ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 19 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 19 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
Gajeriyar hira suka yi bayan ya gabatar mata da kansa ya ce mata yana aiki a PHCN. Bai wani jima ba ya tafi ita a takaice ta gabatar da kanta gare shi.
Zaune suke ita da Muhammad Bashir a farfajiyar gidansu gurin da aka tanada don hutawa, tunda ta hango shi ta ji gabanta ya fadi, yadda ya nufo su kamar wani mawiyacin zaki da ya kwana ya wuni bai ci komai ba.
Ko sallama bai musu ba ya maida kallonsa ga Haana ya ce, “Ke na gaji da wannan rainin
hankalin da ki ke min ya zama dole ki sallami mutumin ta karfin tsiya ko kina so ko ba kya so kin ji na fada miki.”
Cikiin bacin rai ta mike, cikin tsiwa da masifa ta ce. “Ba ka isa ba ba ka da huromin da zai sa ka yi min dole tunda ba a karkashin ka nake ba, a’a wai me ye haka ne ka ki ka bar ni na huta a gida fitina haka makaranta fitina, da wanne ka ke so na ji ne?”
Kafin ya ba ta amsa Muhammad Bashir ya ce, “Malam wai me ye haka ne ka zo ko sallama ba ka yi mana ba ka tsaya kana ta mana ihu aka ka san dai haka baya cikin tsarin Musulunci sallama wajibi ce.”
Cikin kunar rai ya juya ya dube shi cikin wata irin tsawa ya ce, ‘Kai Malam dakata! Ba da kai nake magana ba kuma an ki a yi sallamar idan da hukuncin da za ka yi minto ga ka ga ni kada ka kuskura ka saka min baki cikinmaganar da muke don ba da kai nake yi ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Dole ya sako baki mana tunda a kansa ka ke, please Yaya M.J ka je abin ka ba na son sabon. fitinar nan taka.
Cikin wani irin zafin nama ya cakumo ta kadan ya rage ya hada ta da jikinsa sai dai duk suna jin saukar numfashin junansu riko ya yi mata na tsauri ta ji zafinsa ya ce, ‘Idan ba kirufe min baki ba zan balla miki.hannu za ki sallame shi ko yaya?”
Cikin damuwa Muhammad Bashir ya yi saurin rike hannun M.J ya ce, ‘Kai Malam za ka sake ta ko kuwa matar da zan aura za ka ballawa hannu wane irin hauka ne ya same ka haka ka sakar min ita na ce.
Cikin wata irin mazan taka ya yi sauri ya sake ta ya cakumi wuyan rigarsa ya ce, ‘Kai Malam kada na
kara jin wannan kalmar ta sake fitowa daga bakin kai mahaukacin ina ne da za ka dube ni ka yi min wannan maganar.wanene kai me ka ke takama da shi da za ka dora hannunka a kaina?
Last warning da zan yi maka yau shi ne wallahi idan ba ka fita daga cikin rayuwar Raihana ba zan iya daukar kowane mataki a kanka idan na kara ganin kafarka cikin estate din nan daga kai har motarka sai na sa muku fetir na babbaka ku idan ban yi haka ba to zan sa a yi maka rotse kai da motar taka na ga wanda ya tsaya maka banza kawai.”
Sauri Haana ta yi ta shiga tsakaninsu ta fisge hannunsa daga cukumar da ya yi masa cikin wata irin masifa da ba ta san tana da ita ba ta ce.
“Malam ya ishe ka na fada maka ba ka da wannan right din da za ka hana shi zuwa gurina mijina ne shi kuma zan aura ba ka isa ka ce ba zai zo gurina ba.”
Juyawa ta yi ta riko hannunsa ta ce, Muhammad mu tafi mu ba shi wuri.”
Wani irin kishi ne ya kama shi ganin yadda ta rike hannunsa ji ya yi kamar zuciyarsa za ta fito. Tsakanin kishin da ta hango a idanunsa da kuma irin duban da yake yi wa hannunta da ya gani rike da wani. Ba ta san san da ta yi saurin sakin hannunsa ba, domin tarin bacin ran da ta gani a
fuskarsa. Sauri ya yi ya tare shi ya ce, ‘Dan uban ka zo ka zo ka fice daga estate din nan tunda ba ka da gadonsa minti biyar na ba ka wallahi idan ba haka ba na rantse yau sai na jinya ta ka sai dai yau na yi kwanan cell. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsananin kaduwa ce ta bayyana a fuskarsa ya ce, ‘Raihanah bar ni na tafi na ga alamar wannan mahaukacin da gaske yake duk abin da ya fada na gan shi a cikin kwayar idanunsa zan fadawa Alhaji na a zo a ďauki mataki idan ba haka ba zan shigar da kara ni na wuce sai anjima.”
Bai jira jin amsar ta ba ya juya ya bar wurin cikin sauri ya ja motarsa ya fice. Ta dube shi ta ce, ‘Abin da ka yi yanzu ka
kyauta kenan ko kana nufin yin hakan zai sa na aure ka dole ba ka da wannan right din a yanzu, kuma dole na je na fadawa Abba Aminu abin da ka ke min yau sama da wata daya ka hana ni zaman lafiya, haba wai kai wane irin mutan ne mai son kansa shi kadai?”
Murmushin yake ya yi ya ce, ‘Ki je ki fadawa duk wanda za ki fadawa zaman lafiya ba ke kadai zan hanawa ba duk zuri’a sai abin nan ya shafe su idan ba kashe man din nan na yi ba kowa ya gasgata ba ni da hankali ba to ba za su yarda su ba ni ke ba idan shi Sameer ya hakura ni ba zan iya ba, domin ke kadai aka halicce ni ba ki da miji sai ni.””Ya M.J ka san abin da ka ke cewa kuwa, kisa ka ke cewa fa.”
“Idan ban yi kisan ba to zan jinya ta na raunata shi yadda ba zai amfanu ba domin take shi zan yi da mota ki ba ni nan da sati idan ba ki sallame shi ba za ki samu wannan labarin..
Ba zan bari ki fara zana exams dinki ba zan aiwatar da hakan domin na san kina gamawa za a fara maganar biki ki jira ki gani.” Yana gama fadin haka ya bar gurin cikin wani irin ɓacin rai a tare da shi.
Kasa cewa komai ta yi illa binsa da ta yi da kallo tana mamakin abin da ya furta mata, tunanin ta ya soma ba ta ko wani abu ya fara sha ne dole ta je wa Abba Aminu da wannan batu domin ta ga
tarin gaskiyar abin da ya fada a kan fuskarsa. Tamkar dai mashayi haka ya fada dakin Haj. Babba zaune suke ita da Fadeelah tana mata tausa duk hirar da suke a kansa ne, domin damuwa ta yi mata yawa har tana tunanin barinsa.
Sallama ya yi musu, Hajiya Babba ta amsa yana jin Fadeelah na gaida shi ko ya amsa bare ya dubi inda take.
“Hajiya gurinki na zo don ku yi wa su Abba magana, Raihana ta dakatar da mutumin nan da yake zuwa wajenta idan ba haka ba zan raunata shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ke kuma Fadeelah idan na raunata shi kan ki zan dawo idan har ban yi nasarar samun Raihana ba bazan aure kiba sai dai ki shirya daukan bakin ciki mara misaltuwa kamar yadda nima ki ka saka ni,domin a dalilinki na shiga damuwa nake shirin rasa Raihanah bayan na fada miki ba zan aure ki ba.
To ki shirya zan aure ki sai dai ba za ki taba samun farin ciki ba a gurina duk wata walwalarki sai na hana ki samun ta.
Kai Mahammadu kanka daya kuwa, ni ka ke fadawa haka me ye laifin mutumin da ya ce yana son ka don ana son ka sai ka dinga yi wa mutum abin da ka ke so. To ahir! Din ka kada na kara jin wannan furucin daga bakin ka ‘yar uwarka ce.”
“Eh, Hajiya ‘yar uwata ce amma mara son ganin farin cikina da walwalata ina son Fadeelah mazaunin ‘yar uwa ta jini, amma ba so na aure ba na fada mata ba tun yau ba, amma ta ki yarda sai da ta kai ni bango.
“Za ka rufe min ba ki mara kuunya ba Hajiya za ka yi wa magana ba ni za ka fadawa ina ciki ina jin ka dama tsayawa na yi na ji ka sauka daga rashin kunyar ta ka sai na fito.”
Muryar Mama Bara ya ji, don bai san ta zo ba ma da sauri ya juyo ya dube ta tana fitowa daga bandaki ya duka zai gaida ta cikin ladabi.
“Babu abin da zan yi da gaisuwarka tunda
rashin kunyar taka ya girmama ka fice ka ba ni guri
tunda kai ba ka ganin girman kowa.”
Bai ce da ita komai ba ya juya ya fice, kuka Fadeelah ta shiga yi Mama Bara ta tsaya tana kakllonta cikin tarin takaicin da ya dasa musu. Fiye da sati ake ta wannan ta kaddamar, haka
shi ma Mr. Smeer ya susuce kan Rauda sam ta ki amincewa da shi babu wanda bai kama kafa da shi ba ya kasa nasara, haka duniya ta yi masa zafi daga shi har Malam M.J babu wanda yake cikin dadin zuciya.
Ya Abba da Haaya kuwa a nutse suke kullum so ne sosai yake nuna mata tuni shi ya yi tawakkali addu’a kawai yake yi wa Haana a kan ta samu farin cikinta wato M.J ya san duk abin nan da take masa ta yi ne don dole, domin ya sha kamata a daki tana kuka, duk ranar da suka samu matsala da shi haka zai shiga ba ta baki amma tsabar kafiya da karfin zuciya sai ta ce masa ita ba a kansa take kuka ba.
Bayan ya gama karanta dukkan wani hali da take ciki na farin ciki ko na bakin ciki, abin da take so da wanda ba ta so tuni Allah ya gama fahimtar da shi babu wanda zai sa ta farin ciki a rayuwarta yanzu idan ba Malam M.J din ta ba, dole kawai ita ake yi mata akan Muhammad Bashir fawar da Abba Aminu yake nunawa a kanta abin yana damunsa don dai babu yadda zai yi ne. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sati guda ya yi ya dauke kafa da zuwa makaranta, domin har yanzu babu wata nasara da yake gani a gurinta sam ya fuskanci cewa Raihana ta raina shi ta daina son shi da jin tsoronsa haka ya ajiye a ransa dole ne ya yi abin da zai ankarar da kowa ya san halin da yake ciki tunda kowa ya yi biris da shi.
Yau Lahadi motarsa ya hango suna tsaye jikinta shi da ita sun tsaya da alama ya gama zancen rakiya ta fito yi masa A zuciye ya hangi wani dogon karfe a can gefen get din gidansu da sauri ya dauka ya nufe su. Ba su ankara ba sai da su ka ga ya zo daf da su duk sai da suka razana tunaninsu kansu zai yi har sun fara shirin neman mafaka.
Kawai sai suka ga ya daga karfen nan ya saukewa kyakkaywar motarsa GMC da ta sha tint karamin mahaukaci ya zama bai bar motar ba sai da duk ya fashe mata glass din. Jin karar glass din shi ne ya dauki hankaklin jama’a da dama da suke kusa yana gamawa ya zo ya cakumo shi.
Kan ka ce me ye wannan wasu daga cikin iyayensu sun fito kowa ya zo ya ga mai yake faruwa.
Kowa sai da ya fito wadanda suke gida lokacin sai dai duk tarin yaran da suke cikin estate din babu wanda ya fito saboda da sun fito iyayen suka tsawatar musu dole suka koma sai dai wasu masu tsaurin idon da suka dinga lekowa ta saman bene marasa hankalin kenan, domin maganar gaskiya zuri’a din sun samu tarbiyya babu laifi, wanda suka hango su suka yi musu dakuwa da sauri suka yi ciki.
Muhammad Bashir ba ta motarsa yake ba ta ransa yake domin yau ya yarda da furucin da ya yi masa rannan. Kowa kan M.J ya yi yana ta yi masa fada. Abdul ne ya je ya fadawa Daddy dinsu da yake cikin gida, domin suna tare ya fito da ya ce zai zo ya koya masa hankali.Alh. Jafar yana zuwa ya tambayi jin dalilin a nan Alh. Hamza ya yi masa bayani cikin ɓacin rai ya daga hannu da niyar zai dauke shi da mari, Alh. Aminu ya yi sauri ya rike masa hannu ya ce, ‘Haba Yaya kada ka mare shi mana.”
Haana da take gefe ganin lokacin da Daddy ya dauki hannunsa zai mare shi zare ido ta yi hade da rufe bakinta na tsananin mamakin abin da zai faru duk ta bi ta rude.
Ajiyar zuciya ta yi da Abba Aminu ya tsare shi. “Marin ba shi ne mafita ba ka bar shi ina da maganinsa, Muhammad Bashir zo mu je ka wuce ka dauki motar idan ka je ka cewa Abbanka ya fara shiri next week ya turo wadanda za a daura ku mun fasa jira sai ta gama exam duk gabadaya daura musu auran za a yi bayan sun gama exam din a yi shagalin bikin. Kowa ya wuce abin sa ke Ammi je ki gida abin ki.”
Duk kowa ya tafi aka bar M.J tsaye a gurin cikin KUNAR ZUCI, yana mamakin irin wannan tsanar da Abba Aminu yake yi masa, take ya sawa zuciyarsa cewa dansa yake tayawa kishi tunda shi ma bai samu ba. To shi ma ba zai bar shi ya samu ba wata irin tsanarsa ce ta samu matsugunni a zuciyarsa.
Ji ya yi duniyar tana juya masa wai rana irin ta yau za a daura auran Raihana da wani ba shi ba, shi kuma zai zamo mijin Fadeelah ji ya yi ya tsani kansa da komai na rayuwar gaba daya, haka ya dinga jin kamar ya rasa komai da kowa arayuwarsa yake jin kamar shi kadai ne yake rayuwa a cikin duniyar babu wani mai taimaka masa kiyayyar Abba Aminu ta samu babban gurbi a cikin zuciyarsa, domin shi ne mutumin da yake son nakasta masa rayuwa tunda dansa bai samu abin da yake so ba, to shi ma ya rasa.. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya jima a tsaye a gurin bai san me zai yi ba, take tunani ya fado masa babu wanda zai iya kaiwa kukansa ya taimaka masa kamar babban Uncle din Muktar wanda yake zaune a Dubai.
Akwai shakuwa da ɓoyayyen sirri a tsakaninsu domin babu wanda ya san tuntuni akwai alaka da zumunci a tsakaninsu, zumuncinsu a boye suke tunda yana zuwa suna haduwa a can Katar din ko idan suka zo hutun summer holiday nan London din ya samu damar saninsa da inda yake duk ta dalilin Mominsu domin lokacin da ya zo London a wani Mall suka hadu ya je sun je nan suka hadu. Babu yadda Mommy ba ta yi ba a kan ya zo gidan su ya ki, domin tsabar fusin da suka yi. M.J din bai wani damu ba ya bi shi a haka suke zumuncinsu sosai a boye.
Bugu daya biyu ya yi wa wayarsa ya daga jinsa a cikin tashin hankali ya ce, ‘Dan gidan Uncle me ke faruwa da kaine na ji muryarka haka har yanzu ba ka yi nasara din ba?”
Babu abin da ya ɓoye masa na irin halin da yake ciki da hukuncin aurar da Raihana da ake shirin yi komai ya fada masa ya roke shi da ya zo ya dakatar da auran nan kada ya rasa Raihanah.Jin tashin hankalin da yake ciki ya ce ya kwantar da hankalinsa dama cikin satin nan suke sa ran zuwa Nigeria din ma gaba daya.
Ya dan ji sanyi sai dai bai gama sakin ransa da ko zai samu nasara ba, domin ba haka ya so ya ji ba so yake ya ce zai buga ya yi wa Abba Aminu cewa ba za ai auran ba. Haka suka yi sallama ya kashe wayar. Motarsa ya dauka ya fice daga estate din don ya samu sauki.
Shirye-shirye ake na daurin auransu har ana jibi biki babu Uncle Mukhtar babu wayarsa, kowa sha’ aninsa gabansa yake babu wanda yake bi ta gabansa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ana gobe daurin aure suka diro Nigeria haba sai a lokacin M.J ya samu walwala shi ne da kansa ya je ya dauko su yana dawowa kai tsaye gidan su Zahra ya je don ta taimaka masa ya kasa samun kan Haana. Ta yi masa alkawarin za ta je har gida ta sa su hadu.
Da sidin goshi ta yarda suka hadu ba wani lokaci ta ba sa sosai ba. Yadda ta gan shi ta tausaya masa sai dai ta ɓoye tausayin a kan fuskarta.
Cikin rauni ya ce, “Raihana me yasa za ki yi min haka bayan kin san ke ce rayuwa ta ke ce farin cikina, shin ba kya tausayin halin da zan shiga idan na rasa ki, ba kya ganin abin da Abba Aminu ya yi min mugunta ce, ki daure ki je ki ce kin fasa auran ni ki ke so.”
“Malam M.J ina son ka ina son rayuwa da kai ina son ganin farin cikin ka, kai komai naka ina so
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG