ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 6
ZEENAT YAR JARIDAH
CHAPTER 6
Da misalin karfe takwas da rabi nasafe saiga sarkin girki yakawo mata abin kari
Tana zaune jugum tayi tagumi ta tsunduma cikin tunani batayi isasshen bacciba kwana tayi tana juyi sbd yar banxar yunwar data gallabeta
Saijin magana tayi akanta
“Gashi baiwar Allah tashi kisha yau nasaka miki madara ashayin amma oga baisaniba domin atawa na diba miki kiyi sauri kishanye inyazo ya gani zai hukuntani jiyan ma shiya hana abaki abinci don yace horon yunwa za,a ringa miki donki gaji ki fadi inda kika bada ajiyar camerar.
Ajiyar zuciya zeenat taja tana kallon sarkin girki wato yana tausanta kenan da alamar
yanada hali me kyau.
Tace dashi “nagode mallam Allah yasaka da alkairi Yace mata ” Amin.
Ya juya zai fita yana kallonta kamar xaisake magana kuma yafasa
Har yaje kofar flta kuma yai saurin dawowa yace da ita ” ke kuwa kanwata me zai hana bazaki basu camerar ba domin kisamu ki tsira da kanki kikuma tsirar da mukhtar da aka kama yana hannunsu suna axabtarsa Hawaye yakawo a idonta jin mukhtar na wani hali Tace dashi ” wlh bazan taba bada camerar ba harsaina sadata ga me shari,a
“To ai gobene za,a yi zaman karshe akotun kuma da alamar zasuyi nasara naji suna
xantawa ajunansu ta waya kwamanda da lauya. Gabanta yafadi tahau sharce hawaye batace dashi komiba Shima yajuya sum sum kamar munaflki yafice
Koda ta shanye shayin tunani ta tafl na neman maflta
Aranar data shiryi guduwa hana idonta bacci tayi
Da Allah yataimaketa kuma aranar sarkin kofa me tsaronta yanata tashin shiga toilet atini yakeyi Cikin daren tayi lanbo ta tura kofar tajita gam tahau addu,a akan Allah yakawo mata mafita cikin gaggawa
Aiko ta hango key din dakin akan kujerar da sarkin kofar ke zama yatashi ya tafi toilet din yabarshi akai Ta xuro hannu da dabara da nishi tajanyo zaren jikin makullin aikon key yataho saigashi ahannunta
Batasha wahalaba wajen budewa tayi saurin fltowa
Taga duhu akoina takarewa farfajiyar gun kallo dakuna birjir ajere da alamar akwai mutane awasu dakunan
Tanayin gaba kadan taji muryoyin mutane saitayi saurin labewa ajikin bango ta rintse ido tanajin wani bakin ciki aranta don da alamar taga samune zataga rashi Tanajikin bangon taji hannunta ya bugi wani abu kamar katako Ashe dogon tsani ne a ajiye nan tasaki murmushi lallai Allah yana sonta
Tana makale dajakarta ajiki tayi saurin dane tsanin tahau taflya akansa tanaso takai karshen katangar donta haurata
Saida yarage saura takawa ta biyu tahaye taga anhasketa dal Gabanta ya fadi ta rintse idanunta tana hailala
Mutanen kwamanda ne sukaji motsi shine suka zo gun suka ganta
Dayan yace ” kai sangami ban guri in wullota me kakejirane.
Da sauri tahau basu hkr domin tasan zasu iya
Tafara gangarowa kasa zata sauko jikinta asanyaye
Kam tasauko kasan har mutanen gidan sun firfito sunzo gun
Sangami ya damki kanta ya riko gashinta yaringa janta har daki tana ihu
Sarkin daki yasha mamaki saida ya gaura mata mari yana fada yana cewa ” kaga makirar yarinya kinason kijazamin arabani da aikina oga ya hukuntani sangami ya cillata dakin yarufe suka koma inda suka fito Kafln gari ya waye tayi saurin ciro camerar dake cikin jakar tata ta maidata ma,ajiyarta atoilet
Da gari ya waye kuwa saiga kwamanda yazo dakin yasata agaba yana mata wulakantaccen kallo Kana yace mata ” ke nan ga me wayo k0?
To wayonki baxai amfana miki komiba don inkinga kinbar gidan nan qalau to kin bamu
camerar Barima kiji ayau ba sai gobe ba mudansir xai flto zakuma kiganshi inma kina nufin zaki kai camera atoxartashi ta Allah ba takiba Shiru tayi tanajinsa don aganinta duk shurmene zancensa don tasan babu tayanda xa,ai mudansir ya kubuta babu kwakkwarar hujja ballema me sharia yanata daga kara
Aranar ba,a bata abinci ciba ko sau daya hana abata kwamanda yayi Cikin dare tanata juyejuye saiji tayi ana tashinta
sarkin girkine yakawo mata abincinsa
Tasan sarkin girki yana tausanta shiyasa tahau yi masa godiya
Sarkin girki yace da ita ” keko meyasa kikai haka? ko kinsan cewa duk gidan nan akwai tsaro harta bata sa,a ma kkci da har aka barki da ranki tunda kina musu gardama Kinganni nan nasha hankoron guduwa ana kamani ana min azaba harna gaji na zauna gashi nayi sabo dasu har anbani matsayi tun ina dan saurayina suka kamani har cikin gidanmu da sukaje fashi suka kashen iyayena Zan iya taimaka miki yarinya zan tseratar dake insha Allahu zuwa gobe zansan yanda nayi na sato mk spare key na dakin nan insun tafi aikin fashin nasu saiki gudu kinji.
Tahau gyada kanta tana me nuna masa farin ciki Dayake ahankali yake maganar babu mejinsu harya fice tana kallonsa
Taji tausayinsa shima saida ta zubda masa hawaye tabbas inhar taflta agidan itama saita taimaka masa yafita
Taringa xabga loma hannu baka hannu kwarya cikin sakanni ta cinye shinkafar tasha ruwan daya kawo mata pure watane
Tayi hamdala ta godewa ubangiji takuma godewa sarkin girki.
,,,,,,,,,
Washe gari tana zaune ta idarda sallar axahar saitajiyo motsin mutane annufo dakin da take
Ta zubawa hanyar shigowa ido
Ga mamakinta sai ganin kwamanda tayi mudansir na biye abayansa suka shigo dakin ……
Saida gaban zeenat yafadi ta girgixa ainun da ganin mudansir Da sauri ta mike tsaye tana nuna shi bakinta na motsi da tsananin mamaki akan fuskarta
Kwamanda yafashe da wata muguwar dariya yace da ita ” kin makantu ne? To xauna kiji abinda ya wakana abayan idonki
Mudansir yabita da kallo kawai domin bakinshi nauyin furta masa komai yayi Ta xauna jikinta asanyaye
Kwamanda yace ” gadai mudansir ya fito daga tsareshin da akayi dan haka duk wani shiri da kikayi niyya na mika camerar dake gunki saiki ruguje niyyar taki domin mun nuna ikonmu da arxiki anfito mana dashi kuma alkali ya kori kara sai muga karyar “‘yar jarida‘
Mudansir dake binta da wani salon kallo Yace mata ” zeenatu kike ko wama?
Ta harareshi kawai
Ya gyada kansa yace ” oh! Komai dai yasunan ki ke kk sani burinki bai cikaba nason ganin na wulakanta to hakanki bai cimma ruwa ba sannan kisani nan da kike kinshigo kenan asakamakon son kizama mallakina so nake na aureki ki zauna anan domin ki zama me kula
da wannan babban gidan da mutan gidan dan hik nan da sati guda za,a daura aure.
Wani tsanarsa taji aranta tare da ganin yahaukace jin irin shirmen xancen dayaxo mata dashi Cikin tsiwa tace dashi ” karya kake macuci kai baka isa kaxama mijinaba sai asirinka ya tonu walh saikayi xaman dindin din agidan maxa ta dalilina inhar nabar wannan bakin gidan
Wani murmushi yasakar mata tareda cizar lebensa yakai hannu yashafl gefen fuskarta tasa hannu ta doke masa hannun nasa tareda tofa masa miyau
Kwamanda yakawo hannunsa da sauri zai mareta Mudansir yai saurin tareshi yana girgixa masa kai ” kada ka mari kyakykyawar fuskar data tafu dani one tym ka kula. Kwamanda yace ” walh oga bata isa ta wulakantaka agabana ba ina ji ina gani dole inhukuntata.
Mudansir yace ” kome xataimin kabarta bance ahukunta masoyiyata ba kuma daga yau inaso abata kulawa ta musamman akawo katifa babba asamata adaki akawo fitila tadaina ganin duhu da dare sannan abinci abata mekyau da tsafta banaso tashiga damuwa ko kadan.
Kwamanda yace ” angama oga yanda kace haka xa,ai
Mudansiryace da ita ” zancen camera nakeso muyi anitse domin nasan kinsan inda take tunda mun ritsa mukhtar yace bata gunsa amma shine yadauka yabaki dan haka kifadi inda take sannu ahankali tadawo gunmu gimbiyata. Yakarasa maganar yana murmushi
Tace “hhhhmmm kana hauka kenan ai camera baxaka taba ganln taba harsai taje gun alkali kaganta sannan kuma kaida kace ankori kara mezakayi da ita, ?
Yace ” is ok kiyita ajiyarta inkin gaji da zaman gidan kya badata amma kisani kinshigo kenan ba fita.
Kafin tayi magana harsun mike sun fita
Saida hawaye yazubo akan kuncinta yama xa,ai ta auri wannan badagiren macucin aikon gara takashe kanta da dai tayi tarayya ta auratayya dashi
Aranar zur zeenatu ta wuni ckin takaici da damuwa amma aduk sallarta ta ranar takan yawaita neman tsira agun Allah akan ya fltarta da gaggawa agidan kam faruwar lamarin da mudansir yafurta nason ya aureta Adaren tana cikin bacci taji shigowar mutum dakin duk da akwai duhu saida tagane waye don ba kwamanda bane bakuma sarkin girki bane
Data gano mudansir ne sai gabanta yatsananta da faduwa ta kankame jikinta idonta kirrrr! Acikin duhun tana kallon takunsa ya iso gunta ya zaci ko bacci takeyi yatinkareta yana xuwa ya turmusheta zai mata karfa karfa ’
Ta tattaro karfinta ta tureshi tana ce masa ” dagani macuci maha,inci aina gano ka kuma idona biyu baka isa kayi min fyadeba wallahi ta Allah ba takaba. Har cizonsa tayi
Da yaga zatayi masa kwarmato tuni yafice da sauri bai maganaba Taringa ajiyar xuciya tana addu,a cikin ranta
Wato nufinsa yazo yayi mata fyade kenan tab aiko daya cuceta domin akullum fatanta da burinta takai budurcinta gidan Auranta duk da bata tsaida kowa ba don bata soyayya da kowa
Mutum daya ta taba so aduniya kuma yarasu tun tana sch yana level 4 tana 2 suka kulla Basu wani dadeba Allah yamai rasuwa ta hanyar hadari dayayi Tun bayan rasuwarsa bata sake yarda ta qulla soyayya da wani da namiji ba
Akwai mataya da dama amma itakam tana da tsoro kada ayaudareta kokuma tafara
nunawa mutum So kuma su rabu
Ayau kam tayiwa Allah godiya da bai bawa mudansir damar keta mata budirciba
Awashe garin da abin yafaru bataga kowa yazo mataba sai sarkin girki shima amakare yazo mata amma taga sauyin abinci bakamar na kullum ba dan yau harda nama yanka biyu
Na safema shayinta harda madara
Sarkin girki yace da ita ” ki kwantar da Hankalinki kikuma zauna cikin shiri yau zan taimaka miki yarinya domin yau gidan zasu futa operation tun dare saisafe zasu dawo don sun dade basu fitaba sai xuwan oga don haka ga mukulli kitabbatar kin futa batare da idon me gadinki ba sbd shi kadai zasu bari
Yabata key ta karba yace da ita ” fatana inkin fita daga gidan nan kada ki sake ki dawo Sannan kibar wannan maganar kada ki dagata tunda Akwai Allah fatana kuma aduk inda kike kixamo meyi min addu,a kinji. Tana hawaye tace dashi ” nagode baba kaimin taimakon da baxan manta ba kuma nima saina taimaka maka wataran
Yafuta ta adana key din sannan tahau cin abincin anitse tana farin cikin yau zata fita daga ckin gidan yau zataga gwaggonta Allah sarki yau damuwa zata yaye
Tahau gage hawaye tana tuna irin son da mahaifiyarta ke mata amma anrabasu harna sati guda. Ckin dare kuwa tayi shirin ta hatta camerarta ta dauko tana cikin jakarta ga wayarta ta mace yau kwana hudu kenan balle taga lokaci
Saida taji tsit babu hayaniya sannan ta tabbatardai sun flta hatta sarkin daki batajin motsinsa donta leka taga baya gurin kan kujerarsa kenan.
Har tayi niyyar ta bude ta fita kuma saita fasa wata dabarar ta fado mata domin ta tuno wata yar rariya asaman silin atoilet gara tagwada basirarta ko Allah zaisa ta bulla ta can
Da sauri tashige toilet din ta kunna yar touchlite din da sarkin girki yabata taga gurin Ta hau wani bokiti na karfe taga tsayinta yakai tayage rariyar taga wanwar silin ya taho ya fado
Space din xata iya fita tagun saidai zata iya jin ciwuka Ta sakala jakarta ahannunta ta matseta gam
Tacicciba tahaura kanta yashige Tayita zura kan tana zurajikinta gashi dai tana jin wani ciwo ajikinta amma batai kasa aguiwaba sannan ga hijab dinta ya yage amma bata tsaya ta kulaba
Saida rabin jikinta yakaiga fita sannan hijab dinjikinta ya xame duk yai kasan toilet din
Bata damuba tunda ba jakarce ta subuce ta komaba ga kanta ba kallabi haka Allah yabata damar fucewa ta silin din saigata a kan soro
Aiko ta hanga kasan taga akwai xurfl bata tsorataba ta rintse idonta da sunan Allah cikin ranta ta dirga Saigata abayan gidan
Dakyar ta mike tanakin ciwo akafarta wataqil ko targade k0 karaya tasan dole akwai daya amma ta daure ta waiga koina taga akwai duhu sai karar tsintsaye akoina sai bishiyu da tsaunuka
Bata tsaya wata wataba takalli gabanta gabas kenan ta runtuma aguje
Tayi gudu na kusan awanni ta fadi rifff
Aiko dai tajita akan dutse saida ta dafe kirjinta danta bugu sosai
Ta kara kankamejakarta ga kanta ba dankwali ga wani axaba da takeji akafarta
Amma batai kasa aguiwaba ta mike dakyar taja kafarta ta kara gaba burinta kawai tayi nisa da gidan Axxaluman can ……