ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Dariya ta yi nan suka rankaya zuwa gidan
kakaninsu inda Fadeelah take sauka idan sun zo.
Fiye da mintuna talatin suna tare daga nan suka yi
sallama ganin dare ya fara.
Har za ta wuce gida sai wata zuciyar ta ce ta
dan leka ta ga jikin Rauda mana tunda dama ta ce
Za ta dawo.
Lokacin da ta shiga falon su Na’im kawai ta
gani a falo suna kallo ta tambaye su ya jikin Ya
Rauda suka ce tana ciki ta tashi, Ya Abba yana
dakinta yana mata fada ta ki cin abinci.
Da sauri ta karasa don su hadu su yi mata fada,
tana zuwa bakin kofa ta ji muryar Ya Abba yana
Cewa.
Rauda hakurin nan da dangana shi ne mafita
gare ki, ki cire dukkan damuwarki ki karbi kaddara

cewa Samcer baya cikin kaddararki kamar yadda
nima na hakura da ita, ki saka haka a ranki cewa
Sameer ya yi miki nisa.
Ki daure ki cire son shi a ranki duk da kuwa na
san kina bakin kokarin ki.
Cikin kuka ta cc, Ya Abba na kasa hakuri da
son da nake yi wa Yaya Sameer dole na hakura na
bar mata sai dai ina son ka taya ni da addu’a Allah
ya fitar min da son mijn yar uwata dole ya sa
nake nisantarta, don kada ta gane halin da nake
ciki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Zan taya ki kanwata, ki sharce hawayen ki ki
daina kuka, ki saka cewa haka ta mu kaddarar take
a sannu Allah zai kawo mana mafita, 1ta kuma mu
taya ta da addu a Allah yasa auranta da Sameer din
alheri ne.
Tsananin kaduwa ne da firgita a lokaci guda
suka bayyana a fuskar Rauda bakin ta na rawa ta
ce. Ya Abba Haana ce
A rude ya juyo ya ce, Haana kuma. Ganin ta
a tsaye hawaye duk ya wanke mata fuska ya sake
kidimewa a rude ya ce, Haana yaushe ki ka
shigo?”
Cikin kuka ta ce, Ya Abba me na ji kuna
fada?
Cikin rawar murya ya ce, ‘Babu abin da muka
fada.”


Girgiza kai ta yi ta ce, “Ya Abba kada ka boye
min komai yau na ji abin da ku ke boye min kai da
Kanwarka tunda ni ba ciki daya muke da kai ba, shi
yasa ku ke boye min damuwarku.
Me yasa Abba da Ammi ba su haifa min Yaya
namii ba, wanda za mu iya yin sirri da shi kamar
yadda na ga kuna yi kai da kanwarka.”
Bai san san da ya daka mata tsawa ba ya ce,
Ya ishe ki haka Haana ba za ki daina wannan sanbatun ba.”
Duk da kuwa irin tsoran tsawar da ke yi
wannan karan sai da ta dake ta ji ta daina jin ta.
Ya Abba daga yau na daina Jin tsoron
kowacce irin tsawa a duniya ko za ka kwana kana
yi min ita ba zan razana ba, tunda yau na gane
cewa ni marainiya ce ba ni da wa da muke ciki
daya.
Haana wai ba za ki rufe min bakin ki ba da
irin wannan furucin naki mara dadin ji da ke nake
magana.
Ya Abba ka yi hakuri ba zan iya ba.
Nan ta mayar da kallon ta ga Rauda ta ce,
“Rauda na me yasa ki ka yi min haka? Me yasa ki
ka boye min abin da yake ranki bayan ni bana iya
Boye miki komai, kin zalunce ni kin, kuma zalunci
ZuCiyarki me ya sa tun tuni ba ki fada min cewa
kina son Mr Sameer ba? Www.bankinhausanovels.com.ng
Na gode Allah da ba a yi auran mu da shi ba
hakan ta faru da ba zan taba yafe miki ba, don haka
ki shirya za ki auri Mr. Sameer mutukar ina raye
ko za a kashe ni ba zan iya auran wanda ki ke so
ba, na gode da wariyar da ku ka yi min ke da Ya
Abba ba zan boye muku ba ba ku kyauta min ba. Tana gama fadin haka kuka ya ci karfinta ta
fice daga dakin da gudu.. Tsananin kidima da Ya
Abba ya yi idan ka gan shi a Wannan lokacin sai ka
tausaya masa duk da irin jarumtarsa sai da ya rasa
abin da zai iya cewa da ita, haka ya bi ta da kallo.
Rauda kuwa gadonta ta fada tana kuka domin
furucin Haaana ya daga mata hankali.
Da sauri ya cim mata tun kafin ta fice ya yi
kokarin shan gabanta ya ce, Haana tsaya ki
saurare ni kada mu daga murya su Mmah su san
halin da muke ciki. Yana rike da hannun ta yake
fada mata haka.
Cikin zafin nama ta kwace hannunta ta ce dole
su ji Ya Abba me kuma ya yi saura da za a boye
musu tunda kun yaudare ni kai da kanwarka kun
boye min abin da ya kamata na ji tuntuni sai yanzu
ya zama dole kowa ya ji
Cikin kuka Rauda ta karaso ta ce, Sister ba
yaudararki muka yi ba farin cikinki muke so.
Wane farin ciki kuma Rauda karya ki ke min
ba wani farin ciki damuwa kawai ku ke son sani shi
yasa ku ka yi min haka.
Jin ta fara daga murya ya yi saurin janyo ta
baya daf da dakin Rauda ya ce, Haana kina hauka
ne za ki daga mana murya haka wai ba za mu iya
yin sirri da da ke ba.
Ko ma ina hauka ya Abba to yau na fara,
wallahi wannan abin da ku ka yi min kowa sai ya
fara,
sani don haka ka bar ni na tafi gida. Tana gama
fadin haka ta fisge hannunta ta yi waje a guje.
Tana barin wajen Mamah Me na zuwa ganin
yaranta cikn rudani ta ce Lafiya dai na gan ku
haka, kuma kamar na ji muryar Ammina tana
kuka?
Da sauri Rauda ta zo ta fada jikin mahaifiyarta
tana kuka tana cewa, Mamah yau mun samu
matsala ni da ‘yar uwata ta gaza fuskantar mu ni
da Ya Abba na ga wata irin tsanarmu a fuskarta
wacce ba ta taba yi mana ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ji maganar da muke yi ne ni da Ya Abba.
Nan ta fada mata duk yadda aka yi da yake dama ta
san komai, ta ce ku yi hakuri za ta huce, dama na
Jima da tunanin duk lokacin da ta gano haka da
wuya idan ba ku samu matsala ba a zaton ta kun
ware ta duba da irin shakuwarku da kaunarku,
amma kar ku damu komai zai Zo da sauki Ammi ba
za ta taba yin fushi da ku mai tsawo ba ku ba ta
lokaci.
Kai kuma Yayana ka daure ka ba ta hakuri duk
irin zafi da fushin da za ta yi ka bi ta a haka domin
tana cikin fushin ku, da damuwar da ku ka sa ta
wuce ka je Allah ya ba mu alheri.
To Mamah na gode zan yi yadda ki ka ce,
Rauda ke kuma ki kwantar da hankalinki zuwa
gobe za ki ji yadda muka yi da ita.”
Daga masa kai ta yi tana mai goge hawayen da
suke zuba daga fuskarta. Jiki ba kwari ya yi
sallama da su ya kama hanya ya fice.
Ko da Haaan ta shiga gida ta iske su Ammi falo
dukkaninsu, kafin ta shiga sai da ta yi kokarin
danne damuwarta da yake dare ne babu wanda zai
iya gane yanayin da yakc fuskarta.
Bayan ta yi sallama sun amsa Ammi ta ce, ke
kuma ina ki ka je ki ka yi dare haka?
A Daddafe ta ce Ammi ina wajen Rauda ne ba
ta jin dadi daga nan kuma muka hadu da Fadeela
muna ta hira ban san time ya yi haka ba.
Babu laifi ya jikin nata?
Da sauki, bari na je sama na dawo.
Haka ta wuce a sukwane gudun kada Ammin ta
tsananta mata tambaya.
Da sauri ta shiga dakin ta tana shiga ta rufe
dakin ta fada kan gado tana kuka. Jim kadan ta ji
wayarta na ringing sai yanzu ta tuna ashe ta bar
wayarta a gida tun bayan sun yi waya da Fadcelah.
Ko ta kan wayar ba ta bi ba domin damuwar da
take ciki ta fi karfin daga wayar. Ganin takurawar
da a kai mata da kiran yasa ta yi saurin duba mai
kiran.
Mr. Samcer ta gani jikin kan screen radau ta ji
wani irin haushi da bakin ciki ga wani irin sabon
tsanarsa da ta ji ta zo mata.
Tana kallon wayar ta gama har ta gama kararta
ta daina, ta duba sai ta ga miss called ya kai ashirin
da wani abu tana dubawa ta ga duk shi ne mafi
yawan kiran. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da har za ta kashe waya baki daya sai wani kiran nasa ya ZO.
Da sauri ta daga ba ta cc komai ba tana son jin
mai zaice mata.
Ke Miss Haana wai meye yake yawo a cikin
kwanyar kanki ne da za ki ki daga min wayata na
zo gidan ku don na-ganki ki ka shanya ni ki ka ki
zuwa wai me ki ka dauki kanki ne, haba is better ki
canza mu ajiye dabi’un mu mu fuskanci abin da ke
gabannmu mana.
Jin ya yi shiru da alama yana sauraron abin da
za ta ce da shi. Ta ce, To ka gama naka jawabin
ko, to bari ka ji na fada maka daga yau babu ni babu kai
kada ka kara mafarkin cewa akwai wata alaka ko
dangantaka da za ta kara shiga tsakanınmu gaisuwa
wannan daga yau ta kare tsakanınmu, ka yi nesa da
rayuwa ka fita daga cikın duniyata yadda zan samu
na rayuwa cikin farin cikin.
Ba don komai ba sai don kana so ka raba
KAUNARMU da shakUwarmu ni da ‘yar uwata da
ba ni da kamarta a doron duniyar nan tunda na tasa
ba ni da wacce ta kai ta a gurina, kasan tana son
ka yasa ka ki karbar ta yin soyayyarta ka ce sai ni.
Idan kana so mu shirya doleka koma mata
wallahi ko me za a yi min ba zan taba auranka ba
sai dai a kai gawata gidan ka. Mr Samcer wallahi
na tsane ka ba zan taba daina tsanarka ba har saika
So ‘yar uwata Rauda sannan zan daina tsankarka.
Tana gama fadin haka ta fashe da kuka yana jin
kukanta ya kasa cewa komai. Can ya ce Miss
Haana ki tsaya ki saurare ni mana ki fara bincike
kafin ki jefe ni da wannan maganar tukunna.
“Mr. Samcer na gama magana da kai a kan
wannan gabar ka yi min kawai abin da nake so na
fuskanta don ba ka san zafin s0 ba shi yasa ba ka
tausaya mana ni da na sani ni na san irin halin da
take ciki na azabar so.
Ba ta jira cewarsa ba ta kashe wayarta ta kifa
kanta tana kuka mai tsuma rai.
Safa da Marwa ya shiga yi cikin dakin sa babu
abin da ya godewa Allah a kai da Haana ba ta ji
lokacin da yake maganar cewa har yanzu yana
sonta ba hakuri ya yi na dole saboda farin cikinta.
Kalamanta ne suka shiga yi masa yawo a kunne
inda take cewa, *”Me yasa Abba da Ammi ba su
haifa min Yaya namiji ba wanda za mu dinga yin
sirri kamar yadda ku ke yi kai da kanwarka.
Haka ya dinga jin wannan furucin na yi masa
yawo a kunnensa da sauri yasa hannayensa ya
toshe.
Haana mai yasa za ki fada min wannan kalmar
me yasa za ki yi min haka bayan duk mun yi
hakan ne don farin cikin ba wai don mu cutar da ke
ba.
Dole na samu na fahimtar da ke don ki gane
matsayinki a gurinmu da wannan tunanin ya
kwanta har zuwa tsakiyar dare bai samu ya rintsa
ba, yana ta kullawa da sakawa yadda zai mata
bayani ta fahimce su. Www.bankinhausanovels.com.ng
Can bangarcn Mr. Sameer kuwa ransa ne ya
gama baci da furucin da Haana ta yi masa ya yi
niyyar daukan Zafi. amma da ya tuna yin hakan ba
zai zamo masa mafita ba yai ya yi kokarin danne
ZUCiyarsa domin ya gama fuskantar Haana dama
kadan take jira ta samu ta yi masa, balle sai ga shi
kuma ta samu hujja dole zai yi duk yadda zai yi
don kar ya rasa ta ya same ta ya yi mata bayani don
su zauna lafiya.
Washe gari cikin shiri ta fito don wucewa
makaranta duk a dinning area ta iske kowa na
gidan da yake yaran duk sun yi hutun makaranta
Ya Abba ta hanga cikinsu suna break fast ga
Granny gefensa.
Granny kadai ta gaisar ta sa kai za ta wuce ba
tare da ta kalli inda Ya Abba yake ba. Yana ganin
Zata wuce shi ma ya mike Granny ta ce kai kuma
Ina zaka ka tashi ko ka fasa karyawar ne?
Eh, Granny munyi ne zamu fita da ita ne sai na dawo.
Au Kai da ka san tare za ku fita ka kasa cin
naka tun dazu ko kai ma biye mata za ka yi ka fita
ba ka karya kumallo ba.
Ki ajiye min nawa in na kai ta zan dawo.
Bai jira ta amsar da za ta ba shi ba ta wuce
abin ta cike da mamakin furucin da Ya yi wa
Granny
A fusace ta nufi motarta tanaji yana kiran
sunanta, amma ta yi banza da shi da sauri ya zo ya
sha gabanta.
Cikin fushi yace, Haana wai wane irin sabon
taurin kai ki ka koya ne Ya Abbanki ne yake miki
magana kina ji ki ka yi shiru kina kin kula shi?
Hawayene suka zo fuskarta ta ce “Please Ya
Abba ka je abin ka ban so na ji komai daga bakinka
a yanzu ka bar ni na ji da irin abin da yake damuna,
saboda ban zaci haka daga gare ku ba kai da
Rauda.
Me ku ka dauke ni kuna tunanin ba zan iya
bawa Rauda duk abin da ta nuna tana so a gurina
ba. Kaf cikin zuri’ ata ba ni da kamar Rauda duk
irin muhimmin abin da nake so komai yake a
gurina ta nuna tana so zan iya ba ta shi komai
matsaynsa matukar hakan zai sa ta farin ciki.
Ya Abba
mai yasa ka boye min bayan na san
ka sani cewa Rauda Mr. Samecr take so, no wonder
sai yanzu na kara tunawa lokacin da na fada mata
cewa na kamu da son Mr. Sameer na ga damuwa
da hawaye a fuskarta me yasa ban gane ba, kai
kuma da muka yi maganar dakai ba ka fada min ba.
Saboda ni ba ciki daya muka fito ba ka fi son
farin cikinta a kan nawa?
Tsayawa ya daka mata ya ce Raihana ya isheki
haka kada na kara jin wannan furucin daga
bakinki.
Duk da ta razana da tsawar sai ta yi kokarin
dakewa ta yi murmushin karfin hali tace
Ya Abba tuni na soma sabawa da tsawar ka ba
kai kadai ba duk wanda zai yi min tsawa a yanzu
zan iya jurewa, saboda haka na roke ka da ka bar ni
na tafi makaranta kada ka sani na makara please na
roke ka wannan alfarmar.
Ba zan hana ki zuwa makaranta ba shige muje
na kai ki sai na yi miki bayani ki gane manufarmu
ba ni key din.
Girgiza kai ta yi tana ja da baya, ganin za ta
kawo masa wasa ya kai hannu ya riko ta yana
kokarin karbewa, nan suka shiga kokawa.
Daidai lokacin da Mr. Sameer ya kawo kai
ganin yadda suke kokawa ta shige jikinsa take ya ji
ransa ya baci, wannan shi ne lokaci na biyu da ya
gan su rannan ya ganta ta fada jikinsa yau kuma ga
shi suna wasan kokawa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wato kenan Abba ne ya kunno masa wannan
wutar don ya yi kokarin raba su cikin ruwan sanyi
don ya same ta, haba na yi matukar mamaki da
Abba ne ya fada min cewa wai shi neda kansa
ya ce ya bar minna aura dole yana da wata manufa
a ransa amma irn son da yake gani a kwayar
Idanunsa da wuya a ce zai iya bar misa ita, wani
irin takaici ne da KAUNAR ZUCI suka yi a wan
gaba gare shi bai wani jira ganin bacin rai ba ya
Juya abinsa cikıin damuwa.
Sakar masa key din ta yi ta koma cikin gida da
gudu, bin ta ya yi da kallo fuskarsa cike da
damuwa yana mamakin abin da ta yi masa ya zai yi
ya bi ta, domin bai san kowa ya san da Wannan
matsalar tsakaninsu yake so su sulhunta hakan sai
ga shi Haana tana so ta fallasa kowa ya sani.
Misalin karfe biyar da rabi na yamma mota ta
yi parking a cikin    Dan fillo estate kofar gidan
Alhaji Jafar wanda muke yau ranar Litinin mota ce

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE