ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
maka duk tayoyin ka na yi maka asarar fitar na bi
ta wancan get din tunda estate din ba get daya ne
da shi ba.
Wani irin kallo ta yi masa ta datse lebenta
tsabar takaicin abin da ya fada mata tsayawa ta yi
tunanin mai za ta fada masa ta yi, domin ya gama
kai ta bango take ta tuno abin da zai kona masa rai
lokaci daya, domin haka Haana take da wuya kayi
nasara a kanta in dai magana ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Ayya malam maza wuce abin ka nima
ga can Ya Abba ya dawo zan je gurinsa ya gaya
min kalaman soyayyarsa masu dadi, don ka je kai
ma an fada maka ai ba haushi ko ganin laifi zan yi
ba maza tafi kada kuda ya riga ka.
Tana gama fadin haka ta juya abin ta kafin ta
shiga motar, sai da ta juyo ta ga yadda yanayin
fuskarsa ya canza nan dadi ya kama ta, domin kasa
cewa da ita komai ya yi ta shiga godewa Allah a
zuciyarta ta ce.
Yawwa na gode Allah tunda na gano abin da
zan dinga yi na konawa Man din nan rai ai na yi
masa illa mu je zuwa da shi Haana ce fa.
Key ta yi wa motar ta wani tada kura ta nufi
daya get din ta bar shi a gurin cikin jin haushin
abin da ta fada masa.
Binta ya yi da kallo cikin ransa ya dan sosu shi
da ya yi niyyar ba ta haushi abin ya juya kansa a
gaskiyan ce ransa ya baci da furucin da ta yi masa
yana kishin Ya Abba sosai idan bai yi da gaske ba
kamar za ta iya cewa ta fasa da shi, shi take so.
Dole ya yi wani abu kamar yadda ya fitar ma ta
da son Muhammad ba zai bari Mustapha ya yi
nasara a kansa ba, don yadda yake jin son ta bai jin
zai iya rayuwa babu ita. Tabbas ya fuskanta Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana ‘yar hayakin kai ce mutukar bai bi ta yadda
take so ba, to zai iya rasa ta abin da kuwa bai fatan
haka Allah ne kadai ya san irin tarin son da yake
mata. Ya jima yana sakawa da kuncewa daga nan
ya ja motarsa ya koma ciki, domin zai koma ya
hana ta sakat da Abban da take takama da shi din
idan har da gasken ya dawo daga tafiyar da ya yi.
Gabaki daya zuri’a din maragayi Alh. Nasir
DAnfillo ta hadu guri daya idan ka cire Alh.
Mukhtar da Haj. Amina da Haj. Halima su kadai ne
babu su, don duka ba sa kasar sai dai kowa ya bada
tasa gudummawar addu’a a yi taro lafiya a tashi
lafiya, duk abin da zama ya zauna a kansa to su ma
suna bada goyon baya.
Zaman ya yi armashi domin tunda zuri’a din
take ba su taba yin wannan irin zaman ba, domin
har iyayensu mata sai da suka halacci zaman
yaransu ne kadai ba sa gurin.
Bayan bude taro da addu’a kamar yadda aka
saba Alh. Hamza kusan shi ne mai gabatar da
komai na family din nan ya fara gabatar da dalilin
zaman sanann ya bawa Alh. Mustapha dama na
farko wanda shi ne wanda ya karfafa yin taron.
Nan ya soma bayani tiryan-tiryan har ya kawo
karshe babu wanda bai goyi bayan abin da ya fada
ba duk kowa ya yi murna. Haka kowa ya bada
goyon bayan halin da suka yi, sai da ya ga kowa ya
gama gamsuwa da sakawa abin albarka.
Sai ya ci gaba da cewa,Zaman da muka yi da
shi kansa Mustapha Karami ya roke mu da mu bar
kanwar tasa ta auri wanda take so babu irin kai
ruwa rana da ba mu yi ba, amma ba mu yi nasara a
kansa ba, ba wai don ba mu isa mu zaba masa
wadda yake so ba, a’a gani ya yi wai tana da wanda
take so kuma dan uwansa na jini shi ne ya ce ya
bari ta aure shi, mu kuma mu nema masa wata da
kanmu Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba kowa ba ne wannan sai Sameer dan wajen
Yaya Aminu a cewarsa duba da hada zuri’a da ya
yi guri daya ya sadaukar masa da wannan auran.
To kunji abin da yake faruwa auran Ammina ya
tashi daga kan yayanta Mustapha ya dawo kan
daya Yayan nata Sameer.
Gabaki daya mamaki ya kama kowa ba ma
kamar Alh. Aminu mahaifin Sameer da ya ji
maganar daga sama kamar saukar aradu.
Da saurI ya mike ya ce, “Mustapha haka ba za
ta taba yiwuwa ba ya za ka yi haka yaro ga wadda
yake so za a hana shi a bawa wani sam. Ban
lamunta ba, kwarai Sameer ya zo min da wannan
maganar na kwabe shi na ce bai san dokar da muka
saka ba matukar ya fito da wannan maganar aka
samu matsala a zuri’a zan ki yafe masa.
Dakata Yaya Aminu da ni ne ba ka son hada
zuria ne ko me ka ke son ka ce? Mustapha da
Sameer duk daya suke a gurina ina da damar zaba
musu macen da kowannensu zai aura in dai da
zumunci a tsakaninmu da kai idan har ka bar shi ya
kalle ni a matsayin uba kamar ka.
Jikin Alh. Aminu ya yi sanyi domin ba haka ne
manufarsa ba take ya ce, “Mustapha ba haka nake
nufi ba, na barka ka yi duk yadda ka tsara Allah ya
hada kanmu.
Murmushi ya yi ya ce, “Yaya Aminu na gode
Allah ya saka.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Kowa na gurin sai da ya yaba kyawun halin
Alh. Mustapha hakan ya nuna cewa lallai son da
yake yi wa zuri’a dinsa ba kadan ba ne, babu
wanda bai yi farinc iki ba aka shiga shi wa Ya
Abba albarkar wannan halacci da ya yi aka dinga
cewa Kyawun halin mai sunansa ya biyo.
Har cikin zuciyar Alh. Jafar sai da ya ji kaunar
dan uwansa ta kama shi ya kara yin nadamar abin
da ya yi masa a baya, haka ya dinga jin wani irin
nauyinsa da wani girma na daban da ya kara samu
Cikin zuciyarsa ya yarda Mustapha zuciyarsa mai
kyau ce har kullum.
Nan shi ma ya shiga nasa bayanin da ban
hakuri duk abin da ya taba faruwa a baya kuma ya
ce ya janye duk wata dokar hana auren zumunci
duk wanda yake da yarsa ko dansa yana son
hadawa kowa ya yi zai kuma dauki nauyin komai
wannan alkawari ya yi wa kansa daga karshe ya ce.
Yanzu haka mun hada auran Muhammad din
gurina da Fadeela din gurin Haj. Bara.
Kar ka So ka ga murna gurin Haj. Bara, murna
Za ta kashe ta yar lelenta za ta samu abin da take So.
Alh. Jafar ya kara da cewa, “A matsayinmu na
manya mun yi haka ne don mu bawa kowa damar
Yin hakan don Hausawa suna cewa daga na gabaake gane zurfin uwa
Kai yau kam farin ciki ya ishi dukkan iyayen da
suke cikin zuri’ ar Nasir Danfillo haka guri ya
hautsine da murna, ana ta sakawa abin albarka.
Bayan an dan nutsu Alh. Mustapha ya ce,
Yaya Jafar gani nan da kokon bara ta ina nemawa
danka Mustapha auran kanwarsa mai sunan Haj.
Babba da fatan za ka amince.
Wani irin BUGUN ZUCIYA ne ya zowa Alh.
Jafar jin furucin dan uwansa bai san lokacin da ya
saki murmushi ba ya ce, Babu laifi an yi an gama
na ba shi shi ma. Www.bankinhausanovels.com.ng
Murna ya shiga yi ya ce, Yaya na gode Allah
ya Kara hada kanmu ya kori fitina.”
A zahiran ce ya ce Ameen, amma can kasan
zuciyarsa tunani da rikicin da kwakwalwarsa ta
shiga yake na ya zai yi da diyarsa Haaya na
alkawarinda ya yi mata na tunda suka zo Nigeria
sai ya yi duk inda zai nemo mata Mustapha da ya
hana ta farin ciki ya jefa ta cikin tashin hankali su
kadai suka san irin ciwon da ta yi na rashinsa.
Ga shi bai cika mata alkawarinta ba ya je ya
bada auranta ga wani bai san yadda zai yi ya
fahimtar da ita ba ta karbi wannan zabin da ya yi
mata ba.
Tun bayan rasuwar Hameed cikin
ya’ yansa babu wadda yake tsananin so kamar ta,
haka yake ba ta duk abin da take so tun da ta taso
sai abin da take so yake mata sai ga shi yau satin su
biyu da dawowa ba a je ga ko fara nemansa ba ya
ba da auranta ga dan yar uwarsa.
Shin bai yi ganganci ba, bai kuma jefa ‘yársa
cikin damuwa ba, duba da irin yadda ta gama saka
rai da zai ba ta abin da take nema a gaba dayan
rayuwarta. Bai san ya yi sakaci ba na nuna mata
cewa duk abin da take nema sai ta samu lallai yana
da kalubale a gabansa. Dole ne ya ba ta hakuri ya
tankwara ta ya ba ta hakuri ta yi masa abin da yake
So don ba zai taba hana dan uwansa abin da yake
So a gurinsa ba.
Duk cikin kankanin lokaci Alh. Jafar ya gama
saka wannan tunanin a zuciyarsa, amma ya dake
kamar ba shi da wani tashin hankali.
Kafin a tashi daga taron nan sai da iyaye suka
shiga nemawa yaransu miji da mata, domin a nan
ne Alh. Hamza ya ce wa Alh. Aliyu yana nemawa
dansa Fu’ ad auran yarinyarsa Rauda. Take shi ma
ya amince. A takaice dai aure biyar aka hada a
wannan lokacin haka aka yi addu’a taro ya watse
Cikin farin ciki a gurin iyayen. Wannan kenan mu
je zuwa.
Kuka take kamar ranta zai fita abin duniya duk
Ya bi ya 1she ta. Kwance take a dakin ta a nan
kannenta su uku sun sata gaba sai ba ta baki suke
Yi. Haaya ke nan tun da ta ji zabin da Daddy din ta
ya yi mata ta shiga cikin tashin hankali da damuwa.
Sallamar Daddy din ne yasa ta dago kan ta tana
ganinsa ta sake rungumar filo ta takure a kan gadon
da take zaune. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kannanta ne kadai suka iya amsa sallamar ya
zo ya zauna gefen gadon ya ce, “Hameed, Bilal da
Akram ku ba mu guri zan yi magana da Yayarku.
Cikin sanyin jiki suka ce, To Daddy. Nan
suka mike duk suka fice gaba dayansu.
Matsowa ya yi kusa da inda take ya riko
hannunta ya ce, Haba uwata wai sau nawa zan ba
ki hakuri ne ki zamo mai hakuri da yi min biyayya
na tabbata idan ki ka kwantar da hankalinki za ki
zo ki yi farin ciki, ni kaina ban san ya akai na
amsawa Kawunki cewa na bada auranki ba, ba zan
iya musu da shi ba na yi masa laifuka masu yawa a
baya kullum burina na ga na faranta masa dalili
kenan da yasa ban yi musu da shi ba.
Haba uwata ki daure ki yi min abin da nake so
kada ki ba ni kunya ba ke kadai aka yi wa haka ba,
akwai sauran ‘yan uwanki duk a gurin aka bada
Su.
Cikin jajayan idanuwanta da suka kada suka yi
jajir ta cire kai da ta dube shi cikin kuka ta ce,
“Daddy ba haka muka yi da kai ba, ai mun yi da
kai cewa idan mun zo Nigeria za ka taya ni duba
Mustapha na aure shi, ba ni da wanda zan aura sai
shi, sai ga shi ban rufe ko week a Nigeria ba har
ak hada ni da wani. Da na san haka za a yi min da
ban yarda na biyo ka ba da na tsaya na biyo su
Yaya Muhammad da yanzu haka ba ta faru da ni
ba.
Plcase Daddy ka bawa Uncle hakuri ka ce ina
da wanda nake so na aura, ni ba zan 1ya Son
wannan ba wallahi.
Ransa ya sosu sOsai, amma babu yadda zai yi
ya yi mata zafi duba da ya san irin damuwar da
take ciki, don haka ya kara zage damtse don sake
rarrashinta, domin ba zai taba yi mata abin da take
so ba, duk da kuwa bai taba yi mata musu a kan
duk abn da ta nema wurinsa ba.
Uwata ki dauki kaddara ki saka haka a ranki
shi ne zabin da Allah ya yi miki, tunda Allah ya
rubuta haka ko kina ina sai haka ta faru da ke, kin
rasa Mustapha wancan kin kuma samu wani
Mustapha din cikin zuri’a din ki ina mai tabbatar
miki shi ne zabin da za ki yi farin ciki da shi,
saboda yana da tausayi da bada kulawa yadda
kowa yake yabon sa na san Allah ya baki irin mijin
da zai ba ki irin farin cikin da nake so ki samu
gidan rayuwar auranki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Na tabbata zai kAwo farin ciki a kan fuskar ki
ko da yaushe zai mantar da ke damuwa da rashin
da ki ka yi na wannan Mustapha din, Kuma ki tuna
Nigeria ba kasa ce karama ba, idan har muka ce za
mu fara nemansa ba mu san ta inda za mu fara ba.
Daddy ba na fada maka cewa shi ma a Kano
Yake da zama ba shi da iyayensa.
To na ji yadda Nigeria take da girma haka ma
Kano take da girma. To a Kano a wacce unguwa,
kowacce karamar hukuma? Kin ga ai duk ba mu
sani ba, bare mu fara nemansa kai tsaye.
Uwata ina son ki kwantar da hankalinki zan yi
miki wani abu guda daya ki yi kokari ki cire
wannan damuwar da nake gani a fuskarki ki ci
gaba da addu’a duk lokacin da Mustaphan ki ya
bayyana ni ma zan sa a fasa auran naki da namu
Mustapha din idan har iyayensa sun yarda da
auranku amma idan ba ki gan shi ba kin yarda za ki
auri wannan din?
Da sauri ta ce, Eh, na yarda Daddy, to amma
yi min alkawarin kai ma za ka dinga yi min
addu’ar ganin sa.
Zan
“Zan yi miki dai addu’ar zabin alheri a
rayuwarki; domin ban so ki saka abu a ranki ki zo
ba ki samu ba ki kara shiga irin damuwar da ki ka
shiga a baya.
Daddy Mustapha alheri ne a gare ni tunda har
yanzu na kasa mantawa da shi.
Shi ke nan zan miki abin da ki ke so, amma
nima ki yi min akawarin idan har lokacin da muka
ba ki bai dawo ba za ki auri namu Mustapha din?”
“Eh, Daddy insha Allahu zai ma dawo kafin
lokacin.”
Shi ke nan, to share hawayen.
Da sauri ta zo ta rungume Daddy din ta ce,
Thank you Daddy, kuma insha Allah ba za ka
sake ganin wata damuwa a fuskata ba zanyi duk
abin da ka ce.”
Yauwa uwata ta kaina. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka ya riko hannunta suka fito falon nan suka
iske Mommy da sauran kannanta ganinta cikin
farin ciki duk su ma sai suka fara murna ‘yar
autarsu wato Afra ta ce, Sister kin daina kukan
kenan, Daddy ba zai miki auran dolen da ya ce zai
miki ba ko, nima idan na girma zan ce Daddy kada
ya yi min auran dole.”
Da sauri ta zo ta rike ta ta ce, “Eh, My little Sis,
Daddy ya ba ni dama ki taya ni murna.
Duk suka saka dariya a gurin suna jinjina irin yar
surutu da wayon Afra yar kimanin shekaru shida
zuwa bakwai.
Cikin sanyin jiki ta shigo gidan, Mamah Me ta
gani a falo tana kallo ita da yara, gaisawa suka yi ta
ce, “Mamah Me ina Raudana.
Tana daki tun jiya ta zabawa kanta rayuwar
zama a daki sam ba ta san rabar jama’ a na yi mata
magana ta ki ji ba sai ta je ta yi ta yi ba, ita ta ga za
ta iya aure kuwa babu fashi tunda duk mu ma haka
aka yi mana kuma ga shi mun rayu babu abin da ya
faru da mu, gara ki je ki ba ta shawarar ta yi wa
mahaifinta biyayya tun kafin ya yi fushi da ita.
“Haba Mamah Me ke ya kamata ki kwantar
mata da hankali ba ki yi mata fada ba, kin ga sam
abin babu dadi.”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG