ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 1

ZEENAT YAR JARIDA
labarin Wata jajirtacciyar yarinyace ta taso cikin talauci gashi tanaso ta zama YAR JARIDA 
Kafin ta zama Yar JARIDA tasha wahala sosai ….. 
CHAPTER 1
Tana Zaune a dakinta ita kadai tanata faman rubuce rubuce 
Dare ne sosai kusan biyu saura gari yayi tsit bakajin komi sai rugugin hadari dayake haduwa 
Zeenatu kenan jajirtacciyar “yar jarida wacce takasance batada tsoro a cikin ranta arayuwarta bataki tayi qunar bakin wake ba inharzata cimma burinta 
lnta danyi rubutu jim kadan saita dakata tayi tsai da ranta ta kalli silin din dakinta kana taci gaba 
Ahanakali aka turo dakin aka shigo Ta dago kai da sauri takalli me shigowar  Mahaifiyar tace gwaggo Sa,a 
“Yanxu ashe bakiyi bacci ba zeenatu haryanzun kinata faman wannan rubutce rubucen naki na wahala ayi mutum baxai hutawa ransa ba nifa gaskiya nafara tsanar aikin nan maku zinatu domin bakya hutawa ko kadan kuma bakya kallon 
hatsarin dake ciki ina dalilin hakan. Zeenatu tayi murmushi tace da gwagwgon 
” kwantar da hankalinki gwagwgo na yanzu xan ajiye nakwanta dan Allah kidaina damun kanki da 
Tsaurin da aikina kedashi Duk wani abu na 
hatsarin ciki da yardarAllah bazai kusanceni ba kiyita min addu,arki nasan Allah zai tsareni To hakane Allah yatsareki da tsarewarsa Amma nikam yanda nakejin wasu “yan jaridun ke shiga taskun rayuwa inajiye miki tsoro yar nan da zaki ajiye wannan aikin ki sami wani da zanfi farin ciki. Zeenatu tace 
” oh kash gwaggo kenan yaushe zanyi kasadar ajiye aikin dana samu awahalce haba ai yanda ma nake kaunar aikin jarida banga abinda zaisa na karaya kona fasa yinsaba ai duk tsanani yana tareda sauki kin manta wahalhalun dana sha kafin nasameshi ? Kin manta irin gwagwarmayar rayuwar da nayi gwaggo akan karatun aikinjarida ke kanki kinsha tausayan akan fafutukar dana ringayi wajen buga bugarganin nakammala karatuna kema ai yau innace nadaina aikin jaridar nan saikiyi min fada ko kin manta tun ina karamata nake sha,awar naga nakasance *”YAR JARIDA ne’? 
Gwagwgo taja ajiyar gwauran numfashi tace “to ya zanyi dake yar nan amma gaskiya ina cikin jin tsoron yanda kike kai dare kafin kishigo gida tunda kince wani xubin bakya samun abin hawan dazai shigo dake lungun nan namu gashi antaba biyoki kwanaki abaya kartai Allah yasa kika farga dasu Allah kuma yatsareki kk tsallake rijiya da baya 
Zeenatu tace ” hhhhmmm wannan abun ai ya zama shudadde kima daina tunashi ya wuce guna sai fatan Allah yatsare ni agaba. 
” to Amin Amin dai, yanzu dai yakamata ki kwanta haka 
Zeenatu ta ajiye biron dake hannunta tace ” to gwagwgo na yanzu ma kuwa zankwanta da sassafe naci gaba don da wuri zan fita ma. 9 
Gwagwgon na futa ta kwanta akan katifarta 
Tana kwanciya tahau karanta addu,ar kwanciya bacci Cikin minti biyar baccin yai awon gaba da ita. 
Awa daya da kwanciyar baccinta ta farka afirgice tana salati da addu.a Mafarki tayi me ban tsoro 
Tagantane acikin dokar daji tanata gudu kanta ba dan kwali kafarta ba takalmi ga wani plate C.D ahannunta Da alama akan CD din nan suke binta 
Domin data fada kan wani katon dutse suka cimmata duka suka kai mata suna cewa ta basu plate din 
Da taki basune suka daureta da igiya hannayenta abaya da kafarta sukaiwa daurin Suka dauki CD din suka tafi suka barta adokar dajin nan 
Yayinda wata kura ta tunkarota a yunwace tayo kanta zata cinyeta 
Adaidai lokacin da kurarta bude baki xata cinyeta alokacin ta farka afirgice Gumine yaringa keto mata tahau sarcewa 
Adai dai lokacin taji ankece da ruwan sama tun hadarin daya hadu da daddare ne ba,ai ruwan ba sai yanzun 
Ta tashi ahankali cikin sanyin jiki ta saki labulan windonta ta rufo windon saboda feshi dayake Shigo mata 
Har akai sallar asuba bata komaba Alokacin ruwan yatsagaita sai yayyafi 
Tayo alwala tadawo daki tayi sallarta ta nafita 
tukunna ta bada farilla Ta dade tana yin addu,o,i Afarkon abinda yafara taba mata rai tun farkon fara aikinta da batafi shekara uku da farawa ba 
Mafarkin yau ya taba mata xuciya yasata acikin tunani da wuya inba wani abune zai faru da itaba 
Dayawa takanyi mafarkin abu kuma sai taga yafarun 
Mafarkin yau yabata tsoro matuqa 
Tayita addu.a akan Allah yai mata tsari yakawo mata sauki acikin lamuranta ya tsareta da tsarewarsa 
Karfe takwas harta karya tayo wanka ta shirya tayiwa gwagwgonta sallama tafuce gun aiki. 
><<><>>< 
Mallam yusuf nadabo shine mahaifin zeenatu asalinsa dan Nijar ne 
Buxune farkon zuwansa garin kano yafara aikin gadine agidan wani hamshakin me kudi Alh badamasi 
A cikin unguwar Allah ya hadashi da matar daya Aura sa,adatu wacce take tallan goro kullum 
agu nata yake siya Allah kuma yahada soyayyarsu Sa,adatu me halin kirki iyayanta talakawa ne sosai Watansu biyu dafara soyayya aka daura musu aure 
Gado kawai sukai mata da sif babu sauran kayan adon daki basuda hali 
Kayan gadon ma saida yabada sadaki da abinda suka tara shiyasa suka samu damar siyan kayan gadon da katifa 
A boys quaters yasami matsuguni Nan aka basu su zauna
Shekararsu biyu atare suna zaman Aure Allah yabasu haihuwa suka haifi namiji 
Haruna sunan dan 
Shekararsa daya da rabi ya rasu rashin lfy yayi kyanda ce tai masa kamun kaxar kuku 
Saida sukai shekara biyar sannan Allah yabasa 
Zeenatu yar baiwa Alokacin kuma Allah yasa mallam yusuf yasai gida na kasa acikin gari me dakuna biyu karami 
Shine musabbabin komawarsu gidansu 
Zeenatu nada shekara goma aduniya Allah yayiwa 
mahaifinta rasuwa 
Akwai wani hari da yan fashi suka kawowa Alh badamasi har cikin gida 
” yan fashin babuji ba gani sukaita harbe harbe a cikin gidan 
Sun kwashi kudade da sarkokin gwal gun matan Alhajin 
Yayinda suka harbe Alhajin da matarsa da take tare dashi aranar Amaryarsa kenan 
uwargidan uwar yaransa tana sashenta takulle itada yaranta k’anana dan babban d’anta mudansir yana kasar waje 
wani cikin ” yan fashin sunxo fita yakyallo baba buzu aboye abayan dakinsa yana karkarwa aituni 
babu imani aransa ya sakar masa bundiga aka 
Ko shurawa baba buzu baiyiba yafadi kashirban jini nafita akansa yamutu. 
Tun rasuwar mahaifin zeenatu gwaggo sa,ade ta 
shiga halin ha,ula,i na masifar talaucin rayuwa Domin iyayanta sun rasu sai dangi kalilan dama ita kadai suka haifa 
Dataga bata da gata saina Allah bata zauna ba itanma tahau neman nakanta 
Itace yin wankau da surfau harda wanke wanke agidan masu hali 
Ahakan ta raini diyarta zeenatu tabata tarbiya me kyau kana taringa fadi tashin yanda zata tallafa mata wajen ganin tayi karatun pri. Da sakandare 
Cikin ikon Allah da tallafawarsa kuwa ta kammalasu 
ltakanta zeenatun dake meson karatu ce bata zama raguwa aneman nakantaba 
Tunda tasayo foam a legal na mass com Shikenan ta baxama aikatau gidajen masu kudi Gida biyu takewa aiki 
Akwai gidan da take xuwa daga takwas din safe tayi musu wanke wanke da share share saikuma ta tafi gidan da take yi musu abincin rana da wanke wanken gidan yawa ne bata baro gidan sai uku data dawo kuma zata wuce islamiyya 
Da Allah yasa aka kafe tagano sunanta sai tahau shirin fara karatu 
Anbata admission kudin data tara da wanda mahaifiyarta ta tara haka ta hade taje banki ta biya dubu ashirin da uku 
Dayake partime ce juma,a asabar lahadi zata ringa zuwa sch din 
Bata saki gidajen aikin nataba saidai aranar makarantarta sun daga mata kafa sai raguwar albashi data samu 
tafara karatu da taimakon Allah har sukaxo semester din karshe bataci karo da abinda zai tsaidata karatunta ba burinta yakusa cika nason xama yarjarida* 
bata taba samun carry over ko absent ba 
Allah kuma yana rufa mata asiri da an bukaci kudi kona handout ne tana samu 
Abinda tafara cin karo dashi arayuwa shine nayanda megidan datake aiki yakawo mata farmaki nason yai mata fyade 
Aranar tashiga tashin hankalin da bata taba shigaba 
Da taimakon Allah da karfin da take dashi ta ceci kanta ta dau kwalba tai masa rotse ta gudu dake matarsa ta tafi asibiti da sassafe uwarta aka kwantar 
Tun daga ranar bata sake zuwa kowanne gidan aiki cikiba 
Tofa tundaganan komi yafara tsaya mata cak 
Abinda zasuci yafara gagararsu harsai in gwaggo ce tasamo kalaci agidan aikinta 
Da abu yai abu zeenatu kurar ruwa ta samo ta haya tazama ” yar garuwan karfi da yaji u Hijab take sakawa bata saka gyale sassafe tadau kura taje gidan ruwa tayi lodi ta biya ta tafi kaiwa kostamominta gidansu Gidaje biyar take kaiwa ruwa subiyata 
Hmmm

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE