ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
Dariya ya saka ya ce, “Hohoho! Haaya ban san
lokacin da za ki daina abu kamar su Amal ba to
tashi ki mu je ki dauko min abin da na aike ki ki zo
mu zanta da ke ina son jin abubuwa alot a cikin
family din mu tun zuwanku har kawo yau don
yanzu ke ce ‘yar gida yanzu na san kina da labarin
komai da kowa na family dinmu.
Murmushi ta yi kamar ba ta da wata damuwa ta
ce, “Za ka ji komai kuwa Yayana.
Shi ma dariyar ya yi ya kama hannaycmenta ya
langwabe har da wani cewa. “Wash!
Shi kuma ya ce, ‘Sannu yi a hankali.
Kai tsaye dakin Granny ta nufa da ta shigo
gidan, ko sallama ba ta yi ba ta kutso kai. Zaune ta
iske Granny kan sallaya ta idar da Shafa’l da
Wuturi tana shafa addu’a tana shigowa ciki.
Kai tsaye ta fara magana cikin daga murya,
Granny wane irin laifi na yi muku da za ku yi min
haka ke, Ammi, Abba, Mamah Me, Ya Abba da
Rauda ku dukkan nan da na lissafa ko ne komai na
farin
cikina, kukana, dariyata,
rayuwata, Www.bankinhausanovels.com.ng
damuwata, duk ku ne amma me yasa za ku yi min
haka ku boye min komai bayan na tabbata kun san
duk abin amma ku ka boye min.
Me na yi muku kun yi hakan ne don ba kwason
ku ganni cikin farin ciki ne ko me ye? Haba
Granny na ko wasu za. su yi min haka ina da
yakinin ke ba za ki boye min komai ba za ki zauna
da ni ki fahimtar da ni, kuma zan fahimta. To
amma me yasa ki ka gaza haka Granny? Granny
Why! Why!! Why!!! Granny har dake a ciki…”
Nan kuka ya ci karfinta dole ta tsaya ta ci gaba da
kukan.
Kidimewa Granny ta yi don ba ta gane sam me
take nufi da hakan ba.
Ke gidanku Raihanatu kin ruda ni ki tsaya ki
yi min bayani yadda zan gane me kuma muka yi
miki ki ka lissafo mu haka?”
Kukan ta ci gaba da yi da sauri ta zo ta soma
Jijjiga ta tana cewa, “Don iyayenki ki fada min me
muka yi miki? Da ke nake fa Raihanah?
Cikin kuka ta kwashe komai ta tafadawa Granny
Ta kara da cewa. “Granny me yasa Ya Abba zai
min haka bari na fada miki ban taba fara son wani
da namiji a duniyar nan ba sai shi na jima da boye
so da kaunarsa a zuciya ta gudun furucin da ya taba
yi min a baya na cewa duk runtsi kada na taba
bayyanawa wani da namiji cewa ina son shi ko ya
muke da shi, yin hakan zubar da mutunci da daraja
ne na diya mace da wannan furucin yasa na yi
amfani da shi yasa ban fada masa irin son da nake
masa ba, ganin shi ma bai nuna min ba.
Granny wallahi tunda Ya Abba yana sona to
wallahi ba zan auri Mr. Sameer ba, ko za a kashe
ni. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daidai lokacin Ammi da Abba suka karaso
gurin jin dagawar muryar Haana ganin su Ya Abba
ya yi saurin boyewa a jikin labulen Granny domin
duk ya ji abin da take fada tun farkon zuwanta
rudanin da ya shiga ya kuma rasa da me zai kare
kansa yasa ya tsaya yana jin abin da take fada,
amma ganin hawayenta da tashin hankalin da ya
hango a fuskarta ya rasa dukkan nutsuwarsa Allah
ne kadai ya san irin abin da yake ji cikin zuciyarsa,
domin gani yake zuciyarsa da ta Haana kamar tare
aka yi su duk wani hali take ciki sai shi ma ya ji shi
a cikinsa har ma yana jin kamar yana fin ta jin
abin da take ji a ta shi zuciyar
Haka Ya Abba yake zai iya jure komai na shi
da zai farnu da shi, amma matukar abin ya shafi
Haana baya iya jurewa haka zai za mo uncontrolled da
ZuciyarsSa.
Tana yin ido biyu da iyayenta nan ta kara saka
kuka ta sake duban Granny ta ce, ‘Granny ki fada
musu su warware aurena da Mr Samcer na fasa
Ya Abba nake so.
Abba ya ce, “Umma wai me yake faruwa muna
daki muka jiyo hayaniyar Ammina kamar tana fada
da wani?
Abba ba da wani nake fada ba aurena da
Sameer nake so ku warware tunda ba a riga an yi
ba, Ya Abba nake so ba shi ba.
Hannu ya kai mata da zummar zai mare ta
Granny ta yi saurin rike masa hannu ta ce, Kada
ka dake ta mun yi mata laifi kamata ya yi mu
lallaba ta mu fahimtar da ita ba wai kai ma ka biye
mata ka dau zafi ba, kamar yadda ita ma ta zo min
da zafi.
A nutse Granny ta yi masa bayanin komai har
da rayuwar Ya Abba da Haaya kamar yadda ta yi
mata bayani da kuma kudurinta na fasa auran
Sameer din.
Jikinsa ya yi sanyi ya ce, “Ammi na ba wai don
ba ma son ki muka yi haka ba, mu kan mu yadda
muka yanke a ranmu ba ki da miji da ya wuce
Yayanki Mustapha, amma UZIRIN da ya ba mu
yasa muka karba duba da cewa ke ma da bakin kika fada masa kina son shi kuma magana ta shiga idan muka hana Sameer muka ba shi ke me kike tunanin zaije ya dawo, ni kuma ba na fatan Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani abu na rashin jin dadi ya kara zuwa ya gifta
Tsakanina da zurï’ata tunda mun mantar da wancan.
Ammina ki fahimci wannan maganar tawa.
Cikin kuka ta ce, “To na fahimta Abba, idan an
magance wannan matsalar ya zan yi da ‘yar uwata
Rauda da take son shi Sameer din kamar ranta ko
kuma tunanin hadin da ku ka yi ita da Ya Fu’ad
tana farin ciki da shi, shi kansa ba ita yake so ba
yana da wadda yake so cikin zuri’a biyayya ya yi
muku.
Abba kada garin neman farin cikinku ku jefa
mu yaranku cikin damuwa da rashin kwanciyar
hankali kun tura mu don mu yi biyayya ga mazajen
mu maimakoin haka sai mu fada cikin halakar
Ubangiji, domin ni ko na auri Sameer ba zan taba
yi masa biyayya ba, saboda zan ta tsangwamar
kaima na auri mijin da mafi kusanci ‘yar uwata take
SO.
Abba ku duba ku gani kada ganin ZURI’A
DAYA sun hade ku yi tunanin shi kenan ba ku da
matsala idan har ba ku bawa kowa dama ba za a
samu matsala a nan gaba Abba ka duba maganata
ka gani.
Gaba daya sai jikinsu ya yi sanyi, domin ba su
taba sanin cewa Rauda tana son Sameer ba, domin
Granny da ta sani ba ta fada musu ba ganin ta
tsawatarwa da Haana.
Shirun da Abba ya yi na dan wasu lokaci shi ne
ya bata damar ficewa, side din ya Abba ta nufa
tana goge hawaye, buga dakin take kamar za ta
fasa kofar ba ta bude ba, tana juyawa za ta tafi
suka yi kicibus.
Kallon-kallo suka shiga yi babu wanda ya iya
cewa komai duk da irin cikin damuwar da take
amma sai da ta dage ta iya kirkiro murmushi kai da
ganinsa ka san an yi shi ne kawai tace
“Well, good job, Ya Abba. Sai kuma hawayce
suka biyo baya.
Wani irin abu ya ji ya taso masa daga kasan
zuciyarsa ya ji kamar ya je ya janyo ta jikinsa ya
rarrashe ta. Cikin kuka ta ce.
“Why Ya Abba me yasa ka canza min da yawa
ne gaba Www.bankinhausanovels.com.ng
daya na kasa gane ka a ‘yan kwanakin nan
sam ka sauya yadda na dauke ka da tarin matsayın
da na ba ka ashe duk ba haka ba ne a gurinka, ya
zan yi na gane cewa Ya Abba ne na da can wanda
bai san ganin kankanuwar matsala ta same ni bai
kore ta ba bare har ya bar babba ta tunkare ni.
Ya Abban da da muke dariya tare mu yi kuka
tare, mu yi sharing idea tare, abin da nake so da
wanda bana so shi ma haka ne a gurinsa. Ya Abban
da ba na taba yin abu kai tsaye sai ya ba ni
shawara, haka shi ma; amma yanzu fa duk na rasa
wadannan abubuwan da na jero. Me yasa ka yi min
haka ya Abba? Ashe dama akwai wannan rana da
Zata zo ta same ni? Ya Abba me yasa ka ke boye
min a lot of things naka? Me na yi maka ka canza
mana dangantakarmu haka?”
*Ya isa haka Haana ki saurare ni mana! Ya
fada cikin daga murya domin ganin zubar
hawayenta ya kara daga masa hankali.
Ya Abba na gaya maka cewa a yanzu na daina
Jin tsoron tsawar kowa ka yi ta yi min tsawa dole
ne ka bar ni na fadi abin da nake jin zafinsa cikin
raina domin na samu saukin KUNAR ZUCIN da
ke damuna.
Cikin sauri ya ce, ‘O.K, maza ki fadi abin da
yake zuciyarki saboda ki daina jin kuna cikin
zuciyarki. To amma don Allah ki yi min UZIRI.”
Ya Abba na ji komai da ka rufe min ban sani
ba Haaya ta gaya min duk abin da ya faru ba ta
boye min ba.
Ka sa a ranka ba ka da wata mata a duniyar nan
sai ni ko me za a yi min ba zan auri Mr Sameer ba,
na kuma fadawa su Abba haka shi ne kai ma na zo
na fada maka.
Tana fadin haka ta sa kai za ta wuce ya yi
saurin kamo ta ya ce, “Haana kada ki yi min haka
tuni an riga da an gama magana tuni.”
Fizge hannunta ta yi ta ce, Ya Abba ni na
gama magana yanzu sai dai dama idan so na ne ba
ka yi yasa ka ce ka barwa Mr. Smaeer ni saboda za
a yi maka dole. Tana gama fadi ta yi ciki abin ta
bata ji cewarsa ba.
Tsananin damuwarsa ta yawaita saboda ya kasa
cewa da ita komai tabbas abin da ya guda kenan ya
so ya hadu da Haaya tun farko saboda ita ce kadai
za ta iya boye masa wannan abin ga shi kuma ta
fada. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya yi kokarin yin magana da ita tunda ta ji
muryarsa ta kashe wayar ta ki ta kunna dama a
gurin Rauda ya karbi lamba din, ya tura mata sako
ta wayar, saboda ba ta bude ba, don da ta gani za ta
ba shi amsa domin rokonta ya yi a kan kada ta
fadawa Haana cewa sun san juna sai wasu lokuta
masu tsawo, to ga shi nan ta tona asirin abin da
yake gudu ya faru.
***
Hankalin M. M.J ba karamin tashi ya yi ba
bayan samun labarin duk abin da yake faruwa a
gurin kanwarsa da suka kebe suna hira duk da tana
cikin damuwa haka ta daure ta fada masa saka
ranar auransu da aka yi kowannensu.
Dukan hannunsa ya yi ya mike tsaye yana Safaa
da Marwa a gurin da suke ya ce, Haaya ba zai
yiwu ba babu wanda zai sani na auri Fadeelah
saboda ba ta cikin tsarin matan da nake so na tsani
mace mai jin kai da nuna isa ke in fact ba na son ta
ba zan aure ta ba gaba daya.”
Da sauri Haaya ta ce, ‘Ya Muhammad ka san
kuwa irin yadda Fadeelah din take son ka kuwa?
Cikin daga murya “Ko ya take so na ni bana
son yi k0 za ki yi min dole ne ke ma please Haaya
KI yi min shiru na gama maganata a nan kuma ko
ina za a a kän haka na tsaya.
Dama ta san da hakan za
faru ta riga da ta
gama sanin irin kafiya da budadden hali irin na Ya
Muhammad ba kowa ne ke iya canza masa tsarinsa
ba idan ka cire Mommy shi yasa take ya fada
Fadeelah tana yi a hankali gudun irin wannan ranar
Ya Muhammad dan kansa ne.
Zancen zucin da take yi kenan kawai sai ji ta yi
yana cewa, “Sameer karya ka ke ka yı min haka, ka
san abin da nake nufī ka kuma san burina, wannan
yana cikin dalilin da yasa na kawo ka cikin
rayuwarta ban da UZIRIN da ya taso min da ba ka
isa ka ganta ba bare har ka shigo rayuwarta.
Wait and see Sameer ka ga yadda zamu yi
playing wannan ganme din da kai tunda ta nan ka
biyo min.”
Ficewa ya yi ya bar ta a gurin ta bi shi da kallo
domin babu abin da ta iya fahimta cikin furucinsa
tunda duk a dunkule ya yi shi, ta yi kwafa ta ce.
“Sai Yaya Muhammad dan lalen Mummy zafin
ka ya yi yawa Fadeelah ke kuma na tausaya miki
ke ma watan shiga damuwarki ya kama tunda ke da
kanki ki ka taro hakan.”
A bayya ne ta fadi hakan ta mike ta shiga ciki.
Yau a kalla kwana biyu kenan da faruwar
hakan sam Haana ta tsangami kanta ba ta kula
kowa cikin gidan daga makaranta sai daki ba ta
kaunar duk wani abu da zai shiga tsakaninta da Ya
Abba haka kuma ta ki bari Rauda ta zo inda take,
domin ta sawa ranta cewa ware ta suke yi Mr.
Sameer kuwa har yanzusun ki dadi kwana biyu
yana tare ta a hanya ko za ta tafí makaranta ko
bayan ta dawo.
Duk yadda ya zaci abin gurinta ya wuce haka
dole ya shiga lallaba ta, amma ko kusa ko alama ya
kasa gano kanta, haka tun daga Granny Abba da
Ammi kowa ya share ta bai bi ta kanta
Abba ne yace a yi mata haka da kanta za ta sauko
Idan ta ga ba a nuna damuwar halin da ta shiga ba.
Duk da kuwa bai son hakan da ya yi mata ya yi
haka ne don ya iya daurewa da cijewa kan son
ya ya saboda inganta zumunci, amma ba don haka
ba bazai taba banzatar da damuwar Amminsa ba,
wadda ya fifita sonta da duk sauran “yan uwanta
amma sai take gani kamar sam bai damu da ita ba.
duk da kuwa furucin da ta yi masa har yanzu yana
nan yana masa yawo a zuCiya.
Abba kada garin neman farin cikinku ku jefa
mu yaranku cikin damuwa da rashin kwanciyar
hankali, kun tura mu don mu yi biyayya ga
mazajcnmu maimakon haka sai mu fada cikin
halakar Ubangiji, domin ko na auri Samcer ba zan
iya yi masa biyayya ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ire-iren maganganunta sun taba zuciyarsa da
jefa shi cikin tunani mai tsawo dole ya san abin yi a
kan wannan furuci, domin ya fara hango matsaloli
dole ya kai wannan maganar family meting a duba
tunda wuri kafin ya kai ga zamo musu ga matsala,
da wannan sakar zucin kullum yake kwana da shi.
Sarai Mr. Sameer ya san da zuwa Muhammad
amma ya yi biris da shi kamar bai san da zuwansa
ba tunda shi bai neme shi ba, dole shi ma ya share
shi tunda ya na ganin shi din wani tsiya ne.
Babbar damuwarsa shi ne yadda ya kasa gano
kan Miss Haana dinsa, sam ta ki ta ba shi time ko
bare har su yi magana.
Zuciyarsa tafi saka masa ccwa Ya Abba ne ya
Zuga ta karfi da yaji ya nunawa duniya cewa ya bar
masa amma yabi ta karkashin kasa yana yaki da
shi cikin ruwan sanyi yadda babu wanda zai gane
me yake faruwa.
Nasa tunanin kenan don haka ya yankewa ransa
yau zai nemi Ya Abba ya fada masa magana mai
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG