ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 3
ZEENAT YAR JARIDAH
CHAPTER 3
Saida zeenatu ta tabbatar anyiwa Aisha dinki akan idonta an rubuta magunguna ta karbi katin tagar zaya pharmacy ta siyo musu da kudinta sannan suka rankaya state CID da aka kai mudansir
Anfito mata dashi anbasu guri daga ita sai shi sai Aisha da mahaiflyarta agun tambayoyi take son tayi masa
Babu ko fara,a afuskarsa yana mata wani kallo mara ma,ana
Zeenat ta kara masa abin daukar magana abakinsa
Tace dashi ” mudansir kake kowa kasan wannan yarinyar? Ta nuna masa Aisha Ya kalli Aisha a wulakance yace “Eh nasanta mana Aiki take agidanmu. Ta gyada kanta tace wato dan tana aiki agidanku shine kasami damar lalata mata rayuwa k0?
Ya harzuko mata da fadansa “akace miki ni nayi mata hakan, wato sharri zakiyimin ko, to ta Allah ba takiba.
Tayi murmushin yake tace ” cool down mudassir bana nufinka da sharri domin inada kwakwkwarashaida akanka. Yace ” wacce shaidace dake?
Ta nuna Aisha tace ” wacce kayiwa Aika aikar ma shaida tace gatanan. Takalli Aisha da take mutsitstsika idanu
” Aisha ko zaki iya gaya mana wanda yai miki fyade.
Takara mata bututun maganar itama
Aisha tace ” wannan ne Ta nuna mudansir ” walh shine, dama yasha kawo min farmakin,
yaune dai yafl karfina yadanne ni yaimin ta karfi kuma Allah ya isana. ‘
Zeenat cikin tausayawa tadawo da abin mgynr bakin mudansir tace ” kaji abinda aisha tace ko itanma sharri tayi maka?
Ya gallawa mata harara yace ” wannan ku kuka sani bansan wannan zancen ba don ban taba aikata zinaba balle har takaini ga yin fyade sharri ne wannan karya take min.
Zeenat cikin takaici tace ” to idan itan ma da kayi mawa tayi maka karya ai shaidar hoto zai nuna gaskiya don camera bata karya. Ta ciro yar camerar ta hau nuna masa Cikin mamaki yake ganinsa kuru kuru akwance akan Aisha hotunan sunyi kala biyar ra,ayil shine yana aikata mata fyden Ya girgiza ya tsorata don baida wata mafita tabbas wannan hoton na iya kaishi gidan yari na tsahon shekaru shikuwa yasan amatsayinsa na big guy in takaishi ga hakan angama masa
toxarci asirinsa zai tonu kowa zaiji abinda yayi
Data tabbatar yagani kuma fuskarsa ta nuna alamun tsorata sai tayi murmushi tace ”
kagani ko kuma nasan ka yarda dan haka kajirayi hukunci dai dai abinda ka aikata sannan
kasani kowa zaijika aradio ayau ba sai gobe ba zakuma kaga abinda za.a yi maka ta yanda
masu aikata mugun aikin nan irinka xasu ji suma su kuka da kansu.
Ta mike taja hannun Aisha suka fuce mahaifiyarta ta rufa mata baya
Cizon yatsa kawai yake tabbas wannan yarinyar zata masa sanadin rayuwa yaji yatsani zeenatun yanzu kowa zaiji abinda yai kenan. Tabbas zaisa ayi maganinta zaibada ko nawa ne kuma don abar maganarA ranar zeenat tabada wannan rahoto agidan redio har shifting dinsa akayi akajishi adaren agidajen radios har biyar Mutane sunji mamakin wannan abun
Antausawa Aisha sosai bayama da akaji muryar mahaif’lyarta tana magana tana kuka ga muryar Aishan tana fadin abinda yai matan
Maganar mudansir kuwa da yayi taja masa tsinuwa da tofln tsiya gareshi
Koda mahaifiyarsa hjy Zainabu taji ansako zancen aradio ba karamin girgiza tayiba tayi zaton maganar bata kainanba taxaci za,a rufetane tunda tabada cin hancin dubu ashirin lallai yakamata tayi wani abun akai KafIn abun yazama babba
ltada kanwarta hjy Zulai sukaje har can state CID din suka sami manyan jami,an tsaron akan maganar wani ma,aikacin yace ” agaskiya hjy saidai kiyi hkr domin wannan maganar ta zama babba tunda har manyanmu sunji kuma ansaka hannun za.a turashi kotu domin yanke masa hukunci.
Hawaye ne yaxubo mata akunci yanzu mafl soyuwar dan natane zaiyi zaman kaso lallai dole ta tashi tsaye akai don baxata iya jurar taganshi cikin wani hali ba
Kafln su tafl saida suka kebe da wani ma,aikaci wanda abin yake ahannunsa tabashi dubu hamsin tana kuka tana neman taimakon sa
Yatausaya mata ainun ganin yanda tazama
Yai mata alqawarin kan cewa baxai bari aturashi kotun ba zaisama masa lauya yatsaya kan abin har su cimma burinsu amma tabari maganar tayi sanyi
Nan hankalinta yakwanta taita masa godiya sukaja mota suka nufi gida
,,,,,,,,,
Anshiga kotu Aranar litinin inda lauyan mudansir yakawo kwararan hujjoshinshi na karya Yayinda lauyan Aisha yabada tasa hujjar
Anata gwagwarmayar maganar har dai me sharia yadaga karar zuwa ranar litinin tasama
inda anan zai karbi shaidar da lauyan Aisha yace zai nuna a baynar jama,a Domin azaman farko alkali baya karbar shaida sai axama na biyu
Lauyan mudansir yaje har inda aka killace mudansir yasameshi yace dashi “kana ganin mutanen nan sunada kwakwkarar hujjarda zasu cimma burinsu?
Mudansir yaja ajiyar xuciya yace ” tabbas sunada hujja ranka ya dade domin akwai wata
shegiyar “‘yarjarida‘ wacce keda shaida ta hotunan da aka daukeni alokacin da abin zai faru bansan wane ne yaimin hakanba tabbas duk wanda yadau hotunan nan acikin gidan yake kuma inhar naganoshi saiya gane kuransa sainasa anrabashi da ransa.
Lauyan yace “to kai meyasa kabar kofa abude alokacin? Tun da da ace karufe kofar da baza,a sami damar shigowa adaukaba. ” walh na rufe kofar nikaina bansan yakuma akai abin ba da alama dai akwai makirci aciki
” to nidai kam bama wannan ba kanada wata hanyar da za.a dauko camerar nan batareda ta saniba don kada akaita gun alkali domin inhar ranar litinin aka mikata ga me sharia
tabbas babu ja saikaje gidan dan kande. Mudansir ya nisa yace ” akwai hanya me sauki ma kuwa, ” wacce hanyar ce? Yatambayeshi
“Akwai yarana agefe guda awani daji can bayan gari sukadai ne zasu iya karbar camera din cikin sauki agunta domin sunada makaman tsaro ahannunsu akwai bindiga da wukake da zarar sun nuna mata su tabbas nasan dole xataji tsoro tabada camerar. ‘
Lauya Ashiru yaja ajiyar xuciya yace ” yayi hakan saidai kuma kada asami matsala ka karawa kanka laifl.
” baxa,a taba samu ba domin na yarda da yaran nan nawa suna kaunata yanzuma nasan suna cikin alhinin abin nan don dai basuda yaddah zasuyi ne inkuwa sukaji hakan zasu kiyaye
zakuma su san yanda sukai nafita awannan halin. ” is ok zantafi nasamesu nagaya musu yanda zasuyi donsu karbeta. Nan yai masa sallama yakoma.
Awashe gari lauya Ashiru yabi kwatancen da mudansiryai masa har cikin dajin nan don saduwa da yaran mudansir din
Yasha mamakin dayaga wani gida me lunguna sunyi takwas lungunan cikin gidan me gadin gidan kuwa tsareshi yayi da tambayoyi da yagano daga mudansir ne shine yabarshi yashiga harma yai masa jagora zuwa cikin gidan
Ga wata doguwar katanga agidan da kwalabe asaman katangar badamar dai ahaura takanta
mutanen daya tarar agidan sunyi goma sai shaye shaye suke abinsu Suna ganin lauya suka saurara da abinda sukeyi
Guri suka bashi yayinda suka hau masa tambayoyi kwamandan cikinsu yatsareshi da tambayoyi masu zafl
Har saida yagano daga inda yake Yace da lauyan ” to tayaya zamu gano yarinyar?
lauya yace ” zanyi muku kokari in same hotonta da adress dinta amma tana aiki da gidan jarida da kuma godan radion “yancin mu.
“Ka taho mana da rahotan ta nan da kwana biyu sbd muna cikin jimamin halin da oga yashiga tunda mukaji halin daya shiga muka tsaya da komai namu ko operation mun daina fita
Lauya yace ” angama zuwa gobema zaku iya ganina don nima akage nake inga yafita awannan halin sbd mahaifiyarsa na cikin damuwa kuma akwai alqawarin datayimin me
tsoka inhar nayi mata kokarin fitowarsa cikin satin nan. Anan sukai sallama yatafl
Kwamanda ya busa sigari yakalli sama yace ” tabbas inhar yarinyar nan tashiga hannu zata gane kuranta domin sai munyi mata illar da wacce ake karewa saina dawo da ita gidan nan ta zama kukun mu me dauke mana bukatar mu aduk sonda mukaso koba haka ba kwari? Ya tambayesu yana dariya Suma dariyar keta suka hauyi suna fadin ” hakane kwamanda “! Aikinka yanada kyau hakan za.ayi Allah yakai damo ga harawa oga.
Suka hau kyakyata dariyar mugunta …..
Hmm