ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Cikin murna su ka rufa mata baya, su na fitowa
ba su tsaya ba sai waje, jerin motoci ne da aka je
tararsu, murna da doki suka cika zuciyar Haana,
yadda duk zuri ar su ka fito kowa fuskarsa dauke
da annurin ganin ZUwansu. Cikin zuciyarta ta ce,
Allah na gode maka da wannan tarin farin cikin da
ban taba tunaninsa a rayuwata ba, wai yau
ZURI’A DAYA ta hadu guri guda, kowa na farin
ciki da juna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba tayi aune ba taji tunanin Malam M.J ya zo
mata na sakon da ya tura mata.
Ina mai i maki fatan alheri a dukkan
al’amuran rayuwarki, sai dai na ji haushi da na tafi
ba tare da na hadaki da zuri arku da ku da kika rasa ba,
amma insha Ailahu Allah zai kawo maki wani
cikin rayuwarki wanda zai taimaka miki don
Cikar burinki.
Mun hadu a littafi na hudu,

Wasu tarin hawaye ne suka zo mata cikin
idanunta nan take ta yi kokarin tare su. Cikin ranta
ta ce, Malam M.J na gode da addu’arka gare ni
yau ga shi ta kama ni na cimma burina sai dai burin
nawa bai cika duka ba, tunda ban same ka ba, me
yasa ka yi min haka?”
Jin karan ihun Fadeela da ta buge ta ta nufi
gurin Haaya shi ne ya dawo da ita daga duniyar
tunanin da ta tafi. Da sauri ta cira kanta ta bi
Fadecla da kallo kai tsaye ta je ta rungume Haaya
tana murnar ganin ta ita rungume ta ta yi ta yi
saurin raba ta da jikinta ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Fad idan ki kenan na yi fushi da ke tun a
airport na yi expecting ganin ki ban gan ki ba, kin
ba ni haushi da yawa. Tana fadin haka ta wani
Juya baya wai ita nan ta yi fushi da ita.
Juyawar nan da ta yi fuskarta karaf a kan Haana
take, Haana ta ji wani irin faduwar gaba ganin
tsananin kama da Malam M.J din ta da Haaya tayi.
Nan da nan ta kori wannan mugun imagination din
da ta saba yinsa duk ita kowa ta gani Cikin zuri’a
dinta sai ta ga yana mata kama da shi, dole ta cire
wannan tunanin idan tana son Zama lafiya muddin
ta ga bako cikin zuri’a dinta sai hakan ya faru da
ita.


Nan ta ce, “Malam M.J me yasa ka yi wa
Zuciyata illa haka ka fita cikin rayuwata amma ka
hana ZUCIYA DA RUHI na nutsuwa me yasa na
kasa cire ka da manta ka a cikin rayuwata da
tunanina kamar yadda ka manta da ni a Cikin
rayuwar ka da duniyar ka gaba daya? NI me yasa
na kasa fitar da kai a cikin duniya ta’? Nan da nan ta
kori wannan tunain da yake zuwar mata cikin
zuciya a yan dakiku don kada a gano ta shiga wata
duniyar
Sorry Haaya na kada ki yi fushi da ni mana
kin san dalilina ba sai na fada miki ba. Cewar
Fadeela ta wani tabe baki ta ce, “Hmmm! Fady ba
kya daukan shawara, amma dai bari na yi shiru
kada na yi laifi ta karasa fada tana dariyā.
lta ma Fadeelan hararar ta ta yi ta kai mata
bugu a baya ta sa dariya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haaya ga Rauda da Haana ko nemories dinki
zai lya tuna su shekarun baya.
Da sauri ta rungume Haana ta ce, NIce meet
you ‘yar uwa koma ban gane ba na ji jininsu na
yawo cıkin jinina ki tuna fa ZURA DAYA ne.”
Dariya suka yi gaba daya haka ta zo ta
rungume Rauda ma da yake gefe daya suke ba su
damu da hayanıyar da a ke ta yi a gurin ba.
Rike da hannun Rauda da Haana Haaya ta yi ta
Ce, “Ku zo mu je ku gaisa da MOmmy?
Kafin su juya sai kawai ganin Mommy din
suka y1 a gabansu ta ce, Gani ai ina tsaye ina
ganin ku sai hira ku ke kun ki motsawa ina yaran su
Rauda, Ammi da Fadeelatu duk ku zo na saku a
jikina ta fada tana fara’a.
Gaba daya suka je ta rungume kowa Haaya na
tsaye sai murmushi take gani Haana ma farko ta ji
wan irin kaunarta ya kamata, saboda sunanta kadai
da ta ji sai da ta tunano da Ruhinta Mustapha Aliyu
domin babu sunan da yake so da buri a rayuwarsa
1rin wannan suna Haana ta jima tana kishin wannan
sunan in akwal mai irinsa a cikin zuria dinta sai yau sunan ya yi mata dadi ta ji kuma tana son
wannan din sai dai waccan ta Mustapha din ne ba
za ta so ba, domin ita ce ta yi sanadiyar sh1ga
damuwar da take ciki.
Ya Allah ka hada ni da Mustapha Aliyu a
garin Kano din nan Allah yasa kuma bai yi auren
da kanwarsa ba. Addu’ar da Haaya take yi kenan
cikin zuciyarta.
Gabaki daya aka dunguma aka shigo cikin
gidan Haj. Asiya (Wato Mommy) rike da hannun
Haana ita kuma Haaya ta riko hannun Rauda da
Fadeela.
Wata irin kauna Haana ta ji tana yi wa Mommy
tun wancan zuwan nata babu wanda take so ya rabe
ta cikin yaran zuri’a din kamar ta domin ganin
Haana take kamar murigayiya Azizan Hammed
dinta sai take ganin kamar ita ce ta dawo duniya
komai nasu iri daya. Bayan haka kuma ga irin
tsananin son da danta Muhammad yake mata.
Har cikin ranta ba ta da wani buri da ya wuce a Www.bankinhausanovels.com.ng
ce yau Muhammad dinta ya aure ta domin mantar
da ita babban gibin da ta rasa na marigayi danta da
har yanzu so da kewarsa ke damunta wato Hameed
Allah ya jikansu da gafara da iyayenmu da suka
Riga mu gidan gaskiya dama al’ummar Annabi
(S.A.W) baki daya.
Gefe daya kuma hankalin Haana da tunaninta
gaba daya ya fisga da kanin Haaya mai suna
Hamecd domin tsananin kamarsa da Malam M.J da
ta yi duk inda ta yi don ta kori tunanin hakan a
zuciyarta abin ya faskara dole ta shiga yawan kiran
Hasbunallahu wani imawakil, domin samun
nutsuwarta.
Bayan an gama hargowa da murnar zuwansu
Haana da Rauda suka fita zuwa gida suka bar su
Fadeela da Haaya amma kafin nan sai da suka
shafe fiye da awa biyu suna tare sai da suka gaisa
da kowa sannan suka taho. Kowacce ta yi cikin
gidansu, sun rabu a kan an jima su Haaya din za su
shigo.
Tana shiga daki ta iske wayarta tana ringing da
sauri ta nufa don ta dauko tana kai wa wajen tana
katsewa miss call ta gani ba adadi tsakanin kiran
Ya Abba da Mr. Sameer idanunta ta yo waje da su
ta rasa wayar wa za ta fara nema.
Take ta tsayar wa ranta bari ta fara kiran Ya
Abbanta da yake can garin Lagos yau kwanansa
biyu da tafiya wanda ya wakilci Abba kan wani
taro da za a y1 na wasu manyan kamfanin a kasa
Nigeria to shi ne ya wakilci Abba, domin dama sau
da yawa idan hakan ta faru shi ne zai tura shi ya yi
masa komai, idan yana da wani babban uzuri
sau tari ma ba shi da komai ya kan tura shi ne shi
ma don yana gogewa da hakan saboda bangarensu
daya shi da Abba.
Bugu daya ta yi ya dauka ya ce, “Hello Haana
lafiyarki ke kau kuwa na yi ta kiran layin ki baki
daga ba.
A nutse ta ba shi amsa da cewa, “Don Allah Ya
Abba na ka yi hakuri ba na kusa da wayar ne ka
san yau an yi baki su Kawu Jafar ne da family
dinsa gaba daya aka zo to na bar wayar ne ina can
gurin ba mu dawo ba sai yanzu am sorry ba da sani
na na y1 hakan ba.
Murmushi ya yi ya ce, No kar ki damu na san
ba za ki daga wayata haka kurum ba. To ya bakin
namu suke, tunda dai lafiyarki kalau ai shi kenan
da har hakalina ya tashi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin jin dadi ta ce, “Allah Sarki Ya Abbana
shi yasa nake son ka ko kadan ba ka son ji na cikin
damuwa ko wata matsalar 1na jin dadin irin
wannan kulawar da ka ke ba ni fiye da kowa a
Kar ki damu Haana ni kullum cikin farin ciki
nake da ke mutukar kina Cikinsa to nima zan
kasance a cikinsa.
Ya Abba kana sona da yawa anya kuwa za ka
yi wa matarka 1rin wannan kulawar da ka ke ba ni,
gaskiya ka dinga ragewa kada matarka ta zo ba ta
Samu irin wannan kulawar ba ta fara kishi da ni.
Murmushi takaici ya yi cikin ransa ya ce,
Haana kin yi gaskiya a duniyar nan babu wata ‘ya
mace da nake s0 sama da ke kuma ZUCIYA DA
RUHI na ba za su taba daina miki su ba har sai na
ga kin auri wanda ki ke so sannan zan san ba kya
cikin rayuwata gudun kada na halaka sai na cire ki
a zuciyata.
Hello Ya Abba na ji ka yi shiru ko fushi ka yi
da abin da na fada maka please ka yi hakuri idan
na bata maka rai.
Girgiza kai ya yi kamar tana ganinsa ta ce, “Ko
kadan ba zan taba fushi da ke ba sai dai gaskiya ki
ka fada kowacce mace zan aura ba na jin zan bata
irin wannan kaunar da nake miki KAUNARMU da
ke daban take ba ta da mahadi da ta kowa.
Gaskiya ne ya Abba na gani ko ni da Rauda
ma ina ganin hakan a gurin ka ba don Rauda na
tana sona ba da ta ji haushin yadda ka ke fin nuna
min so a kanta.To na gode ya Abba da wannan matsayın da
nakeda shi a gurin ka, Allah ya saka maka da mafi alkhairinsa.
Ameen.Suna cikin wayar sai ga kiran Mr. Sameer na ta
shigo nmata, amma ta ki cewa das hi za ta katse,
domin bai cancanci hakan a gurinta ba.
Sai t ace, Ya Abba ban ji ka ce komai ba fa kan
maganar da muka yi da kai ranar da za ka taho ta
Mr. Sameer ina son inji ka ce wani abu domin ya
dame ni wai na fadawa su Abba. Ya ka gani don
Jiya ma mun fara maganar da Granny.
To me zance Haana tunda ya kwanta miki a rai
ai ina ganin babu wata matsala, please Haana ki
manta min da maganar Sameer ba dai kina son shi
ba is o.k ina da tabbacin su Abba ba za su hana ki
abin da ki ke so ba, to mu bar wannan maganar ina
da uzuri yanzu nima mayi Magana da ke lctter on.
Yana gama fadin haka ya kasha wayar abin sa.
Bin Wayar ta yi da idanunta Sororo cike da
mamakin abin day a faru da ita yanzu. Shin me
yake faruwa da ita? Ba dai zargi da hasashen da
take yi shi ne yake son faruwa da ita ba, abin da ta
Jima tana karanta yau shi ne zai bayyanar mata.
An ya kuwa ya Abba ba kishin Mr. Sameer Www.bankinhausanovels.com.ng
yake ba kamar yadda ta kwana da sanin cewa, Mr
Sameer yana kishinsa wanda sun sha kai ruwa rana
das hi don yau bai fi kwana hudu ba saida suka yi
fada a kan wai ya gan su da idonsa lokacin da za ta
fadi ya taro ta kuma sun yi wa junansu wani irin
kallo na so.
Wannan irin furuci da ya yi mata ya daga mata
hankali har sai da suka so yin fada daga baya ya ba
ta hakuri
Ta fuskanci Ya Abba ba ya jan Mr. Sameer
jikinsa tun bayan daya fara nunawa cewa yana
Sonta to yanzu kuma ya za ta yi idan har zargin da
take yin a cewa Ya Abba shi ma sonta yake ya za
ta yi da Mr. Sameer? Tabbas furucin da Ya Abba
ya yi shi ne cikin zafi don a zafafe ya yi mata
magana abin da ba ta taba gani hakan ya faru ba,
tunda suke a rayuwarsu ita da shi.
“Ya Abba da gaske kishin Mr Sameer yake
Idan kuwa haka ne me ke shirin faruwa da ni?
Karar shigowar wayar hannunta shi ne ya dawo
da ita daga tunanin da take yi, sunan Mr. Sameer
ne radau ya fito à screen din wayarta.
A jiyar zuciya ta saki ta ce Bari na daga na ji
shi kunma da wacce yazO mata.
Sallama ta yi a sanyaye ta shiga jin sauraron
abin da zai ce da ita.
Ko amsa sallamar da ta yi bai yi ba ya ce,
Dawa ki ke waya kina ganin kirana ba ki daga min
ba, tun yaushe nake kiranki ba ki daga ba na sake
kiranki na ga kuma layin ki busy, ki fada min da
wa ki ke waya da har ki ka ki daga min tawa?
Oh! Hello Mr Sameer what is wrong with you.
Ka fara amsa sallamar da nayi maka mana kafin ka
Fara yin min wannan tsawar da masifar wai me ke
faruwa da kaine kwana biyu na kasa gane kanka
haba na fara kasa jurewa wannan sabon halin da ka
fito min da shi. Sam yanzu ka sauya babu wani
hakuri a tare da kai, please ka bar ni haka mana.”
“Ni duk ba wannan nake son ji ba ki ba ni
amsar tambayar da na yi miki da wa ki ke waya?
Mamaki ne ya kama ta lallai wannan man din
Zai raina mata hankali wani abu yake mata cikin
takama da gadara take ta tuno lokacin da suke ‘yar
tsama da Malam M.J din ta yadda ya dauki kansa
haka ita ma ta dauka tunda baya raga mata 1ta ma
sai ta Zamo kamar shi ba ta raga masa duk abin da
ya ce da ita take-take ba shi amsa a lokacin. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai ga shi yau shi ma Mr. Sameer ya soma
canja mata yana ba ta orde kamar wani ubanta me
ya dauki kansa ne? Ita ma fa tana da zafi tunda har
ta kara da Malam M.J da irin halayansa babu wani
namiji da za ta iya ragawa matukar ya zo mata da
rainin hankali ta fuskanta Mr. Sameer ya fara nuna
power a kanta.
Da Ya Abba nake waya ko kana son ka
iyakance mana dangantaka da shi.” Ta fada bayan
ta gama tunanin da ta yi cikin dakiku.
No wonder dama haka nake tunani shi yasa na
yi miki wannan tambayar dama na jima ina wannan
zargin tun ranar nan da na ganku na miki magana ki
ka musa to yanzu kin nuna min cewa soyayyar da
ku ke ta fito fili ki na son kowa ya sani.
Cikin tsawa ta ce, “Mr Sameer ka san me ka ke
fada a kan bakin ka wa ya fada maka cewa bayan
dangantakarmu ni da shi akwai wata a boye?
Look, Haana kada ki yi feeling dina mana
ga shi na gani a zahiri kuma furucinki ya nuna
min.”
Mamaki ne ya kama ta ta ce, Mr Sameer ka
san koma me ka ke cewa da ni kana cikin sense din
ka kuwa?No am out of it. Yana gama fadin haka ya
kashe mata wayar bayan ya saki wani irin tsaki.
Baki bude ta bi wayar da kallo ta rasa abin
cewa domin ta rasa abin cewa kawai sai ta ji tana
son fashewa da kuka, nan kuwa ta shiga kukanta
mai isarta.
Shin wane kuka ne ya fi daga mata rai na abn
da Ya Abba ya yi mata ko na Mr Sameer domin
duk abin da suke da ya Abba bai taba kashe mata
waya ba, amma yau yadda ta ji ya yi mata abin ya
ba ta mamaki ya kuma tsaya mata a rai dole ta
shiga damuwa, shi kuma wannan maimakon ya
faranta mata rai sai shi ma ya zo ya kara mata wani
tashin hankali duk wanda ta yi kuka a kansa daidai
ne domin yin kukan shi ne zai ba wa zuciyarta
nutsuwa.
Misalin karfe tara na dare Alh. Jafar ne da ‘yar
uwarsa Mama Bara gami da mahaifiyarsu Haj.
Babba zaune suke cikin dakin ta suna taba hirar
yaushe gamo kowa ka gan shi cikin jin dadi sai dai
Haj. Babba ta ciwon kafa yake takura mata abin ka
dama da girma komai sai a hankali.
Alh. Jafar ya ce, Hajiya kafar dai taki da dai
sauki ko dole ne kina sake ganin wanı kwararren
likitan tunda kin ki yarda a fita da ke. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kayya Jataru wane fita kuma shekara nawa za
mu kara nan gaba, kafa dai Alhamdulillah, ba
kamar da ba yanzu ana samun afuwa sosai domin
babu abin da ‘yan uwanka ba sa yi a kai, kai dai
kawai ka bar maganar da aka ce abu ya fara
haduwa da girma sai dai kawai addu’a da kuma
hakuri, amma dai yanzu akwai afuwa sOsai.
“To Allah ya kara sawwakewa.
“Ameen. Hajiya Babba da Mama Bara suka
fada a tare.
Hira mai dadi suka shiga yi zuwa can kuma
Mama Bara ta canza musu ita da maka su kan
Zaman da ta zo domin shi.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE