ZUCIYA CHAPTER 25 KARSHE

ZUCIYA CHAPTER 25 KARSHE

Bayan Ashraf ya farfado ‘yan sanda suka zagayeshi aka fara mai tambayoyi, hankalinsa akwance yake amsawa nan ya sanar dasu akan sako kanwarsa tamai ya kuma nuna musu sakon. Nan suka bukaci anuna musu kanwar. Ya sanar dasu tana gida. Kb ya jasu suka nufi gidan. ******** A bangaren Kawu kam tunda wadanda yasa aiki suka sanar dashi cewa ‘yan sanda sunzo hankalinsa yai kololuwa gun tashi, ya kasa zaune ya kasa tsaye tsoro da fargaba duk sun dameshi. ‘yan sanda sun shigo nan suka tsaya daga waje suka umarci a kira musu Little. Ba’a dade ba sai gatannan, tsoro duk ya kamata, me zaisa ‘yan sanda su nemeta. Bayan ta iso ogan cikinsu ya kalleta fuskarnan a hade rike da littafi yace “Ke kika turama Yayanki sako akan kina san ganinsa?”+ Cikin mamaki tace ” a’a.” Yace ” ina wayarki?” Hankalinta a kwance ta mikamai, ya duba wayar babu sakon, ya kalleta yace ” ki tuna sosai ina kika ajiye wayarki? Ko kuma wa kika ba?” Tace ” ni ban ajiyeta a ko ina ba, mahaifina dai ya amsh wayar dazu.” Kallan juna sukai, yace ” mahaifin naki yana nan?” Tace ” eh.” Yace ” kira mana shi.” Nan ta tafi bangaren Abba. Yana zaune duk hankalinsa a tashe yaji kwankwasa kofa. Hankali a tashe ya bud’e kofar. Little ta kalleshi tace ” Abba ana nemanka.” Yace ” su waye?” Tace ” yan sanda ne, ni kaina bansan me ke faruwa ba.” Cikin tashin hankali yace ” me kika ce musu?” Tace ” tambaya ta sukai a ina na ajiye wayata ko wa naba shine nace kai naba kawai.” Hankali Kawu ya kara tashi cikin fada ya kalleta yace ” bakida hankaline??me yasa zakice ni kika ba? Ko kema kin hada baki da yayanki ne???” Cikin mamaki tace ” me ya faru?” Tureta yai ya wuce cikin takaici yana tunanin me zaice? In ya gudu kuma tabbas yasan zasuyi zargin wani abu. Fitowa yai ya isa gunsu, tare da mikamusu hannu alamar gaisawa. Bayan sun gaisa wannan officer din na dazu ya kalli Mansir yace ” bincike mukazo yi.” Mansir ya kalleshi, Officer yace ” kaine ka amsh wayar ‘yarka wato Maryam dazu?” Kawu ya danne tsoro yace ” nine, amma menene dan uba ya amshi wayar ‘yarsa?” Officer ya kuramai ido kafin yace ” kaine ka turama Ashraf sako ta wayar?” Kawu yai alamar mamaki yace ” ban gane in turama Ashraf sako ba? Akan me zanyi hakan?” Officer yace ” zaka biyomin office da kai da ‘yarka dan tsananta bincike.” Kawu zai yi magana officer din yace ” in har kana san kar a zargeka kenan, in kuma har da abinda kake b’oyewa to.” Kawu yace ” muje, bari na canza kaya.” Nan ya koma bangarensa, ya canza kaya cikin tsananin firgice, tsoro ne fal a cikin zuciyarsa, nan suka taho da Little suka shiga mota suka bisu a baya. Ashraf kam ya ware sai dai yaki yarda a sallameshi, sun hada baki da likitan akan yace har yanzu bashida lafiya. Su Little zaune a station duk tayi tsuru tsuru, shikansa Officer din yasan ba ita bace dan dai ya zama dole ne ayi tambayar nan da ita. Wayarta ta karba ta kira Habib. Ta dade tana ringing kafin ya daga, tace ” yaya kana ina?” Yace ” ina gida ya akai?” Tace ” dan Allah kazo ina police station tsoro nakeji.” Mikewa yai daga kwanciyar da yake cikin rikecewa yace ” ban gane ba me kikeyi acan?” Alama aka mata akan ta miko wayar hakan yasa tai saurin mai kwatance ta mika musu. Kan kace me sai ga habib ya danno mota a guje da gudu ya shigo cikin station din, sam bai kula da Kawu ba gunta ya nufa da saurinsa ya rike hannayenta yace ” Little are u alright?” Kai ta girgiza mai hawaye suka zubo mata tace ” yaya ka kira ya Ashraf kaji ko yana lafiya naji ance yana asibiti.” Cikin mamaki yace ” asibiti kuma?” Kai ta d’aga mai, zaiyi magana suka hada ido da Kawu, wani irin kalli yamai cikin takaici baisan sanda yace ” ka gama lalata rayuwar wasu yanzu ta ‘yarka kake san lalatawa?” Cikin mamaki Little ta kalleshi, kawu ma kallan mamaki yake mai. Habib ya dauke kai sannan ya matsa gun officer dan jin abinda ke faruwa. Sosai officer yamai bayani, ran Habib ya baci cikin fada yace ” Ai ba sai kunyi wani bincike akan wannan baiwar Allahr ba tayayya ma yarinya karama zatai tunanin yin haka? Sannan yayanta ne fa ubansu d’aya banda yanda suke tsananin san juna, shi kuma waccan mahaifinta ne sai dai im shine.” Little cikin mamaki ta kalli Habib tace ” Yaya ya zaka ce Abba ne? Mai zaisa Abba ya cutar da Yaya?” Habib bai amsa mata ba ya kalli Officer. Kawu kam ya ma rasa mai zaice, aransa yace “like father like son dukansu sai zuciya basu iya controlling din fishinsu ba sam. Sai yamma wanda yaje bincike ya dawo dauke da doguwar takarda, duk abinda ya faru a wayarta ne da wanda aka kira da time din kiran da kuma texts. Kawu kam yana zaune ne kawai. Bayan an kawu ne aka ga tabbas an kira Ashraf bayan kuma texts da akamai. Mamaki ya kama Little duk da Yaya ne yace taba Abbanta wayarta inya tambayeta bata kawo komai a ranta ba. Officer ya kalli Little yace ” me zaki iya cewa gameda sako da kuma waya da akai da layinki?” Abbanta ta kalla sannan ta daure tace ” nidai wlh ban kira Yaya ba.” Officer yace ” mahaifinki fa?” Tace ” shima nasan bai kira yaya ba, saboda me zaisa ya kira yaya a wayata bayan ga wayarsa? In ma ya kira wani to sai dai in Nafisa ya kira.” Officer yai murmushi yace ” hakane abinda kika fada me zaisa ya kira yayanki a wayarki bayan ga wayarsa? Wannan itace kalma ta farko da take bukatar bincike.” Kawu kam gabansa sai faduwa kawai yakeyi. Officer yace ” kuje gida zamuyi bincike zuwa gobe.” Habib ya jata suka shiga motarsa sukai gaba. Kawu ya shiga tashi cikin tashin hankali. ************* Datti kam jiki ba dadi da kanshi yake bi gari gari kauye kauye kauye sai dai ba Nafi ba labarinta ba kuma Dan Litti. Hankalin Datti ya kara tashi nan ya fara zuwa gun malamai akan amai addu’a akan yarsa ta fito. Sai dai haryanzu ba labari, Datti duk ya canza magana ma ba damunsa tai ba, ba dukiya, ba ‘yarsa dama wadancan sun gudu, duk ya zama abin tausayi. Yau kwanan Ashraf uku a asibiti, ‘yan sanda sune suke tsaron d’akinsa sai dai duk abinda ke faruwa Dan Litti na kawo mai rahoto, Little kam tayi kuka sosau ganin yayanta cikin wannan hali, haka ma Anisa, duk yanda taso akan ya barta ta zauna agunsa yaki sai ce mata yai ai Umma ma ba lafiya gareta ba kuma tana bukatar ta. Umma kam neman yanda zata fito da Asim kawai takeyi, sai dai duk inda taje ta nemi taimako akaji wannan uban kudin sai kaga kowa yana dauke kai. Yau da kanta ta shirya tazo gun Ashraf, bayan sun gaisa ta kalleshi tace ” Ashraf in har nai abinda kace zakasa a saki d’ana?”+ Ashraf yace ” zan biya kudin da ake binsa zai kuma yi bailing sa ” Tace ” naji yaushe kakeso in fada?” Murmushi ya mata yace ” zan sanae dake lokacin.” Cikin damuwa tace ” Yaushe to zaka sa a fito da Asim din?” Yace ” karki damu saboda ankusa a cikin satin nan ne insha Allah.” Nan ta fito tai gida. Dady shima yazo, kuka sosai yai agaban Ashraf magana d’aya yake cewa “Ashraf ka yafemin, kalmar da kawai yake fada kenan.” Ashraf ya kalleshi yace ” karka damu Dady ko ma menene na yafema.” Yau ‘yan sanda suka isa company din da Kawu yake, shi kam a wannan lokacin nema yake ya tattara komai na company din ya gudu, bai taba tunanin za’a zagayo kansa da wuri haka ba. Yana zaune a office suka iso, ID dinsu ogan ya fito dashi yace ” u are under arrest.” Kawu ya daure yace ” akan me kenan?” Officer din yace ” mun kama daya daga cikin yaran da ka sa su sa wuta a ginin sannan ya bamu tabbacin kaine ka sasu.” Kawu ya rikice yace ” a ina? Karya yakemin, Ashraf ne ya zugashi.” Baiyi auni ba yaji ansa mai ankwa, nan fa hankalinsa ya tashi ya shiga sambatu yana cewa a kira masa Ruma, shifa bai san me ke faruwa ba. Sudai sukai waje dashi. A cell aka garkama shi, sannan aka umarci Ashraf dayazo. Bayan ya zo ne nan ya basu wayarsa sukaji duk abinda ya faru a lokacin. Hankalin kawu ya tashi, ya dinga musu hauka. Nan aka shigar da kara kotu. Kawu kam anga rayuwa, bai taba tunanin zama a cikin dan dakin nan ba duk tsawan rayuwarsa. Duk yayi baki ya jemi, Ruma kawai yake kira, ya ma rasa inda zaisa kansa, yayi tunanin basu kudi su fitar dashi, sai dai inaa duk inda ya bula abin yaki yiwuwa. Har ranar zama a kotu. *********** Nafi sun fito daga masallaci a garin makka, suna tafe ita da Mumy, Mumy ta kalleta tace ” gashi har mun kusa komawa banga ko waya kunyi da Ashraf ba.” Nafi tai kasa dakai tace ” Nasan zai nemimu in har ya nutsu.” Mumy tai murmushi tace ” Nafisa kina birgeni sosai, kinama mijinki uzuri ba kamar wasu matan na zamani ba.” STORY CONTINUES BELOW Nafi ta kalli takaru yanda taga anbiyosu sun smkwashi kayan da suka baza akan titi da gudu kamar me suna zabga gudu, ta kalli Mumy tace ” nikam Mumy wai haka duka takaru suke zama agarin nan sam ba daraja?” Mumy tai murmushi tace ” ba duka bane suke rayuwa haka, sai dai akasarinsu abinda suke kenan, sai dai addu’a.” Nafi sunzo tsallakawa wata ta taho da kayan saidawarta da gudu ta bangaje ta da karfi wanda sai da ta fadi. Matar ta tsaya tana ba Nafi hakuri, Mumy ta kalleta tace ” haba baiwar Allah kudinga abu da hankali mana.” Nafi ta dago dan yima matar magana, mai idanunta zai gani?” Mahaifiyarta ce sanye da wata kodadiyar doguwar riga da hijab tana rike da kayan saidaiwa a hannunta tanayi tana waigawa, ganin an biyosu yasa ta juya zata tafi. Cikin zafin nama Nafi ta kama hijabin ta. Matarta kalleta tace ” Malama kiyi hakuri nace.” Nafi ta kara kura mata ido, tace ” Inna?” Kallan mamaki matar ta mata tace ” ban gane ba.” Hawaye ne ya fara zubo ma Nafi tace ” Inna nice fa Nafi.” Idanu matar ta zaro cikin tsananin kidima tace ” Nafi?” Mumy kam ta fahimci me ke faruwa ganin an biyosu yasa tace ” mu wuce d’aki kwayi magana.” Nan suka karasa hotel dinsu. Nafi hannunta na cikin na mahaifiyarta kuka kawai takeyi, ita kanta matar kuka take. Nafi ta daure tace ” rayuwar da kikeso kenan ki ka barni a kauye ni kadai?” Inna ta share tata kwallar tace ” Nafi ki yafemin wlh nayi dana sani sosai na barinki.” Nafi cikin kuka tace ” menene abin birgewa anan?sannan ina kanina Mudan?” Uwar ta share kwallarta tace ” Mudan tun daya girma ya bi abokai suka shiga hidimar duniya, har abu yake sha, nayi fadan har na gaji, nayi dana sani har ba iyaka, rannan Aka zo min da labarin hadarin mota da sukai.” Hankalin Nafi ya tashi kwarai tace ” meyasa baki koma ba bayan rasuwarsa?” Tace ” da wani idan zan koma? Bayan kayan Datti dana sata na bar iyayena sannan na barki, na kuma yi sanadiyar mutuwar dana, nikuwa mai zan koma inyi?” Kuka sosai takeyi wanda hankalin Nafi ya kara tashi, nan suka shiga yin kuka sosai. Mumy ta tausaya musu, nan taba mahaifiyar Nafi shawara akan ta dawo nan da zama tunda sun kusa tafiya kuma International ne zata biya kudi au wuce da ita. Godiya sosai Inna ta dinga yi haka ma Nafi. ************* Anyi zama a kotu inda Lawyer din Ashraf ya dinga fito da shaidu na garari ciki kuwa harda Auwal Max, Umma, Dady, Alhaji Uba sannan ga wasikar mahaifinsa ga kuma yaran da aka kama yasa wuta. Ga maganar Kawu wanda Ashraf ya dauka, hankalin Lawyer din Kawu ya tashi ganin ba wata mafita, nan fa kowa ya san abinda kawu yai ma Abbas da d’ansa. Kotu ta umarci dole ne ayima Dady da Mumy hukunci sannan Umma ma. Kawu an yanke mai hukuncin daurin rai da rai, saboda ya kashe Abbas sannan ya nemi kashe Ashraf banda dukiyar maraya dayake amfani da ita. Dady kuma an yanke mai hukuncin shekara 10 saboda shima dashi aka hada baki gunyin kisa, sannan shima yaci kudin maraya. Mumy kuna an yanke mata hukunci kala biyu, ko ta je gidan yari ta zauna na shekara 2 saboda karyar da tai akan gadon maraya duk da kuwa danta ne, ko kuma ta biya kudi million 30. Umma kuma an yanke mata hukuncin biyan kudi dubu 200 saboda kin fadar gaskiya datai. Auwal Max ma an mai hukuncin zaman gidan yari na shekara 8 saboda yayi laifin taimako gunyin kisa. An sanar da Mumy bata kasar sai dai ana sa ran nan da kwana 3 zata dawo. Alkali yace tana dawowa a killaceta. Da wannan zaman kotu ya tashi. Littke tayi kuka kamar ranta zai fita jin wannan sabon al’amari, hankalinta ya tashi, labari kuwa ya bazu a gari ko ina ka zaka abinda ake fada kenan. Su Ferry ma Nabil yazo ya basu labari, hankalin kowa ya tashi na mamakin wannan al’amarin, anyi bikin jibiya waccan satin. Shikam kawu maganarsa daya shifa Ashraf ya cuceshi akuma kiramai Rumarsa. Hmmmm nace su kawu sai ai zaman yari lafiya…..lol😂 Kofar ya bude ba tare da kwankwasawa ko sallama ba, a zaune yaga Ashraf yana aiki yana kuma kurban tea dake gefensa, kana ganinsa kasan hankalinsa a kwance yake, jin yanda aka bude kofar ne yasa ya kalli gun, ganin kawu ne yasa ya sakar mai murmushi tare da dagamai hannu yace ” Hi!” Ran Kawu ya kara b’aci matsowa yai gunsa ya kuramai ido. Ashraf ya kalleshi cikin rainin hankali yace “ya akai? Ko shayin zan hada ma?” Kawu yanasan ya tambayeshi ko shine ya fadama Hisham sai dai yana tsoron karya buloma kansa aiki, yaje haka kawai Ashraf din bai san komai ba ya sanar dashi. Daurewa yai ya juya, har ya kai tsakiyar gun yaji Ashraf yace ” Ba tambaya kazo kayi ba?” Kawu ya tsaya cak tare da juyowa ya kalleshi, Ashraf ya mike tare da matsowa inda kawu yake cikin gadara, ya dan tafa hannayensa biyu a hankali yace ” Ohhhh kana tsoron kar inji?”+ Kawu ya buga mai wani kallo, Ashraf ya dan rike kunne yace ” sry kanin Abba, sai dai ya zamuyi? Da alama Dady fa yasan komai.” Idanu kawu ya zaro cikin rawar murya yace ” kai kai ne ka…..” Dariya Ashraf yasa yace “kawu meye hakan? Kar ka badani mana, ya muryarka zatai rawa daga nan?” Kawu ya daure ya nuna Ashraf da yatsa yace ” Ashraf wannan shine last warning dina akanka, ka shiga hankalinka dani, kada kai tunanin komai yana tafiya yanda kakeso kai tunani kaci riba akaina, wlh kayi min kadan, tsohon ka ma bai isa yaja dani ba bare kai da aka haifeka a gabana.” Hannu Ashraf yasa ya kankame jikinsa yace ” Ahh so Scary!!” Kawu ransa ya kara baci yace ” ina tausaya ma dan wlh…….” Ashraf ya hade hannayensa biyu yace ” plzz na rokeka kar ka tausayamin dan Allah, Dan Allah na rokeka kana kwafsamin in naji zancen tausaya war nan.” Zuciyar kawu ta cika taf da takaici, a zuciye yai hanyar fita, Ashraf yace ” ka tabbatar kanacin abinci mai kyau kafin ka shiga prison dan naji labarin abincin can ba dadi.” A zuciye kawu ya bankade kofa yai waje. Yana fita ya kara kallan kofar cikin takaici yai kwafa yace ” in ni banje ba kai ka ziyarci kabarin ka ai.” Daga ciki kuwa yana fita Ashraf ya furzar da wata iska tare da zama akan kujera Ya kira Uncle Salim. ********** Su Nafi an isa kasa mai tsarki sai dai Nafi kam jiki yaki dadi sam, haka suka shiga d’akin da aka basu a kasar madina ita kam duk ta gama fadawa. Mumy cikin kulawa tace ” Nafi ya kamata muje asibiti nikam naga hararwan nan ta isa ga ba abinci kike ci ba.” Nafi ta dago tace ” Mumy Allah in na huta nasan komai zai tafi.” Kallanta Mumy tai tace “kinga yanda kika rame kuwa?” Nafi tai murmushi tace ” Allah ba komai Mumy.” Shiru Mumy tai jikinta yai sanyi. Nafi kam gata dai a kasa mai tsarki garin da take masifar san gani amma gashi tazo a kwance ba lafiya. ************** Da yamma Ashraf ya koma gida, yana fitowa daga mota yaga Anisa na tahowa, hade rai yai jakarsa ya dauka yai kamar bai ganta ba, Anisa ta karaso da saurinta ta rike rigarsa ta baya. STORY CONTINUES BELOW Dole hakan yasa ya tsaya, juyowa yai ya kalleta yace ” ya akai?” Idanunta ne suka ciciko tace ” yaya.” Kallanta yai yace ” ya akai?” Ta share kwallarta tace ” jikin Umma ba dadi, ga ya Asim har yanzu shiru.” Kallanta yai kawai baice komai ba. Anisa ta rike hannunsa tace ” yaya muje dan Allag ka duba Umma, itama tun dazu take nemanka.” Bai musa ba nan suka nufi bangaren Umma. Tana kwance a d’aki tana ganin Ashraf ta shiga kokarin mekewa zaune. Ashraf ya kalleta sannan ya kalli Anisa yace “dan bamu guri ko?” Anisa ta juya ta fita. Umma ta karasa zama sannan ta kalli Ashraf tace ” Ashraf ya maganar Asim?” Kallanta yai sannan yace ” Asim? Ina zan sani in har ku iyayensa baku sani ba?” Mamaki ne ya kamata tace ” Ashraf na rokeka dan Alla…….” Ka tseta yai yace ” duniyarnan al’amuranta na bani mamaki, har kasan zuciyarki daga ke har dan naki banaji akwai daidai da kwayar zarra da san ‘yan uwantaka da kukemin, banda neman halakani da kukeyi, amma wai ko kunya ni kike cewa in taimaki danki?” Umma jikinta yai sanyi dana sani suka ziyarceta tace ” Ashraf na sani sai dai……” Katseta ya sake yi yace ” ni a wannan lokacin ba abinda zaki fada da zan aminta dashi, abu d’aya nazo fada miki yanzu, in har kinason danki ya fito, sannan kinasan farincikin ‘yarki to inaso nima kimin abu d’aya.” Da sauri tace ” zan maka shi ko menene.” Ya kalleta yace “inaso idan na nemi shedarki akan mutuwar mahaifina ki bada shaida yanda kika sani tsakaninki da Allah.” Cikin tsoro ta kalleshi tace ” Ashraf me kake fada haka?” Yace ” wannan ba damuwa ta bace, iya abinda zance da ke kenan, in kuwa har kikaki bada shaida kamar yadda nace to ki jira abu biyu, na farko danki dolene ya ziyarci gidan yari, na biyu kuwa ki jira takardar mutuwar auren ‘yarki kinsani sarai yanda Anisa take sona, na tabbata bazata taba yafe miki ba inhar taji kece sanadiyar mutuwar aurenta.” Hankalin Umma ne yai mugun tashi,Ashraf yace ” sai ki zab’a da mijin da bai taba sanki ba, bai kuma damu da ke ba da ‘ya’yan da kika haifa kike sansu kamar ranku suma haka, sai ki duba kiga wanene zai fi miki amfani nan gaba.” Yana kaiwa nan yai waje. Hawaye ne ya biyo kuncin Umma lalai yau tana ganin tashin hankali ina zata sa kanta da rayuwarta??????? ************ Dady zaune a d’aki kusa da matarsa cikin kunar rai yake sanar da ita komai, hankalinta yayi tsananin tashi da jin abinda ya faru sai dai abinda basu sani ba, Habib wanda ya taho d’akin, cak ya tsaya jin zancen da sukeyi. Hankalinsa yayi mugun tashi da jin abinda ya faru, muryar mahaifiyarsa yaji tace ” Dadyn Habib yanzu ya zamuyi da hakkin maraya da kuma wanda ya rasu?” Dady cikin mamaki ya kalli matarsa yace ” dama kin sani?” Kallansa tai cikin kulawa tace ” najiku a ranar da abin ya faru da safe kuna zancen, wanda hakan yasa nai saurin kiran Ruma na sanar da ita sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe dan alokacin Abbas ma yana cikin mota.” Jikin Habib ne ya shiga rawa, muryar Dady yaji yana cewa ” Na shiga uku, tunda nake a rayuwata ban taba tunanin zan hada kai in kashe wani ba sai gashi nayi akan mijin kanwata wlh kinji na rantse miki tun bayan faruwar wannan abun duk sanda na kwanta sai nayi mafarkin Abbas yana min murmushi wanda hakab ke kara karyamin zuciya sai dai san abin duniya yasa na kasa yin nadama sai ma tunanin yanda zan kara mallakar wata dukiyar tasa da nakeyi.” Gaba d’aya jikin Habib ne ya shiga rawa, da kyar ya iya saukowa daga saman dakin, d’akinsa ya nufa ya zube a kasa sam kwakwalwarsa ta dauke ya rasa ma tunanin mai zai fara abu d’aya kawai yake mai yawo a zuciya mahaifinsa da mahaifin Little sune suka hadu suka kashe mahaifin Ashraf wannan wani irin mugun al’amari ne????? ************ Kawu ne a d’aki sai safa da marwa yakeyi dole yasan matakin dazai dauka akan wannan yaron, dan kuwa baiga mai rabashi da Ruma ba baiga kuma bai rabashi da dukiyarsa ba. Akwatinsa ya dauko na karkashin gado, sai dai ya zaro takardar wasikar da Abbas yamai yaga tagardar ba komai, hankalinsa ya tashi matuka ya fito daga d’akin ya nufi bangaren Umma. Anisa ce kadai zaune a falo, ya shigo kallansa tai tace “Abba kazo duba Umma ne?” Fuskarsa a hade yace ” ke kika bud’emin akwatin kasan gado na?” Gabanta ne ya fadi cikin i-ina tace ” ba ni bace.” Tsawa ya daka mata yace ” tun bayan shigarki d’akina ba wanda ya kuma shiga bazaki fadamin gaskiya ba.” Shiru tai sai gabanta dake faduwa, jitai yace ” Ashraf kika ba?” D’agowa tai ta kalleshi a tsorace tace ” wlh ba ruwan yaya ni……” Lebensa ya ciza da karfi yai waje a zuciye. Bangaren Ashraf ya nufa wanda rabansa da bangaren har ya manta. Jin kwankwasa kofa yasa Ashraf ya mike dan dama yana zaune ne tun dazu yana neman wayar Nafi tunda yasa layin Mumy shi ya amsa da kansa to na Nafin kuma sam ya ki shiga. Yana bud’e kofa yaga kawu a tsaye. Ashraf cikin mamaki yace ” lafiya?” Hannu kawu ya mikamai yace ” bani wasikar daka dauka a d’akina.” Ashraf ya mai kallan mamaki yace “wasika?” Kawu yace ” wanda kasa Anisa tadaukoma.” Ashraf yace ” ohhh wannan? Nikaina bansan inda yake ba.” Kawu yace ” mene?” Ashraf yace ” kunya kakeji kayi karya ka b’oye akan Mahaifiya yace karna auri ‘yarka?ko kuwa kunyar mai illa dakai kakeyi?” Kawu ya juya bai kara magana ba cikin takaici lalai dole ya dau mataki akan yaron nan dan kuwa da alama ya gama sanin komai.Little tayi kuka kamar ranta zai fita, Anisa ma haka, haka suka rungume juna itada Little a kotu suna kuka, Ashraf daga gefe yana zaune yana kallansu, shikansa abinda yake tausayi da tsoro kenan bayasan Little tasan abinda ke faruwa sai dai ba yanda zaiyi.+ Habib wanda ke zaune kusa dashi idanunsa sun kada sunyi jaa kamar goro, yasa hannu ya buga kafadar Ashraf baice komai ba ya mike zai fita, hannu Ashraf yasa yamaidashi ya zauna sannan a hankali yace ” ina zaka?” Duk yanda Habib yaso ya b’oye hawayensa kasawa yai tun balle daya kalli Little yaga yanda take wani irin kuka, a hankali hawayensa suka ziraro ya kalli Ashraf kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ashraf ya mai murmushi yace “karkace komai Buddy nasan abinda ke ranka, so stop feeling guilty, ba laifinka bane haka fatanmu dai Allah ya yafe mana kurakuranmu.” Rungumeshi Habib yai alokacin hawaye ya fara zubomai sosai, cikin takaici da tsantsan tausayi yace “Ashraf na na…….” Kasa karasawa yai dan kukan yamai karfi, Ashraf ya bubuga bayansa a hankalu yace ” karka damu abokina in har zuciyarka ta karye haka, Little fa?” A hankali Habib ya d’ago ya kalleta sannan ya kalli Ashraf. Murmushi Ashraf ya sakar mai sannan yace ” kalli Dady ka gani shikanshi murmushi yakema.” Nan Habib ya kalli mahaifinsa wanda za’ai waje dasu, da sauri ya dauke kansa yace ” ni ai bansanshi ba.” Ashraf ya hade fuska yace ” ka tashi kaje kamai sallama, ko kamanta mahaifinka ne?” Habib ya kalli Ashraf yace ” Haba Ashraf kisa fa?” Sosai Ashraf ya tamke fuska yace ” ka tashi ko kuwa?” Jiki a sanyaye Habib ya mike ya karasa gun mahaifinsa. Yana matsowa Dady ya kama hannunsa yace ” Habib kayi hakuri.” Habib ya kalleshi cikin takaici yace ” Dady ban taba tunanin haka halayenka b’oyayyu suke ba.” Dady ya daure yace ” Ni kaina bansan me ya sameni ba, sa dai fatana kada kasa wannan abun a ranka harya xamemaka wani abun, sannan duk da abinda ke tsakanina da mahaifin Little bazai hanani yimaka sha’awar auranta ba.” Habib ya dago cikin mamaki yace ” Kanaso kace in auri Little bayan abinda kukama mahaifin Ashraf?ai ba Little ba banaji ma zan iya auran wata a duniya.” Yana kainan yai waje da sauri, Dady ya bishi da kallo hawaye suka zubomai. Nan akai gaba dashi, kawu kam ba wanda yaje gunsa haka aka fita dasu aka sasu a mota Sai gidan yari. Anisa kam tana isa gida ta rufe kanta a d’aki banda kuka ba abinda takeyi, tayaya mahaifinta zai kashe mahaifin Ashraf? Itakam ba wani uzuri da zatama mahaifinta ace d’an uwanka?duk da ba uwarsu d’aya ba ai jini jini ne, itakam bataji zata iya ko da cutar da Little ne bari har akai ga kisa.1 Duk yanda Umma ke buga mata d’aki taki bud’ewa, a yanzu kam ta tabbatar da aurenta da Ashraf ya kare haka kuma tasan rayuwarta tazo karshe ba tantama. Ganin taki bud’ewa yasa Umma ta koma falo ta baza tagumi tana kallan tsakar falon, lalai ba shakka duniya abin tsoro ce, itakam komai da yake faruwa jinsa take kamar a wani mumunan mafarki ne da takeyi. STORY CONTINUES BELOW Little kam zazzabi ne mai zafi ya rufeta wanda sai dayakaita ga kwana a asibiti. ************ Mumy da kanta ta nemi mahaifiyar Nafi akan ta zauna da su sannan su tafi tare, Inna kam ta amince da hakan dan batada wani uzuri sai mamakin yanda ‘yarta ta zama takeyi balle yanda taga Mumy na ji da ita. Nafi ta ba Inna labarin duk abinda ya faru wanda yasata kuka kamar ranta zai fita dan kuwa tasan laifinta ne duk abinda ya faru ba shakka itace sila sai dai tayi farinciki na ganin yarta cikin wadata haka da farinciki. Sun shirya tsaf Mumy ta biya kudin komawa da Inna. Nan suka shirya suka baro kasa mai tsarki suka dawo gida Nigeria. A ranar da zasu dawo Ashraf sam ya kasa zaune ya kasa tsaye dama tun washegari kafin su dawo ya dau Dan Litti suka shiga manya manyan company’s na yin furnitures yasa kaf kayan bangarensa aka canza ma Nafi, sannan ya sai akwatuna saiti ya zubamata kaya kala kala, dinkakune, wadanda ba’a dinka ba, dogayen riguna da English wears. Ya dauko masu gyara aka gyara bangaren sosai kana gani kasan amarya za’a kawo. Kayan Anisa na sawa kuwa aika mata b’angaren mahaifiyarta yai, wanda hakan ba karamin tada musu hankalu yai ba, Anisa kam ko abinci bata iya ci kullum kuka kawai takeyi. Yau tun safe ya shirya dan sunyi waya da wani abokinsa da suka tafi tare ya sanar dashi yanzu zasu taho. Bayan ya kintsa tsaf Dan Litti sai tsokanarsa yakeyi wai wannan zumudi haka? Shi bai taba ganin Ashaf a cikin wannan yanayin ba. Ashraf dariya kawai yakeyi, ganin akwai sauran lokaci sosai yasa kawai ya wuce police station nan yai bailing Asim bai tsaya ya ganshi ba yai gaba.1 Asim yayi baki sosai kamar ba shi ba ya rame sosai, ya fito ya tari adaidaita yai gida kamar wani almajiri. Airport ya wuce suka hau jirgi shida Dan Litti sukai Abuja. Sun saita abin suna isa ba dadewa Jirginsu Nafi ya iso. Tunda Jirgin ya fara alamun sauka Ashraf ya kafe jirgin da ido, har ya sauka sannan a hankali alhazai suka fara fitowa kallan mutane kawai yakeyi yanasan ganin matarsa. Bayan sun sauko ne suka taho ahankali aka musu checking nan ya hango Nafi. Wani irin sanyin dadi ne ya dinga ratsashi ba shakka bai taba tunanin akwai ‘ya macen da zatasa yaji irin wannan yanayin ba amma yanzu ya bada kai bori ya hau. 2 Su Nafi suna fitowa daga gun daga nesa ta fara kalla kalle, nan idanunta suka hango mata abin begenta. Tsaya wa tai cak tana kallansa idanunta suka ciciko da kwalla, shikansa kallanta kawai yakeyi, Mumy ganin haka yasa taja hannun Inna sukai gaba. A hankali suka fara takowa idanunsu nakan juna, Ashraf sam bai kula da wani agabansa ba sai jiyai ya bige wani, ya d’ago ya kalleta dariya ta sakar mai shima yai dariya sannan ya cigaba da takowa, sai da suka zo daf da juna ya kai hannu da niyyar rungumota, ta matsa da sauri tare da cemai “yaya mutane.” Kallan mutanen gun yai sannan yadan sauke fuska alamar takaici, tai murmushin farinciki ya matso kusa da ita yace ” ni fa gaskiya so nake na jiki a kusa dani.” Kallan mamaki tamai tace ” yaushe yayana ya zama haka?ba kunya?”1 Mutanen gun ya kara kalla cikin takaici yace ” muje masaukin da nasa a kama mana sai yamma jirginmu zai tashi.” Nafi ta daga kai nan suka fara tafiya a jere, ganin tana jan yar karamar trolly dinta yasa yakai hannu ya amsa. Mamaki abin ya bata sai dai bata musa ba ta sakar mai tana murmushi. STORY CONTINUES BELOW Can inda yabar Dan Litti ya karasa nan yaga Mumy, da sauri ya mikama Nafi jakarta shifa sam idanunsa sun rufe bai kula da ita ba. Nafi tai saurin matsawa daga gun jakar tai kamar bata ganshi ba. Mumy tai dariya tace ” Ashraf jakar zata fadi.” Kallan Jakar yai ya harari Nafi wacce ta matsa dan yasan da saninta, da sauri ya waske yace ” Mumy lallabani tai akan in rike mata wai ta gaji.” Nafi ta zaro ido tace ” a ina kenan akai hakan?” Harara ya buga mata nan aka kwashe da dariya dukansu harda Inna dan ta gane lalai wannan shine sirikin nata. Ashraf ne ya kalleta ba shakka ba sai an tambaya ba akwai kama sosai tsakaninta na Nafisa. Nan ya gaida Mumy ya gaidata sannan suka shiga taxi suka nufi hotel din da suka kama. D’aki uku yasa aka kama d’aya shida matarsa, daya Dan Litti dayan kuwa Mumy. Sanda zasu kama D’an Litti har tsokanarsa yai yace “amma dai Mumy da Nafi ka kamama d’aya ko.”1 Harara ya bugamai yace ” to wa ya sani?” Ana zuwa Mumy ta kama hannun Inna sukai d’akinsu dan tasan da alama Ashraf ba kara a harkarsa ta yau. Shikam ko a jikinsa ya kalli Nafi yace muje. Tsayawa tai tace ” ina zamu? Yaya tarefa muke da mumy?” Ya hade rai yace ” to ko gabanta zamu in jawoki jikina?” Idanu ta zaro tace ” ba kace yau zamu koma ba?” Yace ” dan yau zamu koma sai aka ce a hanani jin dimin matata?” Zatai magana taji ya ja hannunta ya turata d’akin ya rufe. Ita dariya ma abin ya bata tace ” yaya wai yaushe ka zama haka?sam ka manta da wata kalma a hausa wai kunya.” Rungumeta yai ya saki numfashi yace ” Ahh lalai nayi missing matarnan tawa.” Jikimta tadan janye kadan tace ” nifa yaya a gajiye nake sannan wanka nakesan yi.” Zama yai akan kujera tare da juya kai gefe. Nafi ta dauke kai itama ta dau towel ta cire kayanta ta d’aura sannan ta matso kusa dashi ta manna mai light kiss a lab’ansa tace ” is that okay?” Juyawa tai zatai gaba da sauri yasa hannu ya kamota ta fada kan cinyarsa ya kalleta ido cikin ido yace ” Are u kidding me?” Zatai magana taji bakinta a cikin nasa, wani salo yake mata wanda yasa itama dole ta fara bashi murtani, nan fa ya rabata da towel dinta ya shiga sarrafata ta nayanda yakeso, sai numfashi yake fitarwa itakanta tasan yayi missing dinta…….. Sai da suka gama tukunna ya jawota jikinsa ya rungume yace ” I really Miss u Feenah.” Yanda taji ya fadi sunan sai da tsikar jikinta ta tashi, idanu ta kafeshi dashi, baki yasa ya hura mata iska a idanun yace ” kallanfa?” Bata dauke idanunta ba tace ” yayan dan kara fada.” Ya kalleta yace “mene? I miss u?” Kai ta girgiza tace “a’a d’ayan.” Kallan mamaki ya mata yace ” to mene?” Tace ” d’ayan please.” Yace ” wai Feenah?” Kai ta daga da sauri tace “bantabajin dadin sunan ba a bakin wani ba kamar kai.” Idanu ya kanne yace ” badai so kike kicemin haka kikesan indinga ce miki ba?” Shiru tai sannan tana wasa da gashin kirjinsa tace “mene? Bazan iya ba?” STORY CONTINUES BELOW Yace ” sosai, dan ni Baby nake san cemiki dan haryanzu u are a baby.” Baki ta turo tace ” salan ka faracemin baby daga na haihu ka koma cemin Nafisa?” Cikin mamaki yace ” saboda kin haihu sai kawai na daina cemiki?” Tace ” sosai ma dan nasan abinda na haifa zaka koma cema Baby, haka kawai a fara cemin suna ba wani dadewa a canza.” Kallanta yai yace ” to amma?” Sai kuma yai shiru kafin da sauri ya kalleta yace ” ba wani dadewa? Ya akai kika san haka?” Kanta ta cusa cikin kirjinsa tace ” ya za’ai bazan sani ba bayan lokaci kawai suke jira?” Idanu ya zaro cikin tsananin mamaki ya d’agota shima ya zauna akan gadon, ya rike hannayenta yace ” Baby me kike nufi?” Harararsa tai tace ” sai nayi dala dala? Agunka fa na koyi murda magana.” Yawu ya hadiya sannan ya kalleta cikin wani yanayi yace ” Nafisa bana san………” Kiss tamai a kunci sannan ta kai hannunsa na dama kan cikinta batace mai komai ba. Kallanta kawai yake kamar a mafarku yakejin abun, da sauri ya jawota ya rungume tsam yace “Nafisa yaushe?”1 Tace “sai da mukai tafiya sannan na sani.” Wani irin tsantsar farinciki ne ke ratsashi ya kara kankameta, cikin zolaya tace ” kaga banshirya ba na samu ciki sannan gashi ance a satin nan zafa a kafe mana list na makaranta.” Ashraf ya dagota yace ” makaranta?” Kai ta daga da sauri. Fuska taga ya canza yace ” da babyn nawa za’a dinga zirga zirga?salan karatu yasa a ki kulamin da babyna?” Cikin mamaki ta kalleshi tace ” ban gane ba?” Yace ” ki bari dai sai kin haihu.” Kallan tsantsan mamaki tamai tace “yaya mai kake fada haka?” Dariya taga yasa yace ” me? Kinji haushi? Nima ramawa nai ina murnar zanyi d’a ko ‘ya amma kidinga min zancen wai karatu? Nima shiyasa na rama.” Hannu tasa tadan bigi kirjinsa tace ” yaya harfa ka tsoratani.” Mikewa yai ya daga ta cak yai toilet da ita yana cewa gwara tsoron ya tsaya daga ke karki kaimin shi ciki.” Yana ajiyeta a bathtub ta kalleshi tace ” ka gani ko? Dama nasani ina haihuwa zaka daina sona.” Murmushi yai yace “sorry Feenah dan da alama zan daina kuwa.” Haushi ya kamata ta kafeshi da ido, goshinta ya matso ya sumbata yace ” in banda abin ki ai soyayyar da muke ma juna ita zamu yi karo karo mu ba babyn mu.” Ta kalleshi tace ” hmm gashi nan har ka daina cemin baby, shi yasa ma nace kar a fara.” Shigayai cikin bathtub dib ya sakar musu shaya ya jawota jikinsa ya rungume a hankali yace ” Nafisa bansan irin farincikin da nake ba yau lalai ina cikin farinciki mara misaltuwa, ji nake kamar bayani farinciki a duniyarnan.” Murmushi tai ta kara shigewa jikinsa. Bayan sunyi wanka dakansa ya shafa mata mai sannan ta saka wata doguwar riga baka dake cikin jakarta sannan sukai order na abinci aka kawo musu. Shi dakansa ya dinga bata bayan ta koshi sannan shima yaci, ya koma kusa da inda take zaune ya jawota suka kwanta a kan gado, a hankali tace ” yaya ya kuka kare?” Nan fa ya zayane mata duk abinda ya faru Nafi kam tasha kuka kankameshi tai tsam taba kuka tace ” Yaya.” Murmushi yai yace ” karki damu ai komai ya wuce.” STORY CONTINUES BELOW Cikin kuka tace ” wace irin rayuwa ce wannan ace duk mutanen dake zagaye dakai ba sanka suke ba? Ace mutum ya fifita dukiya akan jininsa” Ya sake murmushi yace ” _zuciyar kenan ai kowa da irin tasa_, wani akan kudi ba abinda bazai iyayi ba.” Tai murmushin takaici sannan tace ” yaya wato da rayuwa ta da taka is so similar inaji tamu kaddarar kenan, bamu da kowa sai junan mu, nima daga mahaifina har mahaifiyata kowa rabuwa yai dani saboda san abin duniya.” Ashraf ya kalleta yace ” ya akai naga kamar mahaifiyarki?” Nan ta bashi labarin abinda ya faru, kai ya girgiza cikin takaici yace ” Kaddarar da Allah ya daura mana kenan, ikon Allah ne yankaini garinku har na hadu dake, duk da rashin mutanen da ke sona tsakani da Allah a kalla ina alfahari da matata Nafisa na sona tsakani da Allah.” Murmushi tai tare da goge hawayenta ta kai fuskarta saitin tasa sannan tasa hannayenta ta kare bangare biyun idanunta a rufe suke sai ta bud’esu a hankali tana kallansa, shima kallanta yakeyi tace ” nima ina alfaharin kasancewa dakai.” Murmushi ya Mata yace ” Nafisa tnx alot 4 not living me.” Wani sansanyan murmushi ta saki sannan ta zare hannayenta ta kwantar da kanta akan kafadarsa tace ” zaka cigaba da sona duk da banda komai?” Murmushi yai sannan yace ” zaki cigaba da sona duk da yanda nake?” Idanu ta lumshe tace ” duk rintsi bazaka wulakantani ba?” Murmushi ya sake yi yace ” duk rintsi bazaki gaji dani ba?” Kallan juna sukai suka saki murmushi Nafi tace ” yaya amma Little dita fa?” Ajiyar zuciya yai yace “sai dai kinje.” Ta jinjina kai tace “yaya nisa fa?” Kallanta yai yace “tana gun tsohuwarta.” Cikin mamaki tace ” amma dai ba wai ka saketa bane ba ko?” Ya hade fuska yace ” kinmanta abinda na fada miki? Banda maganin hana daukar ciki datai dani harda ita fa aka hada baki akaina.” Nafi tai murmushi tace ” amma yaya kaima ai kasan yanda take sanka ina sanin da kai tana masifar sanka shi yasa kai amfani da ita gun kama Ya Asim? Da kuma ganin akwatin Kawu?” Ashraf yai shiru bai ce komai ba, Nafi tai murmushi tace ” kabarta ma da abinda takeji plx karka saketa.” Hannu yasa ya tureta ya mike tsaye yace ” wato ke ko kishi ma bakyayi, a iya sanina murna ya kamata kiyi.” Tasowa tai ta rungumeshi ta baya tace ” ni kuwa nake kishinka shine ma yasa na fadi haka, dan ina kishin komai daya shafeka ciki kuwa harda kishin kar idanunka su rufe ka aikata ba daidai ba.” Kanta ta kwantar a bayansa tace” amma yaya nikam maganar wasiyya ta fa?” Juyowa yai ya kalleta yai dan murmushi sannan ya bata labarin abinda ya faru. Dariya sosai tai tace ” amma dai ai bai kamata Abba yabi maganar wani mutum ba.” Ashraf yai dariya yace ” nima da farko na dauka maganar mutumin nan ce ta sashi barin wasiyyar sai dai yanzu na gane ba haka bane, fahimtar dayai su kawu sune sillar halakarsa shine yasa ya mai wasika akan ya janye maganar aurena da Anisa, shi a tunaninsa kawu zai janye, to fatan Abba shine wasiyyar ta isa gun matar da zan aura.” Nafi ta jinjina kai alamar gamsuwa sannan tace ” amma yaya kasan akwai mutane masu baiwar haka kuwa? Duk da bance wannan gaskiya ya fada ba sai dai Allah yana hallintar mutane da baiwa kala kala, wasu in basusan ya zasuyi amfani da baiwar tasu ba sai kaga sun koma harkar duba da bokanci da tsubbu.” STORY CONTINUES BELOW Ashraf yace ” haka ne, amma bakya ganin ya kamata mu maida Inna gun mijinta ta nemi yafiya?” Nafi tai shiru, Ashraf ya dagota yace ” karki damu ba abinda zai faru, iya kaci inyace baisan aurensa da Inna sai mu dawo da ita nan gida.” Kallansa Nafi tai sai dai batace komai ba, tana matukar tsoron Datti gani take bazai taba yafema Inna ba tunda ta satar mai saniya. Da yamma sun taso sun iso garin kano, ya kuma sanar ma Mumy hukuncinta, a da taso ta zabi zaman gidan yarin dan gani take bata kyautama Ashraf ba a rayuwa, sai dai shi da kansa yace gidajenta za’a saida a bada rabi shi zai bada rabi a biya kudin, sai dai sam tace bata yarda ba, sai dai a saida duk kadararta a bada bazata taba yarda ya biya kudin laifin data aikatamai ba. Sun isa gida inda Nafi ta shiga gun Little da sauri, a kwance ta ganta a d’aki ita kadai su Afra suna falo suna kallo, Nafi da sauri ta karasa gunta ta rungumeta tsam a jikinta a tare suka saki wani kuka, kuka suke sosai kafin daga baya Nafi ta shiga ba Little hakuri. Little tace ” Nafisa da wani ido zan kalli Yaya? Da wani ido zan kallu Ya Habibda mumy?” Nafi ya rike hannayenta tace ” Little bakiyi komai ba fa, baki san me ya faru ba, ta yayya zaki daura wa kanki laifin da baki aikata ba?” Little hawaye na zubo mata tace ” ta ya zakice ban aikata ba bayan mutuwar Abban Yaya itace sanadiyyar haihuwata?” Kai Nafi ta girgiza mata tace ” karkiyi sabo Little kaddarace ta riga ta faru fatanmu Allah yasa mu gyara.” Da haka Nafi tai ta ba little baki harta kwantar da hankalinta, nan ta jata bangaren Mumy. Little na zuwa ta fada kanta tana kuka. Asim kam tunda ya isa ya samu abinci agun Umma ya hau ci ba kakkautawa, Umma kam tausayin dan nata takeji ganin yanda yake tutura abinci kamar zan cinye har kwanon, sai da ya koshi sosai ya tam sannan tace yaje yai wanka. Yana fita ta saki kukan takaici itakam ina zata sa kanta, basuda komai sai gun zaman nan yanzu in har Ashraf yace su bar gidan nan fa shikenan tasu ta kare. ********** Da daddare Ashraf yana zaune ya bugama Nafi waya, ta dauka tare da mikewa daga gun su Inna da Mumy da take, cikin rada tace ” yaya ya akai?” Yace ” wai bazaki taho gun mijinki ba?” Tace ” gun mijina?” Yace ” da kina so kicemin a gun Little zaki kwana?” Tace ” naga da acan nake kwana?” Yace “da kenan yanzu ai kayanki zaki tattaro ki dawo bangaren mijinki.”1 Murmushi tai tace ” ni dai kunya nake ji gaskiya.” Yace ” kunya ko? To ni bari nazo na daukeki.” Yana kaiwa nan ya kashe wayar. Dariya tai tace ” in zaka iya kenan ba.” Ta koma suka cigaba da hira, batai minti 10 da zama ba suka ji sallamar Ashraf. Little tai kasa da kanta, shigowa yai ya zauna kusa da Little tare da dagota yace ” kanwata ko neman Habib kike ne?” Dagowa tai da sauri tace “ni kuma?” Murmushi yai yace ” to ni kike nema?” Kasa tai da kanta tana murmushi, Ashraf ya harari Nafi yace ” malama tashi ko?” Nafi ta zaro ido ta kalli Mumy da Inna cikin tsananin mamaki, wai keke damun Ashraf? Abinda tafada kenan a ranta. Mumy tai murmushi tace ” Ashraf bafa inda zataje.” STORY CONTINUES BELOW Kallan Mumy yai cikin mamaki. Mumy tace ” Nafisa tana bukatar wani shagalin biki dan a kara shaida auranku, mutane dayawa basu san matarka bace, ita kanta kunya ya hanata sanar da kawayenta.” Cikin tsantsan mamaki ya kalli Mumy yace ” to ai….” Mumy ta hade rai tace ” mun yanke hukunci da mahaifiyarta nan da sati d’aya za’ai ko yar walima ce sannan ta tare.” Haushi ya kama Ashraf yace “har sati?” ya fada yana kallan Nafi. B’oyewa tai bayan Little tamai gwalo, haushi ya kamashi ya mike yace ” hmm amma da ina tunanin gobe zamuje kauye tare da Inna dan ta nemi yafiyar Datti.” Mumy tace ” hakan yayi kyau, inyaso sai Little ta rakaku.” Yace ” amma mu biyu ma…..” Mumy ta katseshi zan ma Habib magana shima kila zaiso yaje kauyen kaga sai kuje da armashin ku sai ku dauki babbar mota, gashi Afra nan ma xasuyi rakiya.” Haushi ya kama Ashraf yai waje cikin takaici, bangarensa ya nufa ya kalli yanda ya tsara musu bangarensu yace ” har wani sati? Sannan goben ma baza’a barmu mu biyu ba???” ********** Washegari haka suka shirya suka dauki mota babba, Little, Inna,Nafi, Afra da Amra, Dan Litti Habib da Ashraf suka nufi kauyen su Nafi. A hanya Ashraf yai musu siyayya sosai duk da Habib ne ya sashi dan shi gani yake bazai iya kaima Datti komai ba, haka suka isa kauyen A kauyen su Dan Litti suka fara sauka aka saukeshi mutane sai kallansu sukeyi, sannan suka wuce rigar Datti. Sun samu ba kowa a gidan gidan ma a rufe yake nan fa hankalinsu ya tashi sai ga wani yazo wucewa nan ya sanar dasu ai yana gidansu. Nan suka shiga mota suka gangara, Datti na kwance a karkashin bishiya shi kadai abin duniya duk ya isheshi yana ganin mota ma ta tsaya amma ko alamar mikewa baiyi ba, mutane suka zagaye motar, nan fa su Nafi suka fito ba wanda ya ganesu gwarama Inna yayan Datti na ganinta ya ganeta. Sai da aka musu iso suka zauna a ciki sannan yayan datti ya aika a kirashi. Ba’a dade ba sai gashi nan, nan yaga inna sai dai maimakon masifa gani sukai ya saki kuka yana ce mata ” innar Nafi mun shiga uku na saida ma masu yankan kai Nafi.” Kuka yake sosai wanda saida yasa Nafi ma kuka, Ashrad ya kalleshi yace ” baka gane ni ba baffa?” Kallansa yai yanasan gano fuskar sai dai ya kasa, Ashraf yai murmushi yace ” mijin Nafi ne.” Nan fa aka dau salati, nan Ashraf ya zayyane musu komai, Inna ta nemi yafiya shima datti ya nemi yafiyar ta data Nafi. Sun dade kafin daga bisani suce zasu tafi,Datti yace ai auransa nanan da matarsa, jin matsalar data sameshi yasa Ashraf ya ciro kudi masu yawa ya bashi yace ya sai wasu dabobbin, sannan suyi shawara in sunfisan zaman nan to in kuma sunfisan birni sai ya turo a daukosu. Nan ya musu sha tara ta arziki suka fito, kowa sai sha’awar Nafi yake, nan Hanne ma dataji labari tazo taganta alokacib itakuma ‘ya’yantama 2. Su kadai suka taho dan dan litti yace sai yayi kwana biyu, zai dai dawo lokacin bikinsu da Nafi. *********** Duk yanda Ashraf yaso su kebe da Nafi abin yaci tura har ranar zagayowar sati, Nafi tayi rabon Iv gida ya cika sai dai Anisa da Umma sukam suna zaune a bangarensu ko fitowa ba sayi. STORY CONTINUES BELOW Nafi da kanta ta sai kusu kayan da zasu sa a cikin kudin dake katin da ASHRAF ya bata. Ta aikama Anisa da umma. Hall aka kama, ga innarta ta zo itada mahaifinta da hanne, dama ta shirya musu dinkuna. Su ferry da Little amara kirjin biki kenan sai hidima sukeyi, duk inda Little ta wuce Habib binta kawai yake da ido, sosai guri ya cika Abdulkadir wanda ke kula da dan siyasan nan shima yazo dan yanzu ya zama babban mutum Ashraf ya bude mai shago babba anan titin Zoo road inda yake saida kayan masarufai yanzo ko motar da yake hawa ka kalla sai ka kuma kallo, tunda ya iso shikuma ya kyalla ido yaga ferry hankalinsa ya tashi, sosai ta birgeshi. Anyi shagalin biki sosai mutane kowa ya tayasu murna, sai dai Nafi tunda ta zauna Ashraf ya hanata tashi, ko kiranta Dj yai sai yace a mata uzuri haushi duk ya isheta datai magana sai yace wai bazai yarda a wahalar mai da baby ba. Haka aka gama taro aka watse, Little da Ferry sune suka kai Amarya Nafi bangarenta inda Little tai ta mamakin sanda aka canza komai na bangaren. Duk yanda Habib yaso suyi magana da Little abin ya faskara, haka suka kai Nafi bayan sun ajiyeta Little ta juya zata tafi Habib yai saurin binta suna fita yace ” Little haka zamu dawamma ko magana babu?” Kallansa tai tace ” yaya da wani idon kakeso na kalleka bayan mahaifina shine sillar lalacewar rayuwar Dady?” Habib ya kalleta yace ” amma wannan ba ya wuce ba?” Kai ta girgiza mai tai gaba zata wuce, hannu yasa ya rikota da sauri ta tsaya cak gabanta na faduwa yace ” Little bantaba tunanin ina sanku haka ba sai bayan faruwar wannan abun.” Juyowa tai ta kalleshi tace ” nifa?” tafada hawaye na gangaro mata, tace ” nifa da nake sanka tun ina yarinya?” Wani irin kallo suka shiga yi ma juna……. Ferry kam da Abdul bansan ya akai ba can na gansu tare suna hira mamaki ya kamani nace hmmm lalai…… Shikam Ango ana watsewa ya yaye mayafin dake rufe a fuskar Nafi yace ” su Amarya am gama gudun?” Tai kasa dakai wai kunya, dariya yai yace ” au abin Amaren gaske zakimin?”1 Ta turo baki tace ” ba amaryar bace?” Yai dariya yace lalai su Amarya bari in kaiki ciki in gwada ingani ko Amarya ce da gaske.” Zatai magana taji ya sureta………. Washegari da safe taga bangarenta sosai taji dadi sai dai tace ya dawo da Anisa, ya aminta da shawarar sai dai yace sai dai a gyara mata wani bangaren dake cikin gidan dan kuwa inhar ta zauna dasu gaskiya itace a wahale dan kuwa bazai iya adalci ba zai kuma sanar da ita hakan. Da zai fita zuwa gun Anisa ne ya zaro takarda ya mika mata yace ” uwar gida ga wasiyyar ki.” Yai gaba Kan kujera ta kwanta a hankali ta bude takardae. _Zuwa ga sirikata_ _Bansan me zance miki ba, ban kuma san dalilina na yin wasikarnan ba sai dai nasan abu d’aya shine ke rinjayata, dan Allah ina rokonki da kularmin da wannan yaron nawa, amanace na baki kisoshi saboda Allah bawai dan dukiyarsa ba, ki nunamai kulawar dazaisa yamanta shi marayane, wannan ita kadaice rokon da zan iya miki a rayuwa._ _Ga nawa gudun mawar na auranku, ba yawa sai dai wannan nine nake daburin baki ba wanda yasan da zamansu sai ni sai ke sai Lawyer na Salim, nagode kwarai._ Murmushi tai sannan tace ” Abba zan kula da yaya sosai, zan sadaukar da komai nawa a kansa.” Nanta zaro takardar dake bayan wasiyyar, takardace ta nuna mallakin wani gida da kuma shago, mamaki ya kamata, da alama kuma gida ne babba sosai hakama shagon. ************** Bayan shekara d’aya, sauri take sosai tana hada breakfast Ashraf da babynta mace wato Zainab suna zaune akan dinning ya daurata a cinyarsa yana bubuga mata kan dinning da cokali wai tai sauri su yunwa sukeji. Nafi ta taho da sauri rike da plate ta ajiye a gabansa ta sa hannu ta ja kunnensa da karfi yadanyi kara kadan yace ” muguntar ta motsa kenan?” Harararsa tai ta rike kugu tace “Yaya daga nan ina zaka?” Yace ” zama zanyi in huta kadan kafin na fita aiki.” Ta hade fuska tace ” dama shigaban Company an bashi damar kin zuwa da wuri?” Yace ” an fara akaina?” ya fada yana murmushi tace ” ni kuma fa daga nan ina zani?” Yace ” makaranta zaki.” Ya fada tare da sumbatare Zee, Nafi tai kwafa tace ” kai da zaka zauna a gida, mu da zamu fita shine kake min kidan yunwa?” Ya tabe baku yace ” to ya zamuyi Zee ma yunwa takeji.” Ta kalli agoggo ganin lokaci yayi yasa tai daki da gudu ta dauko mayafinta da jakarta ta zo kusa dashi tamai kiss a kunci sannan tama Zee tace “yaya inkun gama wasab naku ka kaita gun Ya nisa.” Ya mata salute yace ” yes ma.” Dariya tai sannan tai waje. Motarta ta fada sannan ta kata key tai gaba. Little ansa ranar auransu da Habib. Dan Litti kuma Ashraf ya turashi kasar Spain dan yin karatu.8 *ALHAMDULILA* _Nan ne na kawo karshen littafina na zuciya kowa da irin tasa, darusan dake ciki Allah ya bamu ikon fani dasu, kura kuran da ke ciki Allah ka yafe mana, Ameen suma Ameen.

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE