ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 4
ZEENAT YAR JARIDA
CHAPTER 4
Zeenat tanata hada hadar harhada takardu a office dinta taji wayarta na ruri batabi takan wayarba don ta duba taga bakuwar nambace kuma saurinta takoma gida tayi wasu ayyukan agidan
Gashi yau tawuce lokacin aikinta don shida takusa kuma biyar ne lokutan tashinsu akullum
Fitowarta kenan titi tana jiran abin hawa taji ansake kiranta da bakuwar nambar nan ta dauka da sallamarta
Abin mamaki saitaji ana kyalkyacewa da wata muguwar dariya kuma ba dariyar mutum daya bace ba
Saita kashe kawai tana jan tsaki don gani tayi aikamar ma raina mata hankali ake
Ta tare wani dan sahu tagaya masa unguwarsu da xaikaita tace masa ga yanda take biya take yace tahau kawai
Tahau tana ganin kirkinsa domin wasu dayawa tirje mata suke inyamma tayi dayawa harsaita kara musu kudi akan yanda take biya kana suke kaita
Suna cikin tafiya taga again kiran mutanen nan bata dagaba ta kyale harta tsinke akaita kira kusan biyar can da suka gaji saiga sako kamar haka
_Zeenatu ikon Allah mace me kamar maza me taimakawa wadanda aka cuta yau munga hotonki kinyi kyau kinyimin dafatan nima inkika ganni ayau xan miki domin kina gab da isowa gun angon naki amaryata na aiko motar daukar amarya ta daukeki dafatan kinyi sallama da gida?_
Ta karanta wannan firgitaccen sako yafi sau uku gabanta taji yana faduwa take tahau addu,a cikin ranta
to wannan wane shaidani ne haka?
Da alama yayine domin ya tsorata ta dakyar ta samo nutsuwar ajikinta ta rubuta masa short message kamar haka _Ta Allah ba takaba wawa mahaukaci kawai_
da sakon yashigo wayar kwamanda bushewa yayi da wata mahaukaciyar dariya ya dubi Ashiru lauya yace “kalli abinda ta turomin lallai yarinya xakiyi dana sanin wannan kalami naki ayau saikin zama
matar wawa mahaukaci arayuwarki
Ya mikawa lauya ashiru wayar shima daya karanta dariyar yayi yace ” kaga kada ka aikata mata fasadi domin mudansir yace kada acutar da ita harsai in
tabada camera din.
Dariya kawai kwamanda yasaki tareda karbe
wayarsa ahannun lauyan
Lauya ashiru ya mike da sauri yace “bari natafi kafin akawota mayi waya latter inji yanda ake ciki.
Kwamanda yace ” to hakan yayi inkaje kayi kokarin hadamu da oga mudanssir.
‘**** ****** *
Tunda zeenatu ta ajiye wayarta ajaka bayan ta tura sako xuwa bakuwar namba bata sake sanin inda kanta yakeba domin kauce hanya yayi me dan sahun nata yaron kwamanda ne shine dan aiken
Yasauka ahanya yaringa kwararar gudu ba tsayawa Taga ya canxa hanya ammafa takasa bude bakin tayi magana domin wani ruwa ya fesa mata akwalba
Sun dauki kusan awa biyu ahanya har duhu yakawo kai
Don sai bayan magriba suka isa kasurgumin dajin
Da suka shiga gidan kuwa binsa kawai take abaya yana kutsawa lungunan da ita zungui zungui take binsa badamar musu balle tirjiya
Sun dau mintina kana suka isa chamber dinsu kwamanda
Zazzafa sunan wanda yakawota ya gurfanar da ita gaban kwamanda
Kwamanda yahau tafa masa yana fadin aikinka yana kyau zazzaafa babu abinda xai gagareka afadin duniyar nan kaga dan gaban goshin kwamanda Yakalli jama,ar dake gun sunyi goma yace dasu
” kusheda daga yau anyiwa zazzafa karin albashi
asakamakon wannan kokarin dayayi. Nan suka hau tafawa suna sowar murna Zazzafa ya rissina yana godiya Kwamanda yace ” ina sarkin gida?
Da sauri wani d ‘an shawalwali mara jiki yafito yarisina yace ” gani ranka yadade adade anayi ayi karko.
Kwamanda ya murmusa yace ” sarkin gida ga ajiyata nan akaita dakin dayafi kowanne kyau da girma domin ta wataya aciki karinga kula da duk wani motsinta duk randa ta gudu daga gidan nan to
abakin ranka
Sarkin gida yace “bama zata iya gudu a gidan nan ba ranka ya dade wace ita tagane hanya ai tashigo kenan.
Kwamanda ya dubi wani dan gajere mummuna yace dashi ” sarkin girki ashirya mata lafiyayyen
abinci inta dawo hayyacinta kada abata abinci irin
na kowa ita din ta daban ce kada ta nemi ruwa amakare akawo mata komi kafin ta bukata inka kuskure abakin aikinka ‘
Sarkin girki ya risuna yace ” angama ranka ya dade zankiyaye.
Kwamanda yace “kada wanda yai mata bincike ajakarta harsai inta dawo hayyacinta ta bamu camera tukunna
Suka amsa da ” to oga!! Ya umarci zeenatu data tashi tabi sarkin daki Ba musu ta mike dama arunkufe take agabansa
Cikin bin umarni taringa binsa hardakinta me lamba 10 aka bude mata tashiga kawai Dayake hijab ne ajikinta kusan har guiwa jakarta na sakale akafadarta ta zauna akan kafet din dake
malale adakin
rufe dakin yayi da kwado yajuya yatafi abinsa….
Hmm