ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Yaya Muhammad dole ne Haana ta shiga cikin
tashin hankali da damuwa hakika tana son ka sona
SOsai, ta sha ba mu labarin yadda suka rabu da
malaminta a lokacin tana kishirwar son ka sai dai
ko kadan ban taba kawo cewa kai ne ba.
Hakika ta so Yaya Samcer amma tudna ta gane
cewa Rauda na son shi ta kuma gano cewa Ya
Abba ya sadaukar da son da yake mata don ta auri
Sameer bai duba abin da “yar ywarsa da suke ciki
daya da shi ba samun wannan labarin ta birkicewa
Yaya Smcer ta cee ba za la aure his ba, har yanzu a
haka ake.

Da farko Ya Abba take mutukar so, amma da ta ga bai taba ba ta kulawar so ba sai ta ‘yan uwantaka dole ta hakura ta ki fito da maitarta sai kuma ga shi kai Allah ya kawo ka cikin rayuwarta ta fara son ka lokaci daya kuma ka yi mata nisa cikin duniyarta.

Don haka sai yanzu ka dawo cikin rayuwarta da duniyarta bayan aminci da shakuwarta da Fadeelah sai kuma ta gane kai ne wanda FAdeelah din take so dole ne ta shiga damuwa saboda akwai ydda da shakuwa tsakaninta da Fadeelah. Ka san ba za ta taba bari ta saka Fadeelah cikin damuwa ba, kamar yadda nima ta yi min haka. Yaya Muhammad, Haana tana da kirki tana son ‘yan uwanta da yawa tana son ta ga kowa cikin farin ciki ita ta rasa nata, saboda haka ne ta yi fushi da ni don ta ce na auri Ya Abba na ce mata na ki.

Www.bankinhausanovels.com.ng

Please, Yaya Muhammad ku dauka ku ukun nan ku sata farin ciki ba wai duk ku taru ku jefa ta cikin damuwa ba, Haana is a good girl, please Yaya Muhammad do something good to her.

Shiru ya yi na tsawon lokaci yana sauraron Kanwarsa ko kadan bai katse ta ba har sai da ya ga ta sauka, ajiyar zuciya ya yi ya ce.

“Haaya na ji dadin wannan bayanin naki kuma na gamsu. Abba da Sameer ba su da matsala saboda kowa ya samu mata. Abba ya same ki, Sameer kuma ya samu Rauda, ni kuma na samu Raihanah, kin ga ai abu ya yi daidai.Zan zauna da su za mu yi masalaha domin kaf cikin su babu wanda zan iya bar wa Raihanah ya aura, saboda na fi su sonta na fi su sanin darajarta a rayuwa gaba daya, ban taba son wata mace a rayuwata ba ko kadan ko da sau daya a rayuwata ba idan ba Raihanah ba, daidai da dakika ko na sakwan daya ban taba bawa zuciyata dama ta yi tunanin wata ba idan ba Raihanah ba, ni kadai na san irin halin da na shiga lokacin da na baro Nigeria tashin hankali na da tunanina shi ne halin da za ta shiga idan ta samu labarin na tafi.

In fact, dai Haaya ni kadai ne na dace da rayuwar Raihanah, ba kowa ba babu wanda ya isa na bar shi ya aure ta. Zan yi duk yadda zan yi ke da RAuda ku samu abin da ku ke so don nima na wa burin ya cika.”

“Yaya Muhammad na ji mu kadai ka ambata ban ji ka sauko Fadeelah a cikinmu ba. Www.bankinhausanovels.com.ng

“Look! Kada ki kara yi min maganar FAdeelah ba ni da damuwa da ita, ita ce ke son nemawa kanta damuwa na fada mata ba tun yanzu ba a kan me zan kuma tsaya ina saka kaina damuwa a kanta, sam babu ruwana idan za ta tsaya ta yi wa kanta fada to idan ta ki ita ta jiyo tunda ni dai ga wacce nake so ba ni da matsala gobe zan je na ga Raihanah mu yi magana daita ta fahimtar juna ki saki ranki kada ki sa damuwa ko daya.”

Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba, domin ta san halin zafinsa tunda ya ce mata haka yin shirun shi ne zai fi mata alheri kada ya boran ce mata.Sanye yake cikin wani farin tsadadden boeyl mai shara-shara kansa ya sha wata hula Tangaran, ya yi matukar kyau sai wani kamshi yake. A falo ya iske Haaya da Abdul suna ganinsa suka shiga yi masa dariya wai ya yi kyau sosai sai ina irin wannan typical Hause Dress din fa.
Murmushi ya yi ya ce, ‘Sai gurin Gimbiyata RAihanah zan je mu yi magana da ita ta fahimtar juna jiya tana cikin rudani da mamakin ganina, na san yanzu tunani da nutsuwar sun zo jikinta.”

Cikin wasa Abdul ya ce, “Ko in zo rakiya ne?” “A’a zauna ka huta, sai dai ina son ku taya ni addu’ar samun nasara a gurinta.

Tare suka ce, ‘Allah ya bada sa’a.” ‘Ameen. Ya ce sannan yasa kansa gaba ya fice.

Kamshin turaren da ta ji tun daga kicin da take hada abin da za ta karya, kasancewar yau ba za ta shiga makaranta da wuri ba. Hakan ya hana ta nutsuwa kukunsu ta sa ya ci gaba da hada mata abin da za ta ci, ta fito ta ga kamshin nan daga ina yake.
Cak! Ta tsaya ta ji kafarta ta rike kamar ta koma da baya, amma ina ya riga ya ganta, ga shi ya wani tsare ta da idanu wanda hakan ya ja hankalin Granny kai duba ga abin da yake kallo.
Ta ce, ‘Ka ganta ne kanwar taka? Raihanah zo
ki gaisa da yayanki.” Da kamar ta ce a’a, amma wani irin kwarjini da ta gani dauke a fuskarsa ta ji ba za ta iya furta ko da kalma daya ba, kasa ta yi da idanunta ta zogefen da Granny take ta dan duka ta ce, “Ina kwana Malam.”
Murmushi ya yi ya ce, “Ni yanzu ba malaminki ba ne Yayanki ne zan fi so ki dinga ce min Yaya maimakon malam din.”
“Ka yi hakuri da shi na saba fadin hakan zai fi min sauki.”
“Ok, babu laifi idan hakan ya fi miki sauki.” Yana gama fadin haka ta mike za ta koma yace, ‘Au! Ya za ki tafi kuma ba ki san gurin ki na zoba. Www.bankinhausanovels.com.ng
“A’a, ni ba gurina ba, please Malam M.J ka bar ni kada ka zo ka kawo min wata damuwa kuma.””Raihanah kada ki yi masa musu tunda ya ce gurinki ya zo ki tsaya ki ji dame ya zo da shi, ai baka iya yanke wa mutum hukunci ba ka tsaya ka ji UZIRInsa ba.” Cewar Granny.
Damuwa ce ta bayyana a fuskarta za ta yi magana Granny ta ce ga guri zauna ni bari na tafi. Ba ta yi musu ba ta samu guri ta zauna sai dai fuskarta babu wani annuri.
Bayan Granny ta bar gurin tsit suka yi babu wanda ya ce wani abu. Can ya numfasa ya ce.
“Raihanah na takura miki ko?” “Eh!” Ta cikin rashin sakin fuska.
Murmushi ya yi na nishadi ya ce, “Well, infact dai na ji duk abin da yake faruwa yanzu haka Granny ta sake min bayani na kuma gamsu sai dai bana jin zan iya hakura da ke kamar yadda Granny take so na yi, sai dai su su hakura domin don ni aka
halicce ki baki da mijin aure sai ni.” “Wa ya fada maka haka? Ni ba zan aure ka ba kai ba kai kadai ba ma dukkanku babu wanda zan saurara bare har na yarda na aure shi.”Cikin KUNAR ZUCI M.J ya cire kansa idanunsa sun kada sun yi jajir da su kamar jan
gauta ya daga hannunsa cikin tsawa ya ce.”Ya ishe ki haka Raihanah bana son sake jin kin fada min haka tamkar kin zuba min garwashi ne a cikin zuciyata, don haka ki nutsu ki san me za fada min.”Cikin wani irin sauti mai tsuma rai ta ce, “Dole ne ka ji Malam M.J, tunda kai ka so hakan idan ba haka ba me yasa za ku zo ku daga min hankali duk cikin ku kowa ya rufe idanu ya ce ni yake so, idan ban da Ya Abba da ya sadaukar da son da yake min ga wani….Nan kuka ya samu cin karfinta dole ta ci gaba da yin sa.Ji ya yi wata irin sabuwar damuwa ta zo ta lullube shi hankalinsa ya kara tashi ganin hawaye a fuskar RAihanah dinsa, kuma domin shi take zubar da shi. Ji ya yi kamar ya je ya rungume ta ya rarrashe ta, ta daina wannan kuka. Nan da nan ya ji ya soma rasa nutsuwarsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
A rude ya shiga cewa, “Calm down Raihanah ba zuwa na yi don na daga miki hankali ba, ki yi shiru ki daina ku ka kada Granny ta dawo ta gan ki kina kuka ta ce min ban kyauta mata ba, domin ce min ta yi na rarrashe ki.”
‘Dole na yi kuka mana tunda kun janyo min yin sa na jima ina addu’ar Allah ya dawo min da kai cikin rayuwata da na san haka za ka dawo min cike da tarin matsala da ban yi addu’ar ba.
Me yasa dukkan ku ku ka dage sai ni, kowa kai kowa sona yake, me sauran suka yi da ba kwa son su? Da me na fi su da zaku ce ni ku ke so? Idan har za ku so ni su ma za ku so su tunda ba mu da bambanci da su.
Don haka na roke ka da ka yi nisa da rayuwata ka je ka auri Fadeelah idan ka yi min haka zan yarda da cewa kana sona. Tsawa ya daka mata har sai da ta razana, amma
haka ta dake ta ci gaba da kukanta, ya ce.Ya ishe ki haka Raihanah kada ki kara cewa
na auri Fadeelah, ba zan aure ta ba, domin ban taba
jin zuciyata zan rayu da ita ba, idan ba ke ba
mutukar ban aure ki ba ba zan aure kowacce mace ba gara na mutu ban yi aure ba.
Tun da na taso a rayuwata ni da mahaifiyata mahaifina bai taba yi mana abin da muke so ba, hakan yasa nima a raina na saka ba zan yi masa abin da yake so ba, dalilin hakan yasa na shiga rayuwarki, tun ban san ya zan gan ki ba bayan kin girma ina ji ina miki wani irin so ina iya tuno loakcin da ki ke karama da wannan fuskar taki, shi na dinga kissimawa a raina har kawo lokacin da na zo cikin rayuwarki. Na yi hakan ne don babu abin
da zanyi na bakanta ran mahaifina irin na shigo rayuwarku na saba da ku har sai na aure ki na daidaita zuri’a ta wanda na san ba shi da wannan burin.
Saboda a duniyar nan a wancan lokacin ba shi da mutumin da yake ki sama da Abba Mustapha yana ganin kamar shi ne sanadin mutuwar Yaya Hameed da wannan tunanin na gina sonki mai tsanani a cikin zuciyata, wanda ban taba yi wa wata amce irin sa ba. Na tafi na bar ki lokacin da muka fara fuskantar juna da shakuwa da sabo, na tafi ne da niyar idan na je na gama jiyar Mommy na dawo, amma abubuwa suka cakude min ga ciwon Mommy ga gurin aiki sun sani gaba ga shi Daddy bai damu da ciwon Mommy ba.
Rudani da tashin hankalin da ciwon Mommy ya sani wanda ba mu yi tunanin za ta tashi ba hakan yasa ki ka ji ni shiru har Allah ya ba ta lafiya, sannan na nutsu.
Rahanah bari na fada miki a takaice ba zan iya hakura da ke ba, ko me za a yi min saboda abu daya da za ki fada min na ji haushin ki shi ne ki ce min na auri Fadeelah.”
“Malam M.J ka san kuwa me ka ke fada min game da Fadeelah kai da kanka fa ka turo min text da cewa kana ba ni hakuri na rashin dawowarka rayuwata, na yi na yi maka fatan alheri za ka zo Nigeria, domin auran ‘yar uwarka Fadeelah ka manta wannan furucin da ka yi min shi ne yanzu don ka jefa ni cikin damuwa za ka zo daga baya ka ce min haka, ba zai yiwu ba, tunda na hakura da kai tun farko babu yadda zan yi yanzu na ce zan aure ka, saboda hujjar da ka ba ni kana son ta ka kuma yarda cewa za ka aure ta sai yanzu ka zo min da wannan maganar ba zan yarda ba.”
“Raihanah tsaya me ki ke son fada min, waye ya yi miki text sam ba ni ba ne, ba kuma wannan text din na yi miki ba, ko kadan ba irin wannan na turo miki ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ji ta yi ya raina mata hankali ta ce, “Ina da hujja ta domin ban goge text din ba bari na nuna maka wanda shine zai nuna maka cewa ba karya na yi maka ba.” Da yake wayarta na tare da ita.
Duk abin da suke a gaban Ya Abba suke duk ya ji abin da suke fada ya ji tausayin Haana dinsa, domin har yanzu tausayinta yake ji, domin ta fi su shiga cikin tashin hankali saboda duk a kanta abin ya fi karewa, dole ne ya yi wani abu ya taimaka mata domin ta samu saukin tashin hankalin da take ciki ba zai iya barinta cikin wannan tension din da take ciki ba, abubuwan sun yi mata yawa, don ma
ita mai juriya ce. “Ga shi duba ba number dinka ba ce ka duba ka gani mana, kana tunanin zan maka karya ne.”
Mika masa wayar ta yi ya shiga dubawa, cikin nutsuwa ya duba abin da ta ke tuhumar da take masa, murmushi ya yi, ya mika mata wayar ya ce.
“Karbi wayarki ni ba ni na turo miki wannan ba, duba number din ta Nigeria ce, sannan ki duba details, date da time za ki gane ba ni ba ne, duka duka yau kwana na nawa da zuwa Nigeria din bare na turo miki don ki gaskata ni ki dubo min text din da na turo miki na farko ki hada da wannan za ki yarda da abin da na fada miki.
Mamaki ya kamata duk da ba ta cikin nutsuwarta da dadin zuciya haka ta jure da yake ita mai juriya ce ta sake duba text din, sai ga wata number can kasa babu suna amma ba ta nan ba ce tana dubawa sai gashi.
Cika ta yi da mamaki ganin yadda mamaki ya bayyana a fuskarta da sauri ya karba ya duba, ya ce, “Kin yarda da ni ko kin yarda da abin da na fada miki? To koma ya aka yi an san da wannan text din sa aka yi editing suna na aka turo da wannan numbar din tunda ga shi wannan da suna na wannan ba suna na.
Raihanah zan tafi zan bar ki ki yi tunani da kanki za ki gano ya a kai hakan ya faru an yi hakan ne don a shiga tsakanina da ke, ki huta lafiya ba zan tsaya ina ganin ki cikin wannan damuwar a fuskarki ba dama na zo ne don na zo na fada miki gaskiyar abin da ke raina ki huta lafiya.”

Yana gama fada bai tsaya jin komai ba ya mike ya fice abinsa, zuciyarsa babu dadi. Kukan ta ci gaba da yi a gurin mai tsuma rai.

Ya Abba ne ya fito daga inda yake ya ce, “Haana ki yi shiru ki daina kukan nan na ji komai yadda ku ka yi da Muhammad na tsaya na ji komai. Ki yi shiru insha Allah komai ya zo karshe daga yau zan yi miki duk abin da ki ke so a sirye nake na yi miki ba zan tsaya ina ganin ki cikin wannan tashin hankalin ba, na yi miki alkawarin yi miki duk abin da ki ke so matukar zan daina ganin zubar hawayen ki da korar dukkan damuwar da nake gani a kan fuskar ki, na yi miki alkawarin kawo farin ciki cikin rayuwarki.”

Cire kai ta yi cikin kuka da damuwa ta ce, ‘Ya Abba da gaske ka ke idan na fada maka abin da nake so za ka yi min shi ko mene ne?”

“Eh, a shirye nake na yi miki alkawari ki fada min ko meye.

“Ya Abba ina son ka ce min ka yarda za ka auri Haaya idan ka yi min haka zan yafe maka dukkan laifin da ka yi min damuwar da kukan da ka sani zan yafe maka za mu dawo kamar da can yadda muke kamar wani abu bai taba shiga tsakanin mu ba a baya.”

“Haana zan yi miki hakan matukar za ki yi

farin ciki na dinga ganin farin ciki da dariya a

fuskarki.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Cikin farin ciki da dariyarta ta ce, “Ya Abba ka yi min alkawari?” “Na yi miki Haana.”

Dariya ta yi ta ce, “Na gode Ya Abbana daga yau ka dinga ganin farin ciki a fuska ta na kuma yafe maka duk abin da ka yi min na samu sauki yau cikin zuciyata nauyin da ta yi min na ji ta yi sauki na gode Ya Abbana na gode sosai.

Ina son yau ka je gurinta ku daidaita kan ku don haka Ya Abba ina son kamar yadda ka ke

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE