BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 7 BY AUTAR MANYA

Tun ma kafin yakai ga fita daga cikin gidan hajja ruwan ya gama jiƙe masa jikinshi sharkaf.
Amman sabida tsabar kafiya da taurin kai irin nashi bai juya ya koma gidan hajja kamar yadda ta bashi shawara ba haka ya shiga cikin motar duk jikinshi ya gama jiƙewa hatta ga saman kanshi ruwan ke ɗiga.
A haka ya tashi motar ya bar layin tafiya yake cikin ruwan wanda hatta fitilar motar shi seda ta dusashe sabida rashin wadatar haske sakamakon ruwan dake zuba kamar da bakin ƙwarya.
Ikon Allah kaɗai yakai Aliyu hotel ɗin daya sauka.
Anan ɗinma ruwan da ake tsulawa yafi na wanda ya baro agidan hajja horn ya danna masu gadi suka tawo aguje cikin lema suka wangale mai ƙaton gate ɗin da sauri ya shigar da hancin motar shi zuwa cikin parking lot na hotel ɗin ya jima yana saƙa yadda zeyi ya fita waje cikin wannan ruwa dubarar kiran Abokin shi nas wanda suka zo kano tare suka kuma sauka a hotel ɗin tare wannan wanda yayi mai magana a tun farkon page ɗinmu na baya, Sedai shi Nas ɗan sanda ne na farin kaya bincike shima ya kawoshi kano dan haka ma tunda suka sauka basu haɗu ba, Dan shi nas zeyi wajan sati ɗaya a kano saɓanin Aliyu daya gama aikin daya kawo shi aranar yau dan banda dalilin gidan hajja ma da tuni ya jima da wuce wa gida.
Wayarshi ya fiddo yana niman numbern nas sedai abin takaici taƙi shiga haka yayita trying amman wayar taƙi shiga tsaki! yaja mai ƙarfi tare da mayar da wayar aljihun jallabiyar yana kallon saukar ruwan ta glasess ɗin motar.
Kashe motar yayi tare da fita waje wanda nan da nan ruwan yayi mai caaa akanshi yana dukan shi.
Da sauri mai kama da gudu yake shiga ciki da gudu ya haye saman benen amman dukkan jikinshi rawar ɗari yake na rashin sabo dan tun asali Ali bayi son ruwa ya taɓashi dukan ruwa na saurin yi mai illah.

Da karkarwa yake buɗe ɗakin daya sauka yana gama buɗewa ya tura ƙofar ya shige ciki ya kunna ƙwai wayar shi ya cillah saman gado da sauri da zafin nama yake ƙwaɓe rigar jikinshi.
Ataƙaice tawul ya ɗaura ya shiga bathroom ya haɗa ruwa mai zafi yana watsa wa ajikinshi.
Wajan mintuna ashirin ya ɗiba kafin ya fito yana zabga atishawa dafe kanshi yayi a galabaice ya sauya kaya zuwa wata jallabiyar mai ruwan toka.

Wayar cikin ɗakin yayi amfani da ita ya kira ɗaya daga cikin ma’aikatan cikin hotel ɗin ya bashi umarnin ya kawo mai black coffee, Ba jimawa yaji bugun ƙofar ya buɗe ya amsa ya koma gefen gado yana kurɓar shi da zafinshi yana kammala wa ya koma bathroom yayi brush ya ɗauro alwalar kwanciya bacci.
Kwanciya yayi saman gado yana dafe kanshi wanda yake mai ciwo ga atishawar daya ke ta faman jerawa gaba ɗaya saman karan hancinsa yayi jajir yana fitar da gumi.
A haka wahalallan bacci ya kwashe shi wanda ko kaɗan baya jin daɗin sa..

 

Hawaye na zuba murmushi na sauka a saman kyakykyawar fuskarta ahaka hajja ta shigo ta tarar da ita.
Tsaye tayi akan ta tana kallon ta cike da mamaki kafin tai gyaran murya tace.
“Ummi lafiyar ki wannan wani irin shashanci ne kina kuka kina murmushi kamar sakarya?”
Hajja take mata wannan maganar bayan ta nemi guri gefen gadon ta zauna.
Turo mitsitsin bakinta tayi gaba cike da sabo da shaƙuwar da sukai da hajja tace.
“Yaya Aliyu ne”
Tafaɗa tana ƙunshe kanta cikin hijabinta.
Murmushi mai ƙayatarwa hajja tayi.
“Me Baffan yayi miki kike kuka da dariya?”
Ta cikin hijabin tace.
“Hajja inna gaya miki zaki yarda?”
Murmushi hajja tayi.
Tare da cewa.
“Haba ummi mahaifiyarki haifarki kawai tayi amman rainonki duk yana hannuna dan kin san ba da ban jarabar ubanki ba da babu yadda za’ai kibar hannuna sabida haka komai kika gayan inna gaskiya ne zan gane inma karya kike zan gane ummi haka kawai Allah ya ɗoran soyayyarki wadda bana wa jikokina dana haifi uwarsu”
Hajja ta ƙare tana dariya.
“Hajja wallahi ban san mai yasa na damu da yaya Aliyu ba tun ma kafin nasan jikan kine naji ina son shi dan Allah hajja ki roƙe shi ya soni”
Tafaɗa tana dunƙule wa waje ɗaya.
Murmushin dake saman fuskar hajja bai gushe ba ta furta.
“Kema kinsan baffa baze ce yana son ki tafarar ɗaya ba sedai muyi masa shigar sauri”
A razane ta ɗago tana kallon hajja dake jefa goro cikin bakinta.
Murya can ƙasa cike da ruɗani ta furta.
“Daman nima nayi wauta nasan ba kowani namijine ze dubi girman ƙaddara ta ya aure ni ba, Dan Allah hajja gaya min hanyar da zanbi domin na kankare faitin dake bibiyata kodan Aliyu ya zama mallakina?”
Tafaɗa tana kuka!
Jan yota jikinta hajja tayi tana shafa gadon bayanta.
“Ummi ba ina jifanki da baƙar magana bane ko ɗaya ni sema daɗin dana ji da kika ce kina son jinina kuma koda kowa ya gujeki wallahi ni bazan gujeki ba! idan har hafsatu ɗiyata ce ta halak! Aliyu ɗanta ne na halak to baya da mata seke ummi wannan karon zanyi masa shigar sauri sedai ko kaɗan bana tunanin Aliyu ze soki sedai yayi maki son tausayi sabida matar shi shu’umar mace ce, sedai kuma ko wace mace akwai tata kalar kirsar ban san taki baiwar ba wataƙil da ita ki janyo shi jikinki”
Hajjah takai maganar tana kokarin miƙewa.
“Hajja na haƙura dashi, Ina tsoron kishiya domin naga zahiri akan Bamu dan Allah hajja karma ki gaya ma Ammi tai masa dole akan ya aure ni bana son yadda mukai zaman boranci agidanmu agidan miji ma na mai maita”
Tafaɗa tana sakin kuka tare da cusa kanta tsakanin kafaɗun hajjah.
“Aifa tunda kika furta kina son jikana sefa kin aure shi rufe bakin ki babu maiji bare ya gani zamuyi abun mu cikin sauƙi”
Hajja takai tana dariya.
Turo baki tayi tare da sakin hajja ta koma gado ta kwanta.
Hajja ce ta fice a ɗakin tana furta.
“Munafuka kyayi kya gama”
Dariya ummul ta sanya tana rufe idanunta bata taɓa zaton komai zezo mata cikin sauƙi ba, Tabbas hajjah mai son ta ce.
Shiko Aliyu koda ze yanka ta gunduwa gunduwa tana son shi zata zauna a haka.
Da wannan tunani bacci mai daɗi ya kwasheta wanda ta jima bata sami irin shiba.
Koda asubahi ma da ƙyar Hajja ta tayar da ita sabida nannauyan baccin daya ci ƙarfinta.
Acikin sujjadar sallarta sosai ta dage tana jaddada neman zaɓin Allah a tsakaninta ita da Aliyu.
Sabida acikin kwana biyun data san shi taji kaf duniya acikin maza masoyan ta bata da gwani azuciyarta kamarshi.
Anan zaune tayi azkar ta miƙe tahau gyarawa hajja ɗakin seda ta kammala sannan ta wuce kicin.
Da kanta take sarrafa abin break fast wanda ta kammala komai tsaf ta jere a center table bayan ta baɗe ɗakin da haɗaɗɗan turaren wuta mai azabar ƙamshi.

Bata da kaya agidan hajja ko ɗaya sabida haka datai wanka seta aika gidansu wajan sadiya ƙanwarta mai bi mata ta amso doguwar rigar atamfa wadda ta matse ta gam

Ta gama komai taci kwalliyar jiran shi tana ta turo baki hajja ta shigo da kallo ta bita aranta tana ayyana lallai iska na wahalar da mai kayan kara.
“Hajja ki kira wayan shi mana harfa 10 ta kusa najishi shuru”
Ta faɗa babu kunya.
Tafa hannu hajja ta hau yi tana.
Cewa.
“Yau naga abin da yafi ƙarfina ni binta wai ummi bazaki hankali ba nikam zan wa hansatu waya akan dole ma a tursasa ɗannan ya aureki karki mace mana”
Shura ƙafafu take tana dariya.
“Amman hajja kika cewa ammi ina son shi zataji wani iri fa”
Tafaɗa tana ƙifta idanu.
“Dama kawai zan nemi auren ne a matsayina na wadda ta isa dashi ummi ina son ki auri baffa kodan ki kawo ƙarshen gwamnatin matar shi marar mutunci na tabbata mahaifiyar shi taji wannan batu zatai matiƙar murnar data xarta tawa,sanan kuma auren baffa ba abu ne mai sauƙi ba dama dole sedai ta silar haɗi amman in dan kanshi ne baze taɓa furta yana son ƙarin aure ba, sabida soyayyar daya ke yiwa matar shi”
Hajja ta faɗa tare da miƙowa ummul wayarta.
Amsa tayi hannu na karkarwa ta nemo numbern sa da aka rubuta.
ALIKO…………

Ta shiga kira wadda seda ta kusan katsewa kafin Aliyu dake kwance saman sallayar dayayi sallar asubah ya ɗauka.
Muryar shi can ƙasa yayi sallama da sauri ummul ta ɗauke wayar daga saman kunnenta sabida yadda taji hucin numfashin sa ya daki zuciyarta.
“Kiyi magana mana ummi karfa kuɗina su ƙare cewar hajja”
Lumshe idanu tayi tare da mayar da wayar saman kunnenta muryar ta na rawa ta furta.
“Amin wa’alaikas salam ina kwana?”
Daga ɓarin Aliyu wanda ke kwance tun da yayi sallar asubahi sabida zafin murar data kamashi ya lumshe manyan idanunshi dasuka ƙan ƙance sabida azabar sarawar kai dake damunshi ya furta.
“Lafiya”
Shuru ya biyo baya.
“Shike nan?”
Taji saukar muryar shi cikin kunnenta.
Ƙifta idanuwa ta shiga yi kafin tace.
“Dama break fast hajja ta haɗa maka kuma tajika shuru koka wuce ne garin ku?”
Tafaɗa a rarrabe tana wasa da yatsan hannunta guda.
Murmushi ya sauke kaɗan yana auna rainin hankalinta wai hajja amman seya basar tare da cewa.
“Ban riga da na tafi ba sabida na kwana da zazzaɓi amman haka nan zan wuce”
Zaro idanu tayi waje tana ji kamar tai tsun tsuwa gare shi cike da ruɗani ta furta.
“Dama ai seda aka ce maka karka fita a ruwan nan shine ka fita ai gaya nan ka kwana da mashash shara”
Lumshe idanu yayi yana sauraran sassanyar muryarta tana magana kamar da sa’anta.
Muryarta ce ta kuma karaɗe mai dodon kunnen shi inda ta kuma cewa.
“Ga hajja zata maka sannu”
Bata jira ba ta miƙawa hajja wadda ta daskare a tsaye tana kallon rashin kunyar ƴaƴan wannan zamani.
Ta amshi wayar tana furta.

“Aliko kai nakeji kana baka da lafiya?”
Daga kwancen daya ke yayi ɗan murmushi a karo na barkatai tare da cewa.
“I Hajjah kinga ruwan jiya fa yayi mani mugun duka!”
Yafaɗa yana dafe saman kanshi.
Daga ɓangaren hajja tace.
“Ai daman kafar kanka Aliko seda nace akwai ɗaki anan ka kwana kaƙi yan zu dai ka zo kaci abinci anan kasha magani”
Murmushi ya sauke mai sauti tare da cewa.
“To hajja zan lallaɓo na zo amman kisa ma min shayin citta”
Yafaɗa tare da katse wayar.
Hajja mita tahau yi na daman tasan tun yana ƙarami baya son ruwa shine ya shiga ga ciwon shi mai naci.
Ita dai ummul da ido take bin hajja tana auna yadda hajja ke tsananin son jikan nata sabida yadda taga duk hankalinta ya tashi.

Da ƙyar yana rangaji ya ƙarasa wajan trolly bag ɗinsa ya fiddo da wasu haɗaɗɗun ƙananun kaya rigar fara ce ƙal mai gajeran hannu se baƙin wando ya sanya su ajikinsa waɗanda sukai mai tsananin kyau suka amshi kalar fatar shi mai tsananin sulɓi da kyawun gani.
Ya ƙarasa gaban mirrow ya fesa turare key ya ɗauka da phone ɗinshi ya kulle ɗakin ya fita.
Kiciɓis sukai da Nas wanda yaketa sauri shima daga gani fita zeyi sukai musabaha suka jera atare suna ɗan tattaunawa har zuwa gaban motocinsu kowa ya shiga cikin tasa suka kama hanyar gate.
Tuƙi yake da ƙyar da kuma taurin zuciya wayar shi ta ɗauki ringing ganin numbern Abbah yasan ya yaɗan rage gudun tare da katsewa ya kirawo shi.
Gaisawa sukai Abba yayi kamar bai san Aliyu yayi tafiya ba, shima sabida tsabar kunya bai iya cewa abban yana kano ba haka sukai sallama A ɓangaren abba yana wa yaron nashi addu’a akan Allah ya sauya mai lamarin shi da alkairi.

Zurfafa yayi da tunani bayan sun gama waya da abbah na yadda a yanzu sam baya kula da mahaifan shi duk da Abba nada kuɗin daya fi nashi amman ai suna da hakki akanshi sau tari koda ya fito daga office idan yayi niyyar shiga gidan Ammi su gaisa seyaji ya shafa’a seyayi gida suna gari guda seyayi wata baije yagan su ba.
Tsananin damuwar daya shiga ta ƙauracewa mahaifanshi daya ke a kwanakin nan se hakan ya ƙara mai ciwon kai wanda kafin yakai gidan hajja ko gani ma da ƙyar yake yi Allah ne kawai ya ƙaddara ze isa gidan hajja lafiya.
A galabaice yayi parking yana dafe kai ya isa bakin gate ya buga salame dake wanke-wanke a tsakar gidan ta wanke hannunta da ruwa ta isa ta buɗe masa tana ganin shi ta russuna tana gaishe dashi wanda da hannu ya amsa mata tare da raɓeta ya wuce ciki.

Ƙasa-ƙasa yayi sallama acikin falon yana mai zubewa saman three seater ya miƙe ƙafafunshi akai hannu ɗaya dafe da kanshi.
Da sauri ummul dake zaune tai tagumi ta ɗago tana amsa sallamar shi wadda seda tai ta maza kafin ta fahimci abin da ya furta.
Ganin shi a kwance ya sanya gabanta faɗuwa da sauri ta ƙarasa bedroom tana kiran hajja sedai kash ta mance fa ashe bayan hajja ta gama mitar ta fita ta siyo mai magani wanda ta bar mata sallahun idan yazo ta sauke shayin data ɗora mai a kicin ta zuba a cup ta kai masa.
Hakan yasa ta juya kicin ta haɗo mai abincin data ɗauke ɗazu takai kicin ta aje sabida rashin zuwan da bai akan lokaci ba, A tire ta haɗo komai ta zo gabanshi ta aje a nutse.
Ido ta zuba mai tana kallon saman fuskarshi wadda idanunsa suke lumshe harya faɗa ma sabida yadda baya jin daɗi.
Kamar zatayi mai kuka ta furta.
“Sannu ka sauko kasha tea ɗin na sirka maka dan karka ƙone da zafi”
Idan ya tanka mata to kujerar daya ke kai ta tanka.
Sake matsowa tayi dai dai saitin kanshi.
Tsintar kanta tayi da ɗauke hannunshi daya ɗora saman kanshi ta mayar da gurbi da nata hannun.
Da sauri ta janye tana ɗan zare idanunta waje.
“Wai zafi kamar wuta sannu”
Ta faɗa nan ma bai magana ba.
Ta shi tayi har tana harɗewa abin tausayi( kai soyayyar bala’i ce )
Ta nufi toilet ɗin hajja ruwa mai sanyi ta taro a bawo ta saka tawul ƙarami ta fito.
A gaban shi ta aje jikinta se rawa yake ta sanya hannu cikin ruwan ta matse tawul ɗin taɗan matsa kaɗan ta yadda bazasu haɗe ba ta ɗora mai tawul ɗin akan shi tana goga mai.
Bakinta yaƙi mutuwa har lokacin sannu take faman zuba mai kamar zata ari baki.
Seda ta taɓa kan taji babu zafin sannan takai bawon ta dawo ta zauna gabanshi tayi tagumi.
A haka salame ta dinga shigewa tana jera kwanuka a kicin harta gama aikinta tai mata sallama ta wuce.
Seda hajja tai wajan mintuna ashirin kafin ta dawo gidan tana ta masifar wai mai chamist ɗin ya riƙe mata canji boska ta siyo mai maganin ciwon kai.
Ta zube a ƙasan carfet tare da zame gyalen ta tana cewa.
“Ummi ɗauko ruwa a firji yasha maganin”
Kamar wadda ƙwai ya fashewa ta miƙe ta ɗauko ruwa marar sanyi tazo ta miƙawa hajja tare da cewa.
“Hajja ai bai ci komai ba”
Salati hajja ta hau yi.
“Haba Aliko kai daman a zahiri ma baka fiye son kaci abinci ba bare kana ciwo tashi zakai kaci abinci ga maganin nan na siyo maka kasha dan Allah karka je gida da sauran lalura”
Tausayi tsohuwar ta bashi na yadda duk ta damu.
Sannu ahankali ya yunƙura yana cije bakin shi ya zauna sosai idanun shi ƙurr akan ummul…………

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE