ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 2

ZEENAT YAR JARIDAH
CHAPTER 2
Gidaje biyar take karar ruwa su biyata 
Arana kullum takan sami dari biyar banda wanda take balance da kudin ruwa datake biya Hakan sai zame mata kwanciyar hankali tana yin duk abinda yataso a school
Sannan batajin kunyar yan unguwa ko surutun mutane baya gabanta 
Bata kuma taba damuwa ba dan samari na gudunta gata dai kyakykyawace son kowa ita ba fara ba ita ba baka ba chocolate kala ce gata da gashi har baya 
Hakan yana mata dadi sana,ar tata tunda suna samun abinda zasuci sannan karatunta natafiya ba gargada 
Saida taga sun zanajarabawar karshen semester daga ita sai fita Hankalinta ya kwanta dataga tafito da result me kyau higher credit Batai kasa aguiwaba ta nemi admisaion a B.U.K Allah ckn ikonsa tasamu Level two tafara shekara biyu nanma tafara gwagwar maya nakaratun taba  hankali dole tabar garuwa tunda kultum tana sch sai weekend nema take futa kasuwa tayi tayin 
neman dako k0 kuma tayiwa wata me abinci wanke wanke tabiyata akullum 
Kai! Jama,a zeenatu taga rayuwa duk abinda tasan zata samu kudi na halak tabayi wanda 
namiji xaiyi itama takanyi batajin kunya kuma baya gagararta Da haka Allah yasa ta gama karatunta a BUK 
Saikuma neman aiki shima taringa bulayi tana fadi tashi a ma,aikatun datasan zata dace Saida tashekara ta samu ta dalilin Npower Tafara da shekara biyu tasamu ci gaba aka kaita gidan radio sannan tana lekawa kusan kullum gidan jaridar dake sa.adu zungur bata yin nawa agun aiki jajirtacciya ce duk inda tasan zata samu rahoton daxa fito da ita zuwa take taga tacimma burinta 
,,,,,,,,,,,,,,
Washe gari Dawowarta kenan daga gidan radio takai wani rahoto data samo adaren jiya na barayin da aka kama sunshiga gidan wani dan kasuwa sunyi sata ankamasu harma tadauki 
maganarsu sannan yan unguwa sun musu dukan kawo wuka 
Da “yan sanda aka kaisu asibiti don ayi treating dinsu najinajinan da akai musu Agajiye ta dawo tana zaune tana har hada wasu files taji anturo kofa da sauri anshigo Ta daga kanta ta xubawa wanda yashigo office din idanu baba masinjane 
Da sauri ta tambayeshi ” baba lafiya meke faruwa ? 
” hjy zeenatu ga wata baiwar Allah can taxo mana afirgice tana wani hali tana neman taimako akan kidauki rahotan maganarta asaka aredio sbd wani ne yacuceta yaiwa yarta 
fyade kuma basu bi takansuba sukai musu wulakanci kitaimaka ki hadasu da yan sanda 
xeenatu taji tsigar jikinta ya mutu ta rintse idanu ranta ya baci xuciyarta ta dugunxuma tace da baba masinja ” Kaje kashigomin da matar yanzun nan.  
Da sauri baba ya juya ya fita 
Matar ta shigo afirgice tana sharce hawaye rikeda yarta da batafl shekara taraba yarinyar ma kuka takeyi 
Zeenatu ta riketa ta kuma tsorota da ganin yanda akaiwa yarinyar mugun rauni alamu ma sun nuna ba sau daya yai amfani da itanba Takalli mahaiflyarta da tausayawa tace ” baiwarAllah bani bayanin yanda abin yake. Ta tsagaita da kukan tana fadin ” wllh “yata ce kinganta nan shekararta tara aduniya babu tasa nakaita aiki gidan masu kudi tana musu wanke wanke da “yan abubuwan gida wata uku kenan, sai yau dan masu gidan ya cutar mini da ita dana kaita baya gari to ya dawo awatannin nan kuma dama anata fadar irin barnar da yakewa yaran mutane da kuma yanda yake cutar da mutane atiti inya taho amota babu kuma yanda talaka zaiyi dashi. Takarashe maganarta da kuka 
Sosai zeenatu ta tausaya mata saida ta fidda hawaye dataga irin barnar daya aikatawa yarinyar me suna Aisha 
Duk jini na bin kafarta dakyar take iya daga kafafunta Take zeenatu tayi yan rubuce rubuce dama tadauki record na voice din matar Ta umarci matardata dauki yarinyar suje gun ” yan sandan gidan jaridar Koda jami,an tsaron ma suka gani suma sun girgixa suka kufula suka tusasu amota sai gidan Alh badamasi Saida sukajene ma taga ashe gidan da mahaifinta yayi gadine inda aka kasheshi 
Batasan yaran gidan ba balle ma wanda yai aika aikanma aturai yai karatu bai dade da dawowaba Da suka shiga dame gadin suka fara zantawa yai musu bayanin abinda yasani baice yaga tabbas ba don tsoron kada akirashi sheda kawai abinda yace yaga shigar yarinyar gidan saikuma fitO da ita da akai sannan yaga xuwan uwarta agigice amma baida tabbas din 
mudansir ne yai mata Zeenatu tace dashi to ko yasanshi da makamancin irin wannan halin?
Sai yace ” walh banace ba mutumin ma da bai dade da dawowa kasar ba balle ayi masa wannan shedar zur din. 
Da zeenatu tagano kamaryana son ya zillewa maganar ne saita kyaleshi suka shiga ciki Polisawan har ciki suka shiga domin su danko mudansir 
Abin bai basu wahalaba domin sunci karo da mukhtar ne meyi musu ban ruwa agidan Shiya nuna musu sashin mudansir din Da zeenatu ta kebe dashi tana tambayarsa ma saita ganoshi atsorace yake amma da alamar bakinsa akwai magana Tajashi can bayan gidan data hango lungu Takalleshi tace ” bawan Allah yasunanka? ” yace sunana mukhtar ” 
” to mallam mukhtar meka sani a kan wannan lamari mezaka gaya mana wanda xamu rika amatsayin shaidar da xamu kama mudansir?  mukhtar yai wiki wiki yahau in ina Tace ” kwantar da hankalinka mukhtar bazan taba tona maka asiriba balle inkiraka kotu sheda. 
Nan yatsaya da kafafunsa dayaji hakan daga gareta yasamo nutsuwa ajikinsa yakalleta yace ” ni da kika ganni aikina agidan nan shine ban ruwa da gyara fulawowi tun bayan rasuwar me gidan nan nake aiki agidan nan mudansir da kika gani ba karamin kwallo bane ya matukar takura mana agidan nan har korata yatabayi mahaifnyarsa ce ta dawo dani ba a son ransaba A rana irinta yau dama baya fita ko ina lnata zaga gidan nan ina tsaftace shi naganshi yana shige da fita tamkar bashida gaskiya Sau biyu ma muna hada idanu dashi Danaga dai abin nashi yai yawa sainabi bayansa naga yashiga sashen da Aisha take kwana Bama kullum take kwanan ba sai ranar da zatayi ayyika dayawa sannan take kwanan gidan To danaga yashiga sainayi saurin fitowa nabi ta bayan dakin na labe a windo 
Dayake akwai yar kemera atare dani tuni nafara daukar hotonsa ta windon batare daya ganniba Saida nayi musu kala goma sannan nabar gun bandaiji abinda yake ce mataba saidai naji yarinyar tana cewa banaso!ni banaso kadainal! 
Zeenatu taja ajiyar xuciya tareda dauke bututun maganar daga bakinsa 
Tace ” nagode malam mukhtar da bani hadin kai da wannan gudunmawa ina fatan kuma xaka bani camera din domin insami damar warware abubuwan cikin sauki 
Mukhtar ya gyada kansa yace ” gatama a aljihuna. Ya zura hannu aljihu yaciro ya mika mata 
Ta karba tana masa godiya suna nan tsaye saiga jami,an tsaro sun fito da mudansir hannunsa da ankwa sai wani hade rai yake yana zare idanu 
Mudansir yakurawa zeenatu idanu tamkar yasanta awani waje Itanma shi take kallo kallo na tsana da k’i Sun fita bakin get suka duru cikin motocinsu 
dama ita zeenatu da motarsu daban bata “yan sanda bace itada uwar Aisha suka shiga wani dan jarida kejansu 
Mudansir dakyar ya shiga motar yan sandan me budadden baya saida wani 
dan sanda yakwala masa bindiga aguiwowi tukunna yashiga 
“Yan unguwa nata kallonsa yara da manya ana tur da halinsa abinda yaguda kenan shiyasa yai musu gardama wajen fitowa 
Kai tsaye aka wuce dashi state CID sannan aka tafl kai Aisha  sibiti. 
Zeenatu ta tausayawa Aisha yarinya karama anrabata da budurcinta tabbas saita kwato mata yancinta saitaga mudansir ya wulakanta koda zata rasa aikinta…. 

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE