ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 8

ZEENATU YAR JARIDA 
CHAPTER 8
Lauya Ahmad tunda lokacin da yaje yaga zeenat a kauyen nan Hankalinshi be kwanta ba _Bayan Kwana biyu_ Lauya ne zaune a office yana Dan rubuce rubuce Zeenat Ce ta fadomai, Tsaki yayi yake tambayar zuciyarshi ya haka Ajiye Biro din da ke hannunshi yayi yai shuru kamar me nazarin wani abu 
Bangaren Zeenat kuwa hankalinta kwance a kauyen dan ba karamin Sabo tai da su inna wuro ba, ko tana da damuwa tana kokarin boyewa Dan Cinma wani burin nata, tasan yanzu 
tana komawa gida confirm rayuwarta Tazo karshe Dan mudansir ba barinta zaiyi ba 
Lauya Ahmad ne ya mik’e daga kujerar da yake zaune acikin office, wajen window ya nufa yanata leken wajen wani nunfashi yaja sannan yazo ya zauna, Friend dinshi Kabir ya kira akan zaiyi taflya ‘ 
Kabir ne yace” Wai aboki these days meke damunka? Daga jin maganar ka nasan something is wrong Ahmad yace” karka damu kakata ce ta kauyan nan bata da Ify kuma kaga bata da kowa nine gatanta dole na dinga zuwa INA dubata akai akai! Kabir yace” oh yes you’re right sai ka 
dawo nan sukai sallama Ahmad ne yai maza yaje gida ya shiga wanka, ya fito cikin shaddarshi ash colour ta matukar mai kyau! Key ya dauka yazo ya tada matar shi, be tsaya k0 Ina se Kauyen nan, Kamar Kullun yana Isa yara suka fito suna ga mota ga mota, Zeenat dake Shirin fltowa kenan taji ana ga mota, tsaki Tayi tace bari nai zamana Dan yanzu INA fita sai yace Nazo kallon mota, haka ta sami waje ta zauna ta dakko charbi tana 
ja Dan gabanta ne taji yana mugun dukan uku uku
AHMAD Kuwa kai ya kutsa cikin gidan na kakanshi ta wangale baki Dan tasan indai Ahmad yazo ta warke, Aiko nan yaje ya gaisheta take mai ya aiki, Ya kuma kokari da hidir da yake akanta? Yai dariya yace kakale dama miji na gajiya da matarsa? (Wasan kaka dajika) tace”ni nasani? 
Wai yaushe zaka kawo mun Sabuwar amaryan ka? Dumm yadanyi Dan shi ko kashe shi za’ai be ma da budurwa balle har maganar aure ta shiga tsakanin su Kaka tace” yakai shuru Yadan wayince yace” yoo ina dake wace amarya kuma zanyi? dariya Tayi tace” Allah dai ya nunamun ranar dai, Ahmad yace” to amin Tunda kin matsa 
Suna zaune suna hira Ahmad shuru ko Zeenat zata shugo, awa kusan biyu sukai zeenat ko ikon Allah bata shugo ba, Nan Ahmad ya fara tinanin Dama fa be taba ganin taba se ranar kodai ta koma garin sune? Nan yan hanjinshi suka kada 
Yaga ba alamarta yace” kaka bari naje nai Sallah, Aiko dama zeenat na labe ne bataso ya ganta Dan tasan wasu yan birnin akwai rainin hankalin 
Aiko tana ganin ya fita tai Sauri ta shiga gidan dama tana Dan mata shara da wanke wanke, Kafin ya dawo tai maza Ta yi ta koma gida Shi kam k0 da ya tafl sallah Bayan ya flto se bin gidajen yan bukkan yake ko zai hangota shuru be gantaba a sanyaye ya dawo gidan kaka 
Yana shiga ya sama waje ya zauna yaga gidan tas yace” wai harYar fltane kin share gidan? Kaka tace” waneni! Wannan Yar nanne ta shugo tai mun dama Kullun haka takemun shara da wanke wanke wata zubin har girki takemun, 
Tana magana Ahmad ya gane wacce take Nufi, Ikon Allah a zuciyarshi yace” gaskiya yarinyar tanada kirki matuka 
Yace” kaka wai dama a gidan nan take ne kobjikar gidan ne? Kaka tace” eh toh nidai inna wuro tacemun tsintarta sukai a garken shanunsu 
Ahmad wani irin kallo yai ma kaka alamar be gane ba yace” me kikace’ kaka? Nan ta 
maimaita mai Tsintar kanshi yai cikin wani irin yanayi ga kirjinjinshi se bugawa yakeyi, kodai irin matan nan ne masu yawon tsiya Wanda suka gagari Iyayansu 
Da Sauri yace” NO baba tunanin haka bema Sani ba, Kakarshi kam binshi da kallo Tayi tace” meye kuma N0? Yace ba komai Nan dai ya shiga Nazarin gaskiya yana so yasan wacece ita? Meye kuma sanadin zuwanta nan Dan yanzu Gashi kakarshi ta tabbatar mai da ba a garin take ba.. Wani tinanin yayi yace” To Kuma kaka ba Wanda Ya biyota ne manta? Kuma bakiji komai game da ita ba? 
Kaka tace” eh toh gaskiya nidai Banji ba amma kuma nima din ina son Sani gaskiya Dan yarinyar akwai kirki, ldan na shiga gidan anjuma aiko zan tambayo yace” OK yama sunan ta? Kaka tace” naji yara sunace mata ‘Natu‘ amma bansan gaskiyan sunan ta ba in kira maka itace kaji a bakinta? 
Yai Sauri yace” ah ah kaka bari na wuce, inanan zuwa cikin satin nan me zan kawo maki? Tace” kayan dadi na birni yace OK toh nan ya f’Ito still yana ta Dan waige waige ko zan hangota shuru be ganta ba Dan haka ya shiga motarshi ya tada ya nufa hanya Zuciyarashi cike da tinanin Zeenatu Zeenat kuwa na daki se faman kuka takeyi, sallamar kaka sukaji, Inna wuro ne tace” ki shugo gamu anan, tace au toh Tana shiga ganin yanda zeenat ke kuka jikinta ne yai sanyi, samun waje tai ta zauna tace”meke faruwa? Inna wuro tace” nayi nayi ta fadamun Kila ke ta Fada miki, Kaka tace” Natu kiyi shuru mike tare dake yanzu ki kwantar da Hankalinki ko me kike ciki ki Fada mana.. 
Nan zeenat ta saida da kukan da takeyi tace” mahaifiyata na tina, Kaka tace” ta mutune? Zeenat tace” ah ah wasu azzalumai ne suka rabani da ita Nan dai sukace basu gane ba tai musu bayani dakyau Nan zeenat ta gyara zama tun daga tasowarta ta basu labari har izuwa ranarda baba ya tsinceta a garken shanu 
Lalle Kaka tace” Ashe ke babbar Matace, Allah Sarki Allah yai miki Albarka insha Allah, Allah zai kawo mafita ki kwantar da hankalinki, Tun daga ranar suke girmama mata wai Ashe ita ma’aikaciya Ce  ko aiki zatai musu Dakyar suke bari wai ita hajiyace Bangaren Mahaiflyar mudansir kuwa Ta kira wayanshi harta gaji, Tsaki Tayi Saboda tasan halin Dan nata bajin magana yakeyi ba, tasan yanzu haka suna chan suna fashin su, Cillar da wayan tayi tace banza se ya dakko 
mun magana yazo yana zare wa mutane ido.
Ahmad kuwa Zaune yake kan sallaya Dan tun asuba da yai sallah be tashi ba har gari ya fara haske Bayan ya gama addu’oi ya rasa meke mai dadi, Zuciyarshi gaba Daya ya tafl wajen tinanin Zeenat 
Jiyai bazai lya zama a gidan ba kasancewar weekend ne ba aiki,Ya tashi ya mi’ke ya shiga wanka yana fitowa mai ya shafa then yasa kaya ya shirya, Ya feshi jikinshi da turare kallo daya zakai mai kasan big boy ne key dai ya dakko hade da bude frigde ya dakko favourite dinshi wato COKE se ruwan faro yayo mota dashi 
Da sauri yabar harabar gidan, yana kan hanyane Kabir frnd dinshi ya kirashi 
Yace” ina yake Ahmad yace” I’m on my way zanje gidan Kaka Kabir Mamaki yai sosai yace” bakada kirki sometimes ai ka kirani muje Mu gaisheta ko? 
Ahmad yace” karka damu next time sai Mu taho tare Kabiryace” Alright no P sai ka dawo Yana dropping phone din kallonshi yai a mirror din dake motar wani murmushi yayi dan 
shi kadai yasan dalilin da yasa zaije kauyen nan da sassafen na 
Yana taFIya yana addu’a a mind dinshi har ya Isa kauyen, Sallama yayi ya tadda Kaka a tsakar gida tana dama koko, Kaka tace ” Kaine da safen nan yace” eh wallahi 
Nan ya shiga daki yace” Nazo a daidai yau zansha kunun yartsohuwa Nan ta samai a cup yana sha yaji ba sugar 
Daurewa yayi dai yasha Dan karta gane 
Gyara zama yayi yace” kaka INA natu? Jim yayi cos tayi mamakin tambayarshi, Shuru yayi tace” ai Ashe natu abun tausayi ne Yace amm bangane ba Tace bari Na shiga bandaki Nazo na baka tarihinta  Ahmad yace” Okay, Tana flta ya sunkuyar da kanshi tinani barkatai yake ‘tayi a zuciyarshi Yana zaune Jum Kadan Sega Kaka tafito, Nan ta zauna Shima ya gyara zama ta soma da cewa” Yarinyar da ka gani sunanta Zeenatu, mahaifinta ya rasu,yanzu ita kadai ne wajen 
mahaifiyarta, Kasan mutanan yanzu bakowa ne keson Zumunci ba, Haka yan uwanta suka barta mahaifiyarta kadai ke dawainiya da ita, Itace karatunta itace komai take mata Ahmad yace” Allah sarki 
Kaka ta kara da cewa” Zeenat a yanda ta fada mana tasha wahala sosai, Ba irin aikatan da batai ba Dan ta samu ta tsiri da mutuncinta, Ahmad yace” amm kaka bangane aikatau ba, Irin wanke wanke na gida? Kaka ta kara magana cikin tausayi tana shirin kuka tace” Ahmad inma wanke wanke na gida ne ai da sauk’i itafa Zeenat har ga ruwa tayi, Ahmad ne ya zare ido cikin mamaki yana tinanin to itako wani karatu tayi da har tai ga ruwa Dan ta sama Kudi! Duk macen da tai wannan aikin to tabbas talauci yakai talauci adai nan Arewan ‘ Kaka ne ta fashe da kuka Dan bazan Iya karasawa ba Dan tabbas Zeenat abun tausayi ce, Ahmad ne yace” kaka kiyi hakuri in shaa Allah zan temaka mata nan Kaka taji wani irin Dadi a ranta, tace” Kai amma Allah yai maka albarka yace” Amiin 
Kaka ko zan Iya ganinta inaso muyi wata Maganane, kaka tace” 0K Bari naje na kira maka ita..nan ta mik’e ta Shiga gidan su inna wuro, tana shiga ta sami Zeenat na yan wanke wanke, Nan Zeenat ta gaisheta Tace” kizo Wani na kiranki a waje, 
Tunda tai maganar Zeenat ta fahimce ko waye, Dan haka tace” uhm OK nan ta tsame hannunta cikin ruwan wanke wanken da take yi ta nufa Wajen tana shirin shiga gidan ta ganshi jikin Mota tai mamaki Nan tamai sallama, Ahmad ya amsa da cewa Wa’alaikumus Salam barkanki dai, Ya gida Tace” Alhamdulillah 
Kowa yai shuru na yan mintina Ahmad yace” wata alfarma Nazo nema wajen ki Zeenat tace” 0K INA jinka 
Yace” Ina son Ki fahimceni bada wani Abu Nazo ba, Nazone na temaka miki kuma Ina Sonki!!! Tace” temako? Bana bukatar wani temako naka! Ahmad yace”  Zeenat kenan! Kowa ya ganki yason kina bukatar temako, Ni ba ma haka ba Ina sonki, Itadai Zeenat batace komai ba, Dan batasan Ko waye shi ba, batasan aikinshi ba bata San daga Ina yake ba, Itadai kawai abun da ta Sani Jikan Kaka ne!! Yace” look Zeenat Wlhi bazan boye maki ba the first time I set my eyes on you na kamu da sonki, Ta dalilinki nake zuwa nan kauyen akai akai, Dan Allah ki amsa bukata ta Ina Sonki Nan Zeenat tai Wani nazari tace” 0K to zanyi shawara yace” Zuwa yaushe tace” Next week yai smiling yace” Zeenat babbar yarinya har se next week? Tace” Eh yace OK Allah ya 
kaimu tace” Ameen nan dai sukai sallama ita ta koma gida shima kaka na zuwa yace” zai 
tafi gida amma zuwa sati me zuwa zaizo tace” 0K Allah ya kaimu 
Zeenat na zuwa gida kamar An dasa mata son Ahmad, dama itama tun randa ta ganshi, taji kirjinta na buguwa tasan tana Sonshi amma tana karyata kanta, bata yarda tana Sonshi ba se yau da sukai 4eyes gata gashi!! Ranar tunda AHMAD ya tafi zeenat wuni tai tana tinaninshi a ranta tace” dama gobe nace ya dawo 
Ahmad Kuwa saboda Son da yake mata bana wasa ba though besan cikakken tarihinta ba amma Yana Sonta sosai, Dan driving yakeyi amma kowa ya gani se su dinga mai gizo Kamar Zeenat …Ahmad ya kamu sosai 
,,,,,,,,,
Bangaren Mahaifiyar Zeenat Kuwa Ayan kwanakin nan tana yawan mafarkin zeenat, Kulkun zullumin ko za’a aiko mata ace zeenat ta rasu ne, Dan gaskiya tana yawan Tina ta, ga mafarkai…mudai munce soon zataga Zeenat dinta
Bangaren Su Goga Kuwa Mudansir Hankalinshi ya kasa kwanciya Kullun Se yayi kuka saboda Zeenat, Sonta yakeyi kamar ya kashe kanshi, Gashi duk inda suke expecting zasu ganta basu ganta ba, Har Yaranshi ya tura layin su zeenat Ko zasu ganta sunce kwata kwata bata ma unguwar, Dan har tambaya suke a layin da wayau ko ana ganinta, Sedai suce” ai tun wani case da taje ta dakko na Wanda sukafl karfinta akan wani yai ma wata yarinya fyade aka dauketa har hau yau a Mace ko a Raye oho 
Mudansir ne ya Tarasu yace” kunga har yanzu fa I’m not safe, Allah kadai yasan inda Yarinyar nan take, Kuma kusan I’m sure kila tana Raye kuma kunsan she‘s smart duk inda zatai Dan na wulakanta se tayi, nidai abun da nake so daku shine as from today bamu ba zaman gida, Dolene Mu shiga kauyukan da suke kusa damu ko Zamu ganta, Dan nasan bazata koma gida yanzu ba 
Wani a cikinsune Wanda ake kira da Jan wuya yace” Boss nima nayi tinanin haka Dan haka Mu shirya kayan aikinmu, muna ganinta ba wata magana kawai a kasheta, 
Mudansir yace” NO banaso Ku kashemun ita ina sontane, Sena dandana zumar ta, ba ita mekai rahoto ba idan na dandana ta duk inda zata kai se takai dukansu suka wani bushe da dariyar mugunta sukace” Boss baka wasa!!! Nan suka fara shirin Barin gidan akan zasu shiga kauyukan da ke kusa da dajin da Suke!! 
‘Bayan Sati daya’ 
Ahmad ne ya tashi da wuri ya shiga kitchen ya samu ya hada tea then ya soya kwai yana gama ci, ya shiga toilet yai wanka, Ya rasa kayan da zaisa, ya gaji da sa shadda, Dan kullun in zaije shadda yake sawa, Dan haka ya dakko wani fakistan ya saka, Ya kalleshi a mirrow kayan yai mugun mai kyau Smiling yayi yace” wannan kwalliyar nakine Zeenat, key ya dauka yai ma me gadi sallama, Yana cikin tafiyane zeenat ta fadamoi a rai, Yai tinanin me zai sai mata? Kaya ya fadomai a rai Dan bata dashi, Kullun yaje da guda daya yake ganinta dashi Dan haka ya nufi shagunan da ake saida kaya ya siyo mata duguwar Riga guda biyu, se Takalmi da yan kayan makeup da hijab Dan bata dashi tun randa ta gudo NATA ya yayyage na inna wuro take sawa, Yana fitowa daga shagon ya nufl inda ake saida su sweet shima nan yasai mata sanna yai ma su kaka da inna wuro suma siyayya sannan ya nufa hanya 
Zeenat Kuma dama tasan Ahmad zaizo Dan haka ta fara zuwa gidan kaka ta gyara mata sannan ta dawo gidan inna wuro ta gyara tai wanka tana zaman jiranshi 
Zaman datai kamar an rura mata wutan Son Ahmad she’sjust can’t wait to see him, Wani murmushi tayi tana cikin tinaninshi taji horn din motarshi alamun he’s arrived, Smile tayi da Ita kanta bata San na meye ba Yana parking gidan kaka ya shiga ya dakko kayan daya kawo mata Dana inna wuro, tana gani ta wangale baki tana cewa” Dan jika na baka gajiya? Yace” dama miji na gajiya da matarshi ne? Tai dariya tace” Allah dai ya saka da alheri, yace” Amin, nan Suka danyi hira sannan yace” daya nata daya na inna wuro, tace” kai amma mun gode, 
Yadanyi shuru yace” yau ba yarane? Tace” me kakeso? Yadanyi maganar yana Dan jin kunya yace” Zeenat nakeso a kiramun 
Kaka tace” bari naje Allah yasa abun da nake zargi ya tabbata, yai dariya yace” kai kaka kufa tsoffin nan akwai sa ido, Tace” kanka akeji bari naje na kirata nasan a matse kake da Son ganinta, dariya yayi yace” Allah yabarmun kaka tace” kaji dashi 
Tana fita ya biyota a baya, ta shiga gidan shi kuma ya shige mota Tana shiga zeenat tace” Kaka! Kaka tace” kije Ahmad na kiranki, duk kunya ya isheta haka ta dakko hijab din inna wuro ta fito, tana fitowa taga benan ta tsaya a kofar gidan kaka, se zullomin shiga take Ahmad Kuwa na kallonta a cikin mota Da yaga kunyar shiga take gidan ta burgeshi dama akwai shi da son yaga mace me kunya, Horn yai mata da sauri ta maida hankalinta kan motar, Ya flto yace” mata I‘m here dakyar ta 
lya karasawa ta Bude motar ta shiga 
Tana shiga Ta zauna tai shuru, Kallonta yayi yaga ta kara mai kyau, ltama kallonshi ta gefen ido tayi aranta tace” damn he’s looking Good! Kamaryasan abun dake ranta, yace” me kike tinani? Tace” Ya Ahmad ba komai Yai smiling yace” to hope dai kinyi shawarar? Ta sunkuyar da kanta ta rufe fuska yace” my shy shy girl frnd, Ta Kara rufe fuska tace” Dan Allah ka dena yace” to sai kin kalleni zan dena! Ta dakyarta dago kai ta kalleshi, hada idon da sukai dukansu sukaji wani sanyi A ransu Ahmad yace” Alhamdulillah 
Nan suka fara hira Yace” please INA rokon Wata alfarma kuma Dan Allah karki boyemun komai! Tace” OK Insha Allah bazan boye maka ba yace” good that’s my girl Yace” inason Sanin cikakken tarihinkil Tun daga yarintarki har izuwa yanzu da muke maganar Wasu hawaye suka zobo mata tace“ I can’t, Yace” karmu fara haka tun yanzu feel free ki Sanar dani 
Zeenat Tace” to nidai sunana Zeenat!!! 

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE