ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

Knocking aka yi wa dakinnasa ya bada damar a
shigo. Turo kofa aka yi hade da yin sallama da
sauri ya mike daga kwanciyar da yake ya amsa
sallamar tare da mamakin ganin wanda ya shigo
dakin nasa. Ba kowa ba ne illa Malam M.J.
Ya dan razana da ganinsa amma da yake
wayayye ne sai ya yi saurin dakewa ya ce, ‘A’ah
mutanen turai sai yau kenan aka tuno da ni ga guri
Zauna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya nuna masa kujera da nuna cewa ya zauna,
mika masa hannu ya yi suka yi musabaha.
Murmushi Muhammad ya yi ya ce, “To ai tunda
ba ka neme mu ba mu sai mu zo inda ka ke tunda
hakan ba laifi ba ne.
“A yi min UZURI abubuwa ne suka yi min
yawa.
“An yi maka. Ya fada lokacin da yake Kokarin
Zama Kan kujera.

Mikewa Mr Samceer ya yi ya ce, ‘Bari na ba ka
drink ka sha.”
No thank you, ka bar shi kawai.
Ba matsala. Ya koma ya zauna.
Dauke wuta suka yi na dan wani lokaci saboda
kowa da irin abin da yake sakawa a ransa. M. ne
ya numtasa ya ce, ‘Sameer da farko dai ina maka
godiya ga tarin kokarin da ka yi na ganin munyi
nasara hada zuri’a dinmu guri daya, na yi farin ciki
sosai kuma wadda na yi don ita na san ita ma ta yi
farin ciki; domin yin hakan shi ne mafi grman
burinta.
Murmushi Sameer yayi
ba ita kadai ba mu gaba daya.”
O.k, koma dai me ye ka gane nufi na, sai wata
magana da na ji wai an saka ranar auranka da
Raihanatu.
ya ce, ‘Ka saka jam’i Www.bankinhausanovels.com.ng
Of course really ba wai ba ne gaskiya ne.”
Ka yi kuskure Sameer, Raihanatu matata ce
me ya kai ka tunanin fara soyayya da ita bayan
contract naba ka na zuwa cikin rayuwarta me yasa
ka kai kanka inda ba a aike ka ba?
Wannan karon cikin bacin rai ya yi magana
ganin wani shan kamshi da Sameer din yake masa.
Ya daga hannu ya ce, “Duba Muhammad ni fa
ba yaronka ba ne, da za ka dinga yi min wannan
maganar kana tunanin kai ne kadai dan uwanta da
Za ka iya sonta, ka bar wannan maganar shirmen.
Na zo rayuwar Raihana ne ba wai don kai ba, a
Je don kai na zo, kana tunanin zan iya ganin mace
irin ta na hakura bayan ina da cikakkiyar lafiya
babu ta inda na nakasa. Na ji contract ka ba ni,
amma ai ba kakA da ikon hana ni yin soyayya daita.


Plcase Muhammad mu bar wannan maganar mai
kama da tatsuniya tunda mu ba yara ba ne yara aka
sani da wannan maganar.”
“Dole mu yi ta Sameer, domin saboda ita na zo
gurin ka na riga ka ganin Raihana ni nake son ta na
zo ne mu yi magana mai guri ya zo sai mai tabarma
ya nade.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Muhammad kada ka daga mana hankali daga
Zuwanka bayan zuri’a tana cikin farin ciki idan
kuma kana da ikon hana iyayen mu zartar da abin
da suka yi sai ka je ka same su ni dai tunda an ba ni
mata ban ga wanda ya isa ya hana ni auranta ba,
gwara ma ka janye wannan bahagon tunanin da ka
zo da shi.


Cikin zafin rai ya ce, ‘Sameer ina son ka tsayaka gani ni da kai za a bambance waye mai
bahagon tunani Raihana tawa ce ni kadai babu
wanda ya isa ya ba ka saboda ni Allah ya rubutawa
a matsayin matata. Ka jira kuma ka gani ba ka isa
na hada nema da kai ba.”
Yana ganma fadin haka ya wuce abin sa ko
sauraron abin da zai ce bai yi ba. Tsaki Mr. Sameer
ya yi ya ce, “Muhammad kai dai ba wani ba, ba ka
isa ba mu je zuwa ba ka isa ka yi nasara da ni ba.”
Ransa a bace ya shigo gidan Momny da Abdul
Suna zaune ya zo ya wuce su.
Kwafa Mommy ta yi ta ce, ‘Aiki ya same ka
Mahammadu na rasa gane irin wannan kafiyar ta
ka dadinta kana da masu taka maka birki bari dai
ka fito da wata fittina Mama Bara kadai ta ishe ka
sai an je ba yadda ta daukaki wannan auren naku.”
Abdul ya ce, “Mommy ina hango tarin matsala
a kan maganar auran nan ya kamata dai a zauna a
kan batun nan kada garin neman gira a rasa ido
maganar gaskiya Mommy, Barrister baya son
auransa da Fadeelah da yana tunanin Daddy zai
hada shi da ‘yar abokinsa yana tunanin masa bore
sai kuma ya zo yaji wannan hadin a gaskiyan ce ba
shi da wadda yake so irin Raihanatu. Idan kawai
ana son zaman lafiya kawai a ba shi wadda yake so
kada a je a yi ba a ji dadi ba, duba da abin da ya
faru tun muna yara.
To uban iya tsara zance idan ba a ba shi ba sai
ya tada mana hankali ya kawo mana rashin zaman
lafiya to ya je ya.yi duk abin da zai yi ga shi nan ga
Iyayen naku mu dai ‘yan gani da ido ne.”
“Mommy ba haka ba ne a dai duba abin ni dai
shawara na bayar.”
“Ka je ka samu wanda suka hada auran ba ni ba
tunda ba a yi wa dan uwanka abin da yake so ba.”
“Ni ba haka nake nufi ba.”
“To ya ka ke nufi?”
“Shi ke nan Mommy mu bar maganar Allah ya
zaba abin da ya fi alheri.”
“Shi ke nan addu’ar da ya kamata ka yı tun
farko.”
Dawowar ta kenan ba jimawa ta jiyo muryar
Fadeelah suna gaisawa da su Amıni suna fada mata
tana ciki.
Sallama ta yi ta shigo dakin Haana kallo daya
za ka yi mata ka gane tana cikin damuwa ta kin
karawa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna hada ido da Haana sai hawaye ya wanke
mata fuska. Idanu waje Haana ta yo da su ta ce,
Fadeelah me kuma ya faru da ke har da kuka
haka?”
Cikin kuka ta ce, Haana ki taimake ni ki yi
min kokari gurin shawo min kan Ya Muhammad
sam ya ki ya saurare ni, yau da na gan shi sai dai
ganinsa bai zamo min dadí ba, domin bude baki ya
yi ya ce shi ba zai aure ni ba, ban da wulakancin da
ya yi min har da cewa na cika naci, ga shi ya fada
ina da naci, sai dai ba ni nake da nacin ba zuciyata
ce da zan iya hakura da shi da na hakura, haka
nake ji kamar zan mutu idan na rabu da shi, Haana
am so deeply in his love a zuciya ban taba yi wa
wani dam adam
wannan son ba.
Zan iya kirankaina mai haukar soyayya Haana
Yaya Muhammad mai tsada ne da yawa ba
kowacce mace za ta fara son shi ba ta daina ya tara
qualities da dama da kowacce mace take son ace
mijinta na da su, he’s so special a cikin maza.
Please Haana ki taimake ni ki je ki shawo min
kansa ba ni da wacce za ta yi min haka sai ke ina
jin tsoron fadawa Mommy dinmu tana da zafi
dalilin abin da za ta yi masa zai sa ya kara tsana ta
don haka yasa na biyo ta gurin ki.”
Cikin damuwa ta zo ta dafa ta tace, “Calm
down Fadeelah ki daina daga hankalinki zan miki
duk abin da kikeso wannan alkawari na yi miki
tun kafin zuwan wannan ranar.
bar ni da shi zan biyo masa ta yadda bai zata
ba, bai isa ya sa Fadeelah na kuka ba don ta ce tana
son shi. Ki jira ni yanzu zan je na same shi dama
ban taba ganinsa ba
Tun da har ya sa ki ka zubar da hawaycnki to
sai ya biya su da tsada ko ya yake jinkansa sai ya
sauko ya zo da kansa ya baki hakuri, insha Allahu
zan yi nasara a kansa.
Ki na ji ni kaina nan da ki ke gan ni ina cikin
matsala babba, amma barı na je na dawo zan gaya
miki irin tawa matsalar bari ki fara nutsuwa idan
kin ji tawa za ki ji kamar tafi taki jira ni a nan na je
na dawo yau duk jin kansa sai ya ajiye da kansa zai
biyo ni ya ba ki hakuri. Ba dai yana gidan ba
yanzu?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Yana nan please Haana ki yi a hankali kada ki
yi masa rashin kunya Yaya Muhammad baya
daukar raini na san halinsa ta wannan bangaren.
Kada ki damu ni ce fa na hadu da wanda ya fi
shi hakan a school dinmu karshe da kansa ya nemi
sulhu da ni ko na yi masa rashin kunya bai isa ya yi
min wani abu ba, saboda irin su sai ka bude ido ku
ke daidaitawa. Ke dai jira ni na dawo.”
Tana fadin haka ta wuce abin ta ba ta jira wani
karin bayani daga gare ta ba.
Ta baya ta zagaya gudun kada kowa ya ga
fitarta, musamman ya Abba da yake ta nacin son
mata magana ba ta kula shi.
Sallama ta yi ta shigo falon matasa uku ta gani
falon zaune sai dai dayan duk ya fi su girma.
Biyun sun gane ta suka ce, ‘Sister barka da
Zuwa.”
Murmushi ta yi ta kira sunan kowannensu, suka
had aido da babban ta dan bata rai kadan ta ce, ‘Ya
Muhammad gurinka na zo fa.
Dariya suka yi mata suka ce, ‘Aunty Raihana
ba shi ba ne ba fa wannan Yaya Abdul ne.”
*Au!’ Ta rike baki ita ma sai abin ya ba ta
dariya ta ce, ‘Am so sorry Ya Abdul.”
Shi ma dariyar ya yi ya ce, Oh really ke ce
dama Raihanatu ina ta jin labarin ki tun zuwanmu
ba ki zo mun gaisa ba munje gidan ku sau biyu ba
kya nan.
Ayya ku yi hakuri na yi laifi Haaya ce ta yi
min laifi da kuma school tunda yau na z0 sai a yi
hakuri. “
“O.k, komai ya wuce ga guri zauna.
A dan gaggauce ta ce A’a, Ya Abdul ba sai na
zauna ba, Ya Muhammad nake son gani idan baya
nan na dawo.”
Zaro ido ya yi ya ce, “Ke da kanki sukutum to
zauna bari na kirawo miki shi da kaina yana falon
Daddy.
O.k, na gode Ya Abdul. Tayi
murmushi, sannan ta sanmu guri ta zauna.
Jim kada sai ga Abdul nan fuskarsa dauke da
murmushi yace  Za ki iya shiga yace?
Ta dan yatsine fuska ta ce, ‘Na shiga kuma shi
ba zai fito ba.” A ranta tace Lallai dan jin kai ne
wato nima sai ya raina min hankalin da jan aji bari
na je zai san nima daidai da shi ce.”
Ke ma fa gidanku ne me ye don kin shiga aiki
yake kan computer bai san tashi ne. Cewar
Abdull. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta fada tana mai
Bari na je dama maganar tamu tana son sirri.
Ya daga kafadunsa ya ce, Kin gani ma hakan
ya zo muku da sauki.”
Murmushi ta yi ta sake duban Abdul ta ga yayi
mata acting da mutumin da har yanzu ya kasa barin
cikin zuciyarta tana ganin da zai dawo cikin
rayuwarta da ta samu saukin matsalar da take ciki,
sai ta bar su su je can su sasanta kansu to amma ina
idan mafarki take ya kamata ta farka, tuni Malam
M.J ya yi nisa a rayuwarta yana can yana
rayuwarsa da “yar uwarsa da zai aura.
“Oh, hello Raihanatu are you o.k?”Muryar Ya
Abdul ta ji ta doki kunnenta nan take ta yi firgigit
ta ce, Am ok. “Ta fada hade da yar kunya sannan
ta mike.
Tun da Abdul ya zo masa da batun zuwan
Haana ya ji wani irin farin ciki da doki suka zo
masa da kyar ya iya daidaita zumudinsa na san
ganin ga shi gata a gabansa ya godewa Allah da
irin damar da yake nema ta zo ta samu a lokacin da
yake tsaka da neman hakan ta kasance a gare shi.
Haka ya dinga jin wani irin farin ciki da sabon
shaukin son yin tozali da ita kamnar yau ce ranar da
ya fara ganin ta don haka ya yi saurin cansa inda
yake zaune ya juya baya yana aikin danne-danne a
computer dinsa, amma duk da haka yana cikin jin
dokin jin muryarta.
Tana daga labulen ta ji wani irin BUGUN
ZUCIYA ya disar mata haka ta kara jin wani irin
tsoiro da faduwar gaba na ta zuwa mata ta fara
neman jin jiri da sagewa da ta ji kafarta na yi mata.
Rintse ido ta yi ta daga kafarta ta saka cikin dakin
gami da yin sallamna.
Wani irin daddadan kamshi ya bugi hancinta ta
rasa inda ta taba jin kamshin wannan turaren, rintse
ido ta yi ta shake shi da karfin gaske, cikin ranta ta
ce Ya Muhammad din nan dan gayu ne irin
wannan kamshi mai dadi kamar dakin amarya.
“Wa’ alaikumus salam
Jin amsa sallamar shi ne ya yi saurin dawo da
Ita cikin hayyacinta daga zancen zucin da ta tafi.
Nan ta yi saurin daidaita nutsuwarta ta dan gyara
tsayuwar ta tare da gyara murya sannan ta ce,
“Ummh Yaya Muhammad dama gurinka na zo kan
wata magana game da Fadeclah.
Kumbura murya ya yi ba tare da ya juya inda
take ba ya ce, “Baki iya gaisuwa ba kai tsaye za ki
fada min abin da ya kawo ki, za ki iya jira na tunda
kin same ni ina aiki kin ga kuma ba zan katse abin
da nake yi ba na saurare ki. Don haka dole ki jira ni
tunda ba ki nuna ke mai ladabi ba ce.”
Ta ji haushin abin da ya fada mata amma
tunawa da ta yi abin da ta yi ba shi ne ya dace da
ita ba sai ta ce, Am so sorry, Yaya Muhammad ba
haka na ke ba. To ina wuni. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Bana amsa gaisuwar da ni na nema za ki tsaya
na gama abin da nake sai na saurari abin da ya
kawo ki.”
Ji ta yi sabuwar wata faduwar gaba ta same ta
saboda kalaman da ya yi mata sun yi kama da
wanda Malam M.J ya yi mata a ranar da ta je
submitting wani assignıment din ta lokaicn suna
cikin ‘yar tsama. Lallai wannan shigen Malam M.J
akwai shi da jinkai da wulakanci, ga shi ya ki
juyowa ya kalli inda take.
Ina ganin tunda kana da abin yi nima ina da
shi zai fi kyau ná je na dawo lokacin kana free
saboda bana iya jure jira ka juyo ka ga da
wanda ka ke magana ko ba komai ai ka nuna ka san
da wanda ka ke magana ai zai ji dadi, amma ka
Juya baya. O.k zan wuce anjima na dawo idan ka
gama.
Ba ta jira cewarsa ba ta juya ta fara tafiya jin
takunta ya san da gaske take yi tafiyar za ta yi cikin
sauri ya juya ya ce, “Raihanah ina za ki ki tsaya
mana ke din nan ce dai har yanzu.
Tsananin rudewa da jefa kwakwalwarta tafiya
lalube cikin kwanyarta don tuno inda ta taba jiyo
wannan mai muryar, ba ta wani yi dogon tunani ba
kwanyar ta ba ta abin da ake son tunowa taketa
karya ta zuciyarta da tunannta.
Amma kawai sai ta yanke shawarar ta juya ta
duba ta gani, tana juyowa ta iske shi nade da
hannaycnsa biyu a kirji yana sakar mata wani irin
Kayataccen murmushi sanye yake cikin dogon
Jeans sky blue hade da jar T.shirt.
Bude baki ta yi da hancin hade da zaro idanu
waje cikin rudewa ta ce, “Malam M.J kai ne kuwa
ko idona ne?”
Kara fadada murmushin ya yi ya ce, “Nine nan
Raihanatu Mustapha Naseer Danfillo, na dawo
cikin rayuwarki wannan karon da matsayi da yawa
na zo miki ba irin wancan lokacin ba da nake a
matsayin malamin ki.
Yanzu a matsayin yayanki nake wanda ki ke da
dangantaka ta jini wanda ku ka hadu cikin ZURI’A
DAYA zuriar marigayi Naseer Danfillo sannan
kuma masoyi wanda ya dawo cikin rayuwarki
domin ki zamo min abokiyar rayuwata farin ciki
kuma uwar “ya’yana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da fatan kin yi matukar farın ciki da gani na a
daidai lokacin da ba ki taba zaton ganina ba?”
Har yanzu mamaki ne a fuskarta ta kasa boye
shi ta tsaya tana kallonsa kamar wani mutum-
mutumi.
“Hey hello Raihana ko har yanzu kin kasa
gasgata abin da idanunki ya nuna miki, is not a
drem or mnagiation, ni din ne bari na karaso
gare ki don ki tabbatar.”

Tofa HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE