ZAFIN RABO CHAPTER 8 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 8 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Nurse ce a gefan ta da take faman shirin mai da mata da drip dinta, sakeena na zaune tayi wani shiru, ga sauran matan gidan da duk suna tsaye sun zuba mata ido tun bayan dawowar ta daga wurin kamal, komai haushi yake bata, wani irin tafasa ranta keyi, tasan tana needing k’arin ruwa dan ta sami k’arfin jikinta da kuwa tayi d’an k’aramin iskokai ta kori kowa a d’akin harta nurse d’in dan tana buk’atar space, maida idanunta kan hannunta tayi da yake d’auke da igiyar drip wanda aka gama saka mata,

“Kiyi hakuri ki gama wannan ruwan dan ki k’ara samin lafiya kuma ki d’an daure ki saka wani abu a cikin ki”

Nurse d’in ta gaya mata, tana gama maganar ta ta fara kwasar kayan ta tayi waje, sisi ma binta a baya ta yi, suna fita bayan sun kullo k’ofa kan tayi wani kwakwaran mosti taga ummeeta da sarah a kusa da ita, har sai da suka bata tsoro,

“Wanne had’add’an gayan da ya tafi yanzu? dan Allah a ina kika sanshi?”

Duk kansu suka fad’a a tare, sakeena kuma ba abinda take in ba binsu da kallo ba dan ta kasa gane inda suka dosa,

“Dan Allah ki mana hanya dashi mana, wallahi shine dream guy d’ina, ina mutuwar san maza irin shi”

Ummeeta ta fad’i bayan ta kamo hannuwan sakeena, idanunta sunyi narai narai dasu, sakeena da tana cikin hayyacin ta da ta saka dariya dan abun dariya ya bata, ita kuwa ta rasa irin mazan da suke burgeta sai irin kamal, wanda bashi da hali, bashi da alk’ibla, bayan haka tunda tazo gidan suke mata kallan gani gani, suna mata habaici, sai yanzu kuma da suna san abu suka saukar da girman kai, tayi shiru ta cigaba da kallan ummeta dan bata san mai zata ce mata ba, can kuma wani abu ya fad’o mata, anya y’an gidan sunsan kamal mijinta ne na sunna kuwa in banda sisi?, dan dukda karuwai ne abun zai mutuk’ar basu mamaki suka san mijinta ne da kanshi ya jefa ta cikin halin nan, k’ara kallan ummeeta tayi,

“Bansan yarda zan miki hanya ba dan babu abinda ya had’a ni dashi, amma tunda ke mace ce na baki izini ki maleke shi duk ta hanyar da kika ga dama,”

Tana gani ummeeta ta zaro idanunta waje, sakeena kuwa da gaske ta ke, duk yarda zataiyi ta maleke shi tayi koda wuri malam ne ko wurin boko zata kaishi, dan bata da abinda zatayi da kamal, koda Allah bai raba auran su ba,

“Amma bari na baki shawara guda d’aya, da kin nemi wani dan wannan ba namiji bane”

Tana gama maganar tayi ma ummeeta da sarah nuni da su matsa tana so ta kwanta, haka suka mik’e bayan kallan mamakin da suka bita dashi dan basu gane me take nufi ba, ga ba daman tambaya yarda suka ga ta had’e rai, haka suka juya suka fita daga d’akin suka ja mata k’ofa daman sauran sun bar d’akin da dad’ewa,

Tana ji an kullo k’ofa ta lumshe idanunta tare da yin ajiyar zuciya, komi ne ya shiga dawo mata d’aya bayan d’aya, yarda rayuwar ta ta zama abun tausayi ta farar d’aya, abunda bata tab’a zata ba koda a mafarki, yau kawana biyar da kamal ya kawota cikin kurkukun nan, yanzu bata da wata hanya sai faman jirin JABIR, yazo ya samo mata hanyar mafita, tunda yace nanda sata d’aya zai dawo, ranar da aka saka a kaida mata haddin ta Allah ya dube ta wannan lokacin ya had’a ta da jabir, da taga ganshi ba d’an k’aramin dad’i taji ba barin ma bayan ya jaddada mata itace mace ta k’arshe ta zai iya cutar wa, dan ta taimake shi lokacin da yake mutuk’ar neman taimako ta kuma mishi gata lokacin da bashi da wani me sauraron shi, dukda bata gaya mishi ta yaya ta shiga halin ba dan yayi mutuk’ar mamakin ganinta a wurin, mace mai gata, mai aji, da ji da kud’i, mace wacce tasan darajar ta ta y’a mace kamar ita ya tsinta a wurin, abun ba k’aramin girgiza shi yayi ba,

Ba wanda yasan ba abunda ya faru tsakaninta dashi, duk azoton su ya keta mata mutuncin ta dan yarda suka tsince ta bayan ya tafi, tayi shiru da ita da daina kuka ko wannan iface ifacen da take, a ganin su duk abunda ya faru ne yayi mutuk’ar tsoratata da girgiza ta, sun k’ara tabbatar wa bayan sunga yarda gadon yayi kaca kaca dashi, duk basu san aikin jabir bane dan kawai yayi alamu kamar akwai abunda ya shiga tsakanin su, k’ara wata ajiyar zuciyar tayi tare da juyawa tazamana tana kallon bango, tana cikin haka taji an turo k’ofa, banza tayi da wurin bata da alamar juyawa dan yanzu bata san shiga harkar kowa,

“Ga waya nan ki tashi kira duk important mutanen da zaki kira sim dinki na ciki ki gama ki bani dan ina da abun yi”

Sisi na gama fad’a ta cilla mata wayar kan katifa, sannan ta samu wuri akan wata plastic chair ta zauna, sakeena kuwa k’ara banza tayi da ita, mai amfanin kiran wayar da zatayi dan tasan ba wanda yasan halin da take ciki, kuma itama baza ta iya gaya musu ba, har zata cema sisi ta dauke wayar dan ba wanda zata kira kawai hamida ta fad’o mata rai, duk bata cikin hayyacin ta ta manta da babbar aminyar ta, ji tayi tana san jin muryar ta ko zata ji dad’i, zumbur tayi ta mik’e ta rarumo wayar a dai dai lokacin kira kuma ya shigo, wata bak’uwar number ta gani, a hankali ta latsa ta saka wayar kunnanta tare da yin sallama, muryar da taji ce ta d’an k’ara sata gyara zama kamar muryar maman su kamal,

“Sai yanzu muka samu daman yin magana dake, kowa na ta neman ki a waya, d’azu na kira shi yace ai wayar taki ce ta sami matsala yau zaije ya k’arbo ta wurin gyara”

Muryar mami d’auke da wasa, ita kuwa sakeena abun d’aure mata kai yayi, wato abunda kamal ya gaya mata kenan wayar ta ta b’aci, yanzu abun shi ya fara daina bata mamaki, itama sakar muryar ta tayi kamar ba ta cikin halin taimako, sam sam bata nuna ma mami akwai matsala ba har suka yi sallama suka kashe wayar, tana ajiye wayar tayi wata ajiyar zuciya, sannan ta nemo number daddy ta kira shi, shima basu wani dad’e ba sukayi sallama, tana kashewa ta kira number mommy, ita kuwa sun sha hira sosai, ta danne duk wata damuwar ta tayi kamar tana cikin kwanciyar hankali, kamar bata da wata matsalar, tana ganin sisi ta saki baki tana binta da kallon mamaki, sai da sukayi sallama da mommy sannan ta kira hamida, ita kad’ai zata iya gaya ma matsalar ta, amma ba halin yi yarda sisi ta zuba mata ido, hamida na d’aukan wayar ta saki y’ar k’aramar k’arar murna, har sai da ta saka sakeena murmushin da bata yi ba na kusan wata,

“Amarya ta sha k’amshi, da kanki yau, Ai ni cewa nayi bari kiyi sati sai na fara neman ki kannan ki gama cin amarci”

Wata harara sakeena ta saki kamar hamida na gefan ta,

“Wacce irin amarya kuma da cin amarci, ina nan ina shan garari”

Dama hamida zata d’ago me take nufi da tace tana shan garari,

“Ai na gaya miki aure is not easy, yanzu danma you are still new, sai da ga baya kin fara tara y’aya abubuwa zasu yi miki yawa”

Dawa zata tara y’aya? da kamal?? Allah ubangiji ya tsareta, aiko auran su bai rabu ba sai ta tabbata bata haifi jinin shi ba, dan tana tsoron d’anta ya gaji mugun halinshi, amma bata fad’i haka ba a fili,

“Kin jiki da wata magana, yaushe nayi auran har kin fara kira mun tara y’aya”

Dariya hamida ta saki ta cigaba da tsokanar ta, ita kuwa sakeena duk abun baya mata dad’i, dan bata san zancen aure ko zancen kamal, amma haka ta hak’ura tayi kamar tana jin dad’in zancen, sun dad’e suna waya har daga baya sukai sallama, sam sam hamida bata d’ago komi ba, harda ma cewa ta gaishe da kamal, tana kashe wayar ta k’ara wata ajiyar zuciyar,

“Bani in kin gama”

Sisi tayi maganar rai a had’e tare da mata nuni da ta mik’o mata wayar, sakeena wata harara tayi a cikin ranta tare da mik’a mata, sisi kuwa ta fisge wayar ta k’arfi

“Kin kyauta ma kanki da bi ki nuna akwai wata matsalar game dake ba”

Tana maganar ta k’ara fice wa daga d’akin, sakeena kuwa tabi k’ofar da kallo, kowa a gidan baya ganinta da k’ima ko da gashi duk ta sanadiyar kamal, dan ya nuna musu su ci mata mutunci duk yarda suga ga dama, ita da a rayuwarta ba na mijin data ke san kasancewa da shi irin namiji mai ganin daraja da mutuncin ta, amma Allah ya had’a ta da wanda yake, tsinane, mugu, azalimi, wata kwalla ce ta k’ara cika idanunta, sauri tayi ta maida ta dan tayi ma kanta alkwarin baza ta k’ara zubar da hawaye a cikin gidan ba.

Da kamil nada rai haka zata faru da ita? Ko wanne ce jarabawar ta?, nayin soyaya da k’ani sannan da auran yayan shi, tana jin tausayin kanta barin ma nan gaba, dan kamal ba kamil bane, kukan dai da bata son yazu sai gashi hawaye sun fara kwarara, ba abunda yake mata ciwo in ta tuna yarda suke mahaukacin kama, baza ka tab’a gane su ba, dama yarda suke kama haka kamal ya kwaso kyan halin kamil ko da kwata ne da an rage wani abun, sa kanta tayi akan gwiwar ta bayan hwayen da suke zuba, Allah ya dubeta ya fito da ita daga hanun kamal shine addu’ar da take yi a ko yaushe.Banka k’ofar palor yayi yana isa gida, har lokacin jin wani irin k’unar rai yake, ga zuciyar shi da bata bar tafasa ba, maganganun da ta gaya mishi sai yawo suke yi a kunnan shi, ta bala’in raina mishi hankali, yana shiga bedroom dinshi ya fara cire kayan jikin shi sannan ya fad’a bathroom ya watsa ruwa ko ya rage jin abunda yake ji, yana fito wa kug’un shi dauke da towel d’aya kuma a hannunshi yana goge jikin shi har ya isa makeken standing mirror d’inshi, kallon kanshi ya shiga yi, idannunshi basu dawo kalar su ba har yanzu a jaa dinsu suke, ga fuskar shi itama da har lokacin a had’e take, alamun ranshi har lokacin a b’ace yake, wani irin wurgi yayi da towel d’in hannunshi tare da d’ora hannunshi akan sumar kanshi, ya jaa da k’arfi, shi ta kalla ta gaya wa wannan maganganun, haka ya fara yin yawo a cikin makeken bedroom dinshi, tunani ya shiga yi me zai yi mata da zai mutar mata da wannan taurin kan nata tunda yaga abunda ya saka a mata kamar bai girgizata ba, can wani abu ya fad’o mishi, sauri yayi yayi wurin daya jefar da kayan shi tare da d’aukan su da fara laliiban wayar shi, yana d’auka yakai kan lamabar hajiya maimuna, bai dade da fara ringing ba ta dauka,+

“Dawo da ita gida, yanzu zan yi miki sending address d’in”

Yana gama fad’a ya kashe wayar tare da shiga cikin closet d’inshi, bayan ya aika mata da address d’in, ya d’auko wata farar riga da wani farin sweatpants ya saka sannan ya feshe jikin shi da turararuka masu dad’in kamshi, yana gama abunda zaiyi ya fito yayi hanyar parlor, ya kunna tv yana jiran news da kuma jiran daowar ta, daman yayi sallar isha dinshi a masallaci, bai ayi awa biyu ba a zaune sai ga horn, kamal a hankali ya mik’e yayi wurin window d’in da yake kallan gate d’in gidan, yana gani security ya tashi ya bud’e k’ofar, sannan motar ta cuso kai har tayi parking a gefan tashi, yana gani hajiya maimuna ta fito, maida kallan shi yayi front seat d’in motar yana jiran yaga fitowar ta, amma shiru, har yaji k’arar doorbell, a hankali ya fara takawa har ya isa ya bud’e kofar amma har lokacin hankalin shi na kanta, so yake ya koma ya cigaba da kallanta ta window yaga taurin kanta zai barta ta fito ko kuma a’a,

“Gata na kawo maka ita, ga kuma wayar da ka kawo mun d’azu”

Kamal kawai d’aga kanshi yayi, had’e da mata nuni ta ajiye wayar akan center table, yana ji ta matsa ta ajiye wayar, ya cigaba da jiran fitar ta amma yaji shiru, d’auke idanunshi yayi daga kallan da suke ma sakeena da take cikin motar tare da maida su kanta, ya fara mata kallon me kike har yanzu a cikin gidana, can wani abu ya fad’o mishi, kud’in ta take jira ne?

“Kan ki k’arasa gida zan aika miki da balance d’in kud’in ki”

Yana gama maganar ya maida kallon shi waje, har yanzu bata fito daga motar ba, tana zaune a ciki tayi shiru, haka ya cigaba da zuba mata kallo maganar da hajia maimuna tayi ce ta dawo dashi daga duniyar da yake,

“Wai dan Allah na tambaye ka?”

Bata jira amsar shi ba ta cigaba da cewa,

“Me ya saka kake wa yarinyar nan haka ne, me tayi maka?”

A hankali kamal ya juyar da kanshi tare da sauke mata wata muguwar harara, fuskar shi ta k’ara had’ewa, wacce ita da zatayi mishi tambayar nan,

“Ki fitar mun daga gida malama, nace zan aiko miki da ragowar kud’in ki”

Murya a had’e yayi magana, ko hajiya maimuna da take babba sai da ta d’an ji dum, wani irin kwarjinin shi ya rufe ta, ta kasa k’ara bud’e baki tayi magana, haka ta juya sum sum tayi hanyar waje, kamal najin k’arar kulle k’ofa ya maida kallan shi kan window, yana gani hajiya maimuna tayi hanyar front seat, tare da bud’e k’ofar, baisan me tace mata ba, sai gani yayi ta jawo hannunta daga cikin motar ta cilla ta gefe har sakeena na shirin fad’uwa, tare da daka mata wata harara, sannan ta koma driver’s seat ta bud’e ta shiga tayi wa motar key ta tashe ta ta bar harabar gidan.

K’ara nanad’e hannunshi yayi a fad’ed’an k’irjin shi, ya bita da kallo, jira yake yaga zata shigo ko kuma a’a, a tsayan da aka barta a wurin haka ta tasaya har na tsawon awa d’aya, kamal shima da yake tsaye yana kallonta har na tsawon lokacin ya dauke idannunshi dake kallan agogon dake manne a parlor d’in, sannan ya k’ara maida su kanta, yana gani ta sami wuri a kusa da wasu flowers ta zauna, da yaga ta zauna abun ba k’aramin d’aure mishi kai yayi ba har sai da ya saki murmushi, tunda yake a rayuwar shi bai tab’a ganin mace mai shegen taurin kai ba kamar ta, wato bata da niyar shigowa,

“Bari mu k’ara bata minti talatin mu gani”

Ya fad’i a zuciyar shi, a haka ya k’ara tsayawa yana kallanta har 11 na dare yayi, wata dariya ya saki da yaga lokaci, da gaske take baza ta shigo ba, ta gwamace sauro da k’waruka suyi ta cizan ta, tabbas wannan budurwa kamil ce dan irin matan da yake so kenan, matan da are very stubborn, wurin intercom yayi sanan ya danna ya kira mai gadin shi, ba kashidin da bai mishi ba da ya tabbata idanunshi nakan ta in har bata shigo ba, kada ya saki yayi bacci in ba haka ba a bakin aikin shi, yana gama wa ya koma bedroom d’inshi ya fara shirin bacci.

Ko bayan yayi sallar asuba da ya fito baiji alamun ta ba, mamkinta ne ya k’ara kamashi, a hankali ya taka har ya kom wurin window, tana nan a zaunen da ya barta jiya da daddare, wani abu yaji ya taho tunda ga tafin kafarshi har kanshi, ko shi da yake namiji baya ji zai iya kwana a zaune a kuma waje, duk taurin kanshi yasan bazai iya ba, haka yaga ta k’ara kudundine jikinta ta k’aton hijab d’in da take sanye dashi, girgiza kanshi yayi sannan ya koma bedroom d’inshi, tunda abunda take so kenan ai sai tai ta zama shi mene nashi, yana hawa kan gado yaja MacBook d’inshi yayi aikin da zaiyi, can kuma ya koma bacci bai tashi ba sai 12, ko da ya tashi bathroom yayi, ya tsara wankan shi ya fito ya shirya cikin wani blue jeans da gray shirt, ya feshe jikin shi da turare, sannan ya fito dan zuwa masallaci ana ta kiran sallar azahar, sai da ya k’ara tsaya wa ta window, yaga ko tana nan amma yaga wurin wayam, gabanshi ne ya fad’i, da sauri yayi hanyar k’ofar waje dan kada yaje da sami hanyar guduwa, yana bud’e k’ofar yaji an bangaje shi da k’arfi anyi cikin gidan a guje, da hannunshi baya ruk’e da handle d’in k’ofar da sai yaji shi a k’asa, haka ya tsaya ya bi bayan sakeena da kallo wacce da gudu tayi cikin bedroom d’inta.Wani irin azababban fistari ne ya matse ta, ta rasa inda zata saka kanta, ga ba daman tsugunnawa tayi a compund d’in gidan, ba irin doorbell d’in da bata danna ba da buga k’ofa amma yak’i bud’ewa, wani irin zagi ta aikawa kamal a k’asan ranta, d’an rainin hankali da gangan zai iya ji yak’i bud’e mata, k’ara buga k’ofar tayi da duk k’arfinta dan sauran k’iris ta saki a wando, Allah ubangiji ya raba ta da abun kunya in tayi fitsari a jikinta ya zatayi, kunya sai ta kashe ta, haka ta ci gaba da rawa a tsaye har kusan minti talatin, itama da shegen taurin kanta, me ya hana ta shiga gidan tun jiya da daddare gashi yanzu har rana ta gama fitowa, ga ana ta kiran sallar azahar, Allah ya taimake ta akwai famfo a waje ta samu tayi sallar asuba, marar tace ta k’ara wani ruk’e wa, bata san lokacin ta tace

“Wayyo Allah na, kamal ka taimaka mun ka bud’e”

Tare da lumshe idanunta ta k’ara matse kafafunta, da danna doorbell, tana ji idanun mai gadin gidan akanta, amma duk bata shi take ba yanzu, har ta gama k’addarawa yau zatayi fitsari a wando kamar daga sama taji an bud’e k’ofar, ai sakeena bata tsaya bi takan shi ba tayi cikin gidan a guje sai d’akin ta, cillar da hijabin ta tayi a k’asan bedrrom d’inta tare da fad’awa band’aki, sai ta ta gama abunda zatayi tsab ta tabbata hankalin ta ya dawo jikinta sannan ta fito, tana fitowa ta tsince shi ya jingina a k’ofar d’akinta, hannun shi a cikin aljihun wandon shi, fuskar shi a had’e tamau yarda dai kullum take, wata muguwar harara ta jefa mishi, tare da yin sauri da k’arasawa wurin hijab d’inta dan a yanayin da dake, rigar jikinta kusan sharara ce ga kanta ba d’ankwali, tana sa hijab d’in tayi hanyar waje, shi kuwa kamal har lokacin bai bar kallon ta, manyan idanunshi kaf a kanta, gabanta fad’uwa ya fara yi, a haka ta samu ta dake,

“Ji yarda yake kallo na kamar wani maye”

Ta fad’i a zuciya, yayin da a zahiri bayan ta fito daga d’akin ta fad’i,

“zan bar maka gidan ka”

Ko kallanshi bata yi ba da tayi maganar, ga yarda tayi maganar a hankali kamar ba laka a jikinta, har tayi rabun tafiyar muryar shi ta tsai da ita,

“Fita zanyi in har kika koma waje to zan tafi da key d’in yarda in uzurin ya k’ara kama ki sai kiyi a jikin ki ko kiyi a waje ko kuma ki shiga band’akin mai gadi kiyi”

Wata kunya ce ta k’ara rufeta, duk laifin shine ai da ya kama ya kulle k’ofa da duk haka bata faru da ita ba, sai data samu ta had’e fuska yarda bazai raina mata wayo ba sannan a hankali ta juyo ta sauke idanunta akan shi, har lokacin yana jingine da k’ofar hannayen sa ma na cikin aljihun shi, fuskar shi kuwa d’auke da murmushin mugunta, wani irin haushin shi taji ya k’ara rufeta da tayi arba da fuskar shi, dan ba abunda ta tsana irin kamar da yake da kamil, wata harara ta k’ara sakar mishi, sannan ta fara takawa a hankali kamar ba kunya ce ta cika mata ciki ba ta wuce shi ta shiga d’akinta, tare da kullo k’ofar a hankali da saka mata key, ta jingina a jikin k’ofar, ba abunda kake ji sai k’arar bugawar da zuciyar ta take da kamshin turaren kamal da ya cika gidan gabaki d’aya,

Shiru tayi tana jiran k’arar k’ofar parlor alamun ya fita amma taji ko mosti bai yi ba, har kusan minti biyar,

“Ko dai ya tafi ne”

Ta tambayi kanta, dan tasan zata fi sakewa a gidan in har baya cikin shi, tayi duk abunda zatayi, a hankali ta murd’a key d’in ta bud’e k’ofar a hankali itama sannan ta lek’a dan taga yanan ko ya fitan amma idanunta sai cin karo sukayi da wannan manyan idanun nashi masu d’aukar hankalin y’an mata, har lokacin yana tsaye fuskarshi ta had’e ba alamun waso ko ko kad’an, da mugun sauri ta k’ara kulle k’ofar dayi mata key tare da fara maida numfashi,

“Ki cigaba da harara ta dan zan zubar da ruwan idanunki, kuma dama zaki daina wahalar da kanki na locking k’ofar dan ina da spare key zan shigo in ina son shigowa”

Jin murayar shi tayi a kunan ta taji gabanta ya fad’i, tsoron shine ya k’ara kamata barin ma yarda yayi maganar ba ta dauke da wasa, ba ayi minti d’aya ba taji k’arar k’ofar parlor alamun ya fita, wata irin ajiyar zuciya tayi tare da zubewa a k’asa, da ruk’e k’irjinta, wani mahaukacin tsoron shi ya gama rufe mata jiki, ta tsani zama dashi ta tsani ganinshi, yanzu haka zatayi ta fama har k’arshen rayuwar ta, anya bak’in ciki bazai kasheta ba, Allah ya raba kamal da shigo mata d’aki Allah kada ya tab’a sa wani abu ya had’a su, mik’ewa tayi da ta tuna bata yi sallar azahar ba, tare da shiga bathroom d’inta.

Bayan ta idar da salla tayi addu’ointa sosai, tana sanye cikin wata atamfa doguwar riga, d’inkin yayi mutukar kyau, kyan fuskarta ya k’ara fito, dirinta ma haka saboda ramewar da tayi duk da ta d’anyi duhu, taji cikinta yayi k’ara alamun yunwa take ji dan rabinta da abinci ta manta, taso ta share amma taga baza ta iya ba saboda yunwar taci k’arfin ta, wani katon hijab ta rarumo a cikin closet d’inta da take cike da kaya sannan ta saka, a hankali ta k’arasa jikin k’ofa ta saka kunnanta ko zataji mostin kamal, dan in har ya dawo sai dai yunwa ta kashe ta dan baza ta fita ba, da taji shiru ta bud’e tayi kitchen da sauri tana shiga shima tayi locking, store tayi direct tana bud’ewa taga abinci mak’il a ciki, harda kayan garar ta,

“Me yake ci”

Ta fad’a a hankali sai kace wani na kusa da ita sobada yarda taga ba abun da aka tab’a aciki, k’ara yin hanyar fridge tayi tana bud’ewa taga ba komi aciki sai ruwa,

“Haka yake zama da yunwa?, ko kuma a waje yake cin abinci”

Duk ta jera ma kanta tambayoyi, can kuwa tayi wa kanta wani rankwashi,

“Me ruwana ko yaci abinci ko bai ci ba, aiko mutuwa naga yana shirin yi sai dai na kalle shi na k’ara gaba dan ba ruwana da rayuwar shi”

Tana gama magana da kanta tayi store ta bud’e kwalin indomie ta d’auko guda uku, dan yarda take jin yunwa gani take kamar zata iya cinye kwalin, sai da ta dafa indomie d’inta lafiyyaya tasha sardine ta saka a plate ta zauna a k’asa ta narkin abinci ta, tana gamawa ta wanke plate d’in tare da gera kitchen d’in yarda bazai nuna alamar anyi girki ba ko an shigo, ta bud’e fridge ta d’auki ruwa sunkai bottle biyar sannanta fito, tana fitowa ta jawo k’ofar tare da maida numfashi, tanayin taku biyar wurin bedroom d’inta sai jin tayi karo da wani abu tana d’aga kai taga kamal a tsaye fuska a had’e, yana mata wani irin kallo, ai bata san lokacin da ta zaro manyan idanunta waje ba da sakin ruwan hannunta tare da ja baya da mugun sauri.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE