ZAFIN RABO CHAPTER 5 BY SAKIEYY
ZAFIN RABO CHAPTER 5 BY SAKIEYY
Duk jikinta ba ya mata wani dad’i tun jiya bayan ta gane wa zata aura, jinta take yi daban, ba abunda bata sak’awa a ranta yanzu da take zaman jiran daddy ya dawo daga tafiyar da yayi, zuciyar ta ba abunda bata ce mata ba, har guduwa tace tayi amma ina baza ta iya ba, tana da hanyar da zata iya komawa wurin dangin mamanta amma in har ta gudu tabar gidan ba tama daddy adalci ba a ganinta,
“Ke adalci yayi miki da zai miki auran dole”
Wani b’ari na zuciyar ta ta fad’i, Sakeena saurin girgiza kanta tayi tare da kawar da tunanin da sauri, tana cikin wannan taji an tab’a ta, tana maida idanunta wurin taga wata k’anwar mommy ce me suna Maryam a tsaye, Maryam d’in ta girmeta amma ba sosai ba, kuma ba laifi suna shiri, tama fi shiri da ita akan shaheeda, duk da akwai aminci tsakanin su bata ji dad’in ganinta a wurin ba, dan tana so ta kad’ai ce ita d’aya dan hayaniya bak’i ce da suka cika gidan ya dameta shi ya saka ta fito garden d’in gidan dan Shan iska da samu ta tattro nustuwar ta,
“Ke kad’ai a zaune tun d’azu ba ko y’an hira”
Maryam tayi mata magana tare da samun wuri ta zauna a kujerar kusa da Sakeena, murmushin yak’e tayi bayan ta maida kallonta kan yatsun hannunta, har lokacin tana jin idanun maryam d’in akan ta,
“Kinga yarda kika rame a yini d’aya kawai, yaushe rabon da kikai wani abu bakin ki?”
Bata amsa ta ba, dan rabon ta da abinci tun jiya da rana, ga yanzu la’asar ta gaba to, kwata kwata bata jin cin wani abu, haka suka zauna ba wanda ya k’ara ce wa kowa komi sai can, maryam ta k’ara cewa,
“Kinsan daddy ya shigo gidan nan tun d’azu”
Da wani irin sauri sakeena ta mik’e har tana jin jiri, ita kuwa maryam binta tayi da kallo,
“Me ya saka baki gaya mun ba tun d’azu”
Tana maganar tayi hanyar cikin gida tana banka wani sauri, maryam ma binta tayi, sakeena direct side d’in daddy tayi, tana kuwa shiga ta tarar da mommy a bakin k’ofa tana shirin fitowa,
“Yauwa dama ke zan tafi nema, kawun ki yace in kira ki”
Wani irin fad’uwa gaban ta yayi, jikinta ya fara rawa, ta kasa mosti, bama tasan lokacin da mommy da matso dab da ita ba sai da taji hanayen ta akan k’afad’arta,
“Ki nustu, in kin shiga wurin shi ki tabbata kin gaya mishi duk abunda ke ranki, kada ki saki ki b’oye mishi komi, nayi mishi magana duk da bai dad’e da dawo wa ba na tabbata zai fi so yaji sauran bayanin daga wurin ki”
A hankali tayi mata maganar, ita kuwa sakeena kanta na k’asa ga idanunta sun cika taf da kwalla, mommy ce ta saka hannuta ta d’aga hab’ar ta yarda zata kalle ta,
“Ba wanda yake sonki duk duniyar nan sama da kawun ki, dukda yana ta tsawri amma nasan zai ji kukan ki ya canza shawarar nan tashi tunda kin nuna bakya so”
Wani sanyi taji a ranta dukda jikinta bai bar rawa kuma zuciyar ta bata bar bugawa ba, mommy na tafiya daga wurin tayi ajiyar zuciya tare da tura k’ofar parlor had’e da sallama da addu’a a ranta.
——–
Daddy ta tarar a zaune akan wata makekiyar kujera, tunda ta shigo idanun shi na kanta har ta samu wuri ta zauna, shiru tayi ta kasa cewa komi tsabar tsoro da fargabar da take ji, sun dad’e a haka ta kasa bud’e bakin ta tayi magana, shi kuwa da ya gaji da zaman shiru ya fara cewa,
“Ina dawo wa aka sanar dani kina da wani muhimmin abu da zaki gaya mun, ki fara baya ni ina sauraron ki”
K’ara jin wani fad’uwar gaban tayi, a haka ta dake ta fara mishi magana a hankali, kan ta gama baya ni fuskar ta ta jik’e sharkaf da hawaye, bayan rawar da muryar ta take, daddy yayi shiru a wurin yana sauraron ta, ga kallo da yake binta dashi, sai da ta gama tsab sannan ya fara cewa,
“Duk wannan bayani da kika mun baki gaya mun dalilin da bakya son ki aure shi ba”
Ta ina zata fara mishi bayani, ta ina za ta fara gaya mishi twin d’in tsohon saurayin ta ne wanda taso kamar ranta, me ya saka daddy bazai gane ba, me ya saka daddy ke san jefa ta cikin mugun hali, har ga Allah bata ji zata iya auran Kamal, barin ma yarda aka ce mata kamar da suke da Kamil tab’a ci, wani sabon kukan da sake saki a wurin, sosai take kuka soboda a lokacin shi kad’ai ne makamin ta, dan watak’ila ya ganta a haka zai hakura ya kyale ta amma da taga har an kusa awa be ce mata komi ba ta d’ago da idanunta da suke kallan k’asa tunda ta shigo ta d’ora a kan shi,
“Daddy wallahi ka aura mun shi zaka neme ni ka rasa, kuma baza ka tab’a samu na ba duk nema na da zakayi”
A lokacin ta d’anga ya motsa, lumshe idanun shi yayi sannan can ya bud’e su,
“Sakeena kina da hankali kike gaya mun wannan maganar?”
Ranshi a mugun b’ace yayi maganar, ita kuwa yanzu ta hawayen ta sun tsaya, ta kuma kafa mishi ido, ka kalle ta idanunta basa d’auke da ko alamar wasa, da gaske take in har daddy ya dage sai tayi aure zata kwashe ina ta ina ta ta bar mishi gidan, ji tayi yayi ajiyar zuciya ya girgiza kan shi,
“Tom shikenan naji, ki tashi ki koma cika amma ki tabbata kin kawo mun wani tsayaye kafin k’arshen shekarar nan, Allah ya miki albarka”
Wani irin dad’i taji ya kamata, har sai da kwalla ta fad’o fuskar ta, ta saki wani murmushi,
“Dan Allah da gaske kake?”
A rikice ta tambaye shi, shi kuwa d’aga mata kai yayi yai mata nuni da ta tashi ta fita, haka sakeena ta mik’e tana zuba mishi godiya har ta bar side d’inshi, tana shiga cikin gida tayi wurin mommy a guje ta rungume ta, tana murmushi ita kuwa mommy da ta ganta a haka tasan an sami abun da ake so, itama k’ara rungumota tayi tana nata murmushi tare da share y’an wurin da ke faman tambayar me ya faru.
———
Tana kwance a kan gadon d’akin ta tana kar k’ad’a k’afa wani littafi na hannunta tana karanta wa, kwana biyu kullum tana cikin farin ciki, jinta take kamar a sama yanzu bata da wata damuwa, sati biyu yanzu ta fasa auran ta da akai, duk masoyin ta da yaji sai da ya taya ta murna, tayi nisa a cikin littafin taji ana kwad’a mata kira tun daga waje kuma muryar mommy, sauri tayi ta ajiye littafin dan kiran da take mata da ga ji ba na lafiya bane, ta mik’e zata k’arsa wurin mommy taga an banko k’ofa ta fad’o d’akin a burkice, Sakeena na ganinta a haka hankalin ta ya tashi, tayi saurin zuwa wurin ta tana tambayar ta lafiya, abun da taji bayan mommy ta bud’e bakin ta ya saka ta shiga cikin tsananin tashi hankali ta farar d’aya,
“Sakeena ya zamuyi, kawun ki ya d’aura miki aure yanzu yanzun nan”Jin wani irin nishad’i yake, da farin ciki da ya mamaye mishi zuciyar shi, wanni in ya ganshi zaiyi zatan farin cikin da yake bai wuce na zama ango ba amma shi yasan sam sam ba haka abun yake ba, dad’in da yake ji ba na komi ba illa na ya cimma burin sa, ya kuma sami abunda yake so, ko sati biyu da suka wuce da abba ya same shi na cewar sunusi zubair ya shawarce shi da dan Allah su d’aga bikin sai nan da sati biyu abun ba k’aramar d’aga mishi hankali yayi ba, a tunanin shi a lokacin ko kawun yarinyar ya gano me yake k’ulla wa, ya shiga tsan tsan tashin hankali sai da ya zauna sosai yayi tunani da ba wanda ya gaya wa abunda ke cikin zuciyar shi kuma bai nuna hakan ba shima a fuskar shi sannan ya sami sauki.
+
Bayan sun dawo daga d’aurin auren da ya gudana a ranar bayan sallar juma’a, suna zaz zaune a makeken parlor d’in abba da manya manya abokan shi kuma mayan y’an siyasa, abinci burjik a gaban su, Kamal da imran suma na gefe dan shi imran ne kad’ai abokin shi, shi dai yayi shiru a wurin yana kawai wasa da teaspoon d’in da ke cikin mug d’in hanunshi me d’auke da tea, jin muryar sunusi zubair yayi da ya saka shi saurin d’ago idanun shi da maida su kanshi,
“Tunda an riga da an d’aura aure, gobe kawai kaje ka d’auki matar ka, kuyi kano, dan barin ta a gida bashi da wani amfanin a wurina”
Tun kan ya k’arasa zancen ya k’ara jin wani mugun dad’i ya kama shi, maida idanunshi kan abba yayi wanda yake faman d’aga kai dan yaji me zai ce,
“Gaskiya kam, tunda gidan da zasu zauna already ya gama had’uwa, zaman ta a gidan bashi da amfani”
Kamal bai san lokacin da ya saki murmushi ba tsabar farin ciki, har sai da imran ya ganshi ya zungurar mishi k’afad’a sannan yayi dariya tare da girgiza kai, abunda ya k’ara ji daga bakin abba ne ya d’an saka jikin shi yin sanyi,
“Amma ni dai a gani na, tunda ko wace yarinya mace aka tashi kaita gidan miji ana had’a ta da y’an uwa da abokan arziki sugano d’aki, why not itama a had’a ta da maman su kamal da kuma matar ka, ko su biyu ne suje su gano d’akin nata, na tabbata haka zaiyi mata mutuk’ar dad’i”
Ina kuma abba ke zuwa, dan Allah kawai a kyalle shi yaje ya d’auke ta su tafi, shi baiga me su mami zasu je suyi ba,
“Haka ma yayi, sai goben su tafi tun flight d’in safe, yarda zasu samu su dawo a goben”
Maganar da sunusi zubair yayi ce ta d’an sami shi sanyi a ranshi, da sauki dai tunda ba kwana zasuyi ba, haka suka saka wata hirar har sai da la’asar ta gabato, sannan kowa ya mik’e dan yin haramar sallah.
———
Tunda take a rayuwar ta bata tab’a zatan mutum zai iya kwana a zaune yana raira kukan da ba sausaci sai akan ta, ita da mommy jiya kwana sukayi a zaune tsabar tashin hankali, ba irin rarrashin da mommy batayi mata ba amma ta kasa daina kuka, wani irin rad’adi da ciwo zuciyar ta ke mata, wani irin jin zafin muguntar da daddy yayi mata take ji a duk sashi na jikinta, jiya tasan daddy bai d’auke ta a matsayin y’arshi ba, ji ya tasan ita ba kowan kowan daddy bace soboda yarda ya nuna mata k’arara a matsyin y’ar ruk’o ya d’auke ta, wani sabon kuka ne ya sake k’uboce mata, ina ma iyayen ta nada rai, ina ma suna doran k’asa da tasan baza ta tab’a shiga cikin irin wannan bak’in cikin ba, sau uku tana fakar idanun mommy tayi hanyar gate dan ta gudu ta bar gidan amma daddy ya baza sojoji a haraba da wajan gidan yadda baza ta tab’a iya guduwa ba, ita kuwa ta shiga uku, ina zata saka ranta taji dad’i.
Ko da aka turo k’ofar dak’in aka shigo bata d’aga idanunta taga wane ba, amma jikin ta ya gaya mata mommy ce, sai da ta isa wurin ta, sannan ta d’ago da kanta wanda yake mak’ale akan cinyar ta,
“Haba sakeena, kukan ya isa haka, in kika cigaba da wannan kukan da ba sausaci za kiyi cuta ne, ba nace miki ba ki dunk’a addu’a ko kuma ki d’auki qur’ani ki karanta, shine zaki samu nustuwa”
STORY CONTINUES BELOW
Hawaye sun k’arayi ma fuskarta wanka, ga idanunta ta sunyi jajawur, ga kanta dake mahaukacin sara mata, kallan mommy da take ya k’ara tuno mata da mahaifiyar ta da ta rasu, wani sabon kukan ta k’ara saki bata san lokacin ba, mommy kuwa ajiyar zuciya tayi sannan ta zauna a gefan ta ta shiga rarrashi, da kyar mommy ta iya sata a band’aki dan tayi wanka kuma har lokacin bata bar kukan ba.
Mommy na cikin dak’in har sakeena ta fito da towel a jikin ta, a sanyaye take takawa har ta sami wuri ta zauna akan gadon ta, har lokacin hawaye na zuba a fuskar ta, mommy gaba d’aya ta rasa yarda zatayi, taya zata fara ce mata yau za su kaita gidan mijin ta bayan tana cikin wannan halin, addu’a ta shiga yima sakeena, da Allah ya bata damar cinye wannan jarabawar tashi, sannan tayi kusa da ita ta jawo hannun ta ta maida ita kan kujerar dressing mirror, sannan ta shiga shirya ta, sai ta gama saka ta a cikin wani coffee lafaya, ga k’amshin dake tashi a jikin ta tako ina, tayi masifafan kyau dukda ba wata kwaliya a fuskar ta, tunda suka fara shirin har suka gama sakeena bata bud’e baki tayi magana ba, kuma ba ta nuna alamun k’in yarda ba dan a zatan mommy zatyi fama da ita kan ta bari ta shirya ta, yanzu kukan nata ya tsaya amma shirun da tayi ya d’aga ma mommy hankali, haka ta barta zaune a wurin ta fita dan zuwa side d’inta tayi nata shirin.
———-
Da tana san auranan da kuwa zata mutuk’ar jin dad’in yarda surukar ta take mata, tunda suka had’u mintu talatin da suka wuce take manne da ita, dan suna dira a airport d’in matar wurin ta tayi kuma abun farko da ta mata suna had’uwa shine ta kamo fuskarta ta k’ura mata ido sannan can ta fara fad’in masha Allah, harda rungume ta, ita kuwa sakeena idanunta na lumshe, tama kasa bud’e su balle ta k’are ma matar kallo, ko a cikin flight d’in hannunta na ruk’e da nata, tak’i sakin ta sai hira take mata, ita kuwa da idanunta nakan cinyoyinta ta kasa kai idanunta wurin ta, a haka har suka suaka a garin kano.
Gaban ta da ne ke wani mahaukacin bugawa bayan k’arar da zuciyar ta take mata a kunanta, ba abunda take in ba addu’a ba, har su mommy da mami suka ajiye da makeken d’akin ta, dukda ba wani kallon gidan tayi ba, tasan makeken gida ne, gidan ya sha naira, yanzu ba shine a gabanta ba, mommy da mami na zaune a kusa da ita suka fara yi mata fad’a me ratsa jiki, ba kuma kalar hak’urin da basu bata ba, Sakeena zama tayi a wurin da dunk’a rairai kuka har sai da tayi me isar ta, sai da suka tabbata tayi shiru sannan suka saka ta a ban d’ake tayi alwala, sai da suka idar da sallar azahar suna zaune sukaji horn, wani irin fad’uwa gaban sakeena yayi har jikinta sai da ya fara rawa, mami ce tayi saurin ce mata ta kwantar da hankalin ta ba kamal bane k’awarta ce dake zama a kano ta kawo musu abincin dan basu da wani nisa, sannan taji hankalinta ya kwanta.
Bayan duk sun gama cin abinci, masu aikin da k’awar mami tazo dasu sun gyara gidan tsab ga k’amshin turaren wuta da yake tashi, sunyi sallar la’asar dukda sakeena ba wani abincin zafi taci ba, dan kawai mommy da mami ma sunyi mata dole ne, bak’in da sukayi sun watse, su ka k’ara jin wani horn d’in, cikin sakeena ne yayi wata irin k’ara, jikinta ya hau rawa, ga zuciyar ta fara wana mahaukacin bugawa, yanzu tabbas tasan shine, tasan dama su mommy shi suke jira yazo sannan suyi hanyar airport su koma abuja, wani k’arfi ne yazo mata tayi sauri kama hannun mommy dake shirin tashi,
“Mommy dan Allah kada ku bud’e mishi, dan Allah kada ku barshi ya shigo, dan Allah mommy ku koma abuja dani kinji, wallahi bana sanshi, bana san zama dash…”
Mommy ce tayi saurin toshe mata baki, sannan ta maida idanunta kan hajiya rahima, wacce tayi shiru tana kallan su,
“Kyale ni da ita, jeki ki bud’e mishi”
K’ara tsayawa tayi tana kallan su kamar baza taje ba sannan can ta fra takawa tayi hanyar barin d’akin, tana fita bayan ta jawo musu k’ofa, mommy ta juya kan sakeena, wacce jikinta yanzu yana wani irin girgiza tsabar k’arfin kukan ta”
“Kina da hankali kuwa?, taya zaki ambaci bakya sanshi a gaban uwar da ta tsugunna ta haife shi, ke a ganin ki zata ji dad’i?, ji yarda take miki tunda kuka had’u kamar zata cinye ki saboda so, haba sakeena tarbiyar da nayi miki kenan”
wani kukan ta k’ara saki, mommy kuwa ta jawota jikinta tana shafa bayan ta, sun dad’e a haka sannan can haj rahima ta dawo tare da ce musu su iso parlor, haka mommy ta kama sakeena har suk shiga parlor d’in bayan ta sauke mata lafaya, tana shiga suka fara gaisawa da kamal wanda ya tsugunna har k’asa ya mik’a gaisuwar shi, ita kuwa sakeena k’ara rud’ewa tayi da taji muryar shi, ga kamar tasan muryar, bayan sun zauna a kan kujera, kamal da sakeena na k’asa suka shiga yi musu fad’a sosai mai ratsa zuciya, tunda suka fara fad’a sakeena ke kuka, sai da suka gama nasu sannan suka kira abba da daddy a waya suma sukayi nasu, sai da suka gama komi sannan suka hau mota sukayi hanyar komawa airport.
———-
Tunda suka bar gidan tana zaune a k’asan da suka barta da kasa ko mosti, tsoro ne fal cikin ta da wata irin fargaba, tana jin mostin shi a kusa da ita, amma ta kasa ko d’aga d’an yatsan hannunta balle har ta juya ta kalle shi, tana ji ya mik’e daga zaman da yake sannan yayi hanyar fita daga gidan, ko magana bai yi mata ba, motar shi taji ya fusga a guje yabar haraba gidan, tana ji ya fita ta saki wata ajiyar zuciya, a hankali ta d’ago kanta ta sauke akan makeken parlor d’in, daula da naira dake cikin parlor d’in sai da ya bata tsoro, a hankali ta mik’e ta fara duban gidan dan tunda tazo tana bedroom d’inta, daddy ya kashe kud’i a kayan d’akin ta ba d’an k’aramin kud’i ba, ko shaheeda bai kashe mata irin wannan mak’udan kud’in ba, gidan side biyu ne, d’aya nada two bedrooms da parlor d’aya shima nada two bedrooms da parlor, ko da tazo gaban bedroom d’inshi ta tsaya sai da gabanta ya fad’i, san bud’ewa take yi ta shiga amma tsoro ya hanata, haka ta dake ta tura k’ofar ta shiga.
D’akin shi is plain and simple ba wani abun hayaniya a ciki, amma dak’in yayi kyau sosai, haka ta shiga tana kalan komi d’aya bayan d’ayan har ta isa bedside drawer d’inshi, wani frame ta gani a tsaye a wurin, da wani sauri sakeena ta d’auke shi ta shiga dubawa shi, hotan kamal da kamil ne, ita kanta da kasa gane wane kamil balle kamal tsabar kamar da suke, ga har kayan jikin su irin d’aya ne, fuskokin su d’auke da identical smile, hotan suna yara aka d’auke shi maybe lokacin suna secondary school, ta dade tana zubawa hotan kallo dan gaba d’aya hankalin ta nakan y’an biyun, bata san lokacin da ya shigo gidan ba, sai da taji wata gigitacciyar tsawa bata san daga ina ba har sai da ta saki hotan hannunta ta juyo a tsorace.Bayan yabi bayan su mami ya tabbata da sun isa airport yayi saurin juyowa ya koma gida, bayan yayi parking a harabar gidan ya fito da yana takawa a hankali har ya isa cikin gidan, yayi zatan zai ganta a parlor d’in da ya barta amma yaga wayam, a tunanin sa ta koma dakin ta shima haka ya fara takawa tare zuwa daidai wurin k’ofar ta, Kamal da wani mugun karfi ya banka k’ofar, ya dan tsaya na sakwani yana dube dube had’e da karasawa cikin d’akin harda bud’e bathroom shima dai bai ganta ba, wani abu ne ya fad’o mishi, kada dai ta gudu?, shi yasan ba san auran take ba, tuni hankalin shi ya tashi da sauri yayi waje dan ya tambaye mai gadi a dai dai lokacin da ya wuce ta bedroom d’inshi ya ganta a tsaye da abu a hannunta ta k’ora ma abun ido, tsaya wa yayi da saurin tafiyar da yake tare da yin wata ajiyar zuciya,
A hankali ya fara takawa har ya isa bakin k’ofa, had’a hannunshi yayi akan k’irjin shi sannan ya jingina da k’ofar ya fara zuba mata kallo, a lokacin k’ara jin wani irin haushin ta yayi bai san daga ina ba, wane ya bata izinin shigo mishi d’aki har ta tab’a wani abunshi?, zuciyar shi ce ta k’ara wani irin hanzarta shi, bai san lokacin da ya daka mata wata irin gigitaciyar tsawa ba, yana gani ta saki abun hannun ta ta juyo a firgice, shi kuwa gaba d’aya fuskar shi ta canza a lokacin, kawai ganinta da yake ya sake saka mishi wani irin bacin rai, sai da ya matso dab ita yaga ta k’ara shigewa jikin bedside drawer din dake bayan ta, jikinta har wani irin rawa yake.
Kamal wani irin mugun kallo yayi mata tare da tsugunnawa da d’aukan frame din da ya fad’i, yana d’ago shi yaga hotan shi da kamil lokacin da suna secondary school, ji yayi wani abu ya soke shi a zuciya, b’acin da ranshi yayi d’azu ba komi bane dan yanzi har duhu duhu yake gani, wane da aikin nan? bai ce kada a saka mishi ko wane abu da ya danganci kamil a cikin gidan nan ba, yasan bai wuce aikin mami ba, damk’e hotan yayi da k’arfi sannan can ya d’aga shi ya rosta shi da k’asa, k’arar da hotan yayi k’ara saka sakeena rud’e wa, d’aga way’annan manyan idanun nashi yayi da sun kowa ja ja wur dan ba’acin rai ya sauke akan ta,
“Wai ya baki izinin shigo min d’aki?”
Yarda yayi maganar sai ya saka ka sakin fitsari muryar shi da fuskar shi basa d’auke da ko alamun wasa, banda rawar da jikinta yake ta kasa yin magana, wani irin haushi ne ya k’ara kama kamal ji yayi gaba d’aya baya san ganin ta a wurin, hannun shi ya saka ya fusge nata hannun da k’arfi sannan yayi parlor da ita, wani irin hurgi yayi da ita har sai da k’ugunta ya daki makeken center table d’in wurin, ta d’an saki k’ara k’adan bai bi ta kanta ba ya fara mata bayanin,
“Kada ki kuskura ki k’ara saka k’afar ki a cikin d’akina balle har ki tab’a wani abu na dan zan iya b’ala miki hannu”
Bayan ya gama nunta da d’an yatsan shi tare da yi mata kashedi ya juya ya koma cikin d’akin, yana shiga ko zama baiyi ba yaji ina ba zai iya zama da ita a cikin gida d’aya ba, komawa parlor d’in yayi ya ganta a inda ya barta tana ta kukan munafinci, ji wani hushin ta ya k’ra ji yaji kamar ya mangare ta, zaiyi mata magana yaga ba shima da time d’in da zaiyi wasting akan ta, ya shiga d’akinta tare da d’auko mata lafayan da yake kan gadon ta, ko da ya dawo parlor d’in ya cilla mata shi a fuskar ta ita kuwa har lokacin, bata bar kukan da take ba,
“Tashi ki saka”
Haka ya tsaya ya tsira ta da ido alamun tayi sauri kada ta b’ata mishi lokaci, sakeena kuwa jikina na rawa ta mik’e ta fara yafa lafaya, da kamal yaga ta kamala tsab ya nuna mata hanyar fita, shima alamun tayi gaba, ta tsaya kamar baza ta tafi ba can kuma ta fara takawa a hankali kamar wace kwai ya fashewa a ciki, amma kannan sai da ta rarumo jakar ta da take ajiye akan kujera tun shigowar su gidan ita da su mommy, yana ganin jakar yayi saurin fusge ta daga hannunta, sannan ya bud’e ya fara lalime, sai dai ya d’auko wayar ta da wallet d’inta, sannan ya maida jan idanunshi kanta
“Wato kina so ki kebe ki d’aya ki kira gida ki kaini k’ara kenan”
Ya fad’i bayan yarda yake nuna mata wayar ta dake hannunshi dai dai fuskar ta, bai bi ta kanta ba da take faman girgiza kai fuska d’auke da hawaye shab’e shab’e, hamdalla kawai yake a ranshi dan Allah ya taimake shi, da mami taji labari kashin shi sai ya bushe, samu yayi ya cire sim d’in wayar sannan ya saka ta aljihun shi, atm cards d’inta kuwa da suke cikin wallet d’inta duka ya fito dasu ya b’alla su gida biyu sannan yayi hurgi dasu, jakar ma cillar da ita yayi gefe d’aya sannan ya saka ta a gaba har suka shiga mota.
Tsit kake ji in banda sheshek’an kukan sakeena, shi kuwa sai sharara gudu yake akan titi kamar ba abunda ya tab’a damun shi a duniya, yi yake yi kamar bata zaune a kusa dashi kuma kamar kukanta baya adabar rayuwar sa, a haka har suka zo unguwar sheka da take a cikin kano, sai da ya sai sai ci wani gida, plastar siminti ne a gidan kamar yaji jiki, sannan yayi parking, daukar wayar shi yayi ya kira wacce zai kira basu jima ba suka kashe wayar, haka ma jiran da sukayi shima baiyi cikkaken minti biyar ba sai ga wata y’ar dattijuwa ta fito, tunda ga nesa ya hango tana washe musu hak’ora, shi kuwa ya had’e girar sama da k’asa fuskar nan tashi a daure, da dattijuwar nan tazo dab dasu kamal ya juya ya kalli sakeena sannan ya umarce ta da ta fita ta bashi wuri, yana gani ta fara mishi kallan tambaya, idanunta d’auke da tsan tsan tsoro,
“Malama baza ki fita bane”
Tsawa ya k’ara daka mata da yaga bata da shirin fita, kan ma yakai ayar maganar shi yaga ta fara lalumar murfin mota tana shirin fita, ga jikinta ta ya k’ara rikecewa sai rawa yake, hawaye sai kwarara suke a fuskar ta, binta yayi da muguwar harara har sai da ta gama fita daga motar gaba d’aya sannan ya maida hankalin shi kan motar shi tare da fisgar ta da barin wurin har yana tayar da k’ura.