ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 9
ZEENAT YAR JARIDAH
CHAPTER 9
“Zeenat cikin shesshekin kuka ta fara cewa nidai sunana Zeenatu, An haifeni a garin kano, Ni kadai iyayena suka Haifa, Babana bame arziki bane amma Ba abun da na nema na rasa saboda ni kadai ne komai suna mun Iya bakin gwargwado
Ananan Dan aikin da babana yakeyi a wani company shi driver ne Aka koreshi, Dan haka ya sama Aikin gadi Awani gida, Yana aikin yana samun abun da zamuci Anan Barayi sun shugo sata suka harbeshi, tun daganan rayuwata ta ta dawo abun tausayi dagani se mahaifiyata Muke tashi fadi dan nasamu Naci gaba da karatu nah Cikin Ikon Allah na samu na kammala amma ba irin aikin da ban yiba, Dan na samu na tsira da mutunci na Dan yanzu ba kowa ne ke da zumucin ba, yan uwan babana suna da hali, Amma tun rasuwarshi suka dena ma kulamu saboda bamu dashi, Ahaka dai Nagama karatuna har na sama aiki Bayan na sama aikin ne, lnayi duk da haka bawai na dena shan wahala bane, Ahmad yace” Allah sarki Allah ya gafartawa baba Amiin, sannan ya kara da cewa In bazaki damu ba dalilin zuwan ki wannan kauyan nakeso please! Zeenat ta kalleshi idonta yayi jajur tace” me yasa kakeson Sani? Ahmad ya kwantarda murya yace” na chanchanta na Sani ne shi yasa na tambaya, Zeenat Tai wani tinani tace” hakane To nidai dalilin zuwa na nan kauyen Ina cikin office INA yan rubuce rubuce, Aka kawo case din wani Saurari yai ma wata Yarinya fyade, Shine muka shigar da karar court SBD naji ana fadan dama yaron ya fitina yan unguwar, Cikin Ikon Allah mukazo gidan kuma muka sama kwakkarar shaida, Saboda Akwai wani a gidan ya dauka hoton lokacin da abun ya faru
Ya bani cameram shine fa Shi Wanda yai laifin INA hanyar dawowa gida yasa aka saceni, suka kaini gidan su nasha bakar wuya, ranar basanan na samu na fito da kyar shine dalilin zuwana Nan kauyen
AHMAD ne ya bita da kallon mamaki, Wato zeenat dai Yar jaridah ce, Nan yaji sonta ya kara karuwa da matsayinta a zuciyarshi, A mind dinshi yace” In shaa Allah zan temaka miki, Kallonta yayi yace” kiyi hakuri kowani Dan Adam da kaddarar da yake samu a rayuwarshi ta duniya tace” hakane
Tace kai kuma fa? Nan ya bata labarin komai nashi, Shima he’s the only son da iyayanshi suka Haifa, His parents died shi kadai ne yake rayuwa se kakarshi data rage shine yake zuwa Wajenta, Tace” Wani aiki kakeyi Ahmad yai dariya yace” babu amma soon zan samu tace” Allah ya temaka yace” Amiin _AHMAD ya boye mata shi babban lawyer ne_ Nan dai suka gama hirarsu Zata tafine Ya dakko Kayan daya sai mata ya bata tai mai godiya sosai Dan dama tana bukayar Kayan , Yace” don’t thank me, Smiling tayi yace” Yar jaridah tah tace” kai ko,,,,Tace” Se yaushe zaka koma? Yace” ai kafana kafarki zan kaiki gidanku ne, ta zaro ido tace” No please INA tsoron su Kasheni,
Yace” ba Wanda zai Kasheki, inanan tare dake har abada, Tace“ uhm,
yace” I’m serious look zeenat zamanki Anan bashi zai warware matsalar da kike ciki ba, so kinga Dolene Mu tafi Ko Zaki ta zama Anan ne? Da Sauri ta dago Kai alamar a’ah nima inaso naje gida naga mamana, I’m missing her,Yace” Nasani karki damu zaki ganta Soon Yace” Anan ma kauyen zan kwana inaso nai ma Su Kaka maganar zan maidake gida kuma inason aurenki, rufe fuskar ta tayi ta bude motar tai fucewarta Binta da kallo yayi yace” Soon Zan mallakeki Zeenat na shiga Gidan ta tadda su inna se Yar hirarsu sukeyi, Nan ta shiga ta Nuna musu
abun da Ahmad ya bata, suma sunji dadi sosai, Kaka tace” inna wuro, yaran nan fa soyayya sukeyi, Inna wuro tace” ai tuni na gane, Basu karasa maganar ba Ahmad yai Sallama! Kaka tace” bari naje nasan tafiya zaiyi, Inna wuro tace” to amai godiya
Tana fitowa Gida suka nufa, nan suka zauna tsakar gida yake sanar da Kaka shifa Gida zekai zeenat, Zamanta Anan be dace ba tunda tanada maihaifiya, Kaka tace” nima nayi tinanin Haka
Yace” idan munje gidan Allah yasa abun ya yiwu daAnsa bikinsu Zaizo ya Sanar dasu, Kaka taji dadi sosai dama burinta be wuce taga Ahmad zaiyi aure ba Suna gama maganar Kaka ta shiga gidan Inna Wuro ta Sanar da ita taji Dadi sosai amma bata so ba saboda Suna son Zeenat, ya zasuyi to tunda ba yarsu bace, Hakanan Inna wuro tasama ranta hakuri, mijinta na dawowa ta sanar dashi gobe Zeenat zata koma gida, Dan dadi yaji amma shima Sam beso ba, sbd Son da sukewa zeenat ya wuce wasa, ranar dai kowa beyi kwanan dadi ba har ita zeenat, Dan dai wajen mahafiyarta zata koma da zamanta a kauyen yafl mata
‘WASHE GARI’
Ahmad ya shirya ya sanar da Kaka nan ta shiga ta kirawo Zeenat, Sega baba da Inna wuro da kaka har Zeenat din Kowa kuka basuso rabuwa ba…Ahmad yace” yayi Alkawarin Zai dinga kawota nan Hankalinsu yadan kwanta amma dakyar suka rabu, Seda baba ya lallashe zeenat sannan ta shiga motar suka kama Hanya
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
Su madansir da mugayan Yaranshi Tun jiya already sun shugo kauyen, Dan har wasu suka gani suka Sanar musu da cewa tabbas sun hango wata yarinya kamin su karaso wajenta ta gudu wadanda Zeenat tana shan mangoro ta hangosu kenan
Mudansir Wani smiling yayi yace” kungani I told you Yarinyar nan na tsakarkanin kauyar nan, Wani dariyar mugunta sukai sukace Zeenat ta kusan zama Nama Hmm nikam Nace Zeenat ta muku nisa
Suna tafe cikin Motar, Tun Daga nesa Zeenat ta hango Motar su Mudansir Wani Gham taji kirjinta ya buga meke shirin faruwa da ita yau dinnan, Batace ma Ahmad Komai ba, Hira yake mata tace” Kayi shuru please kaina ciwo yakemun, Yaga sudden change a tare da ita
amma bece mata komai ba Sai Sannu
Kallon Motar Su madansir tayi gasu suna gab da Haduwa, Kuma tasan confirm zasu
ganta, Da sauri tace” Ahmad ka rufe Glass dinnan duka Sanyi nakeji, Nan ya rufe Allah yasa
glass din irin me bakin nan ne sedai na ciki ya hango na waje, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun Take ta fada, Suma Su Mudansir suna cikin motarsu suka hango Motar su Ahmad Cewa sukai Ashe Ma ana Shugowa kauyan Nan, Da gudu motarsu yazo ya wuce fit, Zeenat kamar suna kallon ta tai maza ta dukar dakai, Su Ahmad suka fita su kuma Suka shiga Kauyen Alhamdulillah tace” a mind dinta
Su Mudansir Kuwa kutsa kai suke ta cikin kauyen Duk inda suka ga mutane sai suce wai kanwarsu ce ta bace, Sedai kowa yace gaskiya basu ga wata kalar birni a kauyen ba haka suka wuni akan abu daya
Su Ahmad kuwa Sun danyi taflya bema nisa ba, Ya kalle Zeenat yace” ya kan tace” Alhamdulillah na danji sauk‘i ka Dan saukar da glass din yace” OK
Sun bar kauyen sun hau kan Titi Ahmad yace” bafa gida zan kaiki ba! Wani kallo ta bishi dashi tace” I don’t get you
Smiling yayi yace” case din da kika shiga dolene a boyeki, Dan yanzu kina komawa gida May be sun sa yan duba da sunga Giftawarki zasu lya sanar dasu tace” eh Nima nayi tinanin wannan tace” yanzu to ya za’ai ni dama a kauyen ka barni se lnma kwatancen lnda mahaifiyata take kaje ka dakkota Kuzo Ahmad smiling yayi da shi kadai yasan shI’rin da yake yi, yace” karki damu yanzu gidana zan kaiki ba Wanda zaisan kina ciki! Zare ido tayi yace” NO plz
Yace Zeenat ki kwantar da hankakinki I promise you ba abun da zai sameki
Shuru tayi tun daga lokacin bata kara magana ba se addua takeyi a mind dinta, Tana cewa lalle ni ’YAR JARIDA NAGA RAYUWA‘