ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
DAN WAYE 4/13
Mun tsaya
Kara fadada murmushin ya yi ya ce, “Nine nan
Raihanatu Mustapha Naseer Danfillo, na dawo
cikin rayuwarki wannan karon da matsayi da yawa
na zo miki ba irin wancan lokacin ba da nake a
matsayin malamin ki.
Yanzu a matsayin yayanki nake wanda ki ke da
dangantaka ta jini wanda ku ka hadu cikin ZURI’A
DAYA zuriar marigayi Naseer Danfillo sannan
kuma masoyi wanda ya dawo cikin rayuwarki
domin ki zamo min abokiyar rayuwata farin ciki
kuma uwar “ya’yana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da fatan kin yi matukar farın ciki da gani na a
daidai lokacin da ba ki taba zaton ganina ba?”
Har yanzu mamaki ne a fuskarta ta kasa boye
shi ta tsaya tana kallonsa kamar wani mutum-
mutumi.
“Hey hello Raihana ko har yanzu kin kasa
gasgata abin da idanunki ya nuna miki, is not a
drem or mnagiation, ni din ne bari na karaso
gare ki don ki tabbatar.”
Har ya zuwa yanzu mamakin take sai dai ta fi
karkata da yadda za ta saita zuciyarta da
kwakwalwarta da suka shiga rudani da dimuwa.
Hura mata iska ya yi a fuskarta wani irin
kamshin mouth spray ne mai kamshin minti ya
doki hancinta ta runtse idanu ta yi baya da sauri.
“Malam M.J kai ne Yaya Muhammad wanda
Fadeeelah take so?”
“Eh, nine Raihanatu ko sai dai tuni na fada
mata cewa bana yi ke nake so nake kuma shirin
aura na jima da fada mata haka, kuma ta sani sai
dai ta yi wurgi da maganar, amma tunda yanzu
ga ke za ta fi daukar maganar da
muhimmanci.’ Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin daya murya Haana ta ce, Ya ishe ka
haka Malam M.J ka bar fada min haka kada ka
ruda ni ka bar ni na hada tunanina guri guda
saboda na gama rudewa ka sana kuwa me ka ke
fada min a madadin Fadeelah na zo gurin nan ban
san kai ne Yaya Muhammad ba na zo ne don na
fada maka irin tarin soyayyarka da take ciki na
daidaita ku shi ne za ka zo min da wannan
maganar?
Please Malam M.J ka bar ni haka kada ka
hauka ta ni ka birkita min tunanina, meka ke nufi
Fadeelah za ta dauke ni maha’inciya ko
mayaudariya?”
“Ko me ta dauke ki ba ki da laifi ta sani ina fada
mata sai dai ba ta san cewa ke din ba ce, don haka
idan kina neman abin fada mata to ki koma ki fada’
mata nima ga irin tarin son da nake miki.
Raihana ina son ki so mai tsanani ba na jin
akwai wani mahaluki da na taba yi wa shi don haka
ki je ki fada mata haka, bana jin akwai wani abu da
za ki so ji sama da haka.”
Kuka ta fara ta ce, “Wayyo Allah na wai wane
Irin rudu ku ke san jefa ni ne a rayuwata Malam
M.J har d akai ma, yau na shiga uku! Tana gama
fadin haka ta juya ta fice da gudu tana kuka.
Abdurraheem shi kadia ne a falon lokacin ya ga
ficewarta da gudu tana kuka bai nemi ba’asi baya
yo ciki inda Yayansa yake, ,yana shigowa ya ga
fuskarsa cikin damuwa kai tsaye ya ce.
Yaya Muhammad me kuma yake faruwa na ga
mutuniyar taka ta fíto a guje da kuka ba dai wani
abu ka ce da ita ba?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushin karfin hali ya yi ya ce,
Abdurraheem damuwa da tashin hankali ta shiga,
wai Fadecelah ce ta turo ta neman sulhu guri na na
San ba ta san ni za ta gani ba da na bari mun hadu
tun farko ba lallai ba ne na samu wannan damar ba,
amma yanzu ga shi cikin sauki na fayyace mata
abin da yake raina ya rage kuma na su ita da
Fadeelah din, domin ita ta janyo hakan ya faru ni
kuwa tuni na gama da babinta.”
“Yaya Muhammad ba ka ganin kun jefa
Raihana cikin damuwa da tashin hankali ba fa abu
ba ne mai sauki ta jewa da Fadeelah wannan batun
abin da ya faru ba saboda abin da ya same ta akwai
ciwo da kuma taba zuciya ka duba yadda ta fito
daga ciki.
“Abdurrahcem ko kadan ban so jefa ta ko sakata
a cikin damuwa ba, kai ma ka duba ka ga yadda
haduwar tamu ta kasance daga ni har ita babu
wanda ya zaci haka.”
“Yaya ina tausayin yarinyar nan lallai tunda ka
ga har ta zo gurin ka kan maganar Fadeelah to
kuwa ba karamin aminci ne da kawance a junansu
ba, ya ka ke ganin wannan dangantaka taku za ta
kasance?
“Abdul ka bar ni kawai ka jira ka gani dole ne
na samu Raihanatu at any cost idan Allah ya so ba
ruwana da wani dangantakarsu ai gaba dayanmu
duk DANGIN JUNA ne, wa za a so a ware wani
kowannensu idan aka zagı Jininsa duka namu ne,
don haka a shirye nake na tunkari duk wani surutu
da kalubale na zuri’a. Abu daya na ajiye a raina ba
za a yi min auren dole ba.”
“Shi ke nan Yaya Muhammad Allah ya kawo
mafita ta kowacce hanya.”
“Ameen. Ya fada lokacin da yake kokarin
Samun gurin zama. Abdurraheem ya bi shi da kallo.
A rude ta fito daga cikin gidan ta rasa yadda za
ta yi ta daidaita tunaninta tsabar tashin hankalinda
take ciki shin da wane idon za ta iya kaiwa ga
Fadeelah ta ce mata Yaya Muhammad shi ne
Malam M.j dinta, da ta taba ba su labari bayan
Kuma ita ga irin tarin son da take masa, idan kuma
ta je ta fada mata ba su hadu ba ya je da kansa ya
fada mata yadda suka yi da me za ta kalle ta?
Ga fushin da take da Rauda ba za ta iya zuwa ta
ganta cikin damuwa ba, domin ta san har yanzu
tana son Mr. Sameer idan ta je mata da wannan
maganar tana tunanin nata mafita? Haka Ya Abba
tana jin haushinsa to za ta kara zuwa masa da
matsalarta tunda ya zamo mai sauki cikın
al’ amarinsa da wanne za ta ji? Www.bankinhausanovels.com.ng
Wayyo Allah na na shiga uku! Allah ka ba ni
mafita ban san ya zan yi da wannan tarin
matsalolin da suka zo suka cinkushe min ba, wai
me yake faruwa da ni ne cikin zuria, domin dukkan
matsalar kowa a kaina ta kare.
Ga Mr. Sameer ga Ya Abba, Rauda, Haaya, ga
uwa uba Fadeelah da Malam M.J da nasu yafi daga
min hankali da kowa. Ya Allah ka fitar dani daga
wannan tashin hankalin da yake kokarin wargaza
min tunanina.
Tana cikin wannan sambatun ta ga direban
gidan su zai fita da sauri ta daga masa hannu ya
tsaya. Yana tsayuwa ta ce.
“Malam Habu don Allah kai ni Sokkoto Road
gidan su Zahra, amma don Allah na roke ka kada
ka fadawa kowa can ka kai ni ka barshi sirri
tsakanina da kai ina cikin damuwa.
Shi ke nan Hajiya insha Allahu babu mai ji
dukkan tsanani yana tare da sauki ke dai ki rike
addu’a da halatto Allah cikin al’amarinki sai ki ga
zuciyarki ta zauna cikin sauki. Ya fada bayan ta
shiga motar sun fara tafiya.
“Na gode Malam Habu na nemi taimakon ka ka
saka ni cikin addu’arka saboda ina cikin damuwa
da rudanin zuciya.
Ba komai insha Allah zan taya ki.”
Tun da ta fada masa ta shiga kuka har sai da ya
sauke ta, Cikin kuka ta fito ta ce, ‘Na gode Malam
Habu, na ji shawarar da ka ba ni ba guduwa na yi
daga gida ba na taho ne don na samu saukin
zuciyata daga kunar da take min zan dawo idan na
ji afuwa.”
“Shi ke nan na ji dadi da furucin ki Allah ya ba
ki sauki ni na wuce, dama Tarauni kasuwa zan je
Amminku ce ta aike ni.”
“Na gode fa, don Allah sirrinmu.”
Haba kar ki ji komai na fuskanci matsalar
taki nutsuwa take so Allah kuma ya ba ki ita ko ta
me ye.
Ameen. Ta fada lokacin da ta taho shi kuma
ya juya abin sa.
Da kuka ta shiga cikin gidan a falo ta iske
Zahra da kannanta lokacin Mamansu ta fita, tana
ganin ta cikin rudani tace, Haana lafiya dai ko?
Kuka ta saka mata ta fada jikinta ta ci gaba da
kukan. Daga Zahra har kannanta duk hankalinsu ya
Tashi tare suka ce, “Rasuwa aka yi muku ne?
Ganin yadda suka nuna damuwarsu sai ta yi
Saurin cewa, “Lafiya kowa yake babu wanda ya
mutu, ku kwantar da hankalinku Khalil ni ce dai na
ke cikin damuwa, Zalıra mu je dakinki.”
Gaba dayansu a tare suka yi ajiyar zuciya suka
ce, “Alhamdulillah!”
Kama hannun Zahra ta yi ta ce “Mu je dakin ki
Zahra.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Babu musu suka yi ciki su kuma kannenta suka
saki ransu suka ci gaba da harkokinsu.
Cikin kuka ta gama labarta mata irin halin da ta
kuma tsintar kanta a ciki da yake duk ta san halin
da take ciki.
Shiru ta yi ta kasa cewa komai zuwa can ta ce,
Raihana ba zan hana ki kuka ba, ki yi mai isar ki,
domin yin sa ne zai sa ki samu saukin kunci da
KUNAR ZUCIN da ki ke ciki.”
Cikin hawaye ta dago ta ce, “Batun jin sauki a
wannan irin bakin cikin da kunci ai sai dai abin da
ya karu na rasa me ye da ni da duk cikin su kowa
yake sona ni kadai. Me nake da shi da sauran ba su
da shi, duk abin da nake da shi dukkansu suna da
shi, asali, ilimi da tarbiyya duk tushe daya muke
duk abin da gidan nan yake da shi wanccan haka
yake da shi. To amma sai kowa yace sai ni yake so
Cikin tausasa murya Zahra ta ce, “Haana kada
ki ce haka duk abin nan da ki ke magana a kai ba
duk lokaci daya ya faru ba daga lokaci zuwa lokaci
hakan ya faru.
Wanda ya faru na ban mamaki shi ne haduwar
ki da Malam M.J idan kin duba shi nasa daban ne
babu ta inda kú ka rayu gida daya sai dai haduwa
ta makaranta. Ya Abba kuma tare ku ke rayuwa,
haka na faruwa don ya boye miki bayan kuma yana
son ki.
Shi kuma Mr. Sameer ta bakin ki shi kuma
lokaci guda ya shiga rayuwarki da zuwansa ya
bayyana miki abin da yake ransa bayan kin gane
dan uwanki ne.
Don haka ki tsaya ki nutsu na san abin da cajin
kwakwalwa ki bari duk wanda Allah ya zaba miki
shi ne alheri a tare da ke, domin dai kin san ba za
ki auri maza uku ba na tabbata iyayenku za su
shiga cikin wannan rikicin soyayyar mai rudani ba
za su taba barin ku haka ba”
Zahra ki ke wannan magana wa ki ke tunanin
zan aura cikinsu bayan cikin ‘yan uwana mata
kowa da wanda take so?
Zan auri Ya Abba ne na bar Haaya cikin
damuwa, ko na auri Mr. Sameer na kwari mafi
soyuwar yar uwata Rauda cikin zuri’a ta ko shi
Malam M.J din zan aura bayan aminci da yardar da
Fadeelah ta yi da ni ta ce na taimaka mata.
Cikin wadannan da na lissafa miki wanne ne ki
ke ganin yana da sauki ki fada min na ce Zahra ki
fada min a naki ganin.” Tana gama fadin haka
kawai sai ta sa kuka. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Na yarda da ke RAihana kaf ciki babu mai
sauki, amma na sani iyayenku za su duba mai
yiwuwa dole dai cikinsu mutum daya za ki aura ba
za su bar ki cikin wannan damuwar ba.”
Zahra ki daina fadin haka, babu wanda zan
aura cikinsu idan ma ba su nema min mafita ba ni
da kaina zan nemawa kaina tunda na zo gidan nan
ba zan koma ba har sai sun auran da su ga wadanda
suke son su saboda idan na zauna a cikinsu zan
zamo matsala a cikin rayuwar yan uwana mata,
don haka zan yi nisa da rayuwarsu gaba daya.”
Haana kina da hankali kuwa kina nufin
gidanmu ki ka gudo na ba ki gurin buya ki jefa
iyayenki cikin damuwa da tashin hankali kina nufin
babu wanda ya san kin taho?
“Eh, babu wanda ya san na zo nan in ban da
Malam Habu kuma ya yi min alkawarin ba zai
fadawa kowa inda nake ba. Ki ke maganar zan sa
su tashin hankali ai. nima sun sani an fada musu ga
wanda nake so suka ki.”
Cikin daga murya ta ce, “Haana ki nutsu ki san
me ki ke fada iyayenki ne ni dai ba zan hana ki
zama ba, amma sai kin sanar mu su ko mu jira
Mama ta dawo a fada mata mu ji me za ta ce.”
Zahra idan kin hana nima ba laifinki ba ne
tunda ni na kawo kaina.”
“Yi hakuri kawata kada ki sauya min fahimta
ki zauna duk iya lokacin da ki ka so shi ke nan
ranki ya yi fari?”
Hararar ta ta yi ta kifa kanta kan gado ta juya
mata baya haka ta shiga surutun ta ta ki tanka mata.
Can kuwa a daki Fadeelah ta gaji da jira har ta
fara kosawa ta shiga kai komo cikin dakin zuwa
can ta yanke shawarar kiranta a waya don ta ji ya
suka yi da shi ta yi nasara ko tana nan suna sa’insa
saboda ta san halinsa, amma tunawa da ta yi cewa
Haana za ta zage ta fada masa irin halin da take
ciki tunda ta fada masa bai yarda ba.
Tana kiran wayar ta ji ringing dinta a cikin daki
tana dubawa ta ga wayar ta na caji ta yatsuna fuska
ta buga wayar a tafin hannunta ta ce, “Oh! Ashe ga
wayar ma nan.” Ta yi tsaki dole ta fito daga dakin
ta nufi cikin ‘yan uwanta ko ta ji ‘yar sa’idar
zullumin da take ciki.
Har aka fara kiran sallar Magariba Fadeela ba
ta ga Haana ta dawo ba, nan ta fara jin damuwarta
na karuwa har Granny ta fara fuskantar ta sai ta ce
mata.
“Wai ina’yar uwar taki ta shiga ne har yanzu ba
ta dawo ba, ko ba tare ku ka shigo ba?”
Granny ban san inda ta tsaya ba, amma daina
fi tunanin wani abu ne ya rike ta, don ba ta ce min
za ta dade haka ba, wayarta ma a gida ta bar ta
gidan su Haaya ta ce min za ta je ta dawo.”
Yanzu watakila ki ganta tunda ga shi an fara
kiran sallah.”
Mikewa ta yi ta ce, ‘Granny bari kawai na tafi
ma hadu a hanya ko idan ta dawo ma yi waya.”
“To babu laifi ki gaida min da su Hajiya ki ce
goben zan shigo.”
“To za su ji.” Ta fada a gaggauce ta mike ta
fice.
Tana tafe tana cewa kai ita kuwa Haana ina ta
tsaya idan ba ta yi nasara ba, ta dawo min idan ya
ki ta nan ai ga Mama nan wallahi sai na fada mata
irin wulakancin da yake min don ba zan iya hakura
da shi ba. bari kawai na kira Haaya ta hada ni da ita
a waya kawai ta fito mu hadu ta bar ni da shi.
Bugu daya wayar ta yi lokacin Haaya suna
zaune ita da su M.J da Abdul suna hira don yau
komai cikin karfin gwiwa yake yinsa tunda ya
gamu da Haana ta gane cewa shi ma dan uwanta ne
ya kuma fada mata abin da yake ransa.
Daga wayar ta yi ta ambaci sunan Fadeelah, da
sauri M.J ya kalle ta ya ji ta ce, “Gaskiya ni dai ban
ga Haana a gidan nan ba haka ta ce miki za ta zo
ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Kafin ta ji abin da za ta fada mata yayi saurin
warce wayar a hannunta ya ce, “Eh, ta zo ta fadi
aikenki ta tafí fada miki, cewar ga sakon da na bata
Dam! Ta ji gabanta ya fadi jin muryar Yaya
Muhammad cikin rashin zato. Cikin in’ina ta ce,
Ba ta zo ba ita na biyo na ji ko tana ina.”
“Well, ta fada mini sakon ki sai dai na ji na ce
ta zo ta fada miki cewa ita nake so ba ke ba, ita ce
Raihanatun da na taba fada miki ina da wadda nake
so, Haana na san kunyarki take ji yasa ta kasa fada
miki to ni ga shi na fada miki fatan za ki sakar min mara na yi fitsari ki huta lafiya.” Yana gama
fadin haka ya kashe wayar ya mikaa Haaya abar ta.
Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar Haaya
da Abdul jin furucin da ya yi shin ina Yaya
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG