ZUCIYAR MACE PART 1 BY MAMAN NUR

M&b foodies school

    Yauma Kamar kullum fitowa sukayi daga makarantar koyar  girki watoh m&B foodies,babban makaranta ce sosai ta koyar da girke girke da a ko wani lokaci busy take dalibai na Kai komo 

      Su uku na hango suna fitowa daga aji sosai Suka ja  hankalina ita kadai ce sanye da hijab sauran kawayenta Kuma kanana gyale itako har socks da Safar hanun kasancewar ana yanayi na sanyi Kuma Bata son sanyi Dan tana da chronic neumonia sanyi ba karamin illah yake Mata ba shiyasa ko Yaya Bata Wasa da sanyi,Rabi’a ce ke zuba surutu tana basu labarin admission da aka samo mata a jami’a itadai Bata ce komai ba sai Rukky dake tanka ta a Haka suka Isa massalaci cikin makaranta sukayi alwala b’angaren Mata Suka shiga Suka gabatar da sallah zuhr itace ta Fara fitowa daga massalaci tana maida safar hanunta ta karasa gindin wata bishiya ta zauna tare da ajiye bag dinta ta bude Zuma  ta fito dashi a gora me kyau Dan Bata rabo dashi saboda tarin dake addabanta a season din Nan lalurarta nasa tana yawan tari ga kaki da take fitawar dan ba karamin wahala take ba most expecially da daddare in har aka shiga period din Nan in dare  yayi toh fah gaskiya bata bacci Kuma komai nauyin baccin mutan gidan in ta Fara tari sai sun farka zani take ajiyewa kusa da ita  Kan gari ya waye ta cika shi da kaki in short she is seriously sick 

     Shan zumar tayi ta rufe gorar ta maida jaka hango wata Yar ajinsu tayi a nisa da ita zaune da saurayinta Jacob Wanda duk Wanda ke makaranta ya kwana da sanin soyyayarsu a makaranta shima dalibi ne girki yake kowa Yana son Zama chef a fad’a mutane in sunyi sure zasu bude restaurant

      Lumshe Ido tayi zuciyarta na rawa domin duk lokacin da ta gan masoya sai ta tuna da marigayi tsohon saurayinta Wanda ya sota tsakani da Allah,Amma ranan d’aura aure sai aka wayi gari bashi  Rai yayi halinsa sakanakon ciwon ciki da yayi cikin dare,mutuwar Ahmed ya girgiza duniyarta domin soyyaya ce me karfi tsakaninsu shekaru uku kenan Amma ta kasa manceshi mutuwar Ahmed ya so zarar da ita Wanda ta Kai ta kawo Saida aka nimi taimakon psychology shekara biyu ana fama da ita kafin da k’yar da addo’oin akayi reviving dinta shi Kuma likitanta ya nuna muradinsa na aurenta tun Bata kula Dr Umar har ta Fara tausayinsa ta amince dashi saboda mutum ne me son ganin farin cikinta bashi da wata buri daya wuce ya ganta cikin farin ciki yanzu Haka bikinsu saura sati uku saidai duk inda ta so ta mance Ahmed ta kasa Yana kasar zuciyarta 

       Ajiyar zuciya ta sauke ta d’auki wayarta dake vibrating Dr ne 

     Da murmushi a fuskarta ta d’aga wayar Dr Umar ne 

Cikin fara’a tace”my doctor ya kake?”

       Yace”cool Ina zaune ne nace Bari in Kira hearty ta inji ya kike Yan Mata”

  Sosai tayi dariya tana Jin dadin kulawar da Dr ke Bata ko kad’an bayq  kyamatarta and Yana Bata dalilin cigaba da rayuwa dukda yasan halin data tsinci kanta a ciki a baya shi ba abinda ya dameshi farin cikinta shine burinsa….ita tasan Bata sonsa kamar inda ta so Ahmed but zata iya sadaukar da komai Dan ya samu farinciki tana son farantan Masa sosai 

         Sosai sukayi waya har su Rabi’a Suka fito sallah Suka Dora hiran makaranta daga inda Suka tsaya saidai Bata sa musu baki kasancewar dukkanin su secondaries ne Kuma Bata Jin tana da gatan komawa makaranta 

       Kira ne ya shigo wayar Rabi’a ta d’aga ko me aka ce oho ta saki wani ihun murna tace”are you serious bamu minti biyar yanzu Zan Faso da friends dina badai ki tabbatar zamu kwashi awuuf ba”

    Yanke wayar  ta Kama hanun Amatu tace”keee ku tashi muje  Mall sadiya ce ta kirani Wai ta samu wani gara so tana son muyi me Reza mu yanke shi yanzu suna b’angaren cin abinci”

   Ta Riga tasan amatu ce matsalanta shiyasa Taki Bata damar yin magana tayi ta janta Haka badan taso ba ta bita Rai ba Dadi Dan tana gudun shiga jama”a saboda tarinta mesa a kyamaceta 

       Keke napep ne ya kaisu Mall suka tafi b’garen cin abinci,hango  sadiyar ko sukayi da wani sugar daddy that is old enough to be her dad karasawa sukayi ai ba kunya tsohon ya sake Suka Shiga Hira Rabia na zuba me surutu bayan sunyi ordering abinci masu tsada 

Tari ne ya tasowa Amatu a dalilin sanyi AC daya dime wajen Bata son tayi a cikin mutane kasancewar abinci ake ci ga tarin na cinta 

Mikewa tayi Rabi’a nayi Mata magana Bata amsa ba hakan yasa Rabia gane abinda ke  damunta sai taji tausayinta ya mugun kamata Saidai Bata nuna ta gano meke damunta ba ta d’au cokali tasa a jellouf din da aka kawo Mata me kyau Wanda da gani zatayi Dadi ga manyan nama 

   Amatu ko da wuri ta bar eatry din tayi packing space da yike ta Hana tarin zuwa a lokacin data kamata sai abin tayi worst Tana zuwa ta Fara sakinsa duk ta galabaita idanun Nan sunyi  jawur saboda wuya 

  Tana cikin tari amai me karfi ta taso Mata duk inda taso Hana kanta Yi kasawa  tayi ko ganin wuri batayi da kyau Daman idanuwan Suma Basu da karfi sai an had’ata da glass da take Kara Mata karfi ita dai Haka Allah yayi ta da lalurori 

        Sakin amai tayi a galabaice ba tare da ta lura da Wanda ya bude wata farar motar ba Wanda da dukkan alamun sun dade a ciki amanta ne ya fito dashi ganin duk ta b’ata me mota da kazanta 

Rai b’ace da zuciya irin ta sojoji ya fito ya fisgota ya bude Baki zaiyi magana kawai ta

Kaiwa yaji saukar amai me dimi a jikinsa me hadiza zatayi in ba dariya ba ta sauke cameran da tayi fixing a sama motar tana video da shi watoh Vlog ta fito tana kyakyata dariya me ban haushi 

   Itako amatu rudewa tayi kokari take tayi magana ta kasa da hanun take me alama da yayi hakuri Amma ya tsaya kyam ko motsi ya kasayi da alamu mutuwar tsaye yayi ga karni amai dake addabansa 

Muryar hadiza ce ta dawo dashi hayyancinsa domin kyakyalewa tayi da mugun dariya tana tafa hanun ga camera data seta kanshi cikin yanga tace”viewers as you can see mun iso mantawale mall nida hubby dina,don’t mind me nida fiance dina,sai Kuma tayi murmushi tace”wait ai zanma iya cewa hubby sati uku fah ya rage tsakanin mu,anyway nida soulmate Dina toh gamu dai muna isowa muka had’u da wata sabuwar kamu that she dont look ok to me to dai Bari in muku gulma in takaice muku a jikin soulmate tayi amai ga daishi Nan ku Sha kallo  kunsan Ni ba ruwa na Ina blogging komai na rayuwa and this is not exceptional ga dai mu Nan munyi cirko cirko kamar marasa lafiya Ina jiran hukuncin soja domin nasan bazai Mata da sauki ba wanan shiru ba na lafiya bane soja ya kumbura fahhhh,I mean in na ganin class din matawalle mall but yau na Raina musu wayau I mean how can they allow such people anan,soja fah baya son kazanta Ni kadai ke iyawa saftarsa shiyasa bani da darrr akan kishiya

        D’auke amatu da yayi da Mari ne yasa Hadiza Kai hanun Baki sai Kuma ta kyalkyale da dariya tace”I told you abin fah zaiyi zafi fahhh gashi ta Fara amsar hukunci “

         Da kyar amatu da tayi kasa ta taso ko gani batayi ta karasa tace”please yallabai kayi hakuri Ina da lalu…..”

Bata karasa ba ya sake d’auketa da Mari zatayi kasa  Rabi’a data biyo ta Jin shiru Bata dawo ba  ta rikota tana kallon soja da jikinsa ke tsuma 

Cikin kuka Kuma a bircike amatullah ta mugun tsorata dan kallo daya zaka Mata kasan soja ne  sanye yake da farar Riga me logon su ta sojoji sai Kuma wando sojoji 

     Kuka ta fashe dashi tace”ki bashi hakuri wallahi ban lura dashi ba shiyasa”

    Hadiza ko dadin abin take ji sai dariya take saki 

  Cikin b’acin Rai Rabia tace”me tayi maka Kai baka San lalura ban…..”

Bata karasa ba ya daka mata tsawa yace my friend will you keep quiet and kneel down over there kafin ma ya Karasa magana Amatu tayi kasa tana sakin kuka 

     Rabi’a ko kin dukawa tayi ta Kai fuskarta gefe tana kunkunin 

Hadiza ta ajiye camera saman mota inda zai dau komai tace”ikon Allah yariyar Nan da alamu Bata San soulmate be son rainin bane shiyasa yau dai akwai show itako mahaukaciyar akwai biyayya Ashe mahaukatai sun San soja”sai ta kyalkyale da dariya Kuma tace”stay tune masoya “

        Sosai amatu ke kuka tana bashi hakuri shiko Rabi’a ta mugun b’ata me Rai hakan yasa ya Fara cire belt  zata gudu yayi hanzarin cafkota ya Fara zuba Mata belt  har amatun 

Ihunta ya jawo hankalin mutane na ciki da na  waje ba karamin Zana yayi musu ba Rabi’a ta ci kuka ta gode Allah saidai bakin be mutu ba 

        Hadiza tace”har yanzu baka hukuntasu ba shiyasa wanan fitsararriyar take da bakin Yi Mana rashin kunya ka ci ubanta “

      Cikin kuka Rabi’a tace”bar ganin kina lokaci yanzu lokacin ki ne Amma ki sani lokacina zai Zo sai na hanaku Jin dadin sai na nuna Miki ke ba komai bane a gunsa badai dashi kike takama ba?toh dukda ban San menene tsakaninku ba na d’au alwashin ganin bayanki wata Rana sai ya tozartaki inda yayi Mana har kike d’auk…..”

Mari ya Kai Mata tuni bakinta ya fashe amatu ta ja guiwa zuwa gabansa ta Kama kafarsa tace*kayi hakuri yallabai wallahi ban Lura da Kai bane ka yafe min please ka daina dukanta”

      Ko kad’an mutane Dake tsaye wajen Basu ji dadin abinda ya faru ba dayawa na jinjina zalincin shi Dan kawai shi soja ne

        Kama hijabinta yayi ya damkota cike da mugunta idanuwanta sun firfito ta kasa magana Rabi’a da sadiya da suka fito suka fashe da kuka 

Cire hijabinta yayi Wanda hakan yasa taji duk duniya ba a tab’a Mata irin wanan tozarci ba ta fashe da kuka damka Mata yayi a hanunta Dan ji yayi be tab’a tsanar wata irinta ya tsani kazanta da kazamai 

Cikin tsawa yace”bar kallona  ki goge min mota da hijabi minti goma na baki ki goge kazantar da Kika zuba min har jikina ‘

       Kallon Rabi’a tayi cikin wani yanayi me wuyan rubutawa Rabi’a ta fahimci girman wanan tozarcin domin amatu macece da Bata iya sayawa ba hijab Koda a gidane 

      Gyara wuyar rigarta tayi Rabia ta Mika Mata gyalle duk abinda ke faruwa hadiza na d’auka Dan wanan dabi’arta ce na komai ya faru a rayuwarta sai ta d’aura a yanar gizo 

      Na jikin motarsa ta Fara gogewa da hijabinta tana kuka bayan ta Gqama na mota ta goge na takalminsa ta juya fuskar hijabi ta gefen me kyau ta kalli fuskarshi  kallonta yake Wanda ya rasa dalili thou zamu iya cewa suman daya kwanta a goqshinta dan har wani saje take dashi  kwance lufff daya karawa fuskarta kyau a kwance yake  Kai tsaye hweakan zai shaida Mata fulanin asali ce ita shi Kuma ya kasance  duniya ba abinda yake so a jikin mace kamar Suma may be wanan suman nata ne taja hankalinsa ga jelan sumanta ta baya Wanda Kai tsye kwakwalwarsa ya basa gashin doki ne sai yaji ya kara 

yasa ta Kai hanun ta Fara gogewa Wanda o yasa suka samu kusanci zuciyarshi ce tayi mugun bugawa kafin ta Fara gudu a 360,,magudanan jininsa na gudu a sittin brain dinsa ta tsaya cak ya rasa dalili kawai sai ya fassara hakan da kiyayar da yake Mata ne gogewa ta

   A tsorace take goge Aman hanunta na mugun rawa ko kadan Bata yarda ta sake dagowa ta kallesa ba saboda a tsorace take 

Ganin fah Kamar sake baje Masa kazanta take yasa ba kunya ya cire Riga ya Bata murya a kausashe yace”duk inda zakiyi kiyi Amma ki tabbatar kin wanke rigar Nan 

    Rigar ta rike ta Fara kalle kalle sadiya ko d’aukar dramar ta su take a waya a cewarta itama tana da Yaya soja Kuma babbane sai bi musu hakkinsu 

Wani Veronica bucket ta gani na wanke hannun kafin ka Shiga  restaurant din,Zuwa tayi ta d’au robar har morning fresh din ta dawo dashi ta Fara wankewa ruwan tayi mugun sanyi kasancewa ana sanyi sosai Kuma a waje take 

Tana saka hanun taji wata sanyi amma Haka ta Dake ta cigaba da cudar farar Riga sai da ta fita ta matse ta kalleshi da ssuri ta sauke idanuwanta tace”a leda za a sama??”

     Ga mamakin jama’ar dake tsaye sai Suka gan yayi tsaki ya shige mota hadiza ta bishi ya ja motar a sittin 

Rabi’a ta bisu da Allah ya isa sadiya tace”wallahi sai na fad’awa Yaya mustapha saboda kawai ya gan shi uniform man ne zai zalunce ku “

Rabi’a tayi tsaki ta fisge rigar tace”ai sai ki wurgar da  rigar ko bana son ma ganin abinda ya dangacesa “

    Girgiza Kai tayi tace”Zan Kai gida in shanya Masa kila wata ran zamu had’u ya tambayi rigarsa ban son matsala’

    Tsaki Rabi’a tayi ta Fara matsifa Amma Amatu Bata kulata ba ta bar wurin Dan ji tayi zazzabi ya lullubeta ko kuka Rabia dake Kiran batayi ba Dan gani take a tsirara take tunda ba hijab jikinta

     Napep ta tare tayi gida direct Wanda through out journey dinsu kuka takeyi ba abinda yafi Bata mata rai Kamar cire Mata hijabi da yayi 

Tana sauka ta Ciro 200 ta bashi ya cire 80# ya Bata canji 120 ta amsa ta shige gida 

Mama ce ke zaune a gaban murhun dake kofar d’akinta tana tuka tuwo tana ganinta ta ajiye muciyar ta zuba Mata Ido sai duk amatu ta tsargu Dan ba hijabi jikinta Amma Bata kulata ba

Wani irin dariya mama ta kece dashi tace”ayi mu gani ai,aikin banza masu lafiyar ma Basu iya niman ilimi ba sai marasa lafiya ragowar ciwo “

Bata kula mama ba ta shanya rigar soja a igiyar Shanyi dai’dai Nan ummi ta fito da murmushi da fara’a a fuskarta tace”amatu har kin dawo toh ya aji?”

Tace”lafiya Lau ummi ya gida ai nayi tunanin ma bazan sameki a gida ba kina gun walimar Aisha ai”

Ummi tace”naje Amma ban Jima ba na dawo Dan in dafa Miki wani maganin da malam ya bada Zaki Sha da lemon tsami sai Zuma zai fidda Miki kakin Dake cike a kirjinki ki samu sauki “

Tace”toh ummi Allah yasa mu dace “

Ummi ta kalli rigar dake igiyar Shanyi ta kalli amatu tace”ya haka’ Ina hijabin wanan Kuma rigar waye?”

        Amatu tace”d’azu ne tari ya addabeni sai nayi a jiki bisa kuskure ya tab’a wani soja shine ya cire ya bani yace”sai na wanke Masa shine na wanke “

     A take fuskar ummi ya sauya Dan tana matukar tausayi yar’ta tasan irin wahalal  da amatu ke Sha in sanyi ya Kama 

Dariya mama tayi tace”ke fa’iza Ina kike toh fito ki ji wata sabuwar barki, anje an biyo maza da sunan karatu har rigar namiji aka kawo aka wanke da sunan Wai anyi amai “

Fa’iza dake kallo a falo ta fito kallo d’aya zaka Mata ka gano Bata da kunya Kuma fitsararriya ce,fa’iza da mama sun tsani amatu a cewar mama bazata tab’a son Yar kishiya ba Haka ta rainin ya’yanta biyar da kiyyayar amatu itako fa’iza tsanar  tayi mata Wai  akan amatu ta fita samun responsible samari Kuma ana zuwa niman aurenta ita tunda take Babu Wanda ya tab’a zuwa Nima aurenta shiyasa Suka tashi tsaye ganin amatu batayi aure ba Amma hakan ya gagara bayan ta rasa Ahmed sai ga Dr Umar ya  Faso yanzu kokarinsu shine Kar ayi auren daya rage sauran sati uku so suke a rugujeshi Dan bazai yiwu ita tana da shekara ashirin da bakwai batayi aure ba kanwar bayanta Yar ashirin da daya ta rigata ba nata asaran zaiyi yawa ga ba karatu ba sure  

      Cike da rainin fa’iza tace”ai muna Nan mama asirin karuwai gidan Nan zai tonu mu gan karshensu ai sai ayi auren mu gan in Banda kaddara bakar baya ce fa da ita duk  mazajen da suka Zo niman aurenta  mutuwa suke tun Kan akai ga  d’aura auren anata cutar da bayin Allah “

DOWNLOAD PART 1 COMPLETE BELOW ⬇️

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE