tai hanyar d’akin ta, tana shiga ta fara rage kayan jikinta tayi closet d’inta ta d’auko wata riga mara nauyi iya gwiwarta ta saka, sannan ta fad’a kan gado bayan ta lalumu wayar ta da take cikin handbag d’inta.

Fuskar wannan mutumin da ta gani a cilantro ta shiga tunawa, ita dai bata tab’a ganin irin kama haka ba a rayuwar ta, gaskiya tasan duk yadda akai mutumin ya had’a jini da Kamil dan kamar tayi yawa, ajiyar zuciya tayi sannan ta d’aga wayar ta me k’irar iphone 11 pro max dadai fuskarta, wayar na bud’ewa ta kai kan number d’in hamida da danna sannan ta saka a kunnan ta, wayar bata dade da fara ringing ba aka d’auka, nan suka fara gaisawa ita da babbar aminyar tata, sai da suka d’an yi hira sosai sannan Sakeena ta fara cewa a hankali,

“Naga mai kama da Kamil yau”

Shiru akayi daga d’ayan b’angaran tasan k’awartata mamakin ta take yi da ta ambaci sunanshi, ita kanta tayi mamakin kanta, amma gani tayi in har bata gaya ma wani ba baza ta tab’a samun sukuni ba, hamida tayi kamar baza ta amsa ba, can kuma tace,

“Ban gane kinga mai kama da Kamil ba?”

Sakeena k’ara wani ajiyar numfashin tayi, ta ina ma zata fara yima k’awartata bayanin abunda ya faru da ita yau, jin muryar hamida ta k’arayi

“Ki amsa ni kinyi min shiru”

Lumshe idanunta tayi, ta dad’e a haka sannan kuma ta fara bama babbar k’awartata labari, tunda ta fara hamida bata katse ta ba, sai da ta tabbata ta gama zancen ta tsaf,

“Wannan wace irin kama ce haka har kikyi zatan shine Kamil bayan kinsan…”

Hamida saurin dakatar ta kanta tayi, tasan ta k’arasa zancen Sakeena zata iya rikice mata yanzun nan, shiru suka k’arayi, hamida ita ta k’ara bud’e baki ta fara magana,

“Ko dai wani d’an uwanshi ne, bai tab’a gaya miki yana da wa ko k’ani ba?

Girgiza kanta tayi kamar k’awartata na kusa ta ita sai kuma daga baya tayi saurin ce mata a’a,

“Duk rayuwata dashi ban san kowa nashi ba, ya dai cemun bashi da kowa scholarship ne ma ya kawu shi karatu garin”

A hankali tayi maganar kuma daga karshen zancen ta kana ji yarda muryar tayi rawa, k’walla ce ta cika idanunta, shi yasa ko kad’an bata son tuna shi dan ranar zata nemi sukuni ta rasa shi, sa hannu tayi ta fara goge hawayen da suka zubo fuskar ta,

“Bazan gaji da gaya miki kin yi babban kuskure, taya za ace baki san komi akan shi ba amma har kika yarda kika afka cikin soyyar shi”

Yanzu Sakeena kuka take wiwi, ta gaji da gaya mata gaskiyar da hamida take, itama tasan tayi kuskure, amma ya zatayi, lokacin so ya rufe mata idanunta da kunnanta bata ji bata gani, sosai take kuka tana jin hamida tayi ajiyar zuciya,

“Ni ba kuka nace kiyi ba, Dan Allah kiyi shiru” haka hamida ta ci gaba da rarrashin ta har ta samu ta rage kukan, sai da ta tabbata nustsuwa tazo ma sakeena,

“Kinsan surname d’in Kamil?”

cema tayi a’a, hamida shiru tayi, sai can tace da tasan surname d’inshi da ta saka Saleem wato mijinta yayi musu background check akan shi, da yake babban soja ne, su gano ko yana da y’an uwa ko ma shi y’an biyu ne tunda tace suka kama sosai, Sakeena dariya tayi da taji abunda k’awartata tace,

“Abun yayi zafi haka harda su background check?”

Hamida ma dariya ta saki, nan sukayi ta wasa da dariya suka ajiye zancen Kamil da mai kama dashi a gefe, sunyi hira sosai sannan sukayi sallama, Sakeena na kashe wayar ta tashi ta d’auko hijab tayi hanyar kitchen dan ta d’ora lunch tunda daddy na gida, baya cin abinci masu aiki sai da ita ko mommy su girka, a lokacin jinta take sakayau kamar bata da wata damuwa, shi yasa take bala’in san hamida, ta iya kwantar mata da hankali, a haka har ta shiga kitchen had’e da fara haramar d’ora abinci.

Bayan ta gama girki ta saka a flask ta jera ma daddy akan dinning sannan tayi hanyar d’akin ta, bathroom d’inta tayi direct dan ta watsa ruwa tayi haramar salla, bata jima ba a ban d’akin ta fito d’aure da towel a jikinta ta, bayan ta zauna a gaban dressing mirrior d’inta tayi shafe shafen ta da ta saba tayi hanyar closet d’inta da dauko wata doguwar riga ta material tare da dauko saban hijab komawa cikin d’akin ta tayi ta saka doguwar rigar had’e da hijab da d’auko abun salla ta fara harama, sai da ta idar tsab tayi aduoin ta data saba sannan ta mik’e komawa kan gado tayi sannan ta jawo bedside drawer d’inta ta d’auko book, ta bud’e zata fara krantawa kenan wani tunani yazo mata,

Sau da yawa in har suna fad’a da shaheeda (y’ar kawun ta) tana yawan gaya mata tana soyyya amma bama tasan wanene saurayin ta ba, tasan shaheeda tasan wane kamil, tasan asalin shi ta kuma san komi game dashi saboda shaheeda akwai san jin kwakwaf amma pride d’inta bai tab’a sawa ta tambaye ta ba, wai ma me ya saka Kamil ya b’oye mata komi tattare dashi, bayan ita ta fayyace moshi komi da ya shafeta, ba abunda ta sani game dashi in har ba sunan shi ba, da suna makaranta bata tab’a ganin shi da wani aboki ba, ko yana dashi bai tab’a kawo mata shi sun gaisa ba, dab da abun zai faru dashi suka fara samun sab’ani yawanci kullum suna cikin fad’a saboda har ga Allah boye mata asalin shi da yake yana yi mata ciwo, ko da ya dawo nigeria sunyi wani fad’a kaca kaca har sukayi sati basa ma juna magana, sai daga baya yazo ya bata hakuri tare da mata alkwarin in har ya dawo turkey ko in har ta dawo nigeria sai gaya mata komi game dashi bazai bar komi ba, amma Allah bai yarda ba, kwalla taji ta cika mata ido tayi saurin kulle idanunta, sai da taga kwallar ta koma sannan ta d’auko wayarta da take gefan ta ta kai kan number d’in shaheeda, dukda basu tab’a shiri ba a rayuwar su yau tana san jin asalin Kamil kuma ta lura ita kad’ai ce zata iya gaya mata, danna kan sunanata tayi tare da saka wayar ta a kunnenta.

Dukan su suna zaune a makeken parlor dake side d’in abban su da ya dawo daga tafiya, har mami ma tana zaune, Kamal na gefe a zaune yayi shiru kamar yana wani tunanin duk hankalin shi baya kansu, basu damu ba saboda sun san halin shi, magana bata cika damun shi sai in har y’an maganar sunzo kanshi, Kamal d’auke idanun shi yayi daga kallon bangon da suke ya mai dasu kan family d’inshi wanda suke faman dariya kana gani kasan suna jin dad’in hirar da suke, ci gaba yayi da kallon sund’aya bayan d’aya sannan da d’an karfi yadda zai maida hankalin su wurin shi yace,

+

“Aure zanyi”

Yana maganar ya katse su gaba d’aya daga hirar da suke, kamila da takai tea bakin ta bata san lokacin da ta zubo dashi ba, kausar da ta d’auki apple itama zata kai bakinta tayi mutuwar zaune, mami ta hangame bakinta tabi shi da kallo, shi kuwa abba kallon da yake mishi kallon d’auke da tambaya, gogan naku Kamal yayi kamar bashi ne yayi maganar ba, ya ci gaba da abunda yake wato kallon bango, kausar ce tayi saurin matsowa kusa dashi, ta fara ce mishi,

“Ya Kamal are you okay?”

Kamal da yake jingine da jikin kujera ya saki dariya, sannan ya k’ara bin y’an gidan nasu da kallo, d’agowa yayi daga kan kujerar sannan ya tattaru nustuwar shi ya maida ta kan Abba da Mami,

“Da gaske nake aure nake son nayi”

Shiru wurin yayi ba abunda kake ji sai k’arar tv, an dad’e a haka ba wanda yace wa kowa komi, shi kuwa abun mamaki ya bama Kamal, yarda sukayi a wurin kamar bai isa yin aure ba, sai can mami ta kalli kausar da kamila tace musu su basu wuri, suna fita daga d’akin ta maida hankalin ta kan tilon d’anta,

“Aure fa kace Kamal, ko sati d’aya da ya wuce da nayi maka maganar aure nuna mun kayi baka san maganar, ta ya akayi yanzu kan canza zancen ka?”

A hankali mami tayi mishi tambayar amma fuskar ta bata d’auke da wasa, Kamal gyaran murya yayi,

“A lokacin da kikayi mun maganar ba wata wacce naji ta kwanta mun a rai, sai da na dawo k’asar nan nagan ta naji gaskiya tayi mun kuma ina so in aure ta”

Duk zancen da suke abba bai ce komi ba sai dai binsu da kallo da yayi, mami ce ta k’ara kallon shi irin kallon tuhuma d’innan,

“dawowar ka kwana hud’u kenan amma har kaji kana son yarinyar har takai da kana san ka aure ta?”

Mami ta san halin d’an nata kamar yunwar cikin ta, tasan yarda mata basa gaban shi, aure bai tab’a damun shi amma ya canza ra’ayin shi da ya dage akai shekarar da shekaru a cikin kawai kwana hud’u akwai alamar tambaya, shi kuwa Kamal d’aga kai yayi sannan ya fara musu bayannan ita y’ar gidan wace, iyayen nashi sunyi shiru suna sauraron shi sai da ya gama tsab, Abba ajiyar zuciya yayi,

“In har y’ar gidan sunusi zubair ce to abu yazo da sauki, dan mutumi na ne, muna shiri sosai dashi, zanje na same shi nayi mishi magana, nasan ba zai k’i zancen ba”

Wani dad’i ne ya rufe Kamal, zai same ta cikin sauk’i kenan, jin zuciyar shi yayi tayi fari, wani irin farin ciki ya mamaye shi, muryar mami ce ta dawo dashi daga duniyar da yake,

“Gaskiya Alhj ban yarda da wannan abu ba, in ita yarinyar bata so fa?, ni a gani nan yaje wurin ta su fara sasan tawa tukun, in har yayi mata to, sai a fara shirin biki in har baiyi mata ba sai yaje ya sami wata, yanzu ai an daina auran had’i”

Ji yayi wuta ta d’auke mishi, bayan wani abu da ya taho ya tsaya mishi a mak’ogarun shi, kada fa mami ta ruguza mishi shirin shi, ya bud’e baki zai k’ara tsaro wata k’aryar dan ya tsara uwar tashi abba ya riga shi,

“Iyayen mu da kakannin mu auren had’i akayi musu sun mutu?

Mai da kallon shi yayi kan Kamal sannan ya nuna shi ta d’an yatsa tare da cewa,

“Ko kina so kice mun d’an naki na da mugun hali shi ya saka bakya san yayi aure?, ni banga aibin abun ba dan ba bare zai aura ba, y’ar abokina ce,”

Wani farin ciki ne ya sake rufe Kamal, yaji dad’i da abba ya nuna yana bayan shi, mami shiru tayi a wurin da taga ran mijin nata nason ya b’acci, bata k’ara cewa komi ba, shi kuwa kamal gode wa Allah ya shiga yi a zuci, mik’ewa yayi ya ma iyayen nashi sallama bayan abba ya gaya mishi gobe zai je ya sami sunusi zubair d’in su tatauna, duk abunda yace zai ji daga gare shi, haka Kamal ya fita daga parlor d’in zuciyar shi d’auke da nishad’i dan jin dad’i.Yau sati d’aya da neman shaheeda a waya bata same ta, har ta gaji da kiran layin ta, jiya ma sai da taje wurin mommy ta tambaye ta ko ta canza number bata sani ba tunda sunyi wata da wata ni basa kula junan su, mommy tace mata wayar tace ta sami matsala sai dai in har ta bata number d’in mijinta dan itama tanan suke gaisawa amma sam Sakeena tak’i kawai tace mata in sunyi waya dan Allah tace mata ta neme ta in har an gyara wayar tata, yanzu kullum tana cikin jiran call d’in shaheeda ta k’osa ta kira ta.+

Bayan da dawo daga office tayi wanka ta ci abinci da dai duk abunda ya zame mata aladar ta, tana zaune gaban MacBook d’inta tana wani aiki da bata k’arasa ba a office d’azu, taji anyi knocking k’ofa an shigo, mommy ta gani a tsaye a wurin, itama binta tayi da kallo,

“Kije kawun ki na neman ki”

Haka kawai tace mata ta k’ara gaba tare da kullo mata k’ofar, Sakeena kuwa bin k’ofar tayi da kallo sai can ta mik’e ta zura k’atan hijab sannan ta fito tayi side d’in daddy, tana shiga ta tarar shi kad’ai ne a parlor d’in da tv kunne yana kallon news d’in karfe tara, samun wuri tayi a k’asa a gefan shi ta zauna, sannan ta fara gaishe shi, sai da suka gama gaisawa sannan daddy ya d’auki remote ya kashe tv d’in ya juyo da nutsuwar shi wurin ta,

“Muhimmiyar magana nake so muyi dake, dan haka ina so ki bani hankalin ki kuma ki saurare ni”

Gaban Sakeena ne ya fad’i, wata muhimmiyar magana kuma, dake wa tayi ta amsa mishi da toh da taga zata barshi da jira, tana ji ya fara ce mata,

“Kinsan yanzu ke ba yarinya bace, shekarun ki sunja, ban san dalilin da ya sa kike zaune har wannan lokacin ba aure ba”

Zuciyar ta k’ara harbawa tayi, me ya kawo maganar aure, me daddy yake nufi tukun da shekarun ta sun ja duka duka shekarar ta 25 kacal a duniya akwai mata da yawa da sunfi shekarun ta amma sunan ba suyi aure ba, k’ara jin muryar kawun nata tayi,

“Tun shekara uku da suka wuce bayan kin gama degree d’inki na zuba miki ido naga ko zaki kawo mun wani, na tsaya naga gudun ruwan ki amma na lura ko ajikin ki ke rayuwar ki kawai kike yi,”

Yana kai ayar zancen shi ya d’an tsaya na y’an skwanni sannan ya k’ara da cewa,

“maganar gaskiya na gaji da ganin ki zaune a gidan nan ba aure dan haka na samo miki miji”

Da mugun sauri ta d’ago idanunta dake kallon carpet da sauke su akan kawun ta, ta ji shi dadai kuwa, ita ya samo wa miji?? a dalilin me?, ji tayi gumi ya keto mata da taga idanun shi basa d’auke da wasa, bayan mahaukacin bugawar da zuciyar ta take, kwalla ce ta fara cika idanunta da kyar ta iya bud’e baki ta fara magana,

“Daddy dan Allah kayi hakuri kada ka mun aure, dan darajar Allah, wallahi nafi son rayuwata a ha….”

Saurin dakatar da ita yayi da hannun shi,

“Bance kiyi mun magiya ba dan duk abunda zaki fad’a bazai saka ni na canza shawarar da nayi ba,”

D’aukar remote yayi ya kunna tv tare da maida hankalin shi wurin labaran da ake yi,

“Ki tashi kije ki fara shiri dan bikin nan da sati biyu ne”

Sakeena da tayi mutuwar zaune ta kasa ko motsi, ga hawaye dake ambaliya a fuskar ta, me ta tab’a mishi a rayuwar ta da yake san yi mata auran dole, wasu sababin hawayen ne suka sake kwarara, da kyar ta iya samu ta mik’e dan jikin ta wani irin rawa yake, haka har ta bar parlor d’in, tana turo mishi k’ofar ta zube a k’asa a wurin kuka mai k’arfi ya kub’oce mata, tunanin iyayen ta da suka rasu ta shiga yi, ta tabbata da suna da rai baza su tab’a yi mata abinda bata so ba, wani irin zafi zuciyar ta take nata, a lokacin taji san iyayen ta da kewar su ya dake ta, kuka take yi a wurin sosai ga babu mai rarrashin ta, sai da ta gama kukan ta sosai sannan ta tashi daga wurin jiki ba kwari tayi d’akin ta.

Tana shiga ta zarce ban d’aki ta yo alwala daman isha tayi, tana fito wa ta samu abun salla ta fara, ko da ta idar ta dad’e akan abun salla sosai tana adu’a tare da kaima Allah kukan ta, tana gama addu’a bayan ta gama shafa’i wutirin ta d’auko qur’anin, shima ta dad’e tana karatu sai wurin goma da rabi ta mik’e daga kan sallayar.

Tana kwance akan gadon ta, kana gani kasan abun duniya yayi mata yawa, ga ba dama ta kira hamida yanzu dan dare yayi sosai kuma tasan in har ta kirata zata tada mata da hankali ne, shiru tayi a kwancen da take sai hawayen dake zuba a idanunta, ba abunda yake tada mata da hankali sai in ta tuna bama tasan wa zata aura ba, bata san halin shi ba, bata san fuskar shi ba, hawaye ne masu zafi suka sake zubowa daga idanunta, me ya saka daddy zaiyi mata haka, a matsayinta na marainiya bai kamata ya zalince ta haka ba dan tasan in har ita y’ar cikin shi ce bazai tab’a yi mata abun da yake shirin yi mata ba yanzu, dan shaheeda wanda take so aka barta ta aura kuma bai tab’a takura mata da maganar aure ba, gaskiya rashin iyaye babbar masifa ne a wurin ta, tashi tayi daga kwanciyar da take ta had’e cinyoyinta da jikinta tare da d’ora kanta akai ta shiga rera kuka me mugun abun tausayi, haka ta k’wana tana wannan kukan sai dab da asuba ta mik’e danyin salla.

Ko da ta fito wurin 7 zata ma daddy breakfast ta tsince mommy a kitchen d’in, da mommy ta ganta sai da tayi mugun firgita, saboda yadda ta koma, idanunta sunyi jaa wur bayan kumburan da suke, a rud’e tashi ga tambayar ta lafiya, Sakeena shiru tayi dan tasan ko ta gaya mata ba abunda zata iya yi, haka mommy ta hak’ura ta kyaleta, ita kuwa da taga mommy na kitchen d’in alamun ita zata yi ma daddy breakfast ta juya ta koma inda ta fito, tana shiga d’akin ta tayi ajiyar zuciya sannan ta rarumo wayar ta ta shiga yima oganta waya na wurin da take aiki tace mishi baza ta sami damar shigowa ba dan bata jin dad’i.

——–

Hamida da ta fito da sauri dan ta bud’e k’ofa saboda k’arar doorbell d’in ta ishe ta ga ba mai aikin ta a kusa, ta na wangale k’ofa taga Sakeena a tsaye tana kallon k’asa, gaban ta ne ya fad’i, ko daga shigar da tayi tasan ba lafiya ba, kafafunta na d’auke da bathroom slippers, bayan wani hijabi da ta maka a jikinta, Sakeena ta d’aga idanunta ta sauke akan k’awartata, hamida bata san lokacin da tayi kanta ba, ruke kafad’un aminyar tata tayi ta fara tambayar me ya faru, kana gani kasan a rud’e take saboda yarda taga kaman ninta ya canza, Sakeena najin muryar ta ta fashe da kuka hamida da mugun sauri ta jawo ta jikinta, haka suka tsaya a bakin k’ofa jiki yayi sanyi, sun dad’e a haka kafin hamida ta ja ta su shiga cikin gidan.

Sun zauna jigum bayan Sakeena ta gama bata labari, itama d’in yanzu kwalla ta cika mata ido ga sakeena da bata bar kuka ba har lokacin, haka ta dage da dunk’a rarrashinta, sai da ta gama kukan ta me isar ta sannan hamida ta kalle ta,

“Yanzu ba abunda zamu iya yi?”

D’aga kanta tayi, “ba abunda zamu iya yi dan duk dangin mu ba wanda yake jaa da maganar daddy, in yayi magana ta zauna ke nan ba mai iya canza ta sai dai in har shine ya canza kuma ma wannan abun ne me wuya”

Kwalla ce ta sake cika idanun hamida, kamo hannun sakeena tayi, ta saka cikin nata,

“Ki saurare ni da kyau kiji abunda zan gaya miki”

Sakeena d’aga idanuta tayi ta kalli babbar k’awartata tare da maida nustuwar ta wurin ta,

“Ki d’auki wannan kamar jarabawa ce daga wurin Allah, ki sani Allah baya taba d’ora wa bawan shi abunda yafi k’arfin sa, in har kika daure kika yi musu biyyaya to na tabbata zaki ga ribar ta, Allah ya gani da zuciya d’aya kike zaune dasu in har sunyi ne dan su cutar dake to suje dan kansu”

Tana gama zancen ta ta saka hannu ta fara share ma sakeena hawayen ta tana kiyi shiru k’awata kinji, bayan komi ya lafa hankalin Sakeena ya kwanta har ta samu tayi wanka ta shirya daman mijin hamida baya gari, hamida ta shiga kitchen ta d’ora musu shinkafa da wake za suci ta da mai da yaji, Sakeena bata koma gida ba sai da hamida ta tabbata ta kwantar da hankalin ta sannan ta k’ale ta tafi.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE