ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


No.1 hausa novels, site all over the world with more than 5000 books uploaded, the site was found on 2014 by A/I/S
All our books are free, we do not charge for uploading , we upload novels, daily and over 400+ chapters montly.


Mun tsaya 

warce wayar a hannunta ya ce, “Eh, ta zo ta fadi
aikenki ta tafí fada miki, cewar ga sakon da na bata
Dam! Ta ji gabanta ya fadi jin muryar Yaya
Muhammad cikin rashin zato. Cikin in’ina ta ce,
Ba ta zo ba ita na biyo na ji ko tana ina.”
“Well, ta fada mini sakon ki sai dai na ji na ce
ta zo ta fada miki cewa ita nake so ba ke ba, ita ce
Raihanatun da na taba fada miki ina da wadda nake
so, Haana na san kunyarki take ji yasa ta kasa fada
miki to ni ga shi na fada miki fatan za ki sakar min mara na yi fitsari ki huta lafiya.” Yana gama
fadin haka ya kashe wayar ya mikaa Haaya abar ta.
Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar Haaya
da Abdul jin furucin da ya yi shin ina Yaya

Muhamnmad ya taba ganin Haana da zai ce ita ce
wadda yake so?
Tambayar da ta zo zuciyar Haaya ta kuma jin
tsoron yi masa ita don yanzu zai hauta da masifa
duk irin kulawa da kaunar da yake mata bai ba ta
fuska ta shiga harkarsa ba. Abdul ne kadai yake da
wannan right din cikin kannansa.
Tsananin rudanin da Fadeela ta shiga har sai da
ta yi namijin kokarin daidaita numfashinta, sannan
ta ji ya dawo kafin ta samu damar masa tambaya
har ya kashe wayar. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Wayyo na shiga uku me ke shirin faruwa da ni
ba dai Haana amanata za ta ci ba, na gama tsara
mata yadda yake ta je ta gan shi maimakon ta fada
masa abin da na ce da ita sai ta bari ya ce yana
sonta ita kuma ta kasa cewa tana kin sa?
Karya ki ke Haana ba ki isa ki ha’ince ni ba
kun yi kadan ke da Yaya Muhammad ku hada baki
ku cuce ni a ina ya san ki zai fake da cewa ke din
ce, kawai dai mai irin sunanki ya fada min amma
ban yarda ke ba ce, sunan ya bi don ya cuce ni
wallahi to ba ku isa ba, duk ku biyun. Da wannan
sambatun ta shige gida cikin tashin hankali ta rufe
kanta tana kuka tana neman mafita, domin ba za ta
yarda a yaudare ta ba, ita ba yarinya ba ce.
Zahra ce da Mamanta suka saka Haana a
gaba a kan ta daina kukan da take, amma ta ki
suka rasa abin da yake musu dadi.


Hajiya Hadiza tace ‘Raihanatu kuka ba zai
zamo miki mafitar matsalar da ki ke ciki ba addu’a
na yarda na kuma goyi bayankı wannan damuwar
da ki ke ciki duk a kan son ganin farin cikin ‘yan
uwanki ne, amma ba ta haka ya kamata ki biyo ba
dole sai manya sun shiga maganar sannan a san
yadda za a magance matsalar barin ki gida ba shi
ne mafita ba, ba dan ki đaga musu hankali babu
abin da za ki yi.”
Cikin kuka ta ce, “‘Mama hakan da na yi shi zai
sa su yi min abin da nake so saboda kowa ya yi
banza da ni baya nuna damuwarsa cikin halin da
nake cikin tun kafin abin da ya faru yau ya faru to
ta ina za su saurare ni, shi yasa na yi haka Mama
kawai ki bar su kada ki fada musu inda nake ki bar
su su ji irin damuwar da nake ciki.”
“Ban yarda ba Raihana ni uwa ce ina jin irin
abin da suke ji idan nima haka ta faru ba ni da
kwanciyar hankali na san duk inda suke yanzu
hankalinsu a tashe yake suna zuba ido su ga ta ina
za ki dawo idan sunsan inda ki ke hankainsu zai
kwanta hakan da ki ka yi musu sa yarda su yi miki
abin da ki ke so. Www.bankinhausanovels.com.ng
Amma ban so a ce yadda kowa yake ganin
hankalinki a zo ana ganin ba ki kyauta ba.”
“Mama, Abba yana da zafi shi ne ya fara nuna
ba zai min abin da nake so ba, sannan Granny da
Ammi suka goyi bayansa.
“Ki kwantar da hankalinki wannan karon zai
miki abin da ki ke so bari na dauki wayata na kira
Hajiya Aisha na fada mata ki na nan amma ba za ki
koma ba sai kin huce tunda kina cikin damuwa.”
Jin an ce ba za ta koma ba yasa ta ji dadi har sai
da yanayinta na damuwa ya diawo fari ciki domin
murmushi ta yi.
Hankalin kowa ya tashi cikin estate din Naseer
Danfillo na rashin ganin Haana tun goshin
Magariba har ga shi tara saura babu gidan da ba a
je nemanta ba, babba da yaro kowa ya shiga
zullumi idan ka cire Fadeelah da ta dauki abin da
cewa rainin hankali ne saboda kada a dora mata
laifi shi ne ta je ta boye kanta daga baya idan kowa
ya ji sai ta fito. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ita ko a jikinta ta san babu wani batan da ta yi,
watakila ma tana cikin estate din nan sun hada baki
da wasu saboda ita mai wayon tsiya ce.
Tunda aka tambaye ta ta ce ba ta ganta ba ta
koma daki ta kira Mama Bara ta gaya mata duk
abin da yake faruwa ta ce rainin wayo ne kawai da
iya shirya deal da farko da Mama Bara ba ta yarda
ba da ta shiga tsara mata magana sai ta bi bayan
yarta ta ce bar ni da su ita da Mahammadun ni za
su kawowa iya shege iyayensu ba su isa ba bare
masu idan ta fito daga inda ta je buyan ki kira ni ki
fada min ba zan bata lokaci ba zan zo Kano din na
sabar musu kuma ba zan dawo ba sai an saka ranar
auranku tunda ke kin gama karatu shi kuma aiki
yake sauran a yi nasu idan sun gama ba za a kawo
min shashancin banza ba.
Cikin jin dadi ta ce, “Thank you Mom shi ya sa
nake son ki ke kadai ce mai son farin cikina, kin gan
ni cikin daki babu inda na fita.”
Yawwa zauna abin ki su da ta raina su su fita
neman su yarinyar kawai, bari na je wajen
Abbanku na ji motsin shigowarsa.
To Mom, na gode sai kin ji ni. Ta kashe
wayar ta shiga murna abin ta.
Rauda ta gama rudewa haka ta shiga kiran
kawayen Haana na school cikin waya don kada su
gane su na cikin matsala duk wanda ta san kusa
take da su ta buga sun ce ba ta zo ba.
Wayar Zahra a kashe sun kira ta ki shiga, a she
Haana ce ta kashe ganin Zahra da farko tana son
kira gida ta fada.
Iyaye maza har an fara neman kiran jami’an
tsaro a fada suna tsaye sai ga kiran Haj. Hadiza ya
shigo wayar Ammi.
Da sauri ta ce, °Ku jira ga wayar mahaifiyar
kawarta mu ji me za ta ce
Cikin nutsuwa ta amsa suka gaisa ta ce, “Haj.
Aisha dama bugowa na yi na sanar da ke cewa
Raihanatu tana gidana wai ta yi muku yaji.”
Godiya ta yi wa Allah duk wanda yake gurin
sai da ya yi ajiyar zuciya, suma suka godewa
Allah,, nan fa ta fara fada cikin daga murya.
“A’a Haj. Aisha ba fada za ki yi ba ki godewa
Allah da ta yi hankali ta zo nan gidan maganar
gaskiya Raihanatu tana cikin damuwa mai tarin
yawa kuma bai kamata ku yi biris da ita ba, kamata
ya yi ku duba halin da take ciki.”
Haj. Hadiza ki kyale ni da ita ba ta jin
magana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Idan zai yiwu Haj. Aisha ki zo gidan nan babu
yadda bamu yi da ita ba ta ki ta yarda ta taho ki zo
ko kuma a bari gobe na kawo ta idan ta huce,
amma maganar gaskiya damuwar da take ciki ta
wuce yadda ku ke tunani.”
Haj. Hadiza ki bar ta ta kwana din goben ki
kawo ta.’ Ta fada cikin fushi.
Aa Haj. Aisha ba dai har yanzu fushi ki ke da
ita ba?”
Abba ne ya karbi wayar ya yi sallama suka
gaisa ta yi masa dan bayani na a duba matsalar.
Cikin gaggautawa ya ce, ‘Hajiya ku jira mu ga
mu nan Zuwa yanzu.
Abba ya yi wa kowa bayanin inda take hade da
cewa yanzu za su je su dawo da ita. Kowa
hankalinsa ya kwanta sai dai ana mamakin me ye
ya faru da yarinya mai hankalikamar Raihanatu ta
yi haka.
Da yake ban da gida biyu babu wanda ya san
matsalar da ake ciki daga gidansu sai gidan su
Rauda sun rufe abin ne ganin kamar za su iya
magance matsalar tunda abin a gidansu yake.
Haana ta saki ranta jin Maman Zahra ta fada
mata cewa ta sanar da gidansu, ta kuma sanar da ita
ba karamin daga musu hankali ta yi ba sai dai ta
Boye zuwan mahaifan nata.
Sosai ta sake kamar ba ta da wata damuwa da
yake haka take da jarumta dukkan tsananin da take
ciki ta kan yi kokarin danne zuciyarta matukar ba
ta kusa da abin da take gani shi ne sila.
Har ta karbi magani ta sha saboda sarawar da
kanta yake mata don ta samu damar yin barci.
Fa’iza ce ta yi sallanma ta shigo kanwar Zahra
ce, suka amsa. Ta ec, *Aunty Haana wai Mama ta
ce ki zo ita da Abbanmu tana son ganin ki.
Da kamar za ta ce na sha magani kwanciya zan
yi sai ta ga hakan bai kyautu ba, kawai sai ta ce,
To ga ni nan, Zahra mu je ki raka ni kunyar Abba
nakeJi.
“Ina ruwana ki je ke ki ka jawo fada kuwa sai
kin sha shi kin san Abba shi ma ba daga nan ba.”
Don Allah mu je.”
Wallahi babu inda zani yadda na kwanta kuma
insha Allahu sai gobe.”
Tsaki ta yi mata ta fice abin ta da yake’yar
gida ce ta san ko’ina a cikin gidan kai tsaye ta nufi
falon.
Tana yin sallama ciki suna yin ido hudu da
Abbanta da Ammi ji ta yi gabanta ya fadi kamar ta
koma da gudu. Amma yadda ta karanci fuskarsu ta
gansu cikin alhini da nuna tausayi a gare ta sai ta ji
dan dama-dama.
Gefe guda ta rakube ta gaida su tunanin ta ba za
su amsa ba sai ta ji duk sun amsa cikin raunin
murya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Abban Zahra ya ce, “Raihanatu dauko
takalmanki ki zo ki wuce ku tafi gida.
Kuka ta fara, ta ce “Abba don Allah ya za kuyi
min haka ni fa na ce ba zan koma ba.
Cikin taushin murya Alh. Mustapha ya ce,
Ammi na har laifinmu yayi girman da za ki guje
mu, haba Ammina yaushe ki ka canza hali kin san
damuwar da ki ka samu shiga da ba mu gan ki ba?
Cikin kuka ta ce ‘Abba ba ku ba ne ku ka yi
min laifi ba “yan uwana ne suka yi min sabada son
kansu ni kuma idan har ba su janye ba ba zan iya
rayuwa a inda suke ba suna son raba ni da ‘yan
uwana mata.
Ki share hawayen ki Ammi yanzu muka samu
duk labarin abin da yake faruwa ki kwantar da
hankalinki muna tare da ke dari bisa dari ni da
Ammin ki har da Granny za mu yi mata bayani
Idan muka koma gida insha Allahu za mu duba
matsalar ki.
Mun fuskance ki duk abin da ki ke yi kina yin
sa ne saboda zumunci da soyayya ta tsakani da
Allah ke da “yan uwanki, ki tashi mu tafi daga yau
babu abin da za mu bari ya dame ki bare har ki yi
shirin tafiya ki bar mu je ki fito mu tafi.”
Murmushi ta yi mai hade da kuka ta ce, ‘Abba
za ku yarda ku yi min abin da na ke so’? Abba za ku
yarda ya Abba ya auri HAaya, Mr. Sameer ya auri
Rauda na, Fadeelah kuma ta auri Mal. M.J a yanzu
duk cikin su babu wanda nake jin kuunya kamar
Fadeelah yadda ta dauki yarda ta ba ni.
Amma da na je gurin Malam M.J ya ce wai ba
ita yake so ba ni zai aura.
“Ya isa haka bayanin duk Mamanku ta yi mana
bayanin komai tun haduwarku da shi a makaranta,
mun jima a cikin gidan nan kafin a aika a kirawo ki
ki je ki zo mu tafi insha Allahu mun daina barin ki
da damuwa, tunda zuciyarki mai kyau ce komai za
ki ki na duba zumuncin Allah, Allah kuma zai duba
ki tunda kina gudun rabuwar zumuncinku.”
Har bakin mota iyayen Zahra suka rako su suka
shiga mota suna saka mata albarka, yadda ta jajirce
a kan zumunci daga karshe suka shiga tsokanarta
da dariya da raha aka rabu. Ita da Zahra suka shiga
dagawa juna hannu.
Tunda Abba ya fara bayani Granny ta yi shiru
tana jin abin da ke faruwa kamar almara ta
tausayawa takwararta jin irin halin da take ciki duk
ta yi hakan ne don sadaukar da farin cikin ta ga
yan uwanta.
Granny ta ce, “To kai yanzu me ka ke gani abin
yi maganar gaskiya dole mu san me za a yi ba za
mu zo, mu lodawa yarinyar nan abin da ya fi
karfinta ba, dole ka bayyanawa ‘yan uwanka
wannan halin da ake ciki, domin mu samar mata
mafíta.”
Haka ne Umma tun muna hanya nake tunanin
haka, ni yanzu ban da wani abin yi illa yi wa
Ammina abin da take so tunda na riga da na gane
me take nufi ba ta son zumunci ya baci, don haka
nima zan iyakar kokarina na ga na samar mata
farin ciki na raba ta da tashin hankalin da damuwar
da na gani a fuskarta, wannan shi ne abin da zan
ya yi mata ke nan.”
“Ina bayan ka na kuma yarda da duk abin da ka
ce ina alfalhari da kai da irin tarbiyyar da ka ba wa
Raihana ta biyo irin zuciyarka na son sadaukar da
farin cikinta ga ‘yan uwanta kamar yadda kai ma
ka ke yi a kan naka “yan uwana Allah ya yi muku
albarka baki dayanku ku da zuri’ar ku.
Kullum burina, son ganin farin cikinku da na
iyalinku Allah ya tabbatar da zumunci da kaunar
juna a cikin ZURI’A din nan me zai sa ka isar da
sako ku zauna ku san yadda za ku magance
wannan matsalar kada ta taba zumuncinmu.
Insha Allah Umma za mu yi bakin kokarinmu
kuma da yardar Allah komai zai zo cikin sauki.”
“To Allah ya sa haka. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Amcen.
A can dakin Haana kuwa ita da Ammi ne tana
ta rusa mata kuka akan cewa ta daure ta sa Abba ya
yi mata abin da take so domin kada su yi mata dole
babu wanda za ta iya aura cikinsu in dai ana son
ganin nata farin cikin.
Cikin tausayawa ta ce, ‘Ki kwantar da hankalin
ki insha Allahu, Allah zai ba mu mafíta cikin
yardar Sa.”
***
Tunda M.J ya samu labarin batan Haana ya
shiga damuwa, sai bayan ta dawo ne ya nemi
labarin jin dalilin haka. Haaya ce ta fada masa
dukkan abin da yake faruwa bayan ta ji cewa shi
ma son ta yake ta fada masa halin da take ciki ita
ma, shi kansa ya sha mamaki jin ashe Abba shi ne
Mustapha da kanwarsa take mutukar so, ashe ita
ma dan uwanta take so ba ta sani ba.
Nan take ya kwashe labarinsa da Haana ya fada
mata har da yadda suka yi da Sameer ya shigo
Cikin rayuwarta, don hada ZURI’A guri DAYA,
komai bai boye mata ba. Ta jinjina al’amarin sai dai
ba ta dorawa Mr. Sameer laifi ba tunda lokacin da
ya turo shi bai gaya masa dalilin son taimaka mata
da yake son yi ba, bai kuma fada masa cewa so
yake ya aure ta ba da watakila ya bar tunanin cewa
zai aure ta.
“Yaya Muhammad dole ne Haana ta shiga cikin
tashin hankali da damuwa hakika tana son ka sona
SOsai, ta sha ba mu labarin yadda suka rabu da
malaminta a lokacin tana kishirwar son ka sai dai
ko kadan ban taba kawo cewa kai ne ba.
Hakika ta so Yaya Sameer amma tunda ta gane
cewa Rauda na son shi ta kuma gano cewa Ya
Abba ya sadaukar da son da yake mata don ta auri
Sameer bai duba abin da “yar uwarsa da suke ciki
daya da shi ba samun wannan labarin ta birkicewa
Yaya Smcer ta cee ba zata aure shi ba, har yanzu a
haka akc.
Tunda M.J ya samu labarin batan Haana ya
shiga damuwa, sai bayan la dawo ne ya ncmi
labarin jin dalilin haka. Haaya ce ta fada masa
dukkan abin da yake faruwa bayan ta ji cewa his
ma son ta yake ta fada masa halin da take ciki ita
ma, shi kansa ya sha mamaki jin ashe Abba shi ne
Mustapha da kanwarsa take mutukar so, ashe ita
ma dan uwanta take so ba ta sani ba.
Nan take ya kwashe labarinsa da Haana ya fada
mata har da yadda suka yi da Sameer ya shigo
Cikin rayuwarta, don hada ZURI’A guri DAYA,
kmai bai 6oye mata ba. Ta jinjina al’amarin sai dai
ba ta dorawa Mr. Sameer laifi ba tunda lokacin da
ya turo shi bai gaya masa dalilin son taimaka mata
da yake son yi ba, bai kuma fada masa cewa so
yake ya aure ta ba da watakila ya bar tunanin cewa
zai aure ta. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Yaya Muhammad dole ne Haana ta shiga cikin
tashin hankali da damuwa hakika tana son ka sona
SOsai, ta sha ba mu labarin yadda suka rabu da
malaminta a lokacin tana kishirwar son ka sai dai
ko kadan ban taba kawo cewa kai ne ba.
Hakika ta so Yaya Samcer amma tudna ta gane
cewa Rauda na son shi ta kuma gano cewa Ya
Abba ya sadaukar da son da yake mata don ta auri
Sameer bai duba abin da “yar ywarsa da suke ciki
daya da shi ba samun wannan labarin ta birkicewa
Yaya Smcer ta cee ba za la aure his ba, har yanzu a
haka ake.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

No.1 hausa novels, site all over the world with more than 5000 books uploaded, the site was found on 2014 by A/I/S
All our books are free, we do not charge for uploading , we upload novels, daily and over 400+ chapters montly.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE