ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
gurina. Oya, go ahead ki fada min matsalarki ki saki ranki kada ki ji komai.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani irin farin ciki ya kama ta ta ji kamar ta rungume Abbansu don dadi, domin tarin gaskiyar da ta gani a kwayar idanunsa. Duk abin da yake ranta ta kwashe ta fada masa babu abin da ta rage daga karshe ta ce.
“Abba na roke ku da ku bar ni na samu wani a
waje na aura saboda bana son wani ya kara nuna min so cikin zuri’a idan na aure shi wanda ba su same ni ba su dauki tsana da gaba su dora masa. wannan shi ne abin da nake gudu. Dubanta ya yi cikin tausayi da yaba hankalinta
duk sai ya dinga ganin kamar marigayiya Azizah
ce a gabansa yake magana da ita, saboda sak suke
kamar an tsaga kara, kokari ya yi ya boye kwallar da ta so zubo masa.
Take ya ce, “Ammi Allah ya yi miki albarka yadda ki ke son faranta ran ‘yan uwanki Allah ya faranta miki, na yi miki alkawarin zan tsaya tsayin daka a kan al’amarinki kuma abin da ki ka ce haka za a yi cikin su babu wanda zai sake saki ki zubar da hawayenki.
Na yi miki alkawarin duk wanda ki ke so ki kawo shi gurina zan tsaya miki sai na ga kin aure shi in Allah ya yarda ki tashi ki je zan ga yayyanki zan musu magana cikin su duk wanda daga miki hankali ki zo ki fada mini kowaye zan yi maganinsa tashi ki je Allah ya yi miki albarka.”
Ji ta yi wani irin farin ciki ya kama ta ta shiga yi masa addu’a yana cewa babu komai.
Kwanan farin ciki ta yi, domin ji ta yi a cikin zuciyarta kamar an sauke mata dutse Dala da Gwauron Dutse. A daren ta kira Zahra ta fada mata irin halin da take ciki ta taya ta murna sai dai ta ce gaskiya ni dai da kin hakura kin auri Malam M.J domin cikin su shi na fi tausayi ba sai ya hada ku ke da Fadcelah din ba me ye a ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsaki ta yi ta ce, ‘Ba ki da hankali ki na son bata min rai ina cikin farin ciki ke Hajiya sai da safe. Ta katse wayar ba ta jira cewar ta ba.
Zaune suke su ukun don amsa kiran Abba Aminu. Sam babu wanda ya san dalilin kiran sai dai kowannensu yana zargin wani abu cikin zuciyarsa game da Haana.Gyaran murya ya yi bayan ya amsa gaisuwarsu ya ce, “Na gode Allah da ya ba ni damar hada ku ku dukkanku na san a ranku za ku yi tunanin me yasa na hada ku, na kira ku ne ba tare da kowa ya san na kira dayanku ba, sai yanzu da ku ka gan ku guri guda.
Dalilin da yasa na kira ku kuwa, na samu labarin gaba dayanku kuna son janyowa a kara samun sabani cikin zuri’a, amma insha Allahu babu abin da zai sake faruwa sai alheri ba za mu kuma barin makamancin abu mara dadi ya sake faruwa cikin zuri’armu ba da yardar Mai sama har karshen rayuwar jikokinmu ba ma fatan haka ta sake faruwa.
Gaba dayansu suka ce, ‘Allah ya amsa. Ya ce, ‘Yauwa wannan kenan, sai magana ta gaba. Kai Muhammad kai ne babba, sai kai Mustapha Karami, Sameer kai ne karami cikinsu, na ji duk abin da yake faruwa.
Muhammad abin da ka yi wa zumuncinmu Allah ya biya ka duk mun ji irin gudummawar da ka yi kai da dan uwanka Sameer. Sai kuma na ji bayan wannan babban aikin
ladan da ku ka yi ku ke son gayyato mana matsala
cikin zuri’a dinmu wanda ba za mu lamunta ba.
Dukkanku wai ku ka ce wai Raihanah ku ke so har kuna ikirarin daukar mataki a hannunku saboda son kai da na zuciya, a ce dayanku ba zai iya hakura ya bar wa dan uwansa ba.
Ku duba ku ga abin da dan uwanku Mustapha ya yi tun kafin mu san da maganar. Kai Sameer ba cewa ya yi ya hakura ya bar maka ita ba, duba da son da yake mata don kawai a samu zaman lafiya.Ku kuma cikinku babu mai iya wannan sai ku tsaya ku kawo mana tashin hankali ku jefa yarinya karama cikin dimuwa da damuwa ko da yake yanzu haka komai ya kau tunda na zauna da ita jiya ta yi min bayanin komai kuma na gamsu. Na ce cikinku ta fada min wanda take so kuma na yi mata alkawarin duk wanda ta fada shi zan aura mata da kaina babu kuma wanda zai kawo min iskanci na bar shi duk cikin ku.
Gaba daya su ukun babu wanda bai samu shock ba (faduwar gaba). Kowa a tosrace yake don jin mai zai fada.
“Ta fada min cewa duk babu wanda za ta aura cikinku, saboda tana son ganin farin cikin ‘yan uwanta. Ta ba ni zabi ma na samo mata wani, amma ba cikin zuri’a ba, na yarda na kuma ba ta goyan baya tunda haka ku ka zaba. Gaba dayanku na ja muku layi na yi muku iyaka da ita kada wanda ya kara zuwar mata da maganar aure duk cikinku wanda na samu labarin ya daga mata hankali to zan yi matukar saɓa masa kowaye a cikinku. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan ita ce maganar da ta sa na tara ku da fatan za ku kiyaye, don dan watanni uku da ya rage ta gama karatunta daga cikin satin nan zan nema mata wanda za ta aura a hada ku duk rana daya a yi auran mu ga ta rigimar da ku ke son yi mana.Saboda haka ku tashi ku tafi iyakar ‘abin da zan fada muku sai dai ban yarda na samu labarin rashin jituwa a tsakaninku ba.”
Haka duk suka mike suka fice domin babu wanda ya bawa damar cewa wani abu. Cikin fushi M.J ya wuce su babu wanda ya Isaya yin magana a cikinsu tabbas ya san halin Abba Aminu shi ma mutum ne mai zafi, kuma duk abin da ya ce babu wanda ya isa ya musa masa ko kawo masa wargi, amma idan akwai wanda ya cuce shi bai wuce dansa ba da ba dan ya yi masa haka ba babu inda zai samu matsala da Raihanah dinsa.
Kin yi karya Raihanah ba ki isa ki ce za ki auri wani ba, ko kashe ni za a yi ba zan bari ki auri wani ba mu zuba ni da ke mu gani, idan za ki yi nasara ban taba karya dokar Abba Aminu ba, amma wannan time din sai na yi saboda son ki da nake yi. Da wannan tunanin ya isa gida ya ɓame kansa cikin daki.
Bayan fitarsu Abba Aminu ya sake kiran dansa Sameer suka zauna su biyu ya hau yi masa fada tare da kashedin kada ya kara jin labarin ya kara yi wa Haana magana matukar ba zumunci ne zai kai shi gidan ba, tunda ba ya son Rauda da take son shi, to ya jira shi ma kamar yadda Raihanah ta nuna na samo mata miji to kai ma haka zan nemo maka wacce ta dace da kai, kuma karya ka ke ka ce min ba ka so ka tashi ka ba ni wuri ka jira lokoacin da zan fada maka wadda za a ba ka cikin yaran abokaina, zan nemo maka tunda iya shege ne abin naku.
Jin haka ya ji ransa ya baci duk da sanin Abban nasa baya daukan wargi duk da haka sai da ya ce, “To Abba don Allah ka yi hakuri ka bar ni na je gurin Rauda din ko kuma ka ba ni damar na samo da kaina.”
‘Karya ka ke a dan wannan lokacin babu wata dama da zan ba ka tunda ka sammu a baya ba ka yi aiki da ita ba, to dole ne ku jira ka ga wacce zan ba ka. Tashi ka je mun gama magana da kai.”
Babu yadda ya iya dole ya mike ya fice domin ba shi da ikon da zai yi musu da mahaifinsa, halinsa ne duk maganar da zai yi maka kai tsaye a matsayin UMARNI yake ba ka, don haka dolensa ne ya bi abin da ya ce.
Lokacin da Alhaji Aminu ya tara ‘yan uwansa ya gaya musu irin zaman da ya yi da duk yaran kowa ya yi murna ganin an magance matsalar da ake ganin za ta afku har da shi kansa Fu’ad da yaso shi ma ya bayyana masa abin da yake ransa, kowa ya ji dadi suka shiga godiya da fatan neman Allah ya kara hada musu kan yaransu da zumuncinsu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan sati biyu da yin haka idan ka ga Haana a wannan lokacin ba ka ce ta shiga damuwa a baya ba, kowa ta shirya da shi, Rauda dinta da Ya Abba kamar babu wani abu da ya taba shiga tsakaninsu.
Fadeelah ce har yanzu ta ki sakin ranta da Haana, domin Mal. M.J ya ki sauraranta. Da farko da Mama Bara ta zo da zafinta ‘yan uwanta maza suka dakatar da ita suka yi mata bayanin abin da suka yanke jin Haana ta hakura yasa ta saki rai ta koma sai dai kafin tafiyarta sai da ta yi wa M.J tatas ta kuma ce masa dole ne aure babu fashi auren zumunci ne sai an yi shi, su ma shi aka yi musu kuma ga shi suna alfahari da abin yanzu.
Zaune suke cikin lecture hall suna jiran sabon malamin da Mal. Mas’ud ya ce zai karbe shi na dan wani lokaci. Haana duk ta kagu ya zo ya fita, saboda tana son ta yi ta koma ta je amsa kiran Abba Aminu.
Zahra, Salma da Rabi’a ne suke ta ba ta bakin me yasa ba za ta saki ranta ba. Tsaki ta shiga yi ta ce, ‘Kawai ji na nake yi duk na gaji sabon malaminnan ba dan shi ne zai shigo ba ban san rules dinsa ba da tuni na tafi gida abu na.”
Rufe bakinta kenan suka jiyo sallama gaba
daya ajin suka maida hankalinsu ga amsa sallamar. Tsananin mamaki ne ya bayyana a kan dukkan daliban da suke ajin jin gwaninsu abin son su malamin da har gobe suke da kishirwar son ganin ya dayo musu, amma ba su samu ba, sai yau wato Malam Muhammad Jafar Nasir wanda suke kira da Malam MJ sun yi murna da dokin ganinsa tsakanin maza da mata.
Wasu daga cikin mazan kasa tsayawa suke da rike murnarsu sai da suka zo suka rungume shi don murna, ba su kadai ba wasu daga cikin matan da dama da suma sun je sun rungume shi. Zahra da su Salma su ma sun yi matukar murnar ganinsa.
Nan aji ya dauki sowa ta ko’ina shi kansa M.J din ya yi matukar murnar ganin yadda kowa ya nuna farin cikin dawowarsa da kyar ya samu ya yi controling ajin.
Ko kadan bai bi ta kan Haana ba wadda ita ce kadai cikin tarin daliban da ba ta nuna jin dadin ganinsa ba. Ta sa a ranta cewa ya dawo ne don ya takura mata, tunda a gida ba shi da wannan right din, da ya yi kokarin bata mata rai za ta nufi kai kararsa gurin Abbanta kuma sabon abokinta, domin ya dauki mataki a kai.
Abin mamaki ya ba ta ganin yadda yake kiran sunan jama’a bai manta da kowa ba ya danci mintina kusan sha biyar kafin ya soma lecture kowa ya gaida shi, amma ban da Haana domin ta san da biyu ya dawo lecturing din nan don kawai ya samu damar abin da zai dinga shiga tsakanin su..
Gudun kada a zaci da wani abu a tsakaninsu ta gaida shi. A takaice ya amsa cikin rashin damuwa. “Raihana ko kina lafiya?” Tabe baki ta yi cikin
ranta ta ce, ‘Ka ji da shi kuma tunda ta nan ka bullo.”
Zahra da ta san dawan garin sai abin ya ba ta dariya, amma dole ta ja bakinta ta yi gum kada mutuniyar tata ta ishe ta da mita.
Sosai ya nutsu yana musu gwanancewa jifa-jifa yana lecture cikin watsowa Haana tambayoyi kasancewarta ma’abociyar son haka ta shiga amsa masa don ta manta akwai ‘yar tsama a tsakaninsu karatun kawai tasa a gaba.
Har cikin ransa yana jin dadin hakan har ya gama lokacin fitarsa ya yi bayan sun gama zai fita dalibai suka tsaya tambayarsa cewa wai ya dawo kenan ko zai koma? Bai ba su amsa ba sai da suka hada ido da Haana ya tabbatar ita ma sauraron amsar da zai bayar take son ji. Cikin murmushi ya ce.
“Bana jin zan tafi har sai kun gama karatun na dauki matata sannan zan koma kun san aure na ya kusa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Haba Malam a garin nan za ka yi aure, ashe duk za mu je. Cewar wasu daga cikin daliban wasu kuma suka ce, ‘Malam yaushe ne ranar auran, amma dai kafin mu gama ne?”
Ummmh. Ya daora hannunsa daya a saman kunnansa alamar yana son tunawa nan take suka hada ido da Haana ya faki idon jama’a cikin ‘yan sakwanni ya kashe mata ido sai ya yi sauri ya ce. “Na manta, amma ana saka wa zan fada muku.”
Nan suka shiga taya shi murna da fatan alheri sun ji dadin ganin yadda ya yi masifar saukowa ba kamar da ba da tari ba ka isa ka yi masa a aji ba, gaba daya daliban babu wanda bai yi farin ciki da lecture din yau ba don ta zo musu da dadi.
Ba ta tsaya gama jin abin da yake ce musu ba ta yi sauri ta tafi abin ta yana kallonta ya yi banza da ita.Tsaye suke bakin motarta tana kokarin shiga ta tafi sai ga wani class mate dinsu da suke kira Barrister Isah ya ce, ‘Raihanah Mustapha, Mal. M.J wai yana son ganin ki yanzun nan.
Shiru ta yi tana son yanke abin da za ta ce da shi da sauri Zahra ta ce, ‘Ka ce masa ga ta nan zuwa.
Haka ya juya ya tafi, Zahra ta dube ta ta ce, “Haana ki bi mutumin nan ku zauna lafiya dan uwanki ne kada ki sake Kirkiro wata matsalar bayan na san abin naki gulma ne fa.”
“Zahra ba na son iskancin nan da ki ke min fa zo mu je ki raka ni,.
Tare suka tafi sai dai ita Zahra din ba ta bari ta karasa inda yake ba ta noke.
Tunda ya hange ta ya shiga sakin lallausan murmushinsa mai kayatarwa. Babu sakin fuska a tare da ita ta karaso gurinsa tare da yi masa sallama. Dubanta ya yi ya wani dake ya dawo mata asalin Malam M.J din na farko babu wani wargi a tare da shi.
Ganin ‘yar wata razana a fuskarta ya yi saurin yin murmushi ya ce, “Raihana ke nan kin hangi abin da ki ka gani a fuskata ko, well mu bar wannan, kin gan ni a karo na biyu matsayin malamin ki ko na san kin ji dadi na san hakan yana cikin burin ki, kuma na hango haka cikin kwayar idanun ki.
“Please Yaya Muhammad ka fada min abin da zan yi maka sauri nake zan je na amsa kiran da Abba Aminu yake min ina ganin idan abin da za ka gaya min kenan to zan iya cewa ban yi ba na san ka dawo ne don ka takura min ka shiga rayuwata.” Ta fada cikin gajiyawa.
Murmushi ya yi ya ce, ‘Ke Raihanah ki tsaya ki ji ni matsayi biyu nake da shi a gurinki, malamin ki kuma yayanki don haka idan muna makaranta ba ki da ikon fada min duk maganar da ki ka ga dama a gida ne ki ke da wannan. Malaminki ne ni a nan a gida kuma yayanki, dolen ki ne nan ki min magana cikin ladabi da girmamawa dole ne ki kiyaye haka.. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ga key dina nan ki je ki dauki jakata da kayan karatuna ki tafar min da su gida, idan na dawo don ba gida za ni yanzu ba zan zo na karba, ba kuma na son ki yi min gardama duk abin da zan ce miki a cikin makaranta zai zamo UMARNI ne a gurinki.
OK, malam babu matsala zan bi UMARNInka a makaranta a gida ma zan bi umarnin ka na matsayin yaya duk zan yi matukar ba za ka shiga rayuwata ba, amma idan abin ya yi min yawa zan iya sanar da Abba Aminu, domin shi ne kadai zai iya ba ka UMARNI bani ba, ba ni key din.” Ta sa hannu ta karbi key din da yake ta hangi motar yana kusa da ita.
Mamaki ne ya kama shi ya saki baki yana kallonta yadda take yin abu cikin kwarin gwiwa, murmushi ya yi ya ce, ‘Yarinya za ki yi laushi ne in dai ni ne.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG